Showing 6001 words to 9000 words out of 73133 words

Chapter 3 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5408

aiki, "Dear na miki maganar tapiyata and u show no concern" tace tana daura agogo "u re free mana star u can fly to any where u want to, nima next week ina da conference da zanyi attending and its a must"
"And u didn't feel its necessary to mention it to me, se yanxu?" Ta yatsina fuska "sometimes in kana behaving kmr mara ilimi wlh" his face turned red, amma yayi kokarin calming kanshi ya samu kujera ya zauna ta tallapi chin dinshi da hannu biyu,
Bata damu ba ta kama hanyarta tai waje
Wacce irin mata ce ya aura haka, konda wasa besan haka take ba, if not baze soma aurenta ba, gabaadaya baza'ayi conversation na minti daya da ita ba bata fadi wata baqar maganar ba, imagine calling ur husband mara ilimi,
Ya furzar da iska sannan a hankali ya zame yayi relaxing kan kujerar,
It is the one thing he lacks all his life, ya dauka idan yayi aure ze huta ze samu abinda yayi lacking amma it never seem to happen, he lost his mom even before he know her,
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 05: Bussiness Trip


Assiddique ya sanar da zee mgnr tapiyar da zasuyi tace mishi to amma barrister baze bisu ba saboda ze zauna nan ya kula da wasu harkokin,
Kudi ya dauka ya bata yace taje tayi siyayya dan yanajin zasu jima in suka tapi, kwanaki biyu bayan nan komai na tapiyarsu ya kammala, ya debi wasu securities din ya barwa minnatu wasu, ko kadan ba wani son tapiyar nan takeyi ba musamman da taji zasu dan dade dukkuwa da btasan wacce kasa zasuje ba,


Mota uku sukayi, yana ta tsakiya a baya itakuma zee a gaba sae driver, sanda suka shiga plane baccinta tayi batasan sun karasa ba, har suka isa masaukinsu bata gane inda sukazo ba,
Irin Apartment din data zaba tace yapi kyau sak shi taga sun sauka, bangaren security na gefe sae ciki kuma daki biyu da falour a tsakiya sannan kofar kitchen, ya nuna mata dakinta shima ya shiga nashi, tana cikin unpacking ne ta zaro frame din, a hankali ta sule ta zauna kasan dakin, its exactly the date, wasu hawaye masu zapi suka biyo kuncinta, ya murda kofar dakin ya shigo, bata san da shigowarshi ba ta sunkui da kai tana shessheqa, ya matso ya tsugunna a gabanta ze zare frame din amma ta rike gam as if her life depend on it, saesanann ta gane yana dakin ta goge hawayenta tana sauke ajiyar zuciya, ya kalleta itama ta dago ta kalleshi, why re u crying? Do u miss home?


Ta girgiza kanta, ya lura batason fadamishi komai sae bai matsa mata ba, i hav meeting to attend now,
Ya fada yana miqewa tsaye, a sanyaye itama ta tashi "pls akwae kayana a daki hop u wont mind unpacking them" ta gyada kai, yace "do you know where we re?"
Ta girgiza kanta yace "europe" da sauri taja baya kamar ya zuba mata ruwan attaruhu jikinta ya soma 6ari,
Tai kokarin saita kanta tana sauke numfashi kamar tayi kokawa da en dambe, yace se na dawo, hop ba wani matsala? Tace no babu, yace good
I will wake u up when im back" tace okay yace take care


Ta koma da baya ta zauna kan gadon da6as, "europe" furucin ya fito tareda ruwan hawayenta, a hankali wani tunani ya shigo ranta, sae taji saukin tsoron daya mamaye ta, kuma taji tamkar tayi tsuntsuwa ta fita ta dinga bin lungu da sako na garin ta dauki frame dinta ta rungume a kirji, sae ta ajiye ta nemi bandaki tae alwala, ta gabatar da salloli sannan ta dade tana jera addu'o'i, ta miqe ta karasa gyara nata kayan sannan ta wuce nashi dakin, komi neat kayan ne kawae ba'ayi unpacking ba, zee a ranta tace "Allah wadaran mata irin mint dae, Ace kanada mata amma bakasan dadinta ba, mata mara kishin mijinta, har ta yarda ta barshi ya taho wata kasar shida wata batareda ta damu ba


Ta soma gyara mishi kayan nashi a nutse, ta kammala komi, sae ta tsinci kanta da sake gyara mishi dakin, ta dan kara abin kamshin daki, juyowar da zatae ta ganshi tsaye bakin kofa tae saurin jaa baya da farko saboda ta razana sae kuma murmushi ya biyo baya dan gajere,
Yace "its late i thought ma kinyi bacci"
"U work day and night without complain, what's there when i overworked too, afterall u re the boss"
Yaji dan dadi cikin ranshi, she cared,


"I need something simple pls, my stomach hurts", tai brief smile, sannan ta wuce kitchen din, 20 minute yayi mata yawa tayi preparing noodles ta kai mishi, tare suka zauna sukaci abincin dan itama bataci ba, ta kwashe kwanukan yace ta dawo ta tayashi aiki, tace to
Zama sukai suka baje a falourn, inda yake mata bayanin ayyukan da sukeyi na kafa reshe anan din dan cigaban kasuwancinsu (anya zee iya aikin personal cook kawae take mishi)
Har karfe 12 na dare zee ta soma haamma ta dan saci kallonshi,
Gabadaya he's focused kan abinda yakeyi, babu alamar ya gaji, ta jinjina kai tunda ubangida bae gaji ba matayi ma bayace ya gaji ba, suka cigaba
Yace akwai takardu a daki ta dakko mishi suma so yake ya gama aikinsu yau, kamar zata fadi saboda bacci haka take hada hanya


Tana shiga bedroom din taji wani sanyi da kamshi, ta kalli gadon da ta gyara dazun sae taji muradin dan kwanciya,,,


Mintuna fiye da 15 sun shude amma bata dakko ba, shidae a iya saninshi takardun a bayyane suke be musu wani boyo ba, ya miqe ya nupi dakin, ya murda kofar dakin, murmushi mai sanyi ne ya subuce mishi ganin ta kwance kan gado tana ta barci abinta amma kafafunta a kasa, ya karasa ya kura mata ido, tana bacci peacefully, a hankali ya gyara mata kafarta ya maida sama sai kuwa tayi juyi ta kuma bararrajewa kan gadon, ya lumshe ido sae yanxu dayaga tana bacci yaji wani gajiya da son yin bacci, ya fita falour ya miqe kan resting sofa ba dadewa shima baccin ya daukeshi


Koda Asuba bae samu sallah ba dan ya makara itakuma da magagi a idonta tai sallahr tana idarwa tabi kan daddumar abinta bakinta dauke da lazumi baccin ya dauke ta, karfe 10 ta farka tana tasbihi, ta bude idanunta tangaran, ta dubi agogon dake dakin sae kuma tabi dakin da kallo, kamar wacce aka tsikara ta miqe daga kan daddumar, sannan a hankali ta soma tuna abinda ya faru, ta fita a dakin ta taddashi a falour yana ta bacci kan resting sofa, ta qarasa nesa kadan dashi tana kallonshi, a hankali ta girgiza kai "may you find eternal happiness in life u deserve it" the guy is the real definition of gentle


Dakinta ta koma tai wanka ta sauya amma harta fito be tashi ba dan haka ta shiga kitchen dan dora mishi abin kari kafin ya tashi, da duba babu wasu en abubuwan dan haka ta fita gurin securities
Ta sanar dasu babu wasu abubuwan kuma tanason mishi girki kafin ya tashi ne, daya daga cikinsu yace ze rakata ta siya dan yakan basu kudi koda wani abu zeyi araising in be nan, ta koma tai rolling kan pink abayar jikinta,


Mall ne amma in ka shiga kamar kasuwa kanta kanta abubuwa daban daban kusan duk abin cefane akwai wasu ma mutun be sansu ba, ta sissiyi duk abinda zata buqata harda wasu spices din datake nema a nigeria ma duk ta samu


A hanyarsu ta dawowa ne wani bature yayi ta binsu dayake a kafa sukaje babu nisa sosai kuma itama zee din tana so taga garin, security din yace "mu tsaya suka samu gefe sukaja suka tsaya, ba kunya kuwa ya karaso su, se washe wa zee baki yake, zee ta turbune fuska hakan yasa security ya rungume hannayenshi yana kallonsu dan ba karamar dariya ke cinshi ba
"U re beautiful dear" baturen ya fada da yaren nasara, ta kara hade rae tana yiwa Afzal(securityn) signal ya korar mata shi amma shikam bayaso show din ya kare tun yanxu
Bata iya amsashi ba ya kuma cewa from which country? And where do u reside?" Taji tamkar ta shaqe shi dan haushi kawai sai tai gaba fuuuu
Hakan yasa Afzal tsaidashi yace matar aure ce kuma babban soja take aure, ya zaro id ya nuna mishi da cewar shima security dinta ne, a fusace ta bude kofar falourn ko lura da bayanan ma batai ba ta zauna tana ciccin magani, Afzal ya kwankwasa kofar sannan ya shigo shima, yana ganin yadda take kumbure kumbure sae ya fashe da dariya, kuma fa gayen ya hadu" ya fada da sigar tsokana ta sake murtuke fuska, bude kofar dakinshi yayi ya fito, sanye da jallabiya da alama har yayi wanka ma,
Afzal ya miqe yayi mai salute sukai musabiha sanna Ya ajiye kayan ya fita, utama ta tsugunna ta gaidashi bae amsa ba strictly yace "wanne gaye ne yake magana" zee ta dan sassauta bacin ranta "wani bature ne ya dinga biyomu abin haushi",
Ya miqe "karki kara fita" ya wuce, zee ta dan yatsina fuska "kamar ranshi ya baci"....
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 06: Blessed hands


Ta dauki kayan cefanen ta wuce kitchen wondering about his mood, baya bata rae har haka musamman yadda ya bayyana kan fuskarshi karara, kuma bata ga aabin bacin rae ba,
Tana chopping Onion ya shigo kitchen din, she's deep in thought da batama san da shigowarshi ba, ya karasa gurin dispenser ya tari ruwa yana kallonta, is like she enjoy loosing in the world of thought, ganin onion din datake chopping ya kare batama sani ba tana kokarin yankan hannunta, yasashi ajiye ruwan hannunshi ya isa gareta yana mai rike hannunta wanda wukan take, ta dago ta kalleshi a dan razane, ya saki hannunta, "What in the world re u thinking about" ta ajiye wuqar ta sunkui da kai, "life's dynamic" ta fada a takaice da rashin son yin wani karin bayani, ya juya ze wuce tai saurin cewa
"Im sorry" ya juyo ya dubeta "about?" Ya tmbya da sakakkiyar mind, sai kuma ya dawo inda take, ta sunkui da kae tana wasa da fingers dinta, a hankali tace "dazu naga ranka ya baci kuma na pita ne saboda akwae abin da zan siya babu" yace is okay,
What re u preparing ta kalli kayan cefanen da ta ware wanda zatai amfani dasu "scrambled eggs croissant" ya samu guri ya zauna
Ya akeyi?", tace its simple, bowl din data fasa kwai me yawa ta dakko ta ce kagani already na fasa kwai da dan dama, sannan na saka ingredient din danake buqata, ta dora saucepan kan low heat sannan ta zuba kwan tana juyawa a hankali sae gashi ya zama scrambled, ta tabbatr yayi ta kashe wutar sannan ta dakko croissant din ta ska a oven ta danyi preheating a oven ta fiddo shi tayi spliting amma ba duka ba yadda ze dan bude sannan ta zuba scrambled eggs din, guda hudu tayi musu tayi plating me kyau, ya tayata dauka itakuma ta dakko mugs din da zata masu tea, kamar wasu brother and sister suka zauna sukaci abincin,
Bayan sun kammal ta kwashe yace taje daki ta dakko takardun jiya in kuma tayi bacci to"
Tayi er dariya cikin jin kunya ta wuce ta dakko ta fito, ya amshi takardun ya miqe qafa dama kan carpet yake already, zee ta lura yana qaunar zama kan carpet,
Itama ta zauna ta facing nashi kamar yadda sukeyi, maimakon yayi mata bayanin aikin da zatae sae ya Amshi takakrdun ya ajiye a dayan side dinshi, sannan ya kalleta, yace "tell me about ur family i heard u re an orphan" zee sunkui daa kai tana tuna abubuwan da suka faru iri iri," tai shiru kamar bazwtace komai ba sae kuma ta mishi bayanin kanta da iyayenta da danginta (sae a gaba me kaaratu zeji komi), yayi shiru yana sake jimanta mata rasuwar iyayenta sannan ya bata haquri ganin da yayi kamar da dawo mata da abin sabone yadda idanunta ke zubda ruwan hawaye,
Wannan yasa Assiddique tunanin maybe shine dalilin dayasa take kuka rannan daga haka suka cigaba da aikinsu


Rannan yana falour be dade da shigowa ba, zee tayi bacci already dan mostly meetings dinsu se da re sukeyi, wayarshi tae kara yaga sunan mint ya bayyana, wanann shine karo na biyu data kirashi tun zuwanshi kusan sati biyu kenan, sae dae ya kira yaji ya take wataran ma in ya kira bata dauka kuma bata biyowa hakan yasa ya rage yawan kiranta, ya daga wayar yana tunanin da wacce bukata kuma tazo yanxu,
Kamar tanajin bacci take maganar kasa kasa, her voice is one of his fav, "star ya kake?" Ya amsa da Alhamdulillh, tace ka duba net yau nayi hira da Arewatv, mantawa nai ban fada maka ba, kuma gobe zanje kano yin wani aikin"
Yaji ranshi ya soma baci "amma kinsan ke matar aurece ko?, meyasa in zakiyi abu bazakina neman permission ba" tace permission kuma sekace a kulle nake" yayi ajiyar zuciya a hankali yace "karki sake ki fita daga garin Abuja" ta dan kara sautin muryarta "me kake nupi kenan, haba kaima wasa kake wlh, nagama arranging komai tafiya kuma dole ce, yace nidae na fadamiki, tun kafin ya kashe wayar ma ita ta katse tana tsaki


Zee ta fito daga dakin da nighties a jikinta tana hamma idanunta a rufe da bacci sosai, ta karasa fridge ta dauki ruwan gora, ta bude ta samu guri ta zauna tana sha, ita batasan dashi cikin falourn ba musamman dayake idanunta da bacci kuma wutar falourn a kashe take, shikuma tunda ta fito yake kallonta, ganin yadda ta zauna tana shan ruwan yasa shi dariya ya murmusa cike da birgewa, bata shanye ruwan ba kuma bata rufe gorar ba
Ya karasa ya karbi gorar ganin zata iya zubda ruwan, yace tashi ki koma daki" ta wuce abinta ya bita da kallo,
Abu daya yayi realizing a yanxun, mint na batamishi rae zee take shigowa picturen ta gyara mishi mind dinshi that made him feel good, he feels great for having her by his side"


Kwana biyu bayan nan, da maraice suna waya da barrister, zee ta fito falourn alamun tayi wanka ne sae bulbula kamshin arabian perfume dinta take, gabadaya attention dinshi yana kanta sae yaji ma kamar be gane bayanin da barrister ke mishi, ya miqe ya barta a falourn, itakuma ta kwanta kan kujerar ta chanja channel tana kallo, sae bayan ya gama waayar ya dawo falourn, ya shigo kallo daya yayi mata ya dauke kai ya zauna ta kalleshi tace "yaya_na yaushe za'a fita dani naga gari" be kalleta ba yace "babu inda zakije kina gida, in wani abu kike buqata ki bada a siyo miki," tace "a'a bakomi kawae fita nakesonyi, yace "NO


Shiru ya ratsa dan tun zamanta da assiddique be taba bata ranta ba se yanxu da ya dage babu inda zataje kuma gashi tana so ta fita din, ta miqe daga kwancen zataje daki yace zo, ta dawo ta zauna, acct. Details dinki nake buqata, ta bashi yace "ki shirya anjima da dare zamu fita amma ki samu hijab ki saka" taji dadi har ranta tace "to
Taji dadi yadda yake protecting dinta kamar kanwarshi, koba komai tasan tana da muhimmanci itama a gurinshi ba iya matsayin cook ya dauketa ba,
Ta dakko wayarta ta bude mishi tace "yaya_na kaga hirar da ya mint tayi a gidan tv", sanda mint tace ya duba ya gani sam yaji beson gani amma yamxu da zee ke son nuna mishi sai yaji muradin gani,
Tare suka kalla hirar, farko tayi shigar less (lace) coffee da pitch sae dae dinki ya kamat gashi wuyan off shoulder ne, duk kirjinta a waje, hakama kanta ta zame dankwalin gaban gashin kanta ya fito hakama jelar attach din ta baya ya fito, gyalenta kuwa a tsintsiyar hannunta yake babu amfanin dayakeyi, ya girgiza kai, Al'amarin mint se ita...


Zee batta da hijab kato dan duk kusan abaya ne ta taho dasu, dan haka ta saka wata A_line gown wacce ta fidda shape dinta ta material, sannan ta dora hijab din a jikinta ya tsaya iya cikinta, ta kalli kanta a mirror ta girgiza kai ta dakko wani gyalen ta dora akan hijab din daga shoulder,
Tana fitowa shima yana fitowa ya gama shiryawa ya kalleta yace banason gyale ta dan bata fuska "hijab din beda tsayi ne" yace to dakko free Abaya ki saka,
Ta koma ta chanja zuwa abaya da hijab din in complete black, yace yawwa better, suka jera suka fita da securities
Zainab taita kallon hanya ko zataga wanda ta sani, sunje gurare sosai, zee taji dadin fitar shi kanshi ma haka, suka nemi ice sweet ya siya mata yace "taste it its good" ta karba tayi tasting, shima ya karba yasha, yes its nice yace yh, suna tafiya yana irga mata restuarant, duk arean da sukazo ze fadamta restuarants din da suke arean sedai in sun tashi ne ko kuma an sake sabbi, sun irga su sunpi 50, a wajesukayi dinner sai wajen karfe 11 suka dawo gida a gajiye, suna ta dariya duk suka fada kan kujera, saeda ta huta sannan ta dauki chocolate din daya siya da wasu lemuka ta kai deep freezer, tana sakawa ne yace "dazu baki tambayeni dalilin dayasa nake irga miki restuarant ba, ta juyo ta kalleshi "obviously i thought its because u like their dishes" ya girgiza kae "No
Na irga miki su ne just to tell u the taste of ur dish is totally unique, different from all the restuarant i know, ur hands
Ta kalli kalli hannayenta yace "yes ur hands are blessed" and she blushed....


Kashegari tana tashi data kunna wayarta taga alert, ta bude tana murna anyi allawee (kudin da ake biyan coppers), amount din data gani yasata sanin wannan kudin ba daga FG bane, ta duba wanda ya turo Abubakar kawae ne a name din kuma its like a company,
Ta cigaba da harkokinta amma abin na ranta, suna zaune suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login