Showing 54001 words to 57000 words out of 73133 words
Chapter 19 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt
hutu gidan nera"
Zakiyya ta dora "ai bikin ma hadi ne amma fa ance yana sonta yaga kyakkyawa duk ya rikice, a yadda naji fa kenan nima ya kubra ke bani lbari, to shine bikinsu yanxu next month ne,... Zee ta katseta "ai ta dawo nan naga har an fara mata gyaran jiki ni gani nake ma cigaba ne dan yadda fatarta ke wani shining"
Ahh kekuwaa ai dole gidan As_siddique fa zata shiga, hmm za'asha shagali ai ni dai Allah yasa su gayyaceni"
Zee tace "Allah ya sanya alkhairi"
Ai da can ya aka kare gani take tapi kowa balle yanxu kuma ai gani zatai mu ko darajar kiyashi ma bamu kai ba, cewar zakiyya
Itadai zee bata kuma tofawa ba...
Karfe 6 harda rabi kamin zee ta kammala shiryawa, tasan ma faruq har se ya rigata zuwa, tayi kwalliyar ta da wani less purple and pink da ratsin black ash, kamshi ne kawai ke fita a jikinta, se fatarta dake bada wani unique shine, ta 'kagu taga faruq dinta suyi spending quality time
Har ta karasa bata kirashi ba shima bataga shigowar nashi kiran a wayarta ba,
Bisa ga mamkinta ko a kofar gurin bataga motarshi ba, "ashe dai makarar ba tawa bace ni kadai" ta je ga special table dinsu da tai reserving yasha kwalliya cikin wani grass isolated place ta zauna tana dialing number dinshi amma to her suprise taji ta a kashe, at once duka smile din dake face dinta yayi vanishing,
Ta zauna tana kallon hanyar shigowa gurin after like 15 minutes ta kuma daukan wayarta tai dialing still suka sanar da ita a kashe, ta kalli kanta ta kuma kalli hanyar shigowa, she just hope faruq will show amma inaa
Tun tana hoping har ta fidda rae and it was all dark, garin ya sake duhu tana nan zaune aka ida sallar isha'i har wasu mintuanan na shudewa buh all she's doing is looking at the way,
A hankali taji takunshi ta kuma zuba mishi ido dayake duhu keda hanyar shigowar bataga fuskarshi ba sanda haske ya dan haska shi kuma sai ta gane ma'aikatan gurin ne, yazo yake cema lokacin da tai reserving ya kare, kamar an fizgeta daga kujerar datake ta son tashi tun dazun ta miqe ta karasa cikon payment dinta dukkuwa da bata taba abincin da sukai serving ba,
Ta fita daga gurin,
Gefen titin ta soma bi a hankali tana tapiya hawaye yana zubowa kan kuncinta lokaci lokaci tana ajiyar zuciya har ta karasa gida ,, she just hope yana lpia, duk disappointment din be dameta ba kamar yadda tunanin mene ya faru dashi,
Ko dinner batai ba ranar tai sallah ta kwanta amma bacci yayiwa idanunta qaura, ta ajiye wayar cikin gajiyawa, meyasa faruq ze na yi mata haka, meyasa ko abu ze faru be tashi faruwa se yau" sune tunanin datake ta ayyanawa cikin ranta,
Ta janyo wayar tana dubawa through contacts dinta, a hankali tayi scrolling baya, ganin lambar datake nema ta bayyana a idanunta,
Tayi dialing jiki a sanyaye, bata da wani option daya wuce ta kira sarah, ita ce kadae zata iya sanar da ita halin da faruq yake indae yana gida, tun ranar da sarah ta karbi numbern ta, tayi mata magana ta watsapp, kuma sukan gaisa lokaci lokaci, amma basu taba waya ba
Ringing ta dade tanayi sai daf da zata tsinke ta dauka,
Hello ant. Zee" saran ta fada zee ta dan yi gyaran murya tana duban agogo jin muryar saran kamar bacci takeyi, karfe 12 ne na dare, sai taji dama bata kira ba, hello, sarah ta sake maimaitawa, oh hello sarah, ya kike? Dafatan kina lpia
Lpia qalau, ya gida, zee ta amsa da Alhamdulillh, sarah tace masha Allah, dafatan dae lpia dan naga dare yayi yanxu, cewar sarah
"Eh lpia qalau, na dae kira ne naji ko kinsan ya faruq yake, wayoyinshi basa tapiya" sarah tai shiruu cikin rashin sanin abinda zata sanar da ita, shin ta fada mata gaskiya ne ko kuma tayi shiru ta kyale ta,
Kinyi shiru sarah, Allah yasa dae yana lapiya," sarah tai gyaran murya, why not gobe kizo da kanki, tana kaiwa nan ta katse wayar ta kuma kashe gabadaya, zee ta rike waya a hannu tana jimami, hakan da sarah tayi ya sake dulmiyata kogin tunani da tarin tambayoyi, dakyar ta samu ta rintsa en en awannin da basu gaza biyu ba,
Tun asuba data tashi ta kasa komawa, ta tsurawa agogo lokaci tana jiran gari ya waye, ta sake jawo wayarta ta lalubi numbernshi amma babu chanji daga abinda ake fada mata jiyan, ta ajiye wayar jikinta yayi sanyi gabadaya
Tun karfe takwas tayi wanka tana gama ayyukanta, sae kuma taga 8 yayi safiya ta fita, ta zauna tana sake danna lambar tashi, aka sanar da ita switch off, itakam da zataga matar dake ce mata switch off data shaqure wuyanta, haushi yasata miqewa, takuma gaji da jira, bata damu ba koda asuba ne ba safiya ba, ta gaji fita zatai
Ta dauki er karaamar handbag dinta ta yafa gyalenta kan daurin dankwalin atamparta, dukda cewa hankalinta a tashe yake hakan bai hanata yin kyau ba dukda batae kwalliya ba,
Ba ta dauki lokaci ba ta isa kofar gate din estate din su faruq, tunda ta taho gabanta ke faduwa har yanxu data tsaya a gate din, bata wani damu ba ta shiga bayan sun gaisa da maigadi, saedae part dinshi a kulle yake gam da padlock, ta tsaya tana karewa part din kallo
"Meyasa faruq ke min hakane, meyasa beda burin daya wuce na daga hankalina na damu a kanshi, banda wani sukunin tinani se nashi cikin halin da ban sani ba, kodae be sona ne" hawaye masu dumi suka gangaro mata, ta saka hannu ta sharesu cikin gajiyawa, haqiqa so wahala ne kawae
Tana nan tsaye tana tadin zuci, sarah ta fito, dan tun shigowwarta ta ganta,
Zee ta juya ta kalli sarah dake karasowa inda take, sanda ta karaso suka gaisa, sarah tace "in bazaki damu ba muje ciki mana" tayi gaba zee tabi bayanta zuwa bangaren sarahn...
Aysha_bee ce
https://www.instagram.com/p/CBI14BnhMto/?igshid=exzlz4093xe3
π *AL_HUBB* π
The love π
By Aysha b. Naseer
Ina masoyana suke ku firfito ku marmatso kuji...
Amma kafin nan bari mu kammala karatu
Episode 36: Aches
Cikin falourn sarah ta zauna tana mai jin kanta na juyawa, sarah tai serving dinta drinks, zainab a ranta kuwa sam ba wadannan ne a gabanta ba,
Wata takarda ta zaro ta miqa mata, zainab ta karba tana son ganin mene cikin takardar dan zuciyarta na fada mata sakon faruq ne, tai hanzari budewa sanann ta soma karantawa cikin ranta
"Assalamu alaikum warahmatullah zainab dina
By the time da zakiyi receiving wanan papern im already gone, so far, yes zainab, amma banaso kiyi tunanin hakan na nupin wae karshen soyayyarmu ne yazo, ko kadan wannan ne ma mafarin soyayyarmu, inda hali ki jirani zainab ina nan zan dawo, in shaa Allah zan kiraki, i will definitely call"
Zainab ta sake karanta takardar cikin rashin fahimta, sae ta dago ta kalli sarah, ina faruq yaje? Meyasa bemin sallama ba? Ya akayi ya bar wannan takardar a hannunki?
Sarah ta kalli zainab cikin tsanaki tace " faruq yaje gurin malamin ku (levelcoordinator) right,
Zainab ta gyada kai yes
"B.u.k sunyi withdrawing dinshi from the department, accusing him of examination malpractice" zee ta miqe
"Sarah are u drunk, are u okay? Kinsan me kike fada man kuwa, faruq dinne yayi exam malpractice? How comes?" Sarah tayi sighing "zauna kiji, zee ta zauna kwakwalwarta na kokarin fassara mata abinda sarah ke fada ko zata yarda amma ina,
"Nidae shi ne kawae abinda na sani gameda wanan if you need more info u can contact your levelcord" zee tayi baya ta jingina kanta a jikin kujerar tana jin juwa, sarah ta dakko wayarta ta miqa mata, zee ta amsa tana maida idanunta kan pictures din,
Ta dan mirje idanuwanta ganin wani almara a cikin wayar, "what the heck" ta fada on top of her voice,
Ta kalli sarah idanunta tap da hawaye, meye haka sarah?" Sarah bata samu courage na kallan idanunta ba ta dan sunkui da kai, hakane zainab wanann shi ne babban dalilin dayasa faruq ya tapi beyi miki ko sallama ba, saboda ya kare mutuncinki ne, saboda yana qaunarki fiyeda yanda yake qaunar kanshi,
Hawayen suka gangaro daga idanunta ta saka hannu ta rufe bakinta tana mai cigaba da kuka zuciyarta na pounding, ta dade tana wannan kuka me qaramin sauti, ta jima tana shatatar hawaye, dan kanta ta lallashi kanta bawae dan kukan ya isheta ba sae dan tana buqatar komawa kebantaccen guri tayishi son ranta
A maimakon ta koma gida sai ta wuce school, ko sau daya ka kalleta sai kasan tayi kuka, idanunta sunyi luhu luhu, still tana tafiyar hawaye na zuba time to time, saedae ta saka bayan hannunta ta sharce, direct office din levelcord ta wuce amma se bata sameshi ba, ta fito ta koma bin titin, duk inda ta waiga cikin school din sae ya tuna mata da faruq, hakan kan kara ingiza kukan nata, can bayan school ta samu kasan wata bishiya, gurin tsit yake dan kamar daji ne saedae wucewar motoci kawae zaka na ji,
Ta tsugunna kasan wata bishiya ta sunkuyar da kanta cikin raunin zuciya hawayenta ke diga kan tafin hannunta, What a mysterious life, ko a mafarki jiya i yanxu bazata ce faruq ze tapi ya barta ba cikin kankanin lokaci haka, ta ciro wayarta tana sliding pictures din, me hakan ke nupi, meyasa sarah zatace sune dalilin tapiyar faruq?,
Bata samu amsarta ba se kurawa pictures din ido da tayi, shot hudu ne kuma sun dauku tarr koyaya imdae kasan zainab zakasan ita da faruq ne cikin hotunan a wani yanayi... Zee tana tuna sanda abin ya faru, lokacin da aka gama hidimar bikinsu zakiyya, taje gidanshi ta taddashi cikin mawuyacin hali, har tayi kokarin taimaka mishi
Bari mu dan koma baya kadan
From episode 34:
"Ta karasa bakin gadon da sauri ta zauna tana kallanshi, idanunshi a lumshe suke ya budesu a hankali yana kallanta,
Ya kara haske akan wanda tasanshi, labbanshi sun bushe fuskarshi ta rame, idanunshi sunyi ciki kamar wanda yayi jinya ta watanni,
Muryarshi ce ta ja hankalinta
Ta dan kara tauri da karfi yace "taimakamin na zauna, batayi wani tunani ba ta riko kafadarshi kusan gabadayanshi a kirjinta yake, (first shot) ta taimaka mishi ya zauna sannan itama ta zauna gefenshi, (another shot) tari ne ya rikeshi, wanda har saida idonshi ya fidda ruwa sannan ya sauka
Itama taji nata idon ya kawo ruwa amma ta hadiye kukanta, kai kana kallan faruq zakasan yana jin jiki,
Da muryar tashi da ta sake rashin dadi yace "nerh nerh ya gida? Ya hiddima?" Ta gyada mishi kai kurun
Mene ya sameka? Kuma bazaka iya kirana ba, kaje asibiti ne?"
Ya lumshe ido tarin ya sake yi sannan yace "mura ce kawai sai ciwon kai, na kira wannan doctorn na momy yazo ya dubani har ya bani magunguna kuma masu aikina na kulawa dani ba wani abin damuwa"
A kufule ta dubeshi "har ni zaka cema babu wani abin damuwa"
Yayi shiru yana kallanta a kasalance bece komai ba, sannan yace ki jirani a falour zan shiga bandaki
Tace to, ya miqe dakyar kamar iska zata kadeshi ya fadi, jallabiya ce jikinshi, sai lokacin ta lura ramar ma har jikinshi ne,
Ganin yana tangadi kamar dan maye, yasa ta zuba mishi ido cikin tausayawa, kasa yayi luuuu
Saukinta a tsaye take ta tafi da sauri ta riko kugunshi (3rd shot)
Dukansu sai suka zube a kasa, gyalen nata ma ya riga yayi nashi guri, (last shot) numfashinshi takeji gaba dayaa fuskarta da kirjinta shine yayi saurin tashi a kanta sannan itama ta miqe"......
Karashen maganarsu da sarah ta soma tariyowa "zee tace "amma meyasa hotunan suka zama dalilin tafiyarshi, in ze tapi ma kuma meze hanashi yimin sallama" sarah tace "nidae i dont know much abinda yace min shi ne "sarah ki fadawa nana zainab dina, ko zan bada rai na fansa bazan bari a taba mutuncinta ba, haka kuma makircinsu baze sakani rabuwa da soyayyarta ba"
Wani tinani ne yazo kanta "kenan su ya halisa sunyi amfani da wannan pictures sukayi manupulating faruq har ya tapi ya barni, meyasa soyayyarmu ta tsaya musu a rai har haka, nikam mene nayi musu a rayuwa da basa son tarayyata da faruq"
Kwanakin zainaab biyu tana zazzabi harda amai da matsanacin ciwon kai, sam taqi zuwa ganin likita, tana dai shan magunguna kuma tana ayyukanta na gida amma sam bata zuwa school, kuma koyaushe tana daki, dayake anty bata wani damu ba itama tana ta hidimar lil saghir yasa bata lura ba,
Tana kwance a daki wayarta tayi ringing, tasa hannu da ciro ta a chargi dan tun ranar da sukai magana da sarah tai watsi da wayarta dama babu chargi se ta mutu, se dazu ta tuna ta saka ta a chargin,
Sallama tai da wata irin murya mai kauri alamun bata da lpia, anty hawwer ta amsa tana tmbyar lpia zainab, ina kika shiga inata neman wayarki tun jiya, zainab ta lumshe ido
A hankali hawaye mai zapi ya biyo kuncinta ta hadiyi yawu mai daci, Anty haww.... Bata qarasa ida furta sunan antyn ba kukan ya kwace mata, bata cire wayar a kunnenta ba kuma bata fasa kukan ba,
Anty hawwer kuma bata ce mata komai ba, kuka take tana ajiyar zuciya da shan majina duk lokaci guda,
Sai kuma ta soma mata bayani cikin kukan "faruq ya tapi ya barni, sun sakashi tapiya bada son ranshi ba Anty, sai kuma ta soma warware mata abinda ke faruwa tun daga last call dinsu dayace mata zeje gurin levelcord, her anniversary suprise, yadda sukai da sarah kashegarin ranar, har zuwa yadda takeji yanxu,
Anty zuciya ta zapi takemin, nagaji nagaji Anty, Ammi ta tapi, Abbah ma ya tapi yanxu kuma faruq ne, shima ya tapi Anty nasan kuma baze dawo ba,
Anty ta katse ta "wane yacemiki baze dawo ba, inace cikin takardar har cewa yayi ze kiraki ya akayi kika kwallafa ranki kan faruq har haka, yanxu ki tashi kiyi wanka zan kira zeena tazo ta rakaki asibiti, banason wannan zaman dayan da kike, kina nupin bazaki karbi kaddara bane ke kam a rayuwa, kina kokarin butulcewa ubangiji, haba mana zee"
Ta share hawayen ta gabadaya rayuwar babu dadi "maza ki tashi kinji" ta gyada kai tohm ta sake goge hawaye "kuma banason wannan kukan kinyi kuka kuma ya isa haka, kina da abubuwan yi da hawayenki, zee tace to bawae dan hawayen sun dena zuba ba
Yadda anty tace hakan tayi ta tashi ta nemi ruwan dumi cikin heater ta gasa jikinta tun daga kai zuwa tafin kafarta ta saki shower, sanan ta cuda jikin nata kadan dan babu wani kwari,
Tana fitowa taga kiran zeena ta dauka jiki a sanyaye "gani nan tafe kinji sannu" tace to, mintunan da basu gaza 15 ba zeena tayi sallama a falour, Anty siyama dake fitowa a kitchen ta amsa mata suka gaisa sannan tace zee din tana daki, zeena ta wuce dakin ta tadda ta zaune karshen gado ta rungume jikinta, zeena ta karasa ta dafata, zee ta daga ido ta dubeta tana mai kokarin kada hawayenta su zubo, zeena batace mata komai ba ta miqe ta dau hijab ta saka suka fice a gidan, bayan sunma anty sallama
Mabiya kuma masoya Al_hubb
Wannan dama ce tazo da dumbin masoya zasu nunamin kauna, yau ina neman alfarma a gurinku karku watsamin kasa a ido, zanji dadi idan kuka karfafamin guiwa ππ»
Please ku biyoni a shafi na na instagram @Ayshabnaseer @aysha_bee_couture
Karku karanta ku wuce inma searching zeyi wuya ga link nan
https://www.instagram.com/p/CBI14BnhMto/?igshid=exzlz4093xe3
Pls surprise me, inaso ku bani mamaki na tashi na tadda followers bila adadin, yadda ban gajiyawa gurin typing dan following dai nasan kuma bazaku dauke kai ba,
Show me loveπ₯
Surprise me
Nima se na cigaba da baku mamaki wajen typingβ€
I will love to see my true fansπ
https://www.instagram.com/p/CBI14BnhMto/?igshid=exzlz4093xe3
π *AL_HUBB* π
The love π
By Aysha b. Naseer
Episode 37: Tawakkul
Basu jima can sosae ba a asibitin suka dawo, likitan ya bata shawarwari da magunguna sannan yace ta dena saka abu a ranta haka nan, gidan Anty siyaman zeena ta rakota suka zauna falourn, zeena na sake mata sannu, ta lumshe ido tanajin kanta na sake mata ciwo, a lokacin anty siyama ta fito ita daya da alama wanka tayi ba dadewa, ta karaso inda suke tana kallan zee sannunku da dawowa, zeena ta amsa
Sai ta kalli ledar magungunan tace "bata da lpia ne" dan harga Allah se yanxu ta lura zee din ta rame, zeena ta amsata da "eh wlh, kuma taqi sanarma kowa batada lpia seda Anty ta tuhumeta" anty siyama ta girgiza kai kadan, bataji dadin hakan ba, amma tace "Allah ya sawwaqe cikin jimantawa
Daki zee ta tashi ta wuce ta kwanta kan gado, zeena ta dibi magungunn ta bita itama, a kwancen ta tadda ta, ta karaso ta zauna saitin kanta, "kiyi haquri zee, ki kara haquri kinji" cikin karfin hali ta daga idanunta ta kalli aminiyar tata sannan ta lumshe ido kamin tace "ai nayi zeena" wani tausayinta ya rufe zeena din
Zee ta tashi zaune ta gyara zamanta ta saka hannunta cikin hannun zeena ta rike, zeena itama ta kara rike hannun da kyau, zeena tace "naji dadi da kikayi haquri kuma inaso kimin alqawarin cire damuwa a ranki dan babu abinda zata rage ko ta kara sedae ma ta sace miki kwanciyar hankalinki amma bazata dawo da faruq ba" zee ta gyada kai sannan ta dafa kafadarta "zeena karki damu in shaa Allah zan daure kuma indae faruq mijina ne nasan ze dawo ya aureni"
"Naji dadin jin wadannan kalamn a bakinki" tai murmushi sannan tace muje na rakaki, zeena tace "a'a karki damu"
"And whoever relies upon Allah, then he's sufficient for him, indeed Allah will accomplish his purpose, Allah has already set for everything a [decreed] extent" Q65:3
Bugu da kari Wasu lokutan Allah yakan rabamu da abu saboda ba alkhairi bane, ko kuma jarrabawa, koda kin rasa faruq kada imaninki ya ragu kokuma kiji kamar Allah be sonki ne, inaso ki dauka a ranki Allah yana jarabtar bayinsa dayafi so ne, gwargwadon imaninsu,
I heard yasmin talking about