Showing 63001 words to 66000 words out of 73133 words
Chapter 22 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt
sai kallonshi da tai ta kuma maida idanun ta rufe, ya fita da sauri ya nemi mint ta taimaka mishi suka fito da ita aka kaita asibiti
saida tai kwanaki hudu a kwance kamin aka sallameta, to dama tayiwa Assiddique magana tun jiya, dayazo dubata tace "yayana dan Allah ka barni naje naga Anty hawwer zanfi jin dadin zama a can din"
Dukda beji dadin hakan ba amma sai yace "shikkenan ba matsala in shaa Allah zan hada komai na tafiyarki in aka sallameki sai ki wuce"
Ta kammala hada komai na tafiyarta, driver ya kaita har airport, bata dadeba jirgin nasu ya tashi zuwa birnin madina, duk wani abu data sani zai tuna mata da faruq sai data tattareshi ta watsar, hatta frame din daya bata da duk wasu takardu ta kone, hakama cikin wayarta ta goge duka hotunanshi tayi taking deep breath sannan a hankali ta furta "May Allah S.W.T make it easy on us"
Jirginsu ya sauka lafiya a birnin madina, suka zauna sukai magana sosae da Anty hawwer, zainab ta sanar da ita "na rigada na haqura da faruq, idan so cuta ne to haquri magani ne, time heals every wound, haka nan ba komai ne mukeso muke samu ba, kuma ko ba komai na koyi darrusa zamana da faruq"
Anty hawwer tace "kina ganin kin yafe ma faruq har cikin ranki"
Zainab tai murmushi sannan tace "wanann ne kuma ban sani ba tukunna"
"Ina mai baki shawara daki yafe ma faruq saboda hakanne kadai zai sa ki manta da komai, rikeshi cikin ranki will do more damage kema ze shafeki ne, amma da zaran kin yafe mishi zakijiki sakayau, daga nan sai ki bama Assiddique dama"
Zainab ta daga ido ta kalli Anty hawwer
"Ke kike fadin haka da kanki"
Tace "yes
Amma kinsan mijin mint ne ko
Tace "and so? Se mene dan mijin mint ne, ai bawai yana nupin dan ita daya aka halicce shi ba
Zainab ta girgiza kai nikam gaskiya banajin ma inasonshi,
Anty hawwer tace "shiyasa nakeso ki yafe wa faruq, hakanne zai baki damar cigaba da gudanar da al'amura har ki bawa wani dama, amma muddin kina rike dashi a ranki to bazaki cigaba ba"
"Duk wannan abin da kikeyi Anty shifa bama cewa yayi yana sona ba"
"To tayaya ze fada kuwa kin kashe mishi kwarin guiwa kin nuna mishi duk duniyarki babu ya faruq, in yayi magana ma sharewa kikeyi"....
Zainab na kwance a falourn Anty tana kallo, wayarta tai ringing, ganin Assiddique ne sai taji kamar kar ta dauka sai data kusa tsinkewa sannan ta dauka da sallama, ya amsata muryarshi cikeda annashuwa sannnan yace "na dauka zee ta manta damu ne, tunda kika tafi kuma ko er waya"
Tayi shiru batace mishi komai ba "yace yaushe zaki dawo ne ko kinyi resigning ne ban sani ba"
In shaa Allah nan bada jimawa ba, yace to Allah ya dawo dake lafiya ina ta neman cook amma har yanxu na gaza samun ya ke, sai na fahimci ke din ke d'aya ce"
Tayi murmushi a takaice sannan tace "ya Ayyuka yayana"
"Gasu nan sunsha mana kai sai hamdala, ina tunanin gobe in Allah yaso zanje egypt, so ki cigaba da min addu'a"
Tace to Allah ya tsare...
Watanni daya bayan nan, Assiddique yaga zee bata da niyyar dawowa gashi zaman nasu da mint babu dadi gabadaya bejin dadin zaman gida, kullum aikinta complain beyi kaza ba beyi kaza ba, ko kuma ita dama dole akai mata ta dawo in be somta ya sawwaqe mata, har ya gaji da jin ita dole akai mata
Zainab ta fito a kitchen din bayan kammala hada musu lunch ta shiga daki tai wanka ta fito ta tadda Anty a falour wacce take dauke da juna biyu na kusan watanni shida, tare sukai lunch harda nihal da tayi wayo sosae yanxu, da la'asar ta saka mata hijab tace da anty safiyya sun tafi masjid dan sunyi missing zuhr,
A kafa suka je kuma suka dawo, zee tai turus a kofar gidan Antyn ya mata murmushi mai taushi sai ta samu kanta da kasa mayar mishi
its short though not too short lol
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 43: Result
Kashegari kuwa likitan har gida yazo dayake Assiddique yana hutu a yau din,
Duka suna falourn su ukun, mint na aikinta shikuma ya saka zainab tayashi duba wasu designs,
Akayiwa likitan iso ya shigo falourn bayan an nemi izinin Assiddique, ya shigo sukayi musabiha
Ya zauna ya ciro takardar ya miqawa Assiddique, yusuf ya karba yana jujjuyata, zainab kuwa ta kurawa takardar ido, ji take kamar ta fizge ta bude,,, Assiddique ya bude takardar sai ya kurama result din ido sannan ya dubi zainab, ta hadiyi yawu, ya miqa mata tasa hannu ta karba, a hankali wani murmushi ya subuce mata, dama jikinta ya rigada ya gama bata hakan
Tashi likitan yayi shima Assiddique ya bishi yi mai rakiya, mint ta juyo ta kalli zainab tace "tashi ki bani guri" da mamaki zainab ta dubeta hannunta rike da takarda sai kuma ta miqe ta bar gurin badan tsoro ba saidan bata muradin wani tashin hanakli yanxu, ta karasa daki ta kira Anty hawwer tana sanar da ita abinda ya faru, zainab tace "Anty kinga result din wai ya bayyana am AA" anty tace masha Allah zee tace "gaskiya nikam Im confused"
Tayaya mutun zeyi test sau biyu kuma result yana differing, anya baki ganin ya yusuf ya saka son zuciya cikin lamarinshi, nifa dama tunda suka dibi jinina naji jikina ya bani result din dole ze fito yadda suke so ne," Anty hawwer tace "hakane abin is confusing gaskiya amma banaso ki nuna mishi baki yadda da result dinshi ba, ki bari in kinzo kano muje na rakaki kiyi inda munsan baza'ayi manipulating result ba, kinga dole cikin biyun nan wani sai ya sake maimaituwa, either na faruq ne ba daidai ba ko kuma na Assiddique" zainab ta gyada kai cikeda gamsuwa
Zainab ta tashi as early as always domin hada mishi breakfast, bayan ta kammala ta kai mishi falour, already ya kammala shiryawa,mint ma ta fito, batayi musu ko sallama ba ta wuce hanyar da zata sadata da babban falour tai tafiyarta, zainab ta zauna sosai itama tai serving nata lokacin shikuma ya soma ci,
Ba al'adarshi bace magana idan yana cin abinci amma wannan karan yayi niyyar hakan, yace "me kike gani gameda alakarmu" ta dago tana dubanshi ta karasa hadiye abincin sanann ta tsame hannunta daga cikin abincin gaba daya
"Zainab inaso ki zama matata, dagaske wannan yusuf din ya fada soyayyar zainab, kuma aurenta zaiyi"
Ta dauki ruwa da hanzari ta kurba ta ajiye, batayi tsammanin maganar soyayya da aure daga bakinshi dukda tasan yana sonta din, amma shi baze duba alaqar dake tsakaninta da matarshi bama,
Ta tattaro duka confidence dinta tace "kayi haquri yayana amma ni yanxu karatu nakeso na dora ba aure ba"
Dukda yaji zafin maganarta amma sai yayi controlling kanshi ya cigaba da cin abincin nashi, amma gabadaya tunani ya cika kanshi
"Tayaya za'ace the able Assiddique wai ya buda baki yace yana son yarinya amma ta bashi haquri" y tashi tsaye abinshi sannan ya wuce
Zainab ta bishi da kallo tana tunanin mene ma ya hana ta amshi soyayyarshi, bayan shidin babu abinda ya rasa saidai tawaya irin ta dan adam da kowannenmu yana da fault,
Inaso nayi karatu mai zurfi kodan na nunawa faruq nidin wata ce kuma na sakashi yin nadamar abinda yayi, im yearning for success badan nawa ra'ayin ba sai dan inaso faruq yaji bakincikin ganina as a successful person,,, Da kudaden aikina zan tara na koma makaranta
Sati daya bayan nan, Assiddique yace zee ta shirya sunada tafiya jibi tace dashi to, Birnin UK jirginsu yayi landing, zee ta fito tana shan iskar dake kadawa mai dadi haka suka wuce masaukinsu, tana mamakin yadda yasan mutane a kasar, a ranar ita daya ta kwana a apartment din daya sama musu dan shikam ya tafi wasu ayyukan, sai kashegari da sassafe ya dawo ya chanja kaya ya dan miqe,
A yammacin ranar yace ta shirya su fita, aikuwa ta shirya cikin Abaya mai kyau, zagayawa yayi da ita makarantun dake kusa dasu sannan yace "zainab ki zabi makarantar da zakiyi karatunki ni zan dauki nauyi"
Ji tayi kamar ta daskare a gurin ta washe baki cikeda jin dadi,
Kafin kace me Anty ta turo credentials dinta, wasu universities din basa offering msc a course dinta dan haka suka nema a oxford, ji take kamar a mafarki, tanajin labarin oxford yau gata zatayi karatu a ciki,
Assiddique na son cika mata burinta,
Sanda suka koma gida ta nemi zuwa kano na kwana biyu ya barta dan shima ba zama zaiyi a Abujan ba wata tafiyar gareshi,
Zee taje gidan Anty hawwer cikin dumbin farinciki, itama Antyn murna take tana godiya ga Allah sai taji duk hankalinta ya kwanta da Assiddique din, aikuwa kashegari suka wuce Asibitin akayi ma zainab test din, yace ko su dawo da magrib su karbi result ko kuma gobe, zainab bata iya jira har gobe ba taje ita daya ta karbo ta dawo
Tun a hanya takeson budawa amma tanajin gabanta na faduwa, ta haqura saida taje gida sannan ta miqawa Anty
Tasa hannu ta buda sai me?
AA pattern a karo na biyu, Anty ta girgiza kai, ashe dai Assiddique ne mai gaskiya ta miqawa zainab tace amshi
Zainab ta amsa tana kalla, haka nan taji wani abu ya taso mata gameda ubangidan nata, in banda abinta ma taya zata soma tunanin zeyi manupulating result amma ya akayi wancan da sukai da faruq ya bayyana AS
Ta rasa amsa ta ninke takardar tana yima Anty murmushi itama maida mata tayi dan ta gane manufar murmushin,
"Kar ki sake rejecting dinshi idan ya sake zo miki da maganar soyayya" zainab ta gyada kai a gamsashe,
Ta koma Abujan kamar yadda tai niyyar amma Assiddique be cikin gidan daga dukkan alamu baima dawo daga tafiyar da yayi ba, hakama mint bata gidan, ta zauna a gadon tana murmushi "lallai burikanta suna gab da cika"
Basu hadu da mint ba a ranar sai kashegari da safe, zainab ta kaima mint abinci sanin da tai mai gidan bai nan, ta zabga mata harara itakuwa zainab ko a gefen slippers dinta
Saida ya sake sati sannan ya dawo, haka nan zainab taji tana zumudin dawowar tashi bama kamar dayayi mata tex personally ya sanar mata da dawowar tashi sannan ya dora da ina fatan zan samu tarba mai kyau"
Hakan yasata zuwa inda tafi k'wari ta zage kuwa ta mishi sabbin dishes wadanda ta tabbatr zaiji dadinsu dan indai fannin cikinshi ne ta gama gane wannan bangaren,
Mint sai shige da fice take itama tun sanda ya sanar da ita dawowar tashi, itace zuwa pedicure manicure, gyaran jiki gyaran kai duka dai,
Ya sauka cikin koshin lpia, saida ya biya gidan yallabai tukunna ya wuto gida,
Gidan yayi shiru sai karan na'u'rori, ko wanne glass sai sheki yake, ga kamshi mai sanyi na fita daga kowanne bangare na gidan, yayi smiling sanda ya shigo, bai tsaya ko ina ba sai falournshi na kasa bayan ya wuce main falour, ya zauna kan kujerar
Zainab tunda taji alamun zuwanshi ta tashi ta dauko hijab ta saka sannan ta sauko ta wuce falourn, daidai shigarta mint ma ta shiga,
Suka hada baki gurin fadin
"Sannu da dawowa" ita zainab da hausa ta fada mint kuma da yaren nasara "welcome home"
Ya kalli zee sannan yace "yi serving pls" mint ta dan bata rai
"Na dauka zakai shower ne" ya girgiza kai wannan yafi muhimmanci beside mura ke neman kamani"
Tace ayyah sannu.. zainab rage mishi gudun AC din, zee ta dau remote ta rage,
Tayi gurin abincin tana kokarin serving mint tace jeki kawae zanyi serving" zee taji babu dadi a ranta amma ya ta iya sai ta miqe,
Yace "a'a barta tayi mint, nafison yadda take plating" mint ta hade rai
Bai kula ba Ya cigaba da fadin "she plate so nicely, it looks impressive always"
Mint tayi cilli da farin plate din dake hannunta, ya bi tiles ya tarwatse
Ta miqe ta kalli zee dake tsaye "fita a nan" zee ta juya tana tabe baki
Ya dan hade rai sannan ya furzar da iska waje "ya ilahi" ya fada a hankali yadda zataji, sai ya miqe ya wuce sama ya barta gaban abincin,
Takaici ya sakata daukan bababn warmer din ta fita dashi ta bawa securities, wasu kananu kuma duka ta zubar a waste bin.....
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 42: Back to work
Ta gaidashi ya amsa sannan ta shiga ta mishi iso, ya shigo bayan ta mishi iso, zee ta tarbeshi da abubuwa kala kala, harda abincin da tai dazun data ajiyewa uncle, rabonda yaci abiincinta ya dade hakan ysa ya sauka ya baje, zainab da anty hawwer suka bashi guri, suka bar mishi nihal, tare suka kwashi garar abincin tana mishi surutanta na yara yana biye mata,
Bayan ya kammala ya nemi yin magana da Anty hawwern ya rage su biyu ne a falourn, "Alfarma nake nema gurinki" tai shiru tana saurarenshi itakuwa wacce irin alfarma mutun kamar Assiddique zezo nema a gurinta "inda hali zanso idan zan wuce gida nigeria gobe na tafi tareda zainab ta koma bakin aikinta ina ganin zama hakan ba dadi ai" Anty hawwer ta nisa kamin tace "wannan gaskiya ne amma kaga yanxu jikin nawa yayi nauyi shiyasa bazanso tai nisa ba tana taimaka min da wasu abubuwa, koda zata koma aikin sai in Allah ya saukeni lafiya ina fatan zakayi mana haquri kayi mata wannan alfarmar"
Baiji dadin maganar ba amma da alama baida wani choice yace "shikkenan ubangiji Allah ya saukeki lafiya ya kaimu lokacin" ta amsa da Amin sannan tace bari na turo ta ku gaisa
Zainab ta kalleshi da tausayawa, ta sani sarae ya zafin so yake, kuma tasani alaqarta dashi bame yuwuwa bace a yanxu dai bata gama fidda abinda ya dace tayi ba amma babu batun soyayya ko aure a ranta nan kusa,
Ta zauna kan kujerar tana yin murmushin dabai kai zuci ba, shima ya maida mata a tausashe,
"Kin dai qi aikin zainab, ko ni ake gudu ne?" Tai smiling nervously
"Ko daya" ta bashi amsa a takaice, naji abinda ya faru tsakaninki da faruq dagaske ne you two broke up? Who told you? Ta tmbya yace my driver but why mene ya faru?
Taji wani tukuki ya bugi zuciyarta idan akwae abinda ta tsana yanxu bai wuce taji wata magana dangane da faruq ba, how dare he walked away just like that without any explanation,
Ganin da yayi mood dinta ya sauya ya sakashi chanja akalar maganarshi, inaga zan wuce, sai gobe zan biyo kafin na tafi in shaa Allah, ta jinjina kai sannan ta bishi da kallo ya tashi ya fita batareda ta mishi rakiya ba....
Anty hawwer ta zaunar da zee trying hard to convince her, ki yafemishi zainab, wannan shi ne karo na karshe da zan roki ki yafema faruq ko dan nutsuwar ruhinki, u'll feel free
Zainab tace "Anty bana tsallake umarninki, bakuma na qin karbar shawararki haka bana bijirewa duk abinda kikazo min dashi amma wannan karan banajin zan iya, idan nace na yafe mishi nayi miki karya ne kawae iya fatar bakina bawae har zuci ba wlh, ki saka kanki a matsayi na, tayaya zakiy tunanin zan iya yafe mishi, farko he left da Alqawarin zai kirani, amma bai kiraba har shekara ta shude, na rarrashi zuciyata ina mishi tanadin kaina, duk tsayin jiran danai finally na hadu dashi, kinsan yadda naji kuwa dana ganshi, tmkar naje na fada mishi duk tsayin kewarshi da nai na nuna mishi duka notes din dana dinga rubutawa idan nai kewarshi, amma hakan bazeyu ba sakamakon baida lpia, kinsan tsoro da firgicin dana shiga kan kar na rasashi, all the sleepless nights n tiring days, and lokacin da za'a mishi aiki, i spent almost all my night kan dadduma ina kuka ina roka mishi sauki gurin Allah, duk saboda ina sonshi, i endured almost everything, but what? He came back am so anxious, exicited and happy to meet him, sai kuma naga wai yanada mata harda da, duk wannan bai sa naji a raina zan rabu dashi ba, naje na sameshi muyi magana hoping zai ce min zainab kiyi haquri, i still love you n i will marry you, amma kash, sai yace dani muyi ending komai, kuma batareda yayimin wani bayani ba ko ya bani kwakkwarar hujja, kawae yayi tafiyarshi ya barni batareda nuna kulawa ba"
Ta karashe tana goge hawayen dake zarya a idanunta, "bai cancanci yafiya ta ba Anty, zan nuna mishi nafi karfinshi i will do everything in my power to become successful, i'll make him regret" .....
Zainab ta cigaba da zama a gurin Anty, har watan haihuwarta ya kama a cikin watanni ukun nan Assiddique yakan ware lokaci yazo ya ziyarci zee dukda busy schedules dinshi,
A daren da Anty zata haihu, ranar zee bata kwanta da wuri ba, tana falour tana kallo kawai sai ji tai ana buga kofar dakin Antyn, ta tashi sanin da tai uncle muzakkir ya fita ba dadewa, a bakin kofar ta tadda Anty cikin mawuyacin hali,
Zainab ta fita ta nemi waya ta kira shi, Allah yasa yana kusa,
A asibitin ta kwana sai gabanin Asuba ta santalo yaronta, murna ba'a magana, bayan an tabbatar ita da jaririn duka lafiya suke aka sallameta,
Dukkansu sunyi mamakin haihuwarta a lokacin sakamakon E.D.D dinta bai cika ba, amma likita ya tabbatar musu babu wani abu,
Bayan anyi suna yaro yaci sunan Abbansu Anty wato muhammad suke kiranshi
Sanda Anty ta cika kwanaki arba'in suka shirya dawowa gida, dama tun kafin haihuwarta sunyi shawara da uncle muzakkir din zasu koma nigeria tunda karatun da suke duka sun kare kuma akwai gida a can din nasu, saidai wasu business daya fara a madinan zai na zuwa time to time shi kadai,
Haka suka tattara suka bar madina suka dawo gida nigeria, dadi kamar Assiddique ya zuba ruwa a kasa ya sha jin sun dawo yasan zee ta kusa komawa bakin aikinta,
Rannan kamar Almara tana daki tana shirin zuwa gidan zakiyya wacce itama