Showing 42001 words to 45000 words out of 68990 words

Chapter 15 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

nata ya zuba mata idanunshi da suka narke dan jaraba irin tasu ta maza musamman ma sabon ango.
"Ɗanyan gwal. Barka da shigowa cikin rayuwata da fatan zaki kula dani fiye da irin kulawar da kika bani a baya? Ki ɗaukeni tamkar jariri sabuwar haihuwa kinga kuwa yana buƙatar kulawa mai yawan gaske. Ɗan wannan zaman da nayi dake a yanzu ya sake dulmiyani cikin soyayyarki. Mata ma suna suka tara ashe?, bari in fito fili in fyeɗe miki biri har wutsiya. Tunda nake ban taɓa shan yawu mai ɗanɗanon naki ba, haka ban taɓa jin fata mai nagartar taki ba, ga ɗumi, madallah da samun ki a matsayin abokiyar rayuwata." Murmushi Bilkisa tayi tace.
"Amman Gwanda ni gaskiya bazan iya shiga bayan gidan tsakar gida ba, ni tunda nake ban taɓa amfani da bayan gidan gargajiya ba. Kuma kamar ni Gwanda sai kawai a ganni na fito zan je wanka? Ina gaskiya bazan iyaba wallahi, su Anty Zinaru ma sunyi magana, ni ina ganin zan yima Dady magana kawai ya kama mun haya kusa da asibiti kawai, daman hakan yaso, amman ganin ka fi sha'awar haɗe mu waje gudane yasa na tausheshi har ya haƙura" Zama Kaila ya gyara yace.
"Kin fi ƙarfin wannan bayan gidan ai Ɗanyan gwal. Ki kwantar da hankalinki zan sa a yanka miki banɗaki a cikin uwar ɗakin ki, sai dai bazai kasance babba ba sai kiyi haƙuri kafin in ƙarashe ginina, ke zan fara kaiwa gidan ki zaɓi in da yayi miki. Amman kafin azo a soma aikin bayan gidan sai ki yi amfani da nawa na cikin turakata, ni kaɗai nake amfani dashi dama, zan yi gaggawar ƙarashe sabon gida, wannan da muke ciki ma inaga a kasuwa zan sa shi, kuɗin sai in ƙundume a sabon gidan, wannan sabon gidan dama dake ya dace, da ace tun farko na tuno da batun sai da wannan tsohon gidan, da yanzu ma muna sabon gida." Jin za'a tayar da salla ne yasa Kaila ya miƙe cikin kasala.
"Ɗanyan gwal bari in je sallah kinji har za'a shiga Masallaci. Ga keyn turaka zaki iya komawarki can, waɗannan ledojin ki tafi dasu" Yana gama faɗar haka ya ajjiye mata keyn turaka ya fice. Da Hajiyayye yaci karo a tsakar gida, bangazarta yayi, yayi ficewarshi yana faɗin.
"Aikin banza aikik wofi duk jarabarki ke baki isa kin hanani shan man Amarya ba" Nan ya barta a tsaye tana cizon yatsanta, dan data ganshi hanya ta tare mishi. Bayan sallar magriba ta kafa ta tsare tana jiran shigowar Kaila domun ta mayar mishi da martanin cizon yatsan da yasa tayi. Shinkafa da miya da nama da latas take ci. Sai taji haf door ɗin ɗakin Amarya yayi kara, juyawar da tayi tayi tazali da Bilkisa cikin wasu fararen riga da wando masu shegen kyau, kanta babu ko kallabi fuskarta sai sheƙi take faman yi. Take numfashin Hajiyayye ya nemi dakatawa, yuu daga ita har Hindatu suka bita da kallon mamaki. Far tayi da idanunta tace.
"Barkan ku dai da gida" Ba ta yi maganar domun lallai sai sun bata amsaba, duba da yanayin sigar ta tayi maganar, kuma tana yi ta nufi turakar Kaila. Ɗan mabuɗi tasa ta buɗe ɗakin ta shiga. Hajiyayye bata dawo daga cikin duniyar mamaki da ruɗu ba Amaryar Kaila ta sake fitowa daga turaka ta nufi ɗakinta.
"Lallai da gani wannan amarya bata da kunya, har tsakar gida bako kallabi, ace amarya daga kawoki har kin soma nuna isa da turakar miji." Ƙuta Hajiyayye tayi. Bilkisa ta sake fitowa daga ɗakinta da ƙaramin akwatinta ja na aure. Tasa kwaɗo ta datse ɗakin nata tayi shigewarta turaka. Abincin da Hajiyayye ta kasa ƙarashe ci kenan. Ajjiye kwanon tayi ta shige ɗakinta.


Hajiyayye:
Tunda ta shiga ta kasa zaune ta kasa tsaye. Kishi kawai ke ɗawainiya da zuchiyarta. Bata san sanda ta fashe da kukan baƙin ciki ba. Bata taɓa tunanin Kaila zai ji marmarin yin wani aure nan kusa ba. Domin a tunaninta da kuma abinda Kaila ya faɗa mata a yayin da yake kan karagar sonta cewa yayi. Tani bata iya gamsar da sha'awarshi in ya shigeta baya ko jin alama, sabida yawan haihuwa ta zama fanko maras amfani a gado. Shi yasa yake son yayi auren kece raini, kuma yana sha'awar mace wayayya wacce zata latatashi a shinfiɗa so yake a dinga lasarshi kamar alawa, kuma mai jin turanci da iya gaye yake so. Hajiyayye tayi tunanin itace mace mafi soyuwa a zuchiyar Kaila, ganin tayi dai_dai da irin macen da Kaila ke ra'ayi. Duk da cewar ita iyakarta sakandare ne kawai, amman tana ɗan jin turanci kuma tana iya mayarwa babu laifi, kana ta iya rubutun turanci, kuma tana karance_karancen littafin Hausa. Tun tana gidansu take bama Kaila dukkan kulawar da yake buƙata. Sau biyu Kaila na kwanciya da'ita a wani shagon abokinshi. Ya kuma nuna mata babu wata mace a zata iya kere mata a matsayi. Sai gashi tun kafin aje ko ina ya nuna mata kalarshi. Zama tayi a kujera tana tuno ranar da Kaila ya fara ribatarta ya jata zuwa shagon abokinshi, ranar daya rabata da darajarta kenan. Irin kalaman soyayya da irin alƙawarurrukan da Kaila yai mata a wannan ranar abun ba'a cewa komai. Kuka ta sake fashewa dashi tace.
"Kaila ka cuceni. Amman wallahi bazan barka kaci amarcinnan lafiya ba, saina ja maka masifa" Wata zuchiyar tai mata gargadi da cewar.
"A'a Hajiyayye kar garin kishi kije zuchiya tasa ki aikata abunda zaki zo kina ɗan daka ce baki aikata ba." Shiru tayi tana nazari. "
"Tani ko tana ɗakinta kamar bata ma gidan. To wai wacce iriyar zuchiyace a ƙirjin Tani, ita bata san ciwon kanta bane ko yaya? Na tatama Tani rashin mutunci da cushen baƙin ciki iri_iri. Amman a tsakanina da'ita sai dai tayi mun murmushi kawai. Tana cikin wannan sambatun Kaila ya ɗaga labulen ɗakin nata, ya zuba mata mayaudaran idanunshi yana nazartar yanayinta.
"Ni zan shiga daga ciki Hajiyayye babu wata matsala dai ko?" Ai Hajiyayye dama kamar jiranshi take ya dasa aya ta miƙe."
"Ai ba sai ka zo kayi mun sallama bane zansan cewar zaka kwana da mace ba. Wanne darene jemage bai gani ba, ƙila itama ka gama shan romon amarcin nata tun daga zauren gidansu, ba girin_girin ba dai tayi mai" Idanun Kaila har ƙanƙancewa su ka yi dan ɓacin rai, ita kanta Hajiyayye data kalleshi sai da tasha jinin jikinta. Amman a zuchiyarta kuma taji sanyi sosai da taga ɓacin rai a shinfiɗe a fuskarshi. Harararshi tayi ta ƙule ƙuryar ɗakinta ta barshi riƙe da labule yana mata kallon mamaki." Dariyar mugunta yayi, bai bi ta kanta ba ya ƙule turaka wajan amaryarshi. A wannan daren Kaila ya tsunduma wata duniya iriyar duniyar da bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba. Me yasa? Sabida wannan shine karon farko daya ɓare matarshi ta sunna dal a leda. Hajiyayye ba wai bai sameta a cikakkiyar budurwa bane, ko ɗaya. Sai dai kawai sun gudunar da kwanciyarne babu nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare dasu. Kuma kasancewar tasu bata zama mai armashiba domun sun kauce ma shari'a( Ƙalubale a gareku ƴan mata masu miƙa ma saurayi kai tun kafin a shiga daga ciki)
Duk wata hadda dake kan Kaila a wannan daren sai da Ɗanyan gwal ta kankare mishi

Tani:
Bayan nayi sallar isha, sai na shiga tunanin yanda zaman gidannan zai sake yi mun zafi. Amman inason da zaran Allah ya saukeni lafiya in tashi tsaye domun cikar burina. Duk da nasan fitowar burina ka iya haifar da matsaloli masu tarin yawan da ni kaina bansan su ba. Amman gani nake yi muddin naci gaba da rayuwa a haka haƙiƙa baƙin ciki da damuwar gidan Kaila ce zata zame mun ajalina. Kaila ya mayar dani tamkar wata jakkar gidansu. Dangin Baba Rammai babu mai ganina da kima, Hajiyayye wanne irin baƙin cikine bata cusa mun ba, ga Amarya kuma bansan ita da wanne salon tazo ba. Ni duk wannan fafutukar inayi ne domin yarana, bana fatan abinda zai sa in tsallake in barsu, nasan babu mai iya kularmun dasu, ƙarshe gararamba zasu ci gaba dayi a anguwa kawai. Wayata ce tayi ƙara ta katsemun tunanina. Yaya Use ke kirana, nayi mamakin kiran duk da dai dare bai yi sosai ba, goman dare ne.
Assalamu alaikum Yaya Use kece da daddarennan haka, Allah yasa dai lafiya?" Dariya Yaya Use tayi daga ɓangarenta tace.
"Babu komai. Inno ce tace in sanar miki gobe zamu tafi ashe ba jibin ba. Tace kizo da sassafe, mun samu mota har gida. Lauwali maƙocinmu direban bektira ɗinnan motarshi zamu bi har Shanono in sha Allah. Yayi mana sauƙi sosai, sai ki soma shiri tun yanzu sai da safe" Sallama tayi mun ta datse wayarta babu shiri na miƙe na shiga zaƙulo kaya. Kayan da Habiba Bala ta bani na ciri kala uku na saka a jaka. Sai lokacin na jawo ledar data rarraba mana a wajan taron. Sabulan wanki dana wanka ne a ciki, sai omon wanki, da turaren wuta, da humra, harda turaren ɗaki na fesawa da ƙaton basilin. Murmushi nayi na jinjina kaina lallai Habiba Bala akwaita da kirki. Kayana dana Hauwa na haɗa tsab, na ware mana wanda zamu saka in zamu tafi, a lokacin wani bacci mai nauyi yayi gaba dani, bani na farka ba sai asuba. Fitowa nayi ina hamma gefe_gefen bakina duk yawun bacci, idanuna kuwa cike da kwantsa bana ko iya buɗe idon sosai. Banɗaki na faɗa na kama ruwa na fito. Ina tsakar gida ina alwala Kaila ya fito da sauri ya fita zuwa Masallaci. Ina gama alwalar na shige ɗaki nayi sallah, na fito na hura wuta dan in ɗaura ruwan wanka. Hindatu ma ta fito tana bakin rijiya tana jan ruwa. Kaila ne ya shigo gidan, boll yayi da butar da nayi alwala na barta a kan hanya. Taje ta haɗu da garu ta fashe, da ido nabi butar, sannan na dawo da kallona wajan Kaila Wanda shima ni yake kallo rai a ɗaure, ni kuwa ko a jikina.
Ina kwana Kaila, an tashi lafiya, ya kwanan baƙuwa?" Jin na ambaci kwanan baƙuwane yasa Kaila ɗan sakin fuska har ya iya tsayawa muka gaisa.
Dama inason in roƙi alfarma, amman ban samu ganinka irin haka ba sai yau" Sai nayi shiru.
"Ina jinki mana Shanono ki faɗi abunda kikeson faɗa, na bar ƴar mutane ita kaɗai a ɗaki"
Shanono dama zamu je dasu Inno biki. Kuma yau zamu tafi shine nake neman izininka"
"Ba Shanono zaku ba, ko bangon duniya zaku je shanono ƙofa a buɗe take, duk inda kike son zuwa ba sai kin tambayeni ba kije abunki" Yana kaiwa nan ya wuce ya barni da sakakken baki.
To me Kaila yake nufi dani ne, duk inda nake son zuwa in yi tafiyata ba sai na tambaya ba, sai kace wacce take zaman kanta?" Kai na gyaɗa kawai na juye ruwan wankana a bokiti, a gurguje na ɗan diddirza jikina na watsa ruwa na fito. Hauwa nayi ma wanka na shiryata tsab. Har Yaya Use ta soma kiran wayata. A gurguje na saka kaya na fito da jakar kayana da jakar mata ta zuwa anguwa. Ɗakina na rufe na shiga cikin gidan nai ma Hindatu sallama, na bata sallahun faɗama Hajiyayye in ta fito. Gidan Sabira ma a tsaitsaye na shiga nayi sallama da yaran, na ba Sabira key ɗin ɗakina na nufi gida.
Na isa gida na samu har sun shisshiga mota, Baffa yana daga ƙofar shiga gaba dafe da Habu sai faɗa yake yi.
"In dai Tani ce kun santa da shauni, Inno shi yasa nace muku aba Lauwali haƙuri ya kaimu gidan nata mu ɗakkota acan." Inno tace.
"To Baffa faɗan ya ƙare ga Tanin nan ta iso sai mu tafi, kai kuma Lauwali kayi haƙuri kasan sha'anin lafiya da mata" Shiga motar nayi, Baffa ma ya shiga gidan gaba shi da Habu. Sai da mota ta soma tafiya sannan muka gaggaisa, Baffa yace.
"Abokan nawa suna gida, na ɗauka zaki riƙo hannun Inno ƙarama a tafi da'ita." Dariya nayi nace.
Suna gida Baffa na barsu, ita kanta Hauwa dan dai babu mai riƙe mun ita ne da har da ita zan bari."
Muna tafe munata taɓa hirar ta zumunci. Hakan ya tuno mun lokacin da muka yo ƙaura daga garin kogi zuwa Ibadan, a lokacin mabaratan koji basu fiye samun kuɗi ba, manyan mabarata daga cikinsu suka zauna domun neman mafita irin su Baffa dan Baffa na ɗaya daga cikin manyan mabarata masu ƙarfin iko. Kasancewar daɗewarshi a bara da gogayya da yarika iri_iri. Allah sarki rayuwa, mun sha yawo gari_gari yawon bara, hakanne yasa babu wacce a cikin mu tayi ilimin addini, mun dai samu na sallah a wata makarantar almajirai, muna jin yaruka da dama, domin duk garin da muka je da irin harshensu muke bara, ko da dai ba zamu iya doguwar hira da yaren ba, zamu iya roƙonsu. Kuma waɗanda ba musulmai ba sun fi ƙoƙari wajan bada manyan kuɗi ma mabarata fiye da Musulmai. Sai kaga Alh ya tsaya a ƙatuwar motarshi, mabarata sun rufeshi ana mai bara. Amman bazai wuce ya raba sababbin nera ashirin_ashirin ba, masu ƙoƙarin ciki suke raba hamsin_hamsin. Haka ƙwaƙwalwata tai ta yawo dani a cikin labarina, wani abun inna tuno in yi ƙwal_ƙwal, wani abun inna tuno na yi murmushi, wani kuma babu yabo babu fallasa. Motarmu tai ta lulawa, misalin sha biyun rana muka ɗan dakata a wani ƙauyen da bansan sunanshi ba. Baffa ya sai mana abinci. Shinkafa garau_garau ce ya siya mana akan wani ɗan tallah. An yi mata zubin ɗari_ɗari, kowa ya ɗauki ƙwano ɗaya. Wata rumfa muka nufa anan muka yi zaman dirshan. Hauwa na sakko daga baya, sai da ta ƙoshi sannan na ci abincin na bi da ruwan leda guda ɗaya. Inno tace.
"Baffa ni kam zan kama ruwa, kaga Shanono daga nan da tafiya sosai, gara in rage marata, Indo muje ki rakani mu nemi wajan ciyayi haka sai in yi." Ai Inno na faɗin haka duk muka miƙe ko wacce da guntun fitsarinta ga mararta. Wani gida muka samu daga bayan wasu rumfuna, a gidan muka kama ruwan, sannan muka shiga mota, bamu tsaya a ko inaba sai a Shanono. Idanu na lumshe na shiga tuno irin rayuwar auren dana gudanar a shanono, duk su ka dinga dawomin. Tuno da Dauda ɗana ne yasa na ɗan saki ajjiyar zuchiya. Baffa ne ya katse mun tunanina da cewa.
"Inno acan gida zamu sauka, jiya ina wajan bara Jafaru ya kirani, nace ya buɗe ɗaki ya ƙyara mana. In yaso ko zuwa yamma ai sai ku kintsa kuje gidan Deluwan ko?" Inno tace.
"Tunda ka yanke hukunci ai shikenan Baffa. Amman ni kam ai so samuna daga nan sai gidan Deluwa, ana can anata sha'anin biki ka sani. Tun shekaran jiya ya kamata ace na iso garinnan fa haba Baffa" Da ihu_ihu Baffa yake magana kamar faɗa irin na makafi, sake ƙwalla muryar tashi yayi yace.
"Da wannan tulin tsarabar kike son ki je gidan biki, shingin duk abi a sace, bazai yiwu ba. Use nuna mishi hanya kinji mu je unguwar Shakogi." Yaya Use tace.
"To Baffa. Lauwali kwana zaka yi, ka miƙe har gaba da ceɗiyar can. Kana yin kwana gidan kenan"........
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 13




_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU👇🏻👇🏻

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻










Bansan sanda na fito zauren kamar zautacciya ba. Idanu muka haɗa da Kaila, ya jefe ni da wani kallon tsana.
"Nayi ɗan daka ce ban je masallacin ƴan taya na ganku a wajan bara ba. Nayi nadamar wannan haɗuwar tamu na farko. Na auro mata marar tarbiyya ƙazama, wacce babu abinda ta sani sai ƙazanta da haihuwa, ga gayyar kuɗin cizo. Ki faɗama Yarki ta bar mun gidana wallahi in ta ƙara shigo mun gida kotu ce zata raba ni da'ita. Ke kuma zaki ga irin mummunan hukuncin da zan yanke miki akan wannan aika_aikar da kishi ya rufe miki ido kuka yi. Nan gaba ni zaku kashe ba ɗana ba ai" Jikina tsuma yake ta ta yi. Kuka kawai nake yi, Yaya Use kuma ta yi kasaƙe tana kallona, bata ce komai ba tasa hijabinta ta ratsa ta gaban Kaila ta fita, har jikinsu na gugar na juna, dan Kaila ya ƙi matsawa, ita kuma na santa da zuchiya, dan Yaya Use asalin irin halin ƴan jagora gareta, girmane yasa ta yi sanyi. Namiji kuma ya ƙara seseta mata nutsuwa. Da harara Kaila ya bi yaya Use.
"Aikin banza aikin hofi. In banda tashanci taya wannan buhun fulawar zata yi faɗa da Hajiyayye in ba dai dama shiryawa su ka yi ba. Ke kuma na dawo gareki Shanono." Nuna ni yake yi da ɗan yatsa jikinshi har rawa yake yi, tunda nake ban taɓa ganin Kaila a cikin ɓacin rai makamancin wannan ba. Ba shiri na durƙushe a gabanshi ina kuka. Hannayena na haɗe waje guda cikin sigar ban haƙuri. Amman Wallahi in buɗe baki in yi magana na kasa. Babu irin zagin da Kaila bai yi mun ba, ya buɗe baki yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login