Showing 39001 words to 42000 words out of 73133 words

Chapter 14 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5414

dundu,
Say it quick pls"
Zee tace dama rannan da kikace am beautiful dagaske kike ? Zakiyya tayi wani murmushi,
Faruq ya fadamiki same abinda nace right?
Ta gyada kai, "ni a nawa tinanin irinsu Anty hawwer ne kyawawa da irinsu..." Se kuma tai shiru bata karasa ba,
"Minnatullahi ko?" Ta gyada kai how do u know ita zan fadi?" Zakiyya tace
"Saboda mostly haka mutane ke gani, ina nupin idan kai ba fari bane to ba kyakkyawa bane, yawanci anfi alaqanta farare da kyau, saboda nasu kyawun yafi daukar ido da hankali dats attraction, amma irin naku kyan daban ne, u re unique, ko colour din skin naki ma abin kallo ce dan koni akace na fadi category din skin colour naki faduwa zanyi cos baki cikin farare kuma baki cikin bakake, irin naku silent beauty din se masu idon basira suke gani"......


Sunyi resuming karatukansu cikin ikon Allah kuma komai yana tafiya daidai, da farko faruq ne ke zuwa daukanta da kanshi kuma ya maidata amma se ta hanashi tace ya dinga maidata kawai tunda akwai mota a gidan, basu dade da komawa ba akayi pasting result, bata shiga school ranar ba hakama faruq dan indai daya beje ba to dayan ma haka,
Shi da kanshi ya kirata lokacin tana kitchen tana girkin abincin rana cikin annashuwa, Anty siyama ce ta kawo mata wayar,
Gashi wayarki na ringing tun dazun (ta barta a falour ne) ta dauka batareda ta damu da wani banzan kallo da anty siyaman keyi mata ba,
"Soulmate An kafe fa" ajiye serving spoon din hannunta tayi ta nemi guri ta jingina,
"Dear me muka samu?" Yace zan miki sending ta whatsapp, ta bata rai "ni banason wannan jan ran naka kawai ka fadamin in banyi abin arziki ba ai shikkenan" a hankali yace "soulmate komai na Allah ne, kuma kowa rabonshi ze samu," faduwar gabanta ta tsananta
"Kin samu clear pass nima haka" ya karasa fada yana kyalkyalewa da dariya, itama dariyar ta saki sannan ta furta Alhamdulillh
Ba karamar kwarinta faruq yayi ba dan kuwa 4 point ya kawo itakuma 3.7 dukansu suna upper, wannan news yayiwa Anty hawwer dadi ba kadan ba, A bangaren faruq ma ya sanarwa Anty safiyyanshi, yace ta fadawa dady, itadai Anty safiyya fadi kawai take lallai zainab Alkhairi ce FUJ ka kula da ita dan Allah"....


A karshen satin akayi sadakar cikar shekarar rasuwar Ammi da Abba, tareda faruq akayi komai, sai zee taji tamkar ta samu faruq ne a madadinsu,


Wataranar litinin zee ta shiga school da safe basuyi waya ba, tun jiya da yamma dayace mata zai tafi birthday din wani friend dinshi, tana falour wayarta tai ringing ta dauka tana murmushi ganin sunan faruq kan screen din, bayan sunyi en gaishe gaishe kamarr kullum yace "soulmate, zanje birthday na wani friend ne sun gayyaceni, a nan kusa damu yake, he's my neighbor, amma fa in baki yarda ba bazanje ba" murmushi mara sauti zee tayi tace "karka damu na yarda ma" yace thank you my queen" tace "karfa ayi dare" daga haka sukai sallama, har tayi bacci kuwa be kira yace mata ya dawo ba kuma bataga tex dinshi ta watsapp ba
Taji wani bacin rai tunawa da yadda sukai jiya, ko tex din safe daya saba mata ma beyi ba, ta cigaba da takawa zuwa hanyar department din nasu, tana kokarin shiga sarah na qoqarin fitowa daga department din, zee tai mamakin ganinta dan basuda alaka ko ta lectures da zata kawo department din,
Harda er sassarfa ta hada ta karaso gaban zee, zee ta kare mata kallo, babu kwalliya a tareda ita sam kamar va safiya ba kamar ma ko mai bata shafa a fatar tata ba, saidai fatar ta boye hakan kasancewar oily skin me shining gareta,
Kuma tayi kalar a rikice take, "zee faruq," sarahn ta fada a dan hargitse batareda ta kula da irin kallon da zee ke kare mata ba, zee ta hautsine "me ya sami my dear, meya faru da my faruq" sai hawaye suka fara zubowa kamar dama jira sukeyi, zeenat ce ta karaso sakamakon hango su datai a kofar department din, harda dan gudunta ta isosu, ta rike zee tana tamabyar sarah datai sororo tana kallon zee meya faru, sarah ce ta soma fadin, "tun jiya en sanda suka kamashi dayaje birthday, dan nima naje amma banje da wuri ba dan an kusa tashi ma, kuma ba tare muka taho ba" to me yayi musu suka kamashi?" Zeena ta tambaya, "wai yayi violating rules na driving"
Wanne police station ne?, sarah ta sanar musu dagaa haka suka dunguma suka tapi,
Koda suka karasa tun basu shiga ba zee ta hangi bayanshi yana cike wasu takardu, da rigarshi a hannu, sai daya gama komai ya fito sannan ya gansu tsaye a waje sai faman kuka zee take babu sauti,
Ya tsaya a gabanta kawai batareda yasan me ze ce mata ba,, zeena taja gefe, zee ta sunkuy da kanta tana cigaba da zubda hawaye da sheshheka lokaci zuwa lokaci, gurin zeena ya karasa ya amshi tissue, sannan ya dawo gabanta ya miqa mata, ta amsa babu musu tana goge hawayen idanunta, kallonta yake tayi kwalliya cikin coffee gown wacce ta fidda tsayinta, sai gyalenta medium data nade kanta dashi, kyalli fatarta ya karu tamkar ka hangi golden ring yana kyalli cikin rana yana daukar ido hakama tata skin din, hancin nan tubarkallah, ya dan kauda fuskarshi, itakuma ta dago bayan ta gama goge fuskarta, ya maida dubanshi kan innocent face nata, yau sai yaga tayi mishi kama da er baby,


Har gida suka rakashi itada zeena ya musu bayanin cewa "wai ya karya dokar tuki ne a yadda suka fada shiyasa suka kulleshi" zee dai batace komai ba sai jimami hakama zeena, bayan kwanaki biyu da faruwar wannan, zee tana gida bata da lecture na safe se karfe biyu ma, ta kammala wanke wanke tayi goge goge ko ina tas, ta koma daki taa zauna tana tinanin yin wanka ta hada ruwa zata shiga kenan wayarta tai pinging alamar shigowar sako, ta shiga batareda ta duba ba, bayan ta fito ne ta shirya ta dakko wayar sai taga wani sako dake neman tarwatsa kwakwalwarta kamar haka;
"Zainab ki fita harkar faruq ba mutumin kirki bane, d'an shaye shaye ne idan kuma baki yarda ba ki duba watsapp dinki"
Wani mugun bugu taji kirjinta nayi mata kamar zai tsage


Naga sakon ta'aziyarku dayawa, nagode Allah ya bar zumunci,
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 27: F.U.J


Gabadaya ji tai wani jiri yana dibanta ta rintse ido ta rike bedsheet din ta damke shi a hannunta, takai mintuna 10 a haka sannan cikin karfin hali ta jawo wayar taana ta girgiza kanta da fatan Allah yasa ba gaskiya banee abinda ake fada mata, ta bude watsappa bayan messages sun gama shiga ta hangi message na bakuwar lamabar datayi mata tex, ta shiga da hanzari
Vedio ne ta bude, tunda ta fara kalla ta kasa kifta idanunta, tabbas faruq dinta ne, yana zaune kan kujera yayi balance, gabanshi kuma wani karamin table ne an jere kwalabe da gani ma ya fita hayyacinshi ga kwalayen sigari da daya a hannunshi, sai sha yake, a zaunen ma layi yake
Wasu zazafan hawaye suka sakko mata, wani tex ya shigo ta watsapp din ta karanta kamar haka, "wannan shine dalilin dayasa en sanda suka kamashi saboda he's drunk and he drive, Allah ma yasa beji wani rauni ba, dont try calling me cos u wont get through"
Ta ajiye wayar cikin kokarin controlling kanta, ta zame kasan tiles din zuciyarta na mata zafi, faruq be mata adalci ba, me yasa ze yaudareta, innalillahi wa inna ilahi raji'un, kuka sosai takeyi, har daga karshe ta kwanta a kasan hawaye na bin kumatunta,
Bazata iya kayyade tsayin awannin data dauka a hakaba, tamkar matacciya haka takejin jinkinta ya mata nauyi, ko dan yatsanta kasa dagawa tayi, wayarta kuwa tayi ringing yafi sau ashirin amma sam bata ma ji ba
A hankali ta turo kofar ta shigo dakin a gajiye, ta subale jakarta kamar ance ta kalli inda take ta sake waiwayawa dakyau, yes mutun ne a gurin, da sauri ta karasa gurinta inda take a zube, jikin nan ya dau zapi rau, ta dago ta amma jikin nata a sake yake gabadaya, zakiyya ta jijjigata
"Zee mene haka, meya sameki, na shiga uku zee yi magana", idanunta a bude sun chanja kala kuma sai kallon zakiyyan take," da sauri ta saketa ta fita ta nemi Anty siyama, Allah yasa driver be tapi suka sakata a mota,
Alluran bacci akai mata hakan yasa batasan meya faru tsakanin kwanaki biyun ba tana ta bacci,
Ta bude idanunta da guntun hawaye a gefe, cikin rashin sa'a tai tozali dashi tsaye duk ya birkice, ya karaso gabanta da sauri ba tareda ya damu ba ya tsugunna a gaban gadonta kan guiwarshi, ta rintse idonta hawaye masu zapi suka soma ambaliya,, muryarta a dashe sosai dan bata fita, koda dama can sanyi gareta,
"Dan Allah ka tapi ka kyaleni banason ganinka" shock ya shiga, shida ya matso ya tausheta, ya dauka zatai farincikin ganinshi ya dauka zataji dadi ne idan ta ganshi ya dauka zataji saukin zazzabin datakeji ne ya dauka zatai appereciating efforts dinshi gameda zirga zirgar daya dingayi cikin asibitin amma se sabanin haka,? Kuma a iya saninshi beyi mata laipin daze saka tace batason ganinshi ba, bayan wayarsu ta karshe ma suna annashuwa sukayi da son ganin juna in lokacin lecture yayi,
Bai iya furta mata komai ba se kallonta dayakeyi ta sake maimaita mishi cikin fusata da tsana "nace ka tapi ka kyaleni banason gaaninka, ka rabu dani dan Allah"
Furucin nata ya sanar dashi lallai dagaske zee ke fadamishi hakan, ya tapi ya barta? Kamar yaya wai? Ya tmbayi kanshi,
Zeena ce ta shigo dauke da flask a hannunta, duka suka dubeta, zee tai yunkuro tana kama hannun zeena sanda ta karaso "dan Allah kice mishi ya fita ya barni, banasonshi a rayuwata" zeena ta zubama faruq ido, a matuqar sanyaye ya juya ya nufi haanyar fita ya rike handle din kofar sai kuma ya saki, lokacin zee ta kifa kanta jikin zeena tana sheshheka a tunaninta ya tapi,
Dawowa yayi a hankali ya tsaya gabanta yayi folding hannunshi kurun, bata san yana dakin ba "zeena faruq ya cuceni, ya boyemin gaskiyarshi, se yanxu danayi nisa a soyayyarshi sannan , Allah ne kadai zai mana sakayya,"
Zeena batace komai ba sai kallon faruq da takeyi wanda ya zuba ma zee ido, sai kuma yayima zeena alamu da yatsanshi ta fita, ta zame jikinta ta fita sakamakon hakan kuma zee ta dago tana kallonshi bacin rai ya zanu a fuskarshi amma who cares tunda dai ita hakan ko a kwalar rigarta,
Ya karaso itakuma ta zuba mishi ido cike da tsanarshi,
"Me nayi miki da zakice Allah ne ze sakamiki? Na yaudareki ne?" Ya tambayeta da dan fada fada, ta mishi banza ta kauda kai gefe, zuciyarta na dagawa da sauri da sauri, shiru duk sukayi batace mishi komi ba shima bai sake maimaita tmbyar ba, yafi mintina 20 a haka sai ya juya a hankali ya fita daga dakin ranshi na tafarfasa,
Tabi bayanshi da kallo ya fita ya rufe kofar daidai nan ta saki wani marayan kuka cikin karyewar zuciya,
A ranar aka sallami zee ta koma gida bayan likita yayi gargadi da ta dena saka damuwa dayawa a ranta, zee da zakiyya a motar driver na jan su,
"Zakiyya banga Anty ba kwata kwata" zakiyya tace "ai Anty itama babu lpia tana hospital tana ta lebour tun daren jiya" duk rashin kwarin jikin da zee keji sai taji wani karfi, "wanne asibiti? Kardai wanda muka baro" zakiyya tace shi ,
Amma saboda Allah shine baki kaini na dubata ba, maida wuqar to tsokanarki nake
Ta haihu har sun sallameta dazu
Dadi zee kamar ita ce ta haihu, "me muka saamu?,ya jikinta?"
Ki bari in munje kya gani keda likita yace ki huta duk kinbi kin dami kanki.."
Aikuwa da sukajee gidan a dan cike yake, da en gida da kuma en uwan Anty harda yaayaa, Anty ta samu namiji kuma tana lpia


Gabadaya satin bataje school ba suna gida sunata hada hada, ranar suna gidansu ta tapi akayi suna, aka sakama yaro sunan muhammad saghir
***
Ta kammala shiryawa domin tapiya makaranta tayi shigarta ta bakar abaya dukda cewar ba fara ce tas ba amma tayi kyau ta yafa gyalen abayar dayasha ado da duwatsu,
Driver ya ajiyeta gaban department tama zakiyya sallama sannan ta fita a motar, ta dan waiga ko zataga motar faruq dukda haushinshi da takeji amma sai babu ita, haka aka gama lectures din ranar amma babu shi babu alamarshi, sai kuma taji tana son sanin halin dayake ciki,
Ta danne ranta ta tafi gida, kwanaki uku zee ta jera tana zuwa makaranta amma bataga ko me kama da faruq ba, duk iya kokarinta na danne rashin damuwar da tai hakan ya faskara sai ta tsinci kanta cikin matsananciyar damuwa na rashin ganinshi
Bata kira driver ba yau kuma bata jira ta gama lecture ba ta fita ta gate din baya ta tari napep ta fadamishi inda ze kaita,
Ta kai mintuna 5 a tsaye a kofar gidan tun da mai napep ya ajiyeta, can dai ta tattaro confidence ta tura kofar gate din, motoci ne parked in the drive in, can gefe a lungu taga motar faruq kasan rumfa har tayi kura,
Ta karasa gun motar tana lakatar kurar data gani ta waiga ta dubi kofar apartment dinshi kaamar kuma wacce magnet ke jaa ta soma tafiya zuwa apartment din nashi, ta tura kofar taji a bude, ta soma hawa matattakalar benen dake bakin kofar, ko gajiya batajiba ta gama haye steps din ta ganta a bakin wata kofa, tasa hannu ta tura
Er kara kofar ta bayar ta sule takalmanta sannnan ta shiga, da dan duhu a falourn dan duka fitilu a kashe suke hakama curtains a sauke suke, amma hakan bai hana ta ganin royal cushion set din da akayima falourn ado dasu ba, masu launin royal blue sai carpet sky blue da ratsin black babu wasu tarkace cikin shi daga set na kayan kallo sai dispenser, ta karasa wajen wagegen window din ta yaye curtains sannan taga switch ta kunna fitilar falourn, take haske ya gauraye falourn, a tsaftace yake amma akwai kura alamun kwana biyu ba'ayi shara ba kuma kamar babu me shiga cikinshi,
Cikin rashin tsoro ta nupi kofar dakin datake kallonta, ta tura kofar kamar waccan tayi kara itama, sai tayi baya da sauri kuma bada nisa ba, sai kuma ta dawo ta shiga dakin,
Tun a bakin kofar dakin take tuntube da guntayen sauran sigari, haka ko ina a kasan dakin wasu ma ba'a kunna ba
Kaca kaca dai dakin ta dubi saman bedsheet din, yayi rubda ciki dukda er kurar dake dakin ma sam be dameshi ba, can gaban gadonshi taga wani frame na hoto, da gani mahaifiyarshi ce a jikin hoton da wata wacce zee tayi concluding da cewar yayarshi ce Anty safiyya datakanji labarinta a gurinshi,
Tana nan tsaye ya miqa hannu yana kokarin jawo sigarin dake kan drower, yayi sa'a ya jawo ya kai baki, zee ta ajiye jakarta ta karasa ta rike sigarin,
Sai a lokacin yaji kamshin perfume dinta, jikinshi a mace ya daga dara daran idanunshi ya dubeta a raunane, kawai ji tai bazata iya rike hawayenta ba, ta tsugunnna a nan ta dora kanta a gadon tana shessheqa, ya miqe zaune cikin rashin jin dadi, dan kanta ta dena kukan ta dago ta kalleshi yana nan zaune
"Ashe dagaske ne kai dan shaye shaye ne?, shine ka boyemin? Ka yaudareni" tai concluding
Ya zuba mata ido kawai, tayi shiru kuma ta kasa miqewa ta tafi.. Can ta tattaro confidence ta miqe,
Da cracked voice dinshi yace "i miss you nerhnerh" ta kalleshi zuciyarta ta raunana, wani sonshi ya taso mata,
"Nerhnerh" ya kirata
Ta zuba mishi idonta na wasu lokuta kafin ta dauke idonta trying hard to control her feelings, "YES is true i smoke but i hav stopped drinking years back " lokaci daya taji wani abu ya soki zuciyarta, ta durqusa cikin kurar tiles din sakamakon rawar da kafafunta suka dauka, "nerh nerh wallahi i stop taking alcohol, i dont drink anymore"
Hawaye suka sillo mata, she's totally broken, kenan dai da gaske ne faruq is a drunkard
A hankali ya tsugunno gabanta shima kan gwiwowinshi, kanta na kasa shikuma itadin yake kalla, am sorry zainab
Sunanta ya fita tar a bakinshi tamkar shi ne ya rada matashi,
I love you pls don't leave me, bata iya ce mishi komai ba se shessheqar da takeyi lokaaci lokaci, dukkuwa da tsananin tasirin da kalamanshi keyi a kanta, ya miqe tsaye yace pls come with me, ta miqe ta bi shi jikinta a sanyaye, wani daki nan kusa dasu ya bude a cikin falourn,
Dakin a gyare yake ba kamar bedroom din ba, saidai babu komai cikinshi sai art accessories, at first in ka shiga zaka fara hangen wani glass yana ta shining kuma an manna qananun fitilu a jikinshi suna bada different colours hakan ya kara mishi sheki, FUJ in bold shine a jikin glass din sai kuma board mai fadi gefen board din akwai table da su colours da different painting materials,
Sai kuma frames da dukansu an juya bayansu hakan ze saka bazaka gane mene jikin frames din ba, wasu kuma an rufe su,
Stool ya jawo mata yace sit, ta zauna tana goge sauran hawayen idonta, ya karasa gaban glass din mai kyau, abinka da mai tsayi bai nemi karawa ba ya ciroshi a hankali, cautiously da alama abin is very precious to him, ya nufo ta dashi, zee ta dinga kallon abin tana burin ta taba shi, ya miqa mata shi, ta amsa tana kalla, sai da yazo hannun ta sannan ta gane ashe award ne, sauran rubutun jiki duk kananu ne, F.U.J ne kawai akayi shi babba yadda ko daga nesa kake zaka ganshi tmkr yana yawo cikin ruwa garai garai,
F.U.J shine abinda bakinta keta mmaimaitawa
The name seems familiar, ohh ta tuna akwai wani frame da akayi designing

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login