Showing 21001 words to 24000 words out of 73133 words
Chapter 8 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt
Jabir bayan umman halipa tayi sati daya ta dawo umman khairi ta tapi,
Cikin zaman da tai a gidan yasata fahimtar abubuwa da dama,
Ta fahimci akwai hassada da suke ma juna a tsakaninsu, kuma kowa be damu da al'amarin kowa ba, wani bai taimakon wani kowa na kyashin taimakon dan uwansa indai ba shine ze amfana ba, ga shegiyar lalaci gun matan gidan harda yaran gidan, zakiyya ce kurun me dama dama hakan yasa sukafi shiri da ita kaf gidan dukkuwa da ba sa'arta bace amma tasu kam tazo daya,
Wata ranar lahadi su zee suna shirin fara jarrabawa, ta maida hankali sosai karatunta take dama ba daga nan ba kam,yau girkin na Anty siyama ne (uwar dakin zee),
zee taje ta gyara mata dakinta da bandakin dan indai tana gida itake mata aikin dakinta, sannan ta fita zuwa main falour inda mafi yawan yaran suke, Anty siyama kuma tana kitchen tana kokarin daura sanwar rana, zee ta karasa tace "Anty siyama kawo yau nayi girkin tunda ina gida," ba musu ta bar mata girkin sannan ta soma mata bayanin abinda zata girka, "jallof ce ta shinkafa zanyi dan inaga zatapi min sauki" zee tace to
Daga haka ta fita a kitchen din, Zakiyya ta shigo tana cewa bari na tayaki da en yanke yanke, zee tai murmushi (note: zee takan taya itama zakiyyan aiki sosai a baya hakan ne ya saka ma zakiyya kaunarta itama tai kwadayin tayata)
Akwai komi da zee ke buqata dan haka ta soma girki, this is the first time dazatayi girki a gidan,
Kan kace me gida ya dau kamshi, daya daya yaran kan leqo kitchen wannan yace mukam me ake dafamana, wani yace "ah'ah yau kece a kitchen kenan" hmmm koni na kagu naci wnn girki, cewar zakiyya dake tsaye ta jingina tana kallon yadda zee ke sarrafa kayan kitchen
To a wannan rana kam ansha santin girki, dukda jallof ce mai sauki tayi musu amma kam sunji banbanci da abincin gidan... Cikin masu santi hardasu kubra dake fadin "ai kawai zee kizo ki bude kafteria a school dinmu wlhy zakiy ciniki" me za'ayi inba dariya ba, itakuma har ranta take fadi.... Suna nan duka suna santin abincin Abbahjabir ya kira wayar Anty siyama, ta dauki wayar yace "ta miqawa Zainab,, " Anty ta miqa mata wayar sai bayan da suka kammala wayar da zee ne, yace ta kirashi da numberta anjima da wasu bayanai, sannan ta miqawa Anty wayar
Bayan taje daki ta dauki wayarta ta kira Abbah jabir din kmr yadda yace shikuma yace ta tura mai acct. Numberta koda ze bukata a gaba, bayan sun gama wayar kuwa tamai sending....
Karatu fa yayi zafi yanxu zee da zeena basa barin school da wuri dan tare suke karatunsu, ita zee tana part of Basic medical sciences ne, zeena kuma Allied health science, lectures dinsu duk na level 1, iri daya ne sai en practicals da ake warewa, daga level 2 kuma kowannensu ze kama bangarenshi but still akwai lectures din da zasu dinga haduwa....
"Zee nikam yanxu kin gama zama typical late comer, kin shahara a makara duk sanda muke da lectures da safe"
Zee ta dara tana kallan yadda Zeena ta dage tana jaraba, "kyayi dariya mana, nidai Allah yasa da exams dinma karki makara dan akwai na safe sosai a ciki, Zee tace "ai da wuri zan dinga tashi, ni na isa na makara da exams"
Kiran Anty hawwer ne ya shigo wayar Zee ta fadada annashuwarta tana maijin dadi ta dauki wayar, gaisawa sukai tana tmbyar ina nihal Anty hawwer tace duk suna nan qalau
"Yanxu Zee saura sati uku ki taho ko? Dan ina nan ina lissafi" Zee ta jinjina kai cikin tsananin murna, eh Anty na, "kina school yanxu?" Zee tace eh "to ayi karatu dayawa, Allah ya baku sa'a, ki gaida zeena dakyau," daga haka suka yanke wayar....
Exams suka fara lami lapiya, dukda Zee kan samu rashin jin dadin karatu dan indai ba a makaranta tai ba to beyi mata dadi sedai ta fita tsakar gida da daddare, dan yaran gidan akwai hayaniya kuma dakin nasu su uku ne babu inda zataje ta kebe,, babu wani aiki datakeyi yanxu dan sanda zasu fara exams din ma Anty siyama ta tapi gun Abbah jabir, kuma ta kulle dakinta, Rannan zasuyi exams Zee bata samu tayi wani karatun arziki ba, gashi kuma ta sassafe ce, dan haka magrib nayi ta kwanta bacci saboda ta tashi sai ta saita alarm dinta,
Karfe 10 ta tashi ta watsa ruwa, tayi sallolinta sannan ta fita tsakargida wani dan lungu, dayake akwai kwan lantarki a gurin yasa sauraye basu dameta ba, taita karatunta, sauran yara da mata kuwa kowa ya koma daki ita ko abinci ma ta mance bataci ba dan sai la'asar ma tai lunch,
Ji tayi karatun be shiga hakan yasa ta gane something is wrong tasan kanta mutun ce me son karatu, ajiye pen din hannunta tai ta shiga safa da marwa da son tuno me ta manta? Mene yasa karatu ya zama boring,
Tana cikin tinanin taga Zakiyya ta pito daga dakinsu dauke da mug na shan tea/coffee, ta dan murmusa sannan ta ajiye takardun hannunta ta nupi gun zakiyya wacce batama kula da ita ba, saida Zee ta dafata sannan ta waigo a dan razane, Zee tasa mata dariya, zakiyya ta tsaya kallonta for some seconds sannan tace Zee kinsan wani abu? Zee ta dena dariya tana girgiza kai ganin serous face din da zakiyya tai
"U re really awesome, u hav dat inner beauty" Zee ta kankance idanu cikin rashin fahimtar inda ta dosa sannan tace "and why re u complimenting all of d sudden?"
"Zee wlhy dagaske nake as u laugh now i just saw a gorgeous Zee in you, or maybe it's bcos u hardly laugh, u smile more our silent Zee our damsel"
Zee tai murmushi kawai tana girgiza kai tai gaba "i donno wat come into u dis night maybe u met with a sprit" ta karasa fadi tana acting horror face... zakiyya tai dariya kadan itama tabi bayan Zeen dake nupar kitchen
A kitchen din Zee ta soma tattara kayan da zatai amfani dasu, Zakiyya tana dariya ta ajiye mug din hannunta "to me za'a dafa mana kuma bari na tsaya nai kallo" Zee tace "tsaya ki gani ko na girka dake ne?" zakiyya tace eh ayi dani, Zee tace okay....
Shiru ne ya biyo baya kamin zakiyya tace "wlhy zee fa dazu gaskiya nake fadamiki, kingane ko, irin silent beauty dinnan gareki wanda ba kowanne ido ne ke iya gani ba, se mai idon basira irin mu" Zee tai murmushi jin hirar zakiyyan, to sannu masu idon basira....Zakiyya bataa fasa ba ta cigaba, "just look at u in kaji ana fadin the real african beauty to kece kat"
Zee ta tura mata mug of coffee din, "ungo ya isa dama cin hancii kike bani to gashinnan asha lpia" zakiyya ta karba, itama Zee ta dauki nata duka suka fito, saida zakiyya taje gun karatun nata sannan tasha tana ta santi, itama Zeen shan nata take, zakiyya tace " the taste is milky sugarcy,no juicy, no tasty indeed its superb" ta fadi tana hade babban yatsanta da manuniya ya bada zero...👌🏻
Coffee din da Zee tasha yayi boosting energy dinta na karatu ya dawo...
Haka wannan semester ta kare bayan sunsha exams, yanxu Zee har ta saba da zaman gidan Abbah jabir, musamman kasancewa da zakiyya wacce ta kasance wadda sukafi kusanci acikin gidan,
Zakiyya ta maida jakar ta rufe, ta karaso inda Zee ke zaune tana danna waya, "nima gaskiya inaso na biki mu tapi gidan Anty hawwer tare, Zee tai er dariya "to ai Abbahjabir zaki fadima ba ni ba" zakiyya ta tabe baki "badai kyaso muje tare amma da kinaso ai da kinyi mai magana" Zee ta dafa zakiyya "er uwa kiyi haquri yanxu kinga lokaci ya kure tunda gobene tapiyar ki bari next in shaa Allah zanyima Abbah magana sai muje tare" Zakiyya tace to Allah ya nuna mana daga haka suka shiga wata hirar har khairi tazo ta taddasu itama tai joining,
Kashegari kamar yadda aka tsara din Zee ta tattara komi nata ta kama hanya dama already sunyi magana da Abbahjabir ta waya ya tabbatr komi ya kammalu sannan ta hau jirgi suka daga saudiyya bayan rakiyar da su zakiyya sukai musu...
Dadi kam da annashuwar da Zee ke ciki ma har ba'a magana, ta rungume hannayenta biyu a kirji tana doki da son haduwa da er uwarta tsoka daya a miya bayan jirgin yayi balance a sama ne ta cire belt din tana mai relaxing kan kujerar sannan ta lumshe idanunta tana mai murmushi lokaci zuwa lokaci,
Ya sake kallonta a karo na barkatai, anya wannan kalau take kuwa, she's just smiling and blushing alone, ya dan ja tsuka bamai sautin qara ba,
Koda masu tmbyar abinda mutun zeci suka zo gun Zee cewa tai itakam ruwa ma kadai ya isheta, dan batajin zata iya cin wani abu yadda take dokin nan bata ma son cin komi, na kusa da ita aka tmbya, itakam se yanxu ta tuna akwai mutun ma kusa da ita,
Dayake shine a window itakuma tana baki,,, sanda tazo ma zamanta kurun tai bata kalli inda yaake ba, shima din bai damu da hakan ba, sama sama ta dan kalli fuskarshi, sai kuma ta sake juyawa ta kallleshi, his face seems familiar, amma a ina tasanshi, ganin kallon nata yayi yawa ne yasa ya kwanta ya rufe fuskarshi da hanky, Zee ta tabe baki a ranta tace aikin banza, amma a ranta tanaso ta tina inda tasan fuskar matashin saurayin da be wuce shekaru 31 ba a duniya,
Dayake jirgin nasu direct saudi ne yasa basui tsaye tsaye ba, koda jirgin su Zee ya sauka uncle muzakkir (mijin Anty hawwer) ne yazo ya dauketa da kanshi danma saida tasha jira yana kiranta yana ta bata haquri kan gashinan, hakan yasa mutane da dama sun tapi sun barta a gun...
A gajiye ta karasa tsararren gidan na Anty hawwer inda suke zaune da maigidanta a birnin madina, uncle muzakkir ne ke sanar da ita Anty hawwern tana school bata dawo ba, er aikinta Binafat kurun ta tadda, dukda gidan kuwa ba wani kato bane, selfcon ne mai dakuna hudu, sai kitchen babba da toilets in each bedroom, akwai dining area, gidan kam tsararren mai kyau, wannan shine zuwan Zee na farko gidan, uncle muzakkir ya nuna mata dakin da zata zuba kayanta, ta karasa takai kuwa, sannan yace shima ze fita anjima ze dawo, Ruwa ta shiga ta watsa lokacin karfe 11 da mintuna ne na rana a saudiyyan, hakan yasa ta kwanta, bata tashi ba sai karfe kusan 12 da en mintoci ta tashi ta wanke fuskarta ta fito ta shiga inda ke sakata nishadi dan har lokacin anty hawwern bata dawo ba, Binafa ta tarar tana aikin chopping veges din da zatai girki dasu, suka sake gaisawa da Zee sannan tace "wat are we having for lunch?" Binafa tace "am yet to decide" Zee ta jinjina kai tana kallan kitchen din da sake dubawa, ta kalli kayan da Binafa tai chopping sannan tace okay just leave the rest to me i will cook today" binafa tai shiru tana tinani "but ma i dont think ma'am will like d idea i think is better u let me do my job pls" Zee ta jujjuya kanta, sannan ta dafa binafa "just trust me she'll not only like d idea but she'll love every bit of it, hav faith in me" Binafa ta jinjina kai tana murmushi kadan nervously, dukda haka bata bar kitchen din ba tana tayata da miko wannan miko wancan,
Special rice ta dafa wacce tasa veges da curry (wanna see d pic? Its on wattpad) snan tai sauce da kaji kamar pepper chicken....
Tun kan ta karasa suka jiyo motsin taba kofar shigowa falourn wanda ya tabbatr musu cewar Anty hawwern ce ta dawo, dan gurin parking din ba hade yake da gidan ba, underground parking space ne saboda su basu fiya parking motoci cikin gida ba sunfi gane su haqa kasa sui underground, duk mostly haka gidajensu yake.... Shigowar datai ne yasaka taji wata kasala ta shigeta saboda kamshin girkin daya turare gidan, (cikin sirrikan girkin Zee shine yanada tashin kamshi ta iya hada simple spices kuma su bada kamshi mai tashi da zai cika duk wani lungu da sako ya tadama da yunwarka,
Wani kasaitaccen murmushi Anty hawwern tayi "this is my sister's handwork for sure" ta fadi tana nupar kitchen din da nihal dake kafadarta tana bacci, Zee na tsaye ta harde hannaye tana jiran shigowar anty hawwern dan tasan tabbas zata shigo din, aikuwa ta shigo tana mai zumudin son haduwa daa qanwarta, dukkansu murmushi suka sakar ma juna mai cike da tarin sakonni, Zee ta karasa gun Anty hawwer dake tsaye dauke da nihal, ta saka hannu ta amsheta tana mai shafa bayan diyan, sannan kuma sukai sidehugging juna, Binafa tana kallonsu tana ta murmushi abinta dan sun burgeta, so classy
Saida Anty hawwer tace a bude mata tayi tasting abincin dake bada wannan kamshi dan ko tantama batayi tasan shinkafa ce saboda sanin soyayar dake tsakanin Zee da shinkafar.... Sanda ta tauna shinkafar ta kusa hadiyewa sanna ta jujjuya idonta, "ohh i really love it," Zee tai dariya ta kalli binafat "haven't i told u she will love it" Anty hawwer tace definitely its yummy".....
Koda uncle muzakkir ma ya dawo, ya yaba da girkin Zeen dukda dama ya sabacin abincika masu dadi daga gurin matar tashi, but still there's special taste in Zee's blessed hands"... Tunda Zee tazo Anty hawwer ta dena tapiya da nihal makaranta, take barinsu tare a gida, kuma Zee ta karbe girkin gidan daga hannun binafa, sedai in Anty hawwer na nan suyi tare abinsu
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 16: challenge
Ba kadan ba Zee ke enjoying zama tareda Anty hawwer ta sake koyan wasu sirrikan girkunan gun Anty hawwern, dana waje dana gida dan har tuwo ta sake kwarewa a wajen girkawa dukda ba wai ita abincinta bane, duk ranar da Anty hawwer battada school sukan fita shaqatawa taita nuna mata gurare, wani sa'in ma idan karatunnata ba yawa tare suke zuwa makarantar su dawo, hakan yasa yanxu Zee tasan gurare dayawa har masallaci ma tana zuwa dakanta in an kira sallah, dan gidan nasu baida nisa da masallacin madinan,,,
Its another bright saturday, weekend, duka su biyun sun kimtsa ko ina babu abinda ke tashi sai kamshin turaren wuta, dukda sukanyi gyara amma aikin na yau na daban sakamakon bakon da zasuyi a gidan,
Zee tace da Anty hawwer "ni fa i don't get it, wats so special about dis guest dat u two are all cautious as if its d sheikh al sudais dats visiting"
Anty hawwer ta girgiza kanta tana tabe baki, "mind ur tongue u girl u re so annoying wallah" Zee itama tabe bakin tayi, okay acikin mu naga waye annoying ai... Haba hav been pleading with since dis morning for u to tell me who is visiting but u re dodging"
"Okay yanxu bari na fadamiki ko hankalin kowa zai kwanta,
Jiya da Abban nihal yaje sallan magrib a masjid ne, suka hadu da wani old friend of his tun school time, kuma babban mutun ne a kasarmu nigeria, dan nasan wa'inda basu san face dinshi ba daddaiku ne,"
Who is he? Zee ta tbaya
"The great Alh. Yusuf Abbakar As_siddique, the As_siddique's CEO, the young billonaire, the African's third billionaire, the Nigerians number one billonaire"
So are u satisfied my lil sis?"
Zee ta jijjiga kai kmar kadagaruwa jin wannan uban kirari da ake mishi,
Kuma kinsan meyasa yace zezo? Zee ta sake jujjuya kanta a sanyaye
"Saboda Abban nihal ya fadamishi babu inda ze samu well served delicious food, se a gidanshi" ta karasa fada tana nuna Zee a matsayin ita kenan me wannan girki,
The moment he heard about d nice dish he quickly agreed without any hesitation, do u know why?"
Zee ta sake karkada kai a hankali
"Well bcoss he loves food my dear, he's addicted to nice dishes and he hardly get the time to eat due to his tight schedules"
Miqomin wayata na nuna miki pics dinshi, Zee ta janyo wayar Anty hawwern, itakuma ta tapi searching sunanshi a insta, saidai taga acct. Din nashi private ne, dan haka ta sauya akala ta koma Wikipedia, nan da nan sai ga hoton, Alh. Yusuf ya bayyana, Zee ta amshi wayar tana kallon hoton, he's d same guy data hadu dashi a jirgi sanda zata taho, her jaw drop.... a cikin ranta take fadin "idan dai har shidin billonaire ne kamar yadda anty hawwer ta fadi, meyasa ya biyo flight bebi private jet ba?, and ya akayi yake da time haka da har ze iya sparing yazo dinner kuma why is he all alone sanda ta ganshi babu wani guards, ko P.A atleast".....
Da idanuwa Anty hawwer kebin abincika da kallo kamar ta cinyesu duka, they re all served in an inviting way, plated so nicely and lovely, but u won't judge until the mastication starts,
Karfe 7 ta buga daidai sanda suka ida parking motocinsu suka shigo cikin gidan, sunata hira jepi jepi abinsu, bazaka kalli As_siddique kace shine As_siddique dinba a yadda yake free abinshi saidai in ka kalli suturar jikinshi zaka san naira tayi ihu, already everything is served on d dining area, koda suka shigo falourn babu kowa, ya sule takalmanshi tun daga bakin kofa, kyawawan kafafunshi suka bayyana, ya karasa dining area batareda ya jira uncle muzakkir ya mishi iso ba,
"I just can't wait seeing d dining full already" ya karashe mgnr yana murmusawa, shima Uncle muzakkir yai dariya, babu wani damuwa ya zauna sosai ya sakko da abincikan kasa dan ba al'adarshi bace cin abinci a sama, yayi serving kanshi dan already, his mouth is watering,
Bai tsaya jiran ayi mishi bismillah ba ya soma ci, uncle muzakkir kuma dakinsu ya wuce ya tarar da Anty hawwer taa fito daga wanka tana shiryawa ma almost done, dankwali kurun ya rage, haka ya saka ta daura tasa gyale suka fito,
Koda ta shigo falour mamaki ya