Showing 30001 words to 33000 words out of 68990 words

Chapter 11 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

yankin daya dace, sai suka yanke shawarar ci gaba da zama a wurin tare da dabbobin nasu. Bayan samun wurin da ya fi dacewa sai SHANU ya yanke shawarar komawa baya kaɗan don gabatar da garin Shanono ya bar JAULERE ɗan uwansa a wurin. (JAULERE TA YANZU) ya zo ya kafa aikin sa (riga) a garin shanono na yanzu har zuwa yanzu Rijiyar taushe a shanono. Garin a halin yanzu ana ganinsa a zahiri. Ga jerin mutane da sarakunan da su ka milki Shanono. Kabiru isyaku ( ɗan shanono na yanzu dakaci shanono) akwai Hakimi. Tun da Shanono ta zama ƙaramar hukuma suka fita daga ƙaramar hukumar Gwarzo a 1989 sunansa Alhaji Bello Abubakar kambun bunun Kano daga 2004 zuwa yanzu. Shanono na da yanki na 697 km2 da yawan jama'a ² a ƙidayar 2006. Lambar gidan waya na yankin ita ce 704(1) manyan mutanen garin sun haɗa da marigayi Alhaji Ibrahim aka Ibrahim ( ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Barau (Ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Haruna Muhammad Shanono. Mariga Alhaji Bawa Mashin (Man0mi) marigayi Ɗan Anni ( Ɗan siyasa) marigayi Alhaji Haruna Naganga ( cocas chairman) marigayi Alhaji Shehu Shanono. Farfesa Nura ( masan kwamfuta) dandalin matasa na shanono ( ƙungiyar ci gaba) da dai sauran fitattu a Shanono da lokaci bazai bani damar jero su ba.

Shanono:
A daidai ƙofar gidan su Baffa Lauwali ya tsaida motarshi. Ai kuwa Baffa Jafaru, da Baffa Yusuf suna gano mu suka miƙe daga kan kututturen da suke zaune, suna shan iska a kasan bishiyar durumi. Rana ake kwanɗawa sosai da sosai, matasa gasu nan daba_daba sunata afkin fira, kasancewar da rani ne, babu noma sai kiwo."
" Naroro, Inno kune da tsakar rana haka, maraba da baƙin birrni. Use, Karime, Tani, Habu, Indo. Sannunku da hanya. Babban direba sannu" Da murmushi a fuskata nace.
Barka da gida Baffa Jafaru da Baffa Yusuf." Baffa yace.
"Kuna gida baku je aikin hatsi ba Jafaru, ko su Tanimu kuka tura?" Inno tace.
"Lauwali mu je ciki kaci abinci, in kayi sallah Allah bashi sai ka kama hanya. Jafaru muna da kaya a mota ku shigo mana dashi ku da su Use." Inno tayi shigewarta ciki, tana ta cogala ƙafarta. Tausayi ta bani dan ƙasar da zafi sosai, gashi ko takalmi babu a ƙafar Inno. Allah ya hore mini in sai ma Inno keke ta huta da zafin rana, ko sanda." Da tulin kaya muka shiga babban gidan mai yalwar filin tsakar gida da yalwar matan gida da yaran gida. Dan Baffa su rai ashirin cib mahaifinsu ya haifa malam Jauro Ja'e. Kuma a cikin ƴaƴa ashirin ɗinnan macen su ɗaya ce itace Goggo Ige. ( Hausawa na kiran sunan Ige ne ga macen da ta biyo maza zuryan)
"Ah Inno maraba lale kune da rana haka, an tawo biki ko? Tani ashe ƙafafuwanki zasu sake taka ƙasar garin Shanono idanunki kenan?" Inji Baba mai riga matar Baffa Jafaru, mace mai faram_faram da son zumunci kenan. Dan duk da yawan yawonmu baisa ta dena ziyartarmu a duk garin da muka ya da zango ba. Ɗakinta ma ta ja mu baki ɗayanmu. Baffa kuma su Baffa Jafaru suka janyeshi shi da Lauwali. Bayan mun zauna mun sha ruwa. Nan fa ɗakin Baba mai riga ya cika maƙil da matan ƙannen Baffa, da sabbin idandunan da ban sansu ba, da yara rututu. Gaisuwa da taɗin yaushe gamo yaƙi ƙarewa. Da ƙyar muka yakice mu ka rama sallah. Baba mai riga ta saukemu da kwaɗon ganyen dimkin yaji albasa da ƙuli. Baba Marka ta kawo mana damammiyar fura da nono wacce ta ji zuma. Kowa ya bar gida gida ya barshi. Haƙiƙa garin Shanono garine mai tsaiwa a rai sosai. Suna da son zumunci, da son taimako. Kuma bugu da ƙari kusan kowa ɗan uwan kowane a Shanono. Inno tace.
"Oh Marka ni ko banga matar Katagi ba, shi kanshi Katagin ban ganshi ba" Ɗan dariya Baba marka tayi tace.
"Wannan yaron ai yana legas da iyalin nashi, ya samu aiki a wani babban gidan abinci. Shekararshi guda da tafiya, wallahi dawowarshi gida na uku, sai Baffansu ya bashi shawarar ya tafi da ita iyalin nashi." Kasancewarshi Ɗan fari a wajanta yasa tai mishi alkunya da wannan yaron, kamar yadda yazo a al'adar malam bahaushe. Hausawan zamanin da an sansu da yakana da kunya, haɗe da kawaici da kara. Amman kwaikwayon al'adun wasu ne yasa tamu al'adun suka samu tawaya, daga wannan lokacin mace macen aure yayi yawa a ƙasar Hausa. Gabana ya yanke ya faɗi da jin an ambaci Katagi. Katagi ya nuna kwaɗayin aurena a fili, ni kuma Allah yana gani tsanar da naima Narani ce ta shafi Katagi, da tuno da Kaila da nayi, da irin kulawar da Kaila yake bani a dai_dai wannan lokacin muna matsayin saurayi da budurwa kuma a lokacin soyayyarmu da Kaila tayi zurfin da bazan iya juya mishi baya ba, kuma ina jin maganarshi fiye da maganar kowa a duniyata. Allah yayi Kaila mutum ne shi mai daɗin baki da iya tsara zance. Daga baya ne na gane ashe tantirin gogaggen mayaudarine. Gashi da iya ɗaukar wanka aljihu babu ko sisi. ( Wannan kuma ɗabi'ace ta samarin Jos. Allah yayi da dama a cikinsu mayaudara masu iya layancewa. Bugu da ƙari akwai iya wanka ba ko tasi a aljihu. A jos ne zaku ga gaye iya gaye, yayi wanka iya wanka, amman yana kan titin salisu Adamu yana tafe ɗai_ɗai kamar bazai taka ƙasa ba. Jasawa ayi haƙuri nima ƴar Jos ce na rayu a Jos sama da shekaru ashirin, nasan komai ). Muryar Baba mai riga ce ta katseni.
"Uhm Inno ai Katagi ya zama babban mutum, gonakin shi a shanono ai sunyi goma. Kuma duk nomesu yake yi tsab, irin wannan yanayi na rani yake fitar da abincinshi cikin garin Kano. Yananan yana ɗanɗasa gida a gaba dasu Tabawa kaɗan. Kuma yaron gashi da zuchiyar yi, in ya tashi yo aikennan baki gani ba, baya mancewa da kab iyayen nashi. Yama kusan ƙarin aure, mai Anguwar anguwar gabanmu ya bashi babbar ƴarshi." Ni dai nayi tsumu_tsumu dani. Su kai ta rabtako zancen Katagi da irin samunshi. Baba Marka ce tace.
"Tani ai ko Dauda yana yawan zuwa gidannan. Su Tasi'u ne abokan wasan nashi. Kinsan Narani ya sashi a gareji, to garejin nasu yana nan anguwar. Amman an kwana biyu baya zuwa wallahi. In ce dai zaki daure ki mance da duk abinda ya faru kije ki ga ɗanki ko shima zaiji daɗi? Tani rayuwar haƙuri akeyi, wallahi duk wacce kike ganinta a cikin ɗakin aure. Imma babba ko yarinyar mace, zaman bazai yiwu mata ba madamar batai haƙuri ba. Yara_yaran cikin gidannan da suka ɗaɗɗauko mata. Kusan rabinsu da kwata du sun yi saki, sakin fa a cikin ƙabilar Hausawa ya zame ma mazan kamar wani ado. Face maza na gari da suka kasance sun san abinda suke yi. Kuma ba rashin addini ba, ba rashin kyawawan al'aduba, face watsi da mu kai da koyarwar Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama, mu kasa ƙafa muka shure al'adunmu, muke hanyen turawa da mutanen kudu waɗanda addini da al'adarmu suka banbanta. Mu da ƙabilar Hausawa bamu san wani yawan mutuwar aure ba. Sai kiga mace sama da shekaru saba'in tana tare da mijinta na lalle. Ta ba gamu ba mun doshi shekaru sittin a ɗakin aure, ɗuwawu duk ya dame da kashi, amman anata bugawa dai. Ke mu fa a al'adar malam bahaushen da, ko anguwa bama fita da rana. Da asussuba muke fita, sai dare ya rufa muke dawowa. Ko kuma mu fita da daddare. Sabida kunya, da killace mace irin na malam bahaushen da, ba irin na yanzu ba." Take kawaye ya soma shatata a kumatuna. Sufa duk a ganinsu, nice nake ƙure duk mazajen da nake aure har take kaimu ga macewar Auren. Da an magana suce mace tayi haƙuri. Sai hawan jini ko ciwon zuchiya ya rabketa ta mutu suce Allah yayi, kwananta ne ya ƙare. Alhalin baƙin ciki ne yai sanadin katse mata numfashinta. Wani sa'in macen ma nason ta zauna a gidan nata duk rintsi duk wuya, amman mazajen basaso, duk hakkinta daya gama ɗauka, da gallaza mata daya dinga yi, bazai isheshiba hakan, sai yayi mata tukuicin saki, wata ma harda tagonashin duka, ko karɓe yaro, irin yadda Narani yayi mun akan Dauda. Inno tace."
"Kune iyayen nata ku dai sake faɗa mata. Dan ubanta ya lashi takobi a wannan karon in ta kaso aurenta, to ba dai gidanshi ba, ba dai Shanono ba. Kuma ita tasan waye Baffa, shi a makafin ma kafiyarshi irin ta kutarece, ga mitar tsiya. Dan a yanzu haka nasan Tani bata ƙi wannan auren ya kuma turguɗewa ba. Kullum tazo gida da abinda zata ƙirƙiro ta faɗa. Sai da uban wata rana data tawo raɓe_raɓe da ciki da goyo wai tayo yaji. Wallahi dukan da Baffa yayi mata ban zaci yarinyarnan gata ba zata haihu a take a wajan ba dan tsabar duka. To da taji fa babu daɗine shine ta dena ƙorafi shekara uku kenan. Sai dai kullum a rame kamar ita ake yanka ana miya" Kuka nake rerawa mai fitar da amon muzanta da tozarta. Jina nake wata ta daban a cikin ƴan uwana mata. Dangi duk sun bugamun hatimin rashin zaman aure. Wasu ma suna kirana da mai auren sha'awa. Wasu suce mun mai ruwan ido. Sunaye maras daɗi dai. Akuyata ta riga da tayi kuka a cikin dangi. Nina kafe tarihin aure biyar, bana fatan wata ta kafa irin tarihina." Baba Marka daga baya su kai ta rarrashina. Inno kuwa wanka tayo ta shirya tsab, tana rabon tsaraba tana sake jaddada musu labarun da in haddace sun riga da sun daɗe da haddacewa. Yadda suke ji, da irin halin da suke shiga, da irin tsangwamar duk da suke shiga in ina gabansu ina zawarci. Wai me yasa iyaye da jama'ar gari basa yi ma BAZAWARA uzirine? Har ta gama rabon tsarabar batai shiru ba.
"To ni kam zan wuce gidan bikinnan. Ke Tani Karime ta raka ki ku je ku dubo Dauda. In yaso kwa same ni a can gidan bikin zamu tafi da su Use. In shi Naranin ya amince muku sai ku ɗauko Daudan ya ɗan zauna dake kafin mu tafi. In bai amince ba ku bar mishi abunshi" Ajjiyar zuchiya na sauke, naji sanyi a raina sosai. Tare da adda'ar Allah yasa Narani ya amince ya ɗan bar mun Daudan mu ɗan zanta" Da haka muka shirya. Na cire tsarabar da nayo ma Dauda na kwancen kaya da takalmi na riƙe. Muka kama hanyar Unguwar Marabutawa. Muna kusantar gidan ina hangoni a lokacin danai fitowar ƙarshe babu ko mayafi balle kallabi. Ina kuka, ina ambaton Ɗana kar ka raba ni da gudan jinina Narani" Abubbuwa da yawa suka shiga yi mun yawo. Bansan sanda na yar da ledar hannuna na wuya ba. Ji nayi na fasa shiga cikin wannan gidan mai ɗumbin tarihi, gidan da anan matsalata ta soma. Gidan dana zama ɗanya ina wari sabida wanka da ruwan sanyi da ɗanyan jego. Gidan da na kusan rasa hankalina tsabar damuwar ɗa namiji."
Kuka nake yi mai ciwo, irin kukan wacce ta fama wani babban gyanbon daya daɗe yana ruruwa a ƙasan zuchiyarta. Yaya Karime ce ta dafa ni.
"Haba Tani wai ke dan Allah ba kya mantuwane? Duk abunda ya faru ai ya riga da ya faru. Yanzu yaro muka zo gani, Narani bai isa ya koro mu ba, bai kuma isa hana ki ganawa ko keɓewa da ɗanki ba. Ki cije mu shiga gidannan ki ga ɗanki. Ki sani shima yana da hakki a kanki, ba kya tsoron shi yaron ya girma ya dinga tunanin kamar kin watsar dashi ne?" Numfashi naja, tabbas shima yana da hakki a kaina. Hawayena na share zuchiyata da hantar cikina nata kaɗawa haka muka shiga gidan a bisa jagorancin Yaya Karime. Sai na tuno sanda aka kawoni gidan a matsayin Amarya, su Baba marka na cewa in shiga da bismillah kuma da ƙafar dama. Duk wani taku dai dai yake da bugawar zuchiyata. Sallamar Yaya Karime ce tasa hankulan matan gidan ya karkato izuwa garemu. Na san da dama, da dama ban sansu ba, basu sanni ba. Sai dai nayi imani ba zasu gaza samun labarina ba.
"Sannun ku, mun same ku lafiya?" Cewar Yaya Karime. Kallon ƙuda muke yi ni da Ta Maulidi. Tana ganina ta datse annurin dake shimfiɗe a kan fuskarta, tsaki taja taci gaba da dakan masarar yin tuwo, wanda ya zama ta'adar gidan. Fiddausi da Ɗausiyya matan ƙannan Narani ne suka ce.
"Tani ashe rai kan ga rai, umman Dauda ashe baki mance da mu ba?" Ɗan murmushi na ƙaƙaro cike da ƙarfin hali da juriya nace."
Ba gashi yau rai ya ga rai ba. Ɗausiyya na same ku lafiya ya bayan rabuwa?"
"Sai Alkhairi Tani. Ku ƙaraso daga ciki Iya mai Fura tana ciki" Naga mun gaggaisa da kowa cikin fara'a banda Ta Maulidi wacce take ta waƙa tana shilla taɓarya tana cafewa"
"Ina wuni Ta Maulidi, na same ku lafiya?" Harara Yaya Karime ta zuga mun tace.
"In ma ba lafiya kika same su ba, meye naki?" Ai Yaya Karime na faɗar haka Tamaulidi ta soma tafi tana dukan cinya. Habaici da gori dai mun shashi, ƴaƴan mabarata. Da kyar na jaye Yaya Karime muka shiga ciki. Iya mai Fura tana zaune tana cura fura muka shiga da sallama. Idanunta ƙifi_ƙifi duk ya dame irin na tsofaffin fulani. Amman ras Iya mai Fura ta gane mu fes. Bayan mun gaisa Iya mai Fura tace.
"Tani ni na ɗauka kin haƙura da Dauda ne ai. Kin tafi babu ko waiwaye, kuma ke iyayenki fulanin tashi ne, ballantana mu mu neme ku mu kai muku shi yayi ziyara. Inno dai tana zuwa ganinshi duk randa ta shigo Shanono. Kuma ana kawo mishi saƙo, kuma ana faɗa mishi daga wajan gyatumarshi ne. Wacce Fatsumar ce a bayanki?" Yaya Karime tayi dariya tace.
"Wannan Hauwa ce ba Fatsume ba?" Baki ta turo tayi zunɗe harda kashe ido tace.
"Duk shegiyar ɗarin ce, itama tsohuwarce ita ta haifi gyatumina" Dariya muka yi dukkan mu. Tace.
"Tamaulidi ta nuna muku Daudan ne? Yanzu ma ya gama bacci a tsakar gidan fa"
A'a bamu ganshi ba" Tashi tayi tasa ƴan uwanshi nemoshi a waje. Fura ta dama ta bamu."
"Ai yana ko almajirci a can wani ƙauye mai nisa, yanzu haka ma sun kusan tafiya. Dan sauran ƴan uwan nashi ma har sun yi gaba. Sun ɗan jima a Shanono wannan karon, tun fa damuna suke, an ƙare noma abinci ya dawo gida, sai azamar komawa bakin karatu" ƙirjina naji ya doka da ƙarfi data ambaci almajirci, yanzu Daudan ne yake ɗaukar nauyin cin shi da shan shi da lafiyarshi? Bakina na rawa nace.
Ai na ɗauka yana zuwa makarantar boko, ta allon na ɗauka makarantar malam babba zai yi ai Iya?"
"E hakane, hakanne ya dace kuma. Da har ya shiga makarantar yana aji uku a firamare, sai uban yace bazai iya ba ya cireshi, sakamakon faɗuwa jarabawa da yake yi. Kinji yadda akayi, ko a ta allon fa bai da ƙoƙari ƙannenshi ma sun wuce shi, amman shi shekara guda yana wai Abasa wata wallah. An sashi a garejin ma, ogan ya hana shi zuwa baya gane komai sai shegen wasa da niman tsokana a cikin Dauda. Ga yawo" Tana cikin faɗar haka wani ɗan yaro ya shigo da yagaggun kaya, yayi futu_futu, sai jan ƙafarashi yake yi. Ga sumar kanshi daka gani kasan fulanine, amman kora ta cinye fatar kan."
"Tani kin ganshi nan ja'iri. Ga uwarka tazo dubaka" Ƙura mishi idanu nayi, ina jin motsin sonshi a dukkan jikina, wani irin so nake yi ma Dauda so irin na yaran fari, so irin na uwar data soma haihuwar ɗanta ta buɗe idanu ta ganshi a matsayin mallakinta fid duniya wal akira. Shima ni yake kallo tamfar ya sanni. Fuskarshi ta yaiwatu da fara'ar data kusan karya kuzarin dana aro na yafa. Sai nake ji kamar bazan iya tafiya in bar Dauda a cikin garin Shanono ba. Hannu na miƙa mishi.
Tawo gun ummanka Dauda" Dariya yayi har wawalonshi ya bayyana, da halama famfara ya soma. Cikin ɗingishi da yanayi na azabar ciwo ya iso gareni. Riƙe mishi hannu nayi dam. Siraran hawayene suka gangaro a idanuna. Ji nake sake rabani da Dauda a karo na biyu tamkar zare mun munfashine, ma'ana nabar doron duniya. A halin yanzu hankalina ya dawo kan Dauda, kuma inason in da so samu ne yaci gaba da rayuwa a gabana, in sashi a boko, wala Allah ko su sa samu damar cika mun burina, tunda ni aure, da yawan yara ya danne burina."
Baka da lafiya ne Dauda, na ga ka kasa zama?" Runtse idanu yayi yana ta ƙoƙarin son zama, amman ya kasa. Cikin nutsuwa na miƙar dashi tsaye na juya bayanshi, na ga jini a bayan rigarshi. Gabana ne ya yanke ya faɗi ras. Hannuna na rawa na ɗaga mishi rigar, wandonshi ma da jinin a jiki. Zuchiyata na tsalle na sa hannu zan zame wandon nashi, cike da tsoro Dauda ya riƙe mun hannuna.
"Innata da zafi karki cire mun. Kema irin abinda Alh Zangina yake yi mun zaki mun? Ciwo nake ji" Rugujewa zuchiyata take shirin yi. Cikin fitar hayyaci nace.
Ba irin abinda yake ma zan yi ma ba, gani zanyi, naga jini a wandonka" Iya mai Fura tace.
"Kaji mun ɗan baɗo, zaka cika mata hannu ko sai na buge hannun da sanda?" A firgice ya cikan hannuna. Jikina a mace na zare mai wandon ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ƙyar. Abunda na gani ya gigitamun lissafina. Tunanina ya gurɓace. Fata_fata takashin Dauda take, ga wani irin mugun wari, ga ɗiwa, harda tsirarin tsutsotsi in ba dai haukacewa nayi ba.
Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun kawai nake ta faman ambato. Yaya Karime ta fashe da kuka. Ni a wannan lokacin wallahi kukan ma ƙin zuwar mun yayi.
"Tashi Tani maza mu tafi asibiti kar yaronnan ya mutu. Iya ku kuna ina wannan al'amari ya faru, ɗan mutum ya ruɓe ba ruwanku. A ruɗe Iya tana kuka tace"
"Wallahi bansan komai ba Karime Tani. Bari matar Shehulle ta fito kuje" Ba wanda ya bi ta kansu. Yaya Karime ta goya Dauda a bayanta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login