Showing 27001 words to 30000 words out of 73133 words

Chapter 10 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5425

shimfide a bakin kofar dakin,
Minnatu na kwance kan gadon daga can cikin dakin itakuma Anty na zaune kan cushions din da aka jera cikin dakin, zee ta karasa ta aje mata a kan glass center table din mulmulalle mai kyau sannan tace "gashi Anty", sannu shine amsar Anty sannan ta dora
"Kinga naga falourn yayi kura dan share ki goge" zee tace to ta fita ta hau aiki, ba laipi yana da fadi falourn dukda set daya na kujeru ne cikinsa amma akwai wahalar shara ga bangaren dining, abu kamar wasa haka Anty tai ta saka zee aiki ita ko sedai tace to, itace ta musu komi a gidan
Yanxu haka ma girkin abincin rana ta sauke, babu komi cikinta sai tea data dan kurba da biscuit, tayi serving kanta nata abincin ta bar musu nasu a warmers dan Anty bacci ma take minnatu kuma na wanka, karfe 5 na la'asar minnatu ta kammala duka shirinta ta dubi Anty dake zaune kan cushion din dakin ta miqe kafa,
"Gaskiya girkin dazu yayi dadi, ke kam anty kin samu cook a bagas"
Anty tai murmushi "tsuntsu ne daga sama gashasshe Allah ya aikon"
duka suka saka dariya...
Minnatu ta kammala nata shirin itama ta tapi, Sanda zee sukai waya da Anty hawwer ta sanar mata duk abinda ke faruwa cikin gidan
Haquri shine abinda Anty hawwer ta bata da fadin "kiyi mata biyayya Zee karki sake ki nuna mata wani abu dan in kinyi mata ba faduwa kikai ba, ki bari ku rabu lpia dan ko kinyi mata rashin kunya ma babu abinda ze kareku daga ke har ita"
Wanke_wanke, Shara, goge goge a takaice duka ayyukan gidan zee keyinsu, wanki ne kurun Anty keyin abinta a washing machine
Ranar litinin ma saida zee taiwa Anty aikin gidan sannan tayi nata shirin na makaranta, saukinta ma tapiyar ita kadaice kuma yanxu a sharada suke dukda akwai er tazara amma ba kamar daa da suke darmanawa ba,
Dayake lecturenta na yau ma safe ne amma practical C.O dinta ne
Ta dora labcoat kan kayanta ta shiga lab din, bayan sun kammala practical dinne ta fito ta nemi wayar zeena,
Kina ina? Ta tmbya zeena tace ina class amma lecturer'n ma bezo ba da alaama bazezo ba,
okay zee ta fadi
Sannnan ta nemi layin hudiyya, hudiyya ta dauka tana fadin "zee ina kika shiga ne" ta fada muryarta kasa kasa alamun bataso ajita
Zee tace kardai akwai lecture hudiyya tace "eh mana munada embryo mana tun 9 ya shiga yanxu saura 1hr ya gama" ganinan to....


Tai tsaye a bakin kofar ajin tana jimamin shiga, kofa daya ce da class din kuma ta gaba babu yadda zata shigaa ba'a ganta ba kuma dole ta gaban malamin zatabi,
Wannan gaurayayyen arabian scent ya daki nostrils dinta lokacin iska ta kado zee ta juya gefen hannun damanta inda ta hangeshi yana cigaba da tahowa iska na karkada gyalenta da kayanta suna yawo, he's dressed in a pure white male Nigerian kaftan well ironed, walking majestically, his right hand buried in his pocket...
Ganin da tayi yana nufo inda take yasata saurin dauke idanunta daga kallon datake mishi, ya karaso yana mai shafa beard dinshi da gyaran murya, zee ta daga kanta tana sake maida kwayar idanunta kanshi a karo na biyu,
Cikin cracky voice dinshi yace "Assalamu alaikum" ta janye daga kallanshi zuwa gurin datake hange wasu korayen flowers, sannan ta amsa mishi sallamarshi
"It seems we re on the same plane... we late"
Zee ta jijjiga kai, tace "u also part of the embryology class?" Ya dan lashi lips dinshi sannan ya gyada mata kai,
Ta dan saki fuska "so am not alone" yace yes am also not alone" sukayi murmushi duka har nashi ya fidda sauti,
Suna nan tsaye babu dadewa malamin ya fito har ya gama...
Karfe 12 na cika zeena ta kirata lokacin tana tare dasu hudiyya cikin theatre suna dan duba lecturen da aka musu, zeena tace "hey latecomer" zee tayi silent smile dinta as always tace "ina department" "okay hurry up mu hadu a cafteria yunwa ze kassheni" zee tace "okay my chop_chop" saida suka karkare karatun da hudiyya sannan tace mata "muje cafteria zeena tana can" hudiyya tace no kuje banjin yunwa, to dayake dama they're not dat close yasa ta wuce
Tana shiga cafterian taji presence dinshi a ciki, ta soma waige waige inda zata hangeshi, he's calmly seated, hannunshi daya rike da waya a kunne yana magana amma idanunshi suna kanta tun sanda ta shigo, suna hada ido gabanta ya yanke ya fadi, ta sauke idanunta kafin ta sake dagasu amma sai ta chanja musu direction, hannun zeena ta gani yana flying a sama hakan yasa ta karasa inda take jiki a sanyaye,
Already zeena tayi ordern sakwara da miyan alayyahu dan har ta soma ci, ta dubi zee "kin zauna kinyi shiru ke dai matsalarki dabance a rayuwa wlh" zee ta dubeta kurun bata damu ba sai kai lomomi take, "me zakiyi order? Dan nasan shegen iyayinki inyi miki order ki yarfani kice bakici kowanne abinci a gurinki beyi ba se naki" zee tace "easy mana duka wannan surutun fa ko so kike se kin kware" zeena ta tabe baki ta cigaba da aikin cin abincinta,
Zee kuwa gabadaya jinta take a takure dan ko tantama batayi tasan kallonta yakeyi, tai tagumi.... tanaso ta juya ta kalli bari dayake amma bataso su hada ido, suna nan zaune taji kamshin nashi ya matso kusa da ita, ta daga kanta ta ganshi gefenta yana tafiyarshi cikin izza still yana magana a waya har ya fita,
Kin sanshi ne? Shine furucin zeena sanin da taiwa aminiyar tata kallo be cikin dabi'arta balle har ta bi mutun kuma namiji ma... Yaddaa take batason alaka da mazan,
Zee ta sauke numfashi ta kalli zeena "i donno, i just feel like i know him, its like we re connected" zeena ta kurama zee ido "are u okay?" Zee tayi banza da ita dan tasan shaqiyancinta,
Ta saka bayan hannunta tana taba wuyanta tana cewa "Allah yasa ba fever ya kamaki ba kike sambatu" cikin sanyi zee ta cire hannun zeena daga wuyanta
Zeena bata fasa zuba ba
"Yau zee kike maganan wani saurayi ai na dauka kece zee dake tsoron mu'amula da samari" zee ta girgiza kai kurun ta kyale zeena...


Sauran lectures dinsu akace duka babu dan haka zee ta kama hanyar gida zeena kuma tana class time din
Koda ta isaa gidan ta tadda Anty a falour suka gaisa ta wuce daki tai refreshing sannan ta fito neman abinda zata saka a cikinta danko la'asar ma yanxu ne ake kira, girkin daren ranar ma zee ta yishi gabadaya dai komai anty ta sakar mata ita keyi
Akwai rashin sabo nayin ayyuka masu yawa haka bayaga zirga_zirgan makaranta hakan yasa zee battajin dadin jikinta sosai
Yauma kafin ta fita lectures haka saida ta kammala ayyuka dukkuwa da jikin nata ba dadi zazzabi kadan takeji da dan ciwon kai wanda kan haifar mata da jiri lokaci zuwa lokaci
* * * * *
Zee ta samu guri ta zauna tana fidda haki na gajiyar tapiyar da tai dukkuwa daba wata doguwar tapiya bace cikin department din nasu ne daga class zuwa lab,
Ta dan dago kanta da kyar jin gaurayyyen kamshin turarukanshi, ta bude idanunta da sukai ja alamun ciwon kai, yana tsaye kanta, a hankali ya jawo kujerar stool ya zauna kamin ya mata cikakkiyar sallama,
Cikin makoshi ta amsa sallamar tashi ta ko yaushe,
"Zainab" ya fadi very low and cracky,
Zee da mamakin yaa akayi yasan name dinta ta dubeshi, tana mai sauke hannunta daga kanta, saidai kanta taji ya sake sarawa ta maida kanta kasa tana mai jin ciwon kan,
Wat is wrong with her"? Tambayar da lab attendant din yayi yana mai dubansu sanda ya karaso kusa da su
"I think she's not okay sir" saurayin ya fada cikin jimamin yanayin daya ganta,
"Take her to the clinic then" lab attendant ya fada in i don't care manner
Okay sir shine furucin saurayin sannan ya durquso kanshi saitin kunnenta kadan yace "zainab can u walk?" Tace yes a hankali
Okay let me accompany you to the clinic...
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 19: Lonely


Tafiyar suke sunayi suna hutawa, tun kan su fita a department ta miqa mishi wayarta tace "pls ka kiramin bes, yace okay password? Ta fada mai yayi unlocking sannan yayi searching sunan da akayi saving da bes yayi dialing, kira yayi sau biyu amma ba reply, yace she isn't picking" ta amshi wayar tana jimami da tinanin ina duka suka shiga yau ba zeena ba hudiyya dan tun da tazo school yau basu hadu da hudiyya ba ko lectures batazo ba balle zeena da ba tare suke lecture ba gashi kuma bata picking call,
Suna fita wajen department, yayi waving wata mota dayaga tana tapiya, mai motar ta karaso ya mata bayanin "mara lpiace zata taiamak sukaita clinic" tace okay"
Zee ta shiga baya shikuma ya shiga gaba dayake clinic din nada nisa daga cikin school,
Bayan anyi examining zee ne doctor ya mishi bayani da cewa "its just stress ba wani abin damuwa bane" ya musu prescribing magunguna da en advice,


* * * * *
Zee ta dube shi ganin zasu rabu kuma bata san koda sunanshi ba,
A hankali tace "Ammmm nace ba...."
Ya watsa mata lazy eyes dinshi cikin nata, still yayi pocketing hannayenshi
"Ur name?" Yace sorry ban fadamiki sunana ba, Am *faruq usman jabbar*... "Nice meeting u faruq"
Yayi shaking head dinshi and at once his face displayed a stunning smile, precised....
Daga haka ta shiga mota driver yaja


Karfe 6 harda mintuna, ta shiga falourn Anty, tana zaune tana karkada kafa, ko gaisuwa bata bari sunyi ba
"Zainab kinga lokaci kuwa karfe nawa yanxu, wato nagane nupinki dan kada kiyi aiki shine kike zuwa makarata ki shantake, to in bakiyi ba nice zanyi miki aikin, muna zaune tare dole kece zakiyi" ta karashe tana mai jan tsuka,"
Zee dai sam bata fadan Anty take ba ta jikinta take, ta karaso gaban anty ta tsugunna ta bude jakarta ta fiddo magungunan, tace "clinic naje Anty banda lpia" sannan ta jawo hannun Anty ta saka a wuyanta"
Jikin Anty yai sanyi "to ai da sekimin bayani mana sannu, jeki watsa ruwa zakiji daidai se kisha magungunan kizo ki bar girkin zan samu wani abu me saukin nauyi naci, kema sai ki duba ko flakes ne kisha"


Ta sake juyi kan katifar tata,
She just can't get him off her mind, oh Allah his voice, his looks, his dress his matured sense of humor, just everything about him "Faruq" tai furucin dayayi daidai da karan wayarta, ta jawo wayar tana tinanin Anty hawwer ce
Ganin da tai na sabuwar number yasata jinkirin dauka, amma se tai picking ba tareda tace komi ba,
Kamar koyaushe dai wannan cikakkiyar sallamar tashi yayi mata, voice dinshi so cool and cracky as always,
Saida zee ta danyi gyaran murya ta saita numfashinta sannan ta amsa mishi sallamarshi,
"Yaya jikin naki en mata"
zee tai murmushinta mai sanyi tace "Alhamdulillah, yace good masha Allah"
Ina fata kinsha maganinki kuma kinci abinci zee ta amsa mai da yes duka nayi,
Itace ta dora da tmbyar "ina ka samu number ta? Kuma ya akayi kasan sunana and wanne department kake?"
"Okay okay, duka zan amsa miki su but bari ayi one by one,
First na samu numberki ne daxu bayan kin tapi... A gurin wata friend dinki, i think hudi... Something ne name nata"
Ohh hudiyya zee ta fadi
Yace "yes tazo tana tmbyata kina clinic ne ance mata nine na rakaki so i told her u hav already left, dats wen i asked her of ur number.... Ina fata bayanina ya gamsheki"
Zee tace um
Good... Sunanki kuma nasanshi ne sanda kikayi mana lecture a biochemistry hall na CHO"
Zee tace "ohh yes"
And nikuma a same department muke nida ke, na shigo ne with D.E in case ma zakice baki sanni ba a baya i recently joined u guys"
"Kin gamsu ko?
Tace eh na gamsu kuma nagode akan dazun nan,
Yace bakomi ai ba wani abu bane
Zee tace wani abu ne mana "u sacrificed ur practical class" kai kadai ne ka iya wolunteer ka kaini clinic"
Wannan ba wani abu bane ni a gurina ki manta ma ya faru,
Daga haka sukayi sallama yana mata Allah ya kara sauki


Xxxxxxxxx


Cikin ikon Allah zee ta tashi tana maijin karfin jikinta
Tana kitchen tana hada musu break ne ta jiyo hayaniyar Anty da alama waya takeyi
"Wallahi ya_bilki bazan bar gidana ya mutu babu inda zee zataje, in kuwa ba haka ba nima ba inda zani wallahi"...
Itadai zee ta fito danta kammala ta taddata a falour ta miqe kafa tai shiru alama bayani akeyi mata a wayar, sai kada kai take
"To shikkenan zan gwada hakan amma idan fa yaqi yarda sedai yayi haquri shima"... Itadai zee ta wuce ta hau shirin makaranta harta gama ta wuce
* * * * * *
Tai tsaye bakin lecture hall din, "lallai.ta bakin zeena ne na zama typical late comer" ta sake jaddadawa kanta,
Tana so ta shiga kuma tana gudun wulaqancin malamin,
Daga ido tayi tana tunanin mafita, sai ta yanke shawarar samun guri ta zauna, gefen class din tayi saboda sanin da tai akwai kujeru gurin, koda ta karasa shi kadai ne zaune yanata faman pressing phone dinshi idanunshi da hankulanshi gabadaya sunaga abinda yakeyi,,, tayi sallama ta samu guri dan nesa kadan dashi ta zauna, A hankali ya dago yana kallanta, sai kuma ya dubi wrist watch din dake daure a wrist nashi, ya maida kallonshi kan wayar yana nodding kanshi kurun,
Zee ta shiga laluben wayar hudiyya saidai bata dauka ba harta tsinke, se kuma sako ya shigo
"Wlh kar ki shigo dan malamin beda kyau yanxu se ya manna miki C.O yace kinyi disrespect ing dinshi, gara idan be ganki bama..."
A sanyaye ta sake karanta sakon kamar wacce tai mantuwa cikin sakon,
Muryarshi ta tsinkayo yana fadin "nikuwa na dauka nafi kowanne dalibi makara ashe duk makarata ma kekam kin fini"
Ta daga kai ta dubeshi hmm shine abinda kawai tace
A ranta tace "yau da ace Ammi nada rai da hakan sam bazata faru ba, gashi tundaa aka dawo semester kowacce safiya sai na makara Allah yaji kanki Ammi, uwata gari," ko kadan batasan tana zubda hawaye ba saida taji damshinsu a kuncinta,
Ta dubeshi ganin ya taso ya nufo inda take, ta saka hannu tana goge kwallar idanunta
"Kiyi haquri i don mean to hurt u zainab"
Tayi nodding "i know nima ba maganarka ce ta sakani kuka ba na tuna Ammi na ne"
Ya sauke numfashi kadan
"Ur mom?" Ta daga mai kai, yes d best mom in d world" yai murmushi yes mom are d best
Itama sai ta tsinci kanta da murmusawar,
"But i hav loose mine she's gone forever, Allah ya jikanki yaaa_ummee (يا امي) " ya fada in a broken way
Ta sake dagowa ta kalleshi "innalillahi, u also lost ur mom?," yace
"Yes tun banyi hankali ba, i was just 8 then.."
"I also lost my Ammi recently, not only her but i lost my Abbah too" she donno why kawai saita tsinci kanta da rufe fuskarta tana kuka
She felt as if they just died, and dis new environment she's into, she don't like it at all,
"yes is okay u cry my dear, but they need ur du'a, more"..... Tai nodding kawai


* * * * *
Tun 1 suka gama lectures, sauran duka practicals ne kuma ba'a soma su ba,
Sanda taje masjid tai sallah, sam bata bukatar saka wani abu cikin cikinta, she just needs to be alone, tasan idan ta koma gida yanxu aiyyuka na babu gaira Anty zata dinga kwakulo mata
Earpiece ta samu ta toshe kunnuwanta sannan ta dauki hanyar zuwa library,
Tana zaune tana juya pen din hannunta "her life now?, she's totally not herself, ta zama tamkar wata 'yar aiki a gidan Anty siyama, bawai bata aiki bane no takanyi girki ma ammi da, kuma tana share mata daki ta wanke toilet, amma wanke wanke, wankin kayanta wannan duka bai cikin aikin datakeyi, she terribly missed Ammi plus Anty hawwer," kodayake bakomi komi ze wuce amma da kamar wuya....
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 20 & 21 : crushing my crush


Can i sit?
Ya fada yana kallonta, Zee ta daga kai tinaninta na katsewa, yana tsaye yayi folding hannayenshi a kirji yana lumshe ido time to time, song din datake saurare a earpiece dinma harta kare bata sani bama, ta zare earpiece din,
Yaja kujera ya zauna dukkansu suna kallan juna, littafin dake gabanta ya jawo yana kalla,, "physiology?" Ya fadi bayan ya gama duba littapin yana kallanta, bata kalleshi ba amma tanajin me yake fadi,
So tell me something about the blood and body fluid (physiology course)
Zee ta daga kai a sanyaye ta dubeshi
Ta girgiza kai "i donno" ta fada a takaice kuma a hankali
"Are u okay?" Ya tambayeta saboda yanayinta
No am not ta amsa shi a takaice
Ya dora duka hannayenshi kan desk din yana sake kallanta a tsanake
"Wats wrong with u?"
Ta kalleshi a takaice kuma ta janye kallanta ta sunkui da kanta,
"So wats even wrong with me?" Ta fada cikin ranta
Kamar mai counting words yace:
"La haula wala kuwwata illah billah".....
Furucinshi yasaka ta dagowa tana dubanshi cikin son neman karin bayani
"Dats wat u re supposed to say"
A duk duniya babu wani abu mai bakinciki muddin ka rabu da iyaye lpia kuma ka kyautata tsakaninka da ubangijinka da mu'amularka da mutane, zainab ki dena barin abu yana zama cikin ranki har yana wasa da farincikinki, duk abinda ya dameki akwai wasu da nasu ya ninka naki, mene ma abin bakinciki ko damuwa a gareki, da kike daa cikakkiyar lapia kike bakida nakasu kina da ilimi daidai gwargwado, da sauran abubuwan ni'ima daa Allah ya hore mana"
Kalamanshi sun zo a daidai gurbin daya dace, kuma sun samu karbuwa
To mene ma na dorawa kai damuwa a rayuwar da karewa zatai, rayuwar da Allah ne ke da iko akan komai, rayuwar da rabonka bai wuce ka,"
Zee ta sauke numfashi "Allah ya bamu wucewa lpia" furucinta kenan dayaja hankalinshi gurin faadin Amin
Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login