Showing 48001 words to 51000 words out of 73133 words
Chapter 17 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt
ba hasken gareta ba, ta saka black abaya,
"Maybe bcos she dress in black and she's black too" ya fada a zolayance dukda yasan she's not black as he said
Zakiyya ta ce "i guess u re blind"
Zee kuwa wannan karan murmushi kawai tayi mai suka shiga motar ya tayasu diban kaya, koda suka karasa diba ma shine ya karbi na zakiyya duka yace ze tayata shiga dasu itakuma ta taya zee,
Anty hawwer na falour, nihal wacce ta soma tapiya lokacin ta taho da dan gudu gurin zee aikuwa ta dauketa ta jujjuya suna dariya, zakiyya ta karasa ta baje kan kujera wlh na gaji dayawa,
Shima ya zauna amma ba kan kujerar da take ba, itakuma zee ta karasa kujerar da Anty hawwer take, "sannunku da zuwa, sannu mujaheed" ta fada tana kallan wanda ya rakosu,
Zakiyya tace "anty hawwer wai kinji be gane zee ba dama be santa ba"
"Eh shima wannan ne karanshi na farko a nan kuma basu taba haduwa ba,"
"Amma Anty hawwer ko kama ai ze gani" cewar zakiyya tana murguda mishi baki,
Yayi dariya a ciki ciki kadan "na ganeku fa kawai inaso na tsokani sister inlaw ne", ya fada yana maida dubanshi kan zee
Da murmushi dama a fuskarta ta miqe taja nihal daki tace "ni nayi nan",
Har zee tai wanka ta sauya kaya ta kwanta bataga gilmawar zakiyya ba, mamaki duk yabi ya isheta suna can suna hira a haka bacci mai nauyi yayi gaba da ita,"
Dayake bayan zuhr ne sanda ta kwanta bata tashi ba sai la'asar, ta tadda zakiyya zaune a gaban dressing mirror da alama tayi wanka itama dan gashi ta chanja kaya, ga nihal a gefenta tana baccin itama,
Tashi tayi tayi sallah sannan ta jawo wayarta a nan taci karo da missedcalls din faruq, tun da rana yake kiranta kusan 5 missedcalls, tayi dialing numbershi amma sai bata tapiya ta ajiye ta haqura
Mujahid ya sakasu a gaba sai sunje masallaci sallar magriba, Anty hawwer tace "kaidai barrister baka gajiya da surutu wallahi, ka rabu dasu su huta tunda basu son zuwa"
Zee tace "Au Anty barrister ne?" Zakiyya tace "eh mana" zee a mamakance take kallon zakiyya
"Ke kuma yaushe kika san hakan"
Zakiyya bata amsaa ba sai mujahid ne ya amsa da cewar "ba kin tapi baccinki dazu ba, mukuma nan muka sha hirar mu babu ke" zee tace yayi,
Aikuwa se ga kiran sallah, yace to minti 2 kuje kuyo alwala" babu musu zakiyya ta miqe dan dama itakam tanason fita, zee ma ta tashi,
Duk sukai Alwala suka dauki nihal itama, dukda babu nisa sosai amma sai suka taddashi a bakin mota yana jiransu, (motar uncle muzakkir ce yakan barta a gida idan school zeje cos basu da wani nisa sosai)
Zee tace "ya mujahid a kafa zepi dadi" yace "salon mu rasa sallah ko"?
Ya dubi zakiyya dake rike da nihal yace "mutuniyar zo ki shiga abinki", ya bude mata gidan gaba, zee ta tabe baki ta shiga baya
"Ba mutuniyar ba aljanar ce"....
Ta zaro wayarta ta sake dialing number faruq amma har lokacin bata tapiya, jikinta taji duk yayi sanyi, sukakarasa masallacin ya saukesu suka shiga bangaren mata ya zagaya bangaren maza,
Bayan an idar da sallar, nihal taja hijabin jikin zee, tace "ya akayi"
Cikin gurbatacciyar hausarta Tace "fitsari", suka kalli juna da zakiyya, tace muje nasan bandakin,
Zakiyya ta shiga tareda nihal zee kuma ta tsaya jiransu a waje ta sunkui da kai tana dialing number faruq amma babu network gurin dan haka ta fita er harabar, ta dan daga kanta kenan ta shaqi wani kamshi da yake familiar, a take kuma kwakwalwarta ta sanar mata da waye, ta juyo a hanzarce.... Yana tsaye ya rungume hannayenshi ya jingina jikinshi da pillar cikin harabar masallacin datasha ado..
Ayi haquri da typos #not edited
Episode 32: Madeena
yayi winking dinta yana mai murmusawa a tausashe
Jikinta ya dau bari ji take kamar taje ta rungumeshi, wani sonshi tkeji ana karamata buhu buhu, ta hanzarta sunkui da kai tana kallan katon hijab din dake jikinta har kasa,
"God knows i love him" ta fadi hakan cikin ranta kirjinta na dagawa wanda beyi mata hakan sai sadda ta hadu da faruq,
Tayi baya kadan da jingina da pillar din itama dan ji take bazata iya tsaiwa ita daya ba,
Allah yasa ba mafarki nake ba ta ayyana ma kanta hakan a fili,
Dagowa yyi daga jikin pillar ya soma takowa, bataso ta daga kai taa kalleshi the next second ta tsinci idanunta cikin nashi, haka har ya karaso hannayenshi birne cikin aljihun wandonshi, yauma whites dinne amma yard ne mai laushi da haske karrr
Bai bari dayansu yayi magana ba yace "Assalamu alaik ya habibtee" ta kasa dena kallonshi kuma kirjinta ya kasa dena dagawa,
Sun shude seconds a hakan kafin ta samu ta sauke idanunta zuwa kan bakaken takalmanshi da sukayiwa farar fatar kafarshi mai dauke da dogayen en yatsunshi kyau,
A hankali ta bude bakinta tace "wa'alaikassalam warahmatullah"
Ta fada murmushi na subuce mata, yayi dariya itakuma ta rufe bakinta da hannayenta
"Ashe dai kaine" ta fada still tana dariya mai cike da annashuwa,
Yana facing dinta a tsayen shima murmushin yake "ashe dai nine" ya kwaikwayi muryarta, takuwa kyalkyale da dariya....
Wayarta da take faman ringing ta katse musu jin dadi,
Zakiyya ce ke kiranta "ya akayi?" "Kuje kawai ina tare da SHI" sai kuma ta sake dariya ta katse kiran,
Su dinma jerawa sukai suka fita a masallacin, yace ta kaishi ya gaida Anty hawwer tace to
Saukar yaushe?" Yace yanxu fa babu dadewa nace bari na tsaya nai sallah, ashe rabon naga tauraruwata ne, no wonder naji wani magnet na jana"
Zee ta dubeshi ta dubi sorrounding dinsu, babu mutane sosai inda suke, gashi sama tayi kyau,
Ji take kamar ta mutu dan dadi, ga ta ga faruq a birnin madina, no moment is will be greater saidai ko ranar bikinsu,
Ya katse mata tunanin da fadin "tinanin me kikeyi? Ta tsugunna da sauri da wayyo kafata
Shima ya tsugunno a hanzarce me ya sameta, sai ta daga kai ta dubeshi duka suna tsugunnen, a kasalance tace "so nake mu huta na gaji da tapiya", yayi smiling briefly sannan yace zo
Ta kalleshi taga dai ai kusa suke
Ina?
Yace ba kin gaji ba? goya ki zanyi sai ta miqe da sauri wasa fa nake maka, ta fada a kunyace
Haka suka jera har gidan Anty hawwer zee se wani shagwaba take mishi abin kuwa se birgeshi yake,
Koda suka karasa sukai knocking a bude take suka shiga babu kowa a falourn sai ita daya, ya tsaya daga waje itakuma ta shiga harda dan gudunta, ta fada kan kujerar ta boye fuskarta cikin dankwalin anty hawwer tana dariya da tarin nishadi
"Ke mene Haka"
"Anty SHI NE"
Tai tsaki kadan tana fizge dan kwalinta ni matsa in kin gama dariyar kya fadamin inda kika barosu barrister"
Zee ta dago "au wai basu dawo ba" da mamaki Anty tace "to ba tare kuka fita dama ina zasu dawo kuwa"
Zee ta fadawa Anty hawwer yadda sukai sannan ta dora da bata labarin zuwan faruq,
"Kiji sakara dan Allah kuma kika barshi tsaye kikazo kinata babbakamin dariya" ta tashi tsaye
Jeki ce mishi ya shigo, sannan ta wuce bedroom ta sako hijab, kafin ta dawo har ya shigo kuwa
Anty da kanta tai serving dinshi da drinks, ya tsugunna har kasa kuwa ya gaidata dukkuwa da yasan ya girmeta amma ya tabbata ta bawa zee shekaru kusan 5 koma fiye,
Bai wani dade ba urgent call din momy ya shigo a wayarshi ya dauka ya amsa with respect sosai sannan yayi musu sallama, zee ta rakashi a hanzarce ya fita da fadin ze dawo gobe in shaa Allah tunda yana gari,, bayan tapiyarshi kuwa ba kadan Anty ta dinga yabawa da hankalinshi ba,
"Kai zee amma gayen nan ya samu tarbiyya massha Allah, ga yadda ya gaidani, ga yadda yake magana da tarin ilimi"
Zee tai shiru kawai sai ta tsinci kanta da tunawa da rayuwar faruq, har yanxu batada tabbas ko ya dena shan sigarin ko be dena, amma tasan koda be dena ba to ya rage sosai, bata taba jin warinta a jikinshi, hakama bazaka taba kallanshi kace yanasha ko ya tabasha ba, jajayen labbanshi har wani spark suke badawa, a ranta tace
A gida zee tai sallar isha'i sai after isha'i su zakiyya suka dawo, bayan anty ta gamawa zee mitar "ni dama tunda naga suna wani kirki nasan akwai wata a kasa tsakaninsu wato shine ya kwasshi mota suka kama hanya suka fice aikuwa bazan kirawo su ba in sun gadama karsu dawo ma"
Da en ledoji suka dawo a hannu, zakiyya ta ajiyesu a falour sai wani annaashuwa takeyi, nihal kam tayi bacci, iya zee kadai suka tadda a falourn, ya mujahid ya wuce nashi dakin, zakiyya tace "zee zo kiga gowns din da yaya ya sai min
Dayake zee mayyar gowns ce aikuwa se gata a gabansu ta dinga budawa tana nuna mata kala 4 ne sunsha adon stones kana gani kasan ba karamin uban kudade ya kashe ba, sai guda daya ta zee din, sak kalar fatar zee golden brown, zee tasa ihu, tana karawa a jikinta tana kalla a mirror din dake dining area, wayyo Allah gobe ita zan saka idan zamu hadu da SHI,
Haka suka gama santin gowns itama Anty hawwer tazo ta gaggani ta saka albarka, harda su chocolate da shawarma ya siyo, dasu sukai dinner ranar
Tun tapiyar faruq jiyaa basui waya ba ya barta da tarin kewarshi dan ko ta kirashi ma be shiga, hakan yasa yau duk ranta babu dadi tunda ta tashi,
Ko da wasa ko kadan bataso taga sunyi nisa itada faruq, ya zama jini da tsokarta, cewar tana sonshi ma ya zama bata furuci, a gaban kowama bazataji kunyar cewar tana sonshi ba,, a haka ta cinye ranar lugus da ita, duk zakwadi da burin su hadu din kuwa ya tashi a babu ta dauki gown din ta maida wardrobe, daga ance za'aje sallah kuwa zata riga kowa yin alwala, amma haka har isha'i,
Kawai sai ta samu kanta da shiga toilet ta zauna a seat din toilet din tana dialing numbershi tana kuka, basu fasa ce mata wayar a kashe ba itama bata fasa kirannashi ba, daga karshe ta rungume wayar ta saka mudubi a gaba tana kallon kanta tana zubda hawaye, kanta har wani sarawa yake,
Zuuu wayar ta dau vibration, next second fuskarta tai displaying wide grin, sakamakon idonta da suka sauka kan sunan dear calling, kamar ba ita ce ke kuka ba
Tai picking wayar amma ta tsinci kanta da kasa cewa komai, yau baiyi sallamar ba
"Nerh nerh shine furucinshi na farko"
Ta sauke numfashi can ciki kuma tace na'am
Yace im so sorry kinji"
Tace me kayi kke bada haquri?, yace "jiya kinsan muna tare momy ta kirani so dama batasan na bar kasar ba, nd she call me back urgently, so im back to 9ja"
Ta gyada kai ita daya, tace okay lets chat yace okay kawai... saboda cost din kudin
Ta chat yake sanar da ita kamar haka
"So i was supposed to update you today kan maganr mu danacee miki akwai labari"
Sorry its short
Sharee
Episode 33: Challenge II
"Tace eh"
"To munyi magana da momy tun sanda nace miki zan fada mata, and her respond was superb baby"
Zee tai juyi kan gadon cike da jin dadi, "yace ta goyi bayana 100% kuma zata saka ayi bincike a kanki tace
"indai abinda na fada akanki hakane to kar mu damu duka zata fadawa dady na"
Shine jiyan ta sameshi da maganar ta phone tace mishi ina gama makaranta aure zatamin ko yanaso ko beso, so ranshi ya baci yayi ta fadaa sosai daga karshe ya kashe wayar,
Daga baya kuma ya kirata yace
"ta fadamin ya yarda in na gama school nayi aure amma da sharadi daya"
kuma sharadin shine, se munje anyi genotype nidake, im pretty sure he knows my genotype and i know mine too"
Da sauri zee tai typing
"Wats ur genotype?" Yace "AS"
So it all depend on urs now,
Tace
" i dont know mine dear buh im pretty sure im not AS"
Duka sukai shiru for some seconds kamin yace "okay don't worry in kin dawo din zamuga yadda zamuyi" tace to
Bata sanarwa da ko Anty hawwer abinda suke ciki ba, faruq a nashi bangaren ya gyara kwanciyarshi baayan kammala hirar su, a hankali memorynshi ya tapi kan asalin maganar sai yaji tmkar yanxu ne momy ke sanar dashi
"Sharudanshi guda biyu ne faruq, na farko shine zakuyi genotype dakai da ita dan already yasan naka so indae ita ba AS bace shikkenan yace ya yarda... Sharadi kuma na biyu shine saidai idan zaka hada ta itada Hamra ka aura, yace ya rigada yayiwa kanshi alqawari tun a baya ita ze aura maka saboda maraicinta,....
Yaji wani abu mai karfi ya tokare mishi makogwaro,
"its impossible, never possible, babu wata hamrah daze aura ma kawai zeyi kamar ya yadda ne rigimar tsohon nan tapi karfinshi" (ni Aysha b nace anya Zaka iya yiwa dady wayo kuwa)
abu kamar wasa soyayya tsakanin zakiyya da barr. Tayi karfi gwanin ban sha'awa kowannensu burinshi ya farantawa dan uwanshi,
tun suna boyewa ma har suka dena dan an rigada an gano su, sai zee taji inama ita da faruq ne cikin gida daya wayyo da an buga soyayya kuwa,
Wannan karan dama ba dadewa zasuyi ba, dan haka kafin su wuce 9ja suka biya makkah gabadayansu sukayi umarah sannan suka dawo gida 9ja,
tun daga airport gidan Anty suka wuce dukkansu, yayi kura babu laipi to dayake sunada yawa sukai ta aiki, shikuma uncle muzakkir ya fita neman abinda babu, ya siyo bayan sun kammala kowannensu yayi wanka sukaci abinci suka huta, a daren ranar uncle muzakkir ya daukesu duka sukaje gaida hajiyarshi,
Danginshi suna son Anty hawwer, itama sosai tayi ma kannenshi mata guda biyu tsaraba, hakama hajiyarshi dayake shine ke kulawa da qannenshi tun bayan rasuwar mahaifinsu, har shi kanshi barr. Ma da taimakon uncle muzakkir yayi karatu mai zurfi har haka kuma yake aikinshi a kano yanxu ma hutu ya dan dauka yaje can gurinsu Anty hawwern, se kuwa ya hadu da zakiyya dama hajiyarshi ta matsa mishi da maganar aure, su zakiyya se wani sunne kai take, wai ita anzo gidan surukai
Se kusan 10 suka bar gidan suka bar barr. Tunda dama nan yake zama da cewar gobe zasu dawo,
Kashegari kuwa tun bayan tashinsu da safe suka ida komai suka kama hanya gidan Abbah jabir, suka kai tsaraba a can suka bar zakiyya, sannan gidan Anty siyama itama suka kai ma little saghir tashi da tata tsarabar, a can suka tadda minnatullahi itama ta dawo kasar ta gama karatunta na medicine a U.S tana cukucukun service shine ta dawo gidan Anty, zee bata zauna ba tabi Anty hawwer gidan hajiyar uncle
A can suka yini ranar, har zee ta fara sabawa da su bahijja da badi'a (qannen uncle muzakkir)
Nihal kam gabadaya gidan ma ta koma, hajiya tace su bar mata ita tunda ba yanxu zasu koma saudi ba,
Zee babu kunya taqi komawa gidan Anty siyama tana gidan Anty hawwer abinta
Kwana biyu bayan nan, su biyu ne kawai cikin gidan tunda nihal tana gurin hajiya uncle ma ya fita
Zee tana zaune basu dade da gama waya da faruq ba, duk ta gaji da zaman gidan sai yanxu ta gane irin shaquwar da sukai da zakiyya da ko hira ce tana nan tana yi mata ko mitar wani abun
Sallama taji ta amsa tana miqewa jin kamar muryar zakiyya aikuwa se gasu su uku da kubra da khairi da ita,
Nan fa aka dinga murnar ganin juna, suka baje hira har suka tada Anty dake bacci itama ta fito suka gaisa
Zakiyya harda jakar kayanta, aikuwa zee ji tai kamar ta hadiyeta dan dadi,
Anan suka yini khairi da kubra suka tapi suka bar zakiyya,
"Zakiyya tace "haba inaaa zee ai yanxu bazan iya zaman gidan nan ba shiyasa na gudo wlh ni yanxu ai na saba dake" suna cikin hira yayo sallama
Zee ta kalli zakiyya da tuhuma
"Kodai bazaki iya zama babu shi ba, kin saba dashi" zakiyya ta dauke kai oho dai....
Wannan time din zee tare da faruq sukai karatun semester me zuwa ta level 3 yayinda zakiyya kuma zata shiga level 2
Result na wancan semester din shima ya fito, zee da faruq sunyi wuta shi 4.4 itakuma 4points dot,
Sai bayan sunyi registration sannan Anty hawwer da uncle suka koma suma su zee suka koma gidan Anty siyama, ta tarbe su sosai kuwa dan tayi missing dinsu, ta gane amfaninsu sosai sanda basa nan,
Zee da faruq sun shirya kan ranar laraba zasuje ayima zee test din dan sanin genotype dinta, momy da kanta ta hadasu da wani doctor ma ba lab attendant ba, a bisa umarnin dady din
Suna zaune jigum suna jiran result tabbas idan aka auna bp dinsu a lokacin ya hau,
Sun dan sha zama danma sune sunsan doctor din da saidai suje su dawo, aka miqo result din faruq ya karba sukai musabiha da doctorn,
Sai da suka shiga mota sannan faruq ya soma budewa, zee tai jigum tana kallanshi, har dauke numfashi tayi sanda ya bude gabadaya
AS pattern shine abin da ya bayyana... Ya ajiye yana mai dora kanshi kan sitiyarin,
Zee tasa hannu ta dau takardar hannunta na karkarwa
"How comes AS"
bata ta6ayin genotype ba amma babu AS a gidansu tasan both Amminta da Anty hawwer AA ne Abbanta ne dai bata sani ba tadai san ba SS bane
Hawaye yabi kuncinta murya a raunane tace "shikkenan karshen alaqarmu tazo?, itama momy bazata yarda ba, Abbah ma baze ta6a yarda ba,, luck is not on our side"
Ta fashe da kuka
"Only if they knows" ta dago tana maimaita furucinshi kan labba, only if they knows, they will for sure mana faruq, doctor ya sani kuma ze fadawa momy"
"Ko duk duniya zasu hadu babu wanda ya isa hanani aurenki balle wannan takardar" ba zato ya kunna motar yaja a guje, sautin mumfashinsu ne kadai ke tashi har ya isa kofar gidan ya ajiyeta, saidai batakoyi yinkurin fita a motar ba shima baice mata fita ba
Sun shafe