Showing 66001 words to 69000 words out of 73133 words

Chapter 23 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5426

takeda ciki ya soma girma sannan su wuce gidan kubra suga yaranta twins data haifa, wayarta tai ringing ta dauka da mamakin ganin sunan Assiddique jiki, yace da ita yana garin ya kawo mint gida tayi mishi kwatance yazo
Mamaki tayi sosai takuwa yi mishi kwatance aikuwa babu dadewa sai gashi da wasu securities ya barsu a waje, zee ta mishi iso ya shiga,
Sun dan taba er hira sannan yake sanar da ita sai nan da kwana biyu zasu koma kuma yana fatan in zasu koma ta shirya su wuce tare, tace dashi in shaa Allah,
Bai wani jimaba ya tafi,
A daren ranar da uncle muzakkir ya dawo ya sanar da ita lallai lallai ta shirya ta koma bakin aikinta idan su Mint zasu koma ta bisu su tapi tare, batayi wani musu ba dama itama din tanason komawa aikin dan akwae abinda ta kudura


Ta hada duka kayanta, shi da kanshi yazo ya dauketa, sannan ya shiga ya kira su mint, ko kadan mint bata san tareda zee zasu koma ba,
Motoci sunyi convoy mint da Assiddique suka shiga ta biyu yayinda zee ke cikin ta uku, saida suka isa airport sannan zee ta fito mint ta ganta,
Mint Ta kalleshi sannan tace "itakuma daga ina?" Yace "aikinta zata koma", zee tace "ya mint kinyini lpia" tayi mirsisi taki amsawa Haka sukai tafiyar kowa da abinda yake sakawa cikin ranshi, kan kace me sun sauka


Kwanaki biyu bayan nan, zee ta kammala mishi gurkinshi sannan tasa waya ta kirashi yace "kawomin office bazan samu zuwa gida ba", ta shirya ta nemi driver suka wuce office din, yana cikin office din FC (food court) ya biyo duba ayyukansu ta shiga ta ajiye mishi kan wani table karami dake gaban sofa, ya fita itakuma ta soma serving bai dade ba ya dawo amma wani mutun na biye dashi a baya yasha coat da wata kit a hannunshi,
Suka zauna suka soma cin abinci su biyun har zata fita yace tai zamanta, bayan sun kammala dayan mutumin yace "ita ce kenan" ya gyada kai eh bismillah
Zainab ta soma kallonsu daya bayan daya yayinda mutumin ya bude kit dinshi ya ciro kayan aikinshi,
Assiddique yace "bashi hannunki (cubital fossa) zainab" ta kura mai idanu tana kallon allurar dake hannun mutumin
Mutumin yace "karki tsorota, ba wani abu bane sample na jininki zan diba kadan zamuyi test ne" kamar kar ta miqa hannun amma duk sun kafeta da idanu haka tanaji tana gani ta miqa ya zuqi jininta cikin syringe.


Bayan nan Assiddique ya hana zainab komawa gida yace yau tare zasu koma, tace "girkin dare kuma fa" yace "ai a nan zaki zauna a hada dinner dake sai muyi takeaway" tace mishi to
Ya tafi ya barta a restuarant din sukai aiki tareda ma'aikatanshi, bayan magrib yazo ya dauketa suka koma gida tare,
Mint na tsaye a bolcony tana jin dadin iskar dake kadawa, sai taji alamun dawowar mai gidan nata, ta dan zagaya ta daya bangaren da zatafi ganinshi da kyau, bisa madaukakin mamakinta sai ganinsu tai a tare su biyu dayake itama bata dade da dawowa daga gurin nata aikin ba,, haka nan taji wani tukuki ya mamaye zuciyarta, a take tsanar zainab ta ruru cikin ranta,


Dama har akwae macen data isa Assiddique ya kalleta, ai ta dauka babu ita, ta dauka duk fadin duniya ita kadaice ze kalla, amma da yanayin kallon dayake ma zee yasa taji ta tsani zee din amma sai ta danne zuciyarta da fadin "aiki kurun take mishi," ta yarda akan hakan dan gani take babu fa wata da zata iya samun gurbi a zuciyar star dinta domin gani take ta mamaye ko ina...


Zainab ta dubi Assiddique a sanda yake cire hadadden covered shoe din kafarshi
"Yayana genotype za'ayimin ne shiyasa aka dauki blood sampls dina ko?"
Yayi nodding,, ta tabe baki sannan ta wuce nata dakin...
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 44: wedding bell


Abinda mint keyi yana kara bakanta ta gurin Assiddique ne kawai shikuma yana karajin son auren zainab har ranshi
Shirye shiryen makarantar zee ya kammala komai akayi yana updating zee saboda ta zauna cikin shiri,, ranar tafiyarta yazo, a lokacin baya nan dan haka dole ita daya ta hau jirgi ta tafi, duk wannan abin da ake mint bata san karatu zee ta tafi ba, sai da Anty siyama ta kirata take sanar da ita, karkuso kuji zagi kala kala a bakin mint nan fa hankalinta ya soma tashi ta fara tsinkewa da lamuran mijin nata akan zainab


Zainab kuwa batasha wahalar gane abubuwa ba sam, hakama a cikin makaranta da taimakon GPS, tsakanin Apartment dinta da school din babu nisa hakan yasa bata buqatar Abin hawa, ita kanta ma tafi son tafiyar da kafa
Assiddique ne ya kama mata tun kafin ta zo room and falour ne da kitchen da toilet a cikin room din, cikin estate yake,


Sukanyi waya da Assiddique din sosai in baya aiki wani sa'in kuma suna dadewa basuyi ba idan ayyukan suka tashi, Haka ma su Anty duk sunayin waya, fannkn karatunta kuwa zee ta maida hankali kan MSC dinta dan ma babu wani stress a farkon
Cikin satin nan zee ta lura sun dan jima basu gaisa da Anty ba dan haka ta dauki waya ta kirata, Antyn ta dauka amma daga ji inda take akwai hayaniya, zee tace "Anty kin fita ne" tace "a'a zainab biki akeyi, wai dannar kirji akazo"
Waye za'ai wa kishiya, zainab din ta tambaya Anty tace "Abban nihal ne yake angwancewa gobe daurin aure"
Zainab ta kusa daskarewa a gurin "aure fa kikace Anty" Anty tace "eh zainab aure fa,


Zainab bata sake yarda ba saida ta kira Zakiyya itama ta tabbatr mata da hakane, zainab ta zabga tagumi kai kace ita ce za'aiwa kishiya, abin ya tsaya mata a rai, zataso taje taga wacce ce wannan ta auri mijin yayarta


Bayan komai na biki ya lafa zainab ke tambayar Anty hawwer wai wace ce ya aura, tayaya uncle muzakkir zaici amanarki yayi aure
Anty hawwer tace
"Dan ya kara aure bawai yaci amanata bace, Allah ne ya halasta mishi kan me ze haramtawa kanshi, ki dena wadannan tunanin zainab, idan namiji ze kara aure wlh ko zaki hada sama da kasa indai yayi niyha sai yayi, haukan da mata keyi ma shi ne ke kara tunzura maza kan lallai se sun karo ma ko dan su gwada ma mace karfin ikonsu, idan kinndaga murya kin tada jijiyar wuya, ki sani kin ragewa kanki mutunci ne a idonshi amma da zamu gane mu kwantar da hankalinmu, shi fa komai a rayuwa Allah ya rigada ya rubuta, idan Allah yayi mata hudu Abban nihal zai aura zainab a rubuce yake tun ran gini tun ran zane, tabbas akwai ciwo dama dole akwae ciwo amma dole haka mutun ze danne yayi addu'ar Allah ya hadashi da abokiyar zama nagari, mun karanta wannan abin cikin Alqur'ani, meyasa zan jahilci lamarin, fatanmu Allah ya bamu jarrabawar da zamu iya ci" Zainab ta gyada kanta cike da gamsuwa haqiqa maganganun Anty haka suke


Zainab na kitchen tana kallon fool din dake bayan gidan nata, takanga mutanen dake estate din suna zuwa zama itama yau sai taji muradin fita gurin ta zauna,
Ta kammala wanke abinda zata wanke haka nan taji muradin dora abinci yau dan takan jima batai girki ba musamman breakfast da dinner, dan lunch mostly a school takeyi saidai ranakun da bata fita ba


Rich Faten dankali tayi ma'ana yasha kayan dadi, kama daga kifi, naman kaza, da ganyayyaki masu dadi da kamshi,
Ta ida ta sauke ta dauka ta kai fridge ta saka, haka nan taji tayi kewar Assiddique, ta sake kallan falourn, ko nawa ya kashe mata haka, tai murmushi sannan ta dau littafinta da wayarta tayi kofa,
Tana bude kofar shima yana karasowa, ta tsaya tana jujjuya kwayar idanunta dan tunani take mafarki ne, ya sake matsowa yace "Barka da yau zainab"
Muryarshi ce" taji zuciyarta na rada mata,
A take murmushi y samu gurbi kan fuskarta, sai ta matsa daga bakin kofar ta koma ciki shima ya bita ya shiga ya zauna kan kujerar, Abincin t dauka ta sake sakawa kan wuta sannan ta zauba mishi ta kawo ta dakko ruwa da lemo ta ajiye mishi
Ya sakko kasa, itakuma ta koma kitchen din ta zuba nata
Bayan sun kammala cin abinci tace "yaushe kazo?" Yace "tun jiya" .
Nazo ganin gidan da zamu zauna ne, na bada ayimin aikinshi"
Da rashin fahimta ta dubeshi gidan da zasu zauna shi da wa?
"Ko bazaki aureni ba zainab?" Ya fada kamar zeyi kuka, haka nan dariya ta subuce mata sai tasa gyalenta ta rufe fuskarta Yace "to tashi maza ki shrya mu fita" tace yayana karatu zanyi fa, yace bazamu dade ba


Babu nisa da inda gidanta yake can sosae, sai gasu gaban wani babban building, da alama gida ne ake renovating dinshi kuma ake sake mishi fasali, yace wannan ne gidan da zamu zauna in shaa Allah zainab ni da ke matsayin mata da miji,
Ta kara daga kai ta kalli gidan, wannan ko gidanshi na nigeria ma ai Albarka


Wasa wasa soyayya mai karfi ta soma shiga tsakanin zainab da Assiddique koda dama wancan karan ma ita ce taqi bashi hadin kai, idan makaranta zataje tare zasu fita ya kaita, idan karatu zatai shima sai ya debo taakrdu yana nashi aikin tana nata karatun
Sai da yayi sati daya sannan ya soma shirin komawa nigeria, gabadaya zee taji babu dadi, "yanxu sai yaushe zaka dawo" yace "im not sure amma nan kusa in shaa Allah, zanje gurin Abbah jabir na mishi maganar mu"
Ta sunkui da kai cike da kunya, haka tanaji tana gani ya tafi,


Ashe dagaske ne da hausawa sukace shi SO tsuntsu ne, bata taba tunanin zuciyarta zata iya samun gurbin wani mahaluki ba bayan faruq amma da haquri da lokaci gashi komai ya wuce gabadaya sai taji zuciyarta ta sassauto akan tsanan faruq bawai kuma soyayya ba amma kuma ta rage jin haushinshi,


A bangaren mint kuwa ta lura mijin nata gabadaya ya sauya mata dakyar magana ke hadasu idan ma yana garin fa kenan dan taga ya tsiri tafiyu iri iri baya ma cika zama a gidan, ta kudurce a ranta koda zainab ta dawo to bazata dawo mata gida ba, ya nemi wata cook din amma ba zee ba,


Assiddique ya sanar da yallabai maganar zainab, yallabai ya zuba mishi ido
"Ita yarinyar ina ce a karkashinka take aiki, kuma ita kakeso ka aura" yace eh yallabai
"To ya maganar genotype kuma" yace munyi yallabai babu wani matsala AA ce
Hakan yayi wa yallabai dadi yace "Amma ka gyara tsakaninku da minnatullahi kafin ka kawo wata sannan ka zauna ka tsara ayyukanka kafin ka auro er mutane ka kasa kulawa da ita"
Ya gyada kai cike da ladabi to yallabai


Gaskiyar yallabai ne shi ba mutun ne da zai iya rike mata biyu ba a halin da yake ciki dan haka dole ne a samu mafita kar ya tauye wa wata hakkinta,


Yallabai da kanshi yaje ya samu Abbah jabir suka tattauna magana, a take aka tsaida biki bayan ta kammala wannan shekarar kafin ta juya se a daura sannan ta cigaba, wannan abu yayiwa Abbah jabir dadi sosai, yallabai ya nemi Abbah jabir yayi shiru gameda maganar tukunna har sai Assiddique ya shawo kan matarshi da kanshi...


Yusuf ya samu minnatu tana aikin nata na kullun a gaban system din da har ta soma kashe mata idanu yanxu in zatayi aiki sai da glasses
Ya zauna, ta dan kalleshi ta watsar ta dauka bukatarshi ta kawoshi ammma sai taji yace "minnatu magana zamuyi, in Allah ya yarda nan da watanni biyar za'a daura min aure"
Idanuwa ta zaro waje sakamakon yadda maganar ta daketa, "Aure, Aure, Aure fa kace yusuf"
Yayi blinking idanunshi "Hakane"
"Kai dama wai har ka isa ka kara aure? Har akwae macen da ta isa nai kishi da ita, tukunna ma wacce karyar ce take bimin miji" yayi shiru bai amsata ba sai ma maida hankali dayayi ga TV
Amma dai kai kasan wlh nafi karfin wukaqanci, kuma kasan dai babu macen data isa ta shigo min gidana


Kawai sai tayi daki fuuu tana kuka, nan da nan ta kira Anty siyama a waya ta sanar mata tana rantse rantse be isa wlh yayi aure ba,


tafiya zanyi na bar mishi gidan Anty, kokarin kwantar mata da hankali take amma ina ita kawai gani take yaci mata mutunci ne
Dakyar Anty ta shawo kanta ta fasa tafiya


Sai ta dauka tsokanarta yakeyi ganin ya cigaba da Al'amuranshi dan haka taje ta sameshi
"Na yarda kayi aure amma kan sharuda guda biyu"
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 45: forgive n forget


Batareda ya kalleta ba yace "fadi sharudanki"
Tace "sharadi na farko bazaka kawo amaryar ka wannan gidan ba, saidai ka nema mata wani gidan dan bazeyu ta zauna min a gida ba" ya jinjina kai yana jin karfin hali irin na mint yace "na biyun kuma fa"
Tayi rolling idanunta sannan tace "ka nemi wata cook din ka sallami zainab bana so ta dawo bakin aikinta" ya gyada kai yana tabe baki
Shikkenan naji, amma ki sani na yarda da sharudanki ne badan ina tsoronki ba bakuma wai dan sai na yarda ne auren ze yu ba, a'a saboda masalaha tsakani na dake ne da kuma kyautatawa ta zaman tare wacce na lura ke sam baki san da ita ba, kuma inaso ki zauna ki gyara halayyarki indai ba so kike amarya ta kwace miki ni ba dan saura kiris ma
Maganar zainab dama can banine na kawota gidan ba, kece kika nemi tazo saboda bazaki iya da hidimar mini girki ba, gida kuma naji bazan hada ku ba


Mint ta jima tana juya maganganunshi musamman inda yace "ki zauna ki gyara halayyarki" hakan yasa ta soma zargin ko tana da wata mummunar halayya ne, kuma me kyautatawa take nupi a zamantakewa irin ta aure


Zainab t kammala shekararta ta farko ta dawo gidan Anty dan dama jira kawae take ta dawo a hau mata gyara, itace sha wancan sha wannan duka dai,
Rannan zainab tana daki tana bacci ta jiwo hayaniya cikin babban falourn Anty hawwern ta tashi ta dubi kanta a madubi, tasa hannu ta shafi skin dinta ita kanta burgeta skin din keyi, tayi kyau ta murje sosai, yau saura sati biyu cif a daura aurensu fa.... Anty ce ta turo kofar dakin ta shigo tace "saka hijab ki fito ku gaisa" zainab tace Anty su waye tace "amaryar Abban nihal da qaninta" ta fita tana murmushi zainab ta dan tabe baki ko mene abin murna dan amaryar mijinka t ziyarce ka, ta saka hijab ta fita falourn,


A hankali take takawa tana kara gasgata abinda idanunta ke fada mata "su kuma me sukeyi a nan, mene hadinsu da amaryar uncle muzakkir"
Anty tace karaso zainab, zainab ta karasa tana mai dubansu duka
Ta dan danne mamakinta
Ta gaida su ciki ciki, ita kadai ce ta amsa amma shi bai amsa ba idanunshi na kallon kasa ne kawae


Anty hawwer tace " Zainab ita ce Amaryar Abban nihal"
"Ya safiyyan?" Zee ta tambaya a mamakance tanaji kamar kar ta yarda a ina Abban nihal ze san su faruq,,, sunzo ne domin suyi magana da ke zainab,
Zee a ranta take ayyana "wato Anty tasan ya safiyya Mijinta ya aura shine bata samarmin ba"


Anty hawwer ta tashi ta basu guri ya rage sai su uku cikin falourn
Ya safiyya ta matso kusa da zainab ta kamo hannayenta
"Zainab nasan ko wace faruq yayiwa abinda yayi miki bazaki yafeshi ba ni banga laipinki ba
Bawai kuma ina nema mishi afuwa bane dan shidin dan uwa nane ba" rabuwarki da faruq yayi ne domin kwanciyar hankalinki zainab, nan Anty ta sanar da zee reason din faruq duka"


Zainab taji jikinta yayi sanyi "bata taba tsammanin faruq na sonta har haka ba dama mutun yana nashi ne Allah ma na tashi"
Ta dubi faruq din wanda a yanxu ko ishasshiyar lafiya ma bata isheshi ba balle abin kula da iyali
"Nayi tunanin bazan iya yafe maka ba a baya amma yau na yafe maka faruq kuma gaskiyanka a lokacin da ka fadamin dalilanka da bazan yarda ba saboda im blindly inlove, im desperate to become ur wife ban ganin laipinka ko kadan, bazan gane meke jira ba a time din bakuma zan karbi uzurinka ba, madalla da wannan soyayya taka a gareni faruq, haqiqa yanxu kam nagode maka kuma a tsakani na dakai babu komai sai mutunci da zumunci"


Sai a lokacin yayi smiling yace "nagode zainab Allah ya sanya Alkhairi a aurenki" tace Amin kaima kuma haka


Haka nan zuciyar zee tai mata wasai, wannan shi ne beauty of forgive and forget, if you keep holding grudges it will keep affecting you, zai shafi lafiyar mutun, kullun tunanin mutun zai tsaya ne kan ya zan raam abinda wane yayi min, gabadaya zaka manta goals dinka na rayuwa kayi focusing kan mutun daya jal wansa haka zeyi tasiri wajen rashin cigaban rayuwar mutun ne, dan Allah mu zamo masu yafiya ko muma ubangiji ya ji 'kan mu


Zainab ta sanar da Anty duk yadda sukai dasu faruq, Anty taji dadi sosai, dan zataso er uwarta ta shiga gidan aurenta babu wani digon tsana a ranta, yadda zata bada zallar soyayya wa mijinta
Anty tace
"Lokacin da Abban nihal yace zeyi aure nayi kokarin sanin wace ya sanar dani wata tsohuwar budurwarshi ce daya taba haduwa da ita a europe sanda yake zuwa gurin barrister dake karatu a can, tun kafin muyi aure ya sanar dani magaanr ta kuma ni shaida ce yana kaunarta kawai dai dadynta yaqi yarda shima hajiyarshi taqi amincewa a lokacin har ta nema mishi aurena
A sanadin gorin da Abbanta yayi mishi na cewar baida ilimi ya sakashi komawa makaranta bayan munyi aure nima ya sakani nayi masters, mafarin zuwanmu karatu saudiyya, gashi yanxu yakai matakin PHD har yana sake wasu research din"


A hankali zainab ta dinga relating labarin da faruq ya taba bata na Ya safiyya da saurayinta a europe da labarin Anty hawwer, sai taji ta gane komai, ikon Allah kenan gashi a karshe dayake ya safiyya matar uncle muzakkir ce bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login