Showing 72001 words to 73133 words out of 73133 words

Chapter 25 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5412

rike cheeks din


Suka raba kwanaki tsakaninsu, Assiddique ya zama d'an gata tsakanin mint da zee, sun koma makaranta, babu wani stress,
Watanni hudu bayan nan zainab ta fahimci bayyanar ciki a jikinta, sanda Uban gayyar ya fahimta sai ya hanata komai yace babu abinda zatana yi shikam ya haqura, dukda haka takanyi wasu abubuwan idan baya kasar


Zainab ta kammala karatunta sucessfully lokacin cikinta nada watanni 7 har ya fito, taso komawa gida amma ya hanata saboda cikin ya tsufa yace a nan zata haihu, sanda mint taji labarin cikin zee tayi nadama har cikin ranta, ta tuna kyakkyawar yarinyarta Asma'u, haka nan ta barwa Assiddique zainab har zuwa ta haihu tace yaje ya zauna da ita tana buqatar wani kusa da ita,
Ba kadan ba mint ta birgeshi yaji babu ya ita a wannan lokacin,


Zuwa yanxu zanso naji daga bakin mai karatu wanne darasi kuka tsinta cikin wannan labari


💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 48: Finale


Las las las
Zainab ta haifi beautiful daughter dinta, skin clour na Assiddique, amma kusan gaba daya kamar zainab tayo, Ranar suna aka maida wa yarinyar Asma'ul husner, zainab ta dawo nigeria inda tayi wankanta a gidan Anty hawwer, bayan ta gama wanka ta zagaya gidajen 'en uwa har gidan Anty siyama tayi mamakin yadda Anty siyaman ta sake mata sai gashi harda hirarsu,
Raanr da zainab zata koma gidanta da kanshi yazo daukanta, motoci uku ne kawae, zo kuga zumudi gurin Assiddique dan ba karamar kewar Amaryar tashi yayi ba, zainab tayi kwalliya tayiwa husner ma, Anty hawwer ta sake mata hade hade na gyara wanda zata cigaba koda ta koma gidanta,
Har ya shigo gidan Anty ta bashi abinci ya san taba bai ganta ta ko gilma ba, ya kammala ya tashi yace to Anty zamu wuce, ya fita ya tsaya jiranta


Tana sanye cikin atampa da babban gyalenta Anty na rike da husner suka fito, ya zuba mata idanu yana murmushi shi daya,Anty ta miqa mishi husner tace "to Allah ya tsare" yace Amin Anty
Ya zagaya ya shiga, zainab tayiwa Anty sallama ta shiga itama
Ya kalli husner dake hannunshi "tubarkallah har tafiki kyau" zee ta dan bata fuska "haba dai" yace kwarae ma kuwa ko baki yarda ba" tayi mishi shiru
Ya kamo hannunta yace "kinyi shiru" tace "kasan yadda na soma sonka?"
Yace "A'a tell me how"
Ta ce "i fell inlove with you the way you fall Asleep slowly and then all at once"
Idan kika kalleni how do you feel
Tayi murmushi idan na kalleka i remember the verse "So which of the favors of your lord will you deny"
(Cikin suratu Arrahman fabi'ayyi'alaa i rabbi kumaa tukazziban)....


Wannan karan gidan yallabai suka sauka saboda nemansu dayakeyi, zainab ta sunkui da kai gaban yallabai kamar yadda taga Yusuf yayi, shikuma yallabai yana rike da husner yana wasa da en yatsunta
Wasu takardu aka kawo, yallabai yace da mutumin ya miqawa zainab, zainab ta saka hannu biyu ta karba yace "Lokacin da er uwarki ta samu juna biyu nayi mata irin wannan makamanciyar kyautar, dukda nata kudi ne, kekuma takardu ne na makaranta,
Tunda sakamkonku ya fito kuma yayi kyau yadda ake buqata na tambayi mai gidanki wanne aiki kike sha'awa sai ya sanar dani baki muradin aikin Asibiti kin fison koyarwa so samu a university ko college, wannan makaranta health college ce kuma mallakinki ce, komai na bukata An zuba sai dai in kika sake dubawa sai muga me ne akai missing tunda harka ne na project kuma mutun ajizi"
Zainab sai taji hawaye ya zubo mata "Nagode Abbah ubangiji Allah ya raya zuri'a Allah ya jikan magabata ya kyautata namu karshen" yayi matuqar ji dadin Addu'arta yayi murmushi irin nasu na manya ya cire wani zoben azurfa dake hannunshi ya saka a karamin hannun husner yace itama ga nata tukuicin


Sai yamma likis suka baro gidan yallabai zainab sai murmushi take ita daya tana ta fadin Alhamdulillh ala kulli haal,
Hanyar gidan mint suka dauka zainab dai batace komai ba, har suka karasa amma sai yasa akai packing a kofar gidan, suka fita suka shiga da kafarsu


Gaba daya taga gidan ya sauya, maimakon su yi hagu sai sukai dama, taga wani tamfatsetsan gini ya bayyana gabanta, barka da zuwa sabon gida sabuwar Amarya, ta juya ta kalleshi kawai sai ta rungumeshi
Dukda gidan zee baikai na mint girma ba amma tsararre ne sosai, kuma duk a hade suke, wancan na uk kuma duk wacce ya tapi da ita sai ta sauka tunda dukansu ayyukansu a nan nigeria yake


Shekarun husner hudu kafin zainab ta samu wani cikin a lokacin zainab kana kallonta kasan ta amsa sunan matar Assiddique din, naira da dollar sun zauna, itama mint bayan bayyanar cikin zainab t gane ta samu rabo, batareda kowa ya sani ba tayi running test domin a gane genotype din yaron aikuwa cikin sa'a ya fito As ranar sai da tayi kuka ta koshi dan murna ta kuma godewa sarki jalla, ta sanar da mijin nata komai, shi kanshi yaji dadi sosai bama kamar ganin irin farincikin dake kwance kan fuskarta, Assiddique yana iya kokarinshi wajen yin Adalci tsakaninsu


Tammat bi hamdillah,
Alhamdulillh Allah yayi na kawo karshen wannan littafi nawa, idan kun karanta kuma kunji dadinshi kun karu da wani abu nima kuyimin Addu'a nagode


Ga tattaunawar da mukai tsakanina da 'yar uwata fatima gameda wannan littafin


Fadima: Wai nikam in tmbayki Me yasa Baki aurawa Faruq Zee ba


Aisha: 1. Haka na tsara labarin
2. Zee loves him too much irin wannan soyayyar da Allah ya hana
3. Inaso mutane su gane ba kowa ne zakuyi soyayya ze zama dole mijinka ne ba
4. Ya kamata mint ta gane wasu darussan


Fadima:
2 dai is d strong one
Kinsan me yasa na gne hkan Sbd Ina wurin da Prof ya kirata yyi mta warning
Kinsan Faruq ya shigo gidan Yana lallashinta
1. Ya rike mata hannu
2. Ta kwanta akan kirjinshi Bata San ma tsawon time din da suka dauka ba
3. Zuwa gidanshi da tkeyi Kuna masoya Kuna kebancewa is not fine
Duk wnn sun sabawa Allah sbd soyayar da ta rufe musu Ido Kuma Bata taba Jin ma Alamar nadama ba .


Number 4: Kingane Sosai ma kuwa kaii a wnn ma Kamar ba mace ba, Akan wani dalili zan bar wata tanawa Mijina girki Ya dauke ta su bar kasar for weeks da sunan cook wllh ba wnn mgnar tab!


Aisha: yes yes
Kawae wahala zatasha hannunshi da rashin kwanciyar hankali
Kuma ya kamata ta girbi sakamakon tawakkalinta
Bawae dan faruq baya sonta ba


Fadima:
Yh I understand
Amma sometimes rabuwar yna Zama maslaha
Shikam Yusuf is d lucky one Allah ya biya Masa ladan hakurin da yyi da Mint


Ina fatan 'en kungiyar Assiddique #teamAssiddique zaku gane dalilin dayasa na aura mata shi bawae dan kun rinjayi en team din faruq ba... Allah yasa mu dace
Nan bada dadewa ba in shaa Allah zan fara sabon book
Gaisuwa gareku masoyana
Ayshab ✍🏻🤝🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login