Showing 57001 words to 60000 words out of 73133 words
Chapter 20 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt
tawakkul
"What exactly tawakkul means?, it means i dont see the solution, i dont know what's gonna happen tomorrow but i do know one thing FOR SURE and that's 'inna ma'iya rabbi sayahdeen' indeed my lord is with me and he'll guide me through,
When we have that kind of attitude Allah promise of something, He'll spilt cease for us, that situation that look impossible Allah will make a way out, that situation we dont see a solution Allah will give a solution'
Zainab ta kara gyara zama tana sauraron jawabin da Anty hawwer ke mata tana mai qara jin kwarin gwiwa da sallamawa ubangiji dukkan lamuranta, zuciyarta na cooling
Sannan ta dora da fadin
Again cikin alqur'ani mai girmaa Allah yana cewa "wani lokaci zakuqi wani abu amma shi ne Alkhaiirnku, wani lokaci kuma zakuso wani abu amma ba Alkhairi bane a gareku" a karshe yace "Allah shine mafi sani, mukuma bamusan komai ba"
Tunda Allah shine ya sani se mu miqa lamuranmu gareshi muyi fatan ya mana zabi na alkhairi cikin rayuwarmu, mukuma karbi al'amura da haquri da tawwakali sannan a karshe mu tsarkake zukatanmu",
Ubangiji ya kan jarrabemu ne gwargwadon imaninmu"
Zainab ina fata zakiy aiki da abinda na fadamiki kuma kiyi nazari sannan ki nutsu ki kumaa godewa Allah cikin lamuranki, domin idan kika gode mishi ze qara miki"
Zainab ta gyada kai kmar kadangaruwa,
"Se nakeji a rayuwa nafi kowa sa'a, samun 'yar uwa kamarki abu ne da se an tona, nagode Anty Allah ubangiji ya raya miki zuri'a, Allah kuma ya biya mana bukatunmu na alkhairi"
Tana cikin scrolling wayarta a twitter tayi karo da wani post da mufti menk yayi
"Quit worrying especially over things you can't control. If you want peace of mind hand things over to the Almighty after you hav done your best. You hav played your part so now let Him take over. Remember whatever you let into your mind has the potential to manifest in your life"....
With all the encouragement she finally get back to school,
Saukinta ma duka courses din sun fara karatunsu da faruq kuma project ne me muhimmanci dan haka ta maida hankali dukda wasu lokuta she feel lonely and so empty, wasu lokutan kuma bata iya controlling tears dinta, as duk idda ta juya ze na tuna mata da faruq ne, amma se take rarrashin kanta, with "this too shall pass"
Result ya fito (na previous semester) kuma tayi abin arziki kmaar ko yaushe taji dadi ta gode Allah, and she smiled lightly saboda tunawa da faruq da tai, babu wani abu dawwamamme
Ta sami levelcord a office bayan sun gaisa ta nemi inda hali ya sanar da ita wata magana gameda withdrawing din faruq a school amma yace baze iya disclosing wani details ba, all he can say is "an kama faruq yayi exam malpractice kuma an koreshi, kumaa ba shi kadai bane harda wasu students dinma,
Bikin minnatullahi ya matso sosae shirye shirye ake ta ko ina, saukinta ma mostly a Abuja suke shirin nasu tunda can gidan mijin yake, Takan zo gidan Anty siyaman idan ta gaji da hayaniyar biki, se ta shigo ta huta,
A haka bikin yazo, bangaren amarya zasuyi Dessert party itada friends dinta sannan sai mother's eve na iyaye, wanda ke a mazaunin kamun amarya da Ango, sanda akazo rabon iv zee batai tsammanim za'a bata ba sekuwa aka bata itada da zakiyya wae baza'a bama kubra ba saboda tanada ciki me laulayi zata batamusu biki, khairi kuma ba'a garin take ba
Aikuwa kubra tayi bala'i tace dama ko sun bata bazuwa zatae dangin marasa mutunci kawae, zakiyya me zatae inba dariya ba, tace mukuwa zuwa babu fashi...
Yau za'ayi kamun da aka gayyacesu, zakiyya dama tun ba yau ba fadi take, "zainab muyi ado mu kece raini, in ta fadi haka zee sae tayi murmushi kurun,
Zee Ta fito a shower tana goge jikinta, a ranta take tinanin wanne irin kamu ne bayan magarib kamar za'ayi dinner, ta sauke idanunta kan wannan frame din da faruq ya bata na anniversary dinsu, tayi murmushi wanda baikai zuci ba, ta juya ta cigaba da shiryawa, ta jawo drower kenan zata dauki eye pencil idanunta suka sauka kan wata jotter daya taba designing da kanshi, anyi painting front page din da zanen rose yayi kyau (pic on wattpad)
Ta dakko ta ta dora kan mirror, sanda ta kammala shiryawa seta dubi kanta a mirror, da lokacin da suke tarene idan tayi kwalliya haka zece mata "ki dauka min hotonki na fara gani" takan ce mishi abinda makaranta zanzo zaka ganni" se yace "a'a banaso kafin ki karaso wani yaa rigani ganinki"
Yanzun ma seta tsinci kanta da daukan hoton kanta dukda babu faruq din da zata ma sending
Ta jawo jottern ta dauki red pen ta soma rubuta
"Dear heart
Being apart is more difficult than i ever imagined. I see reminders of you everywhere i looked, and they make me ache to be near you again.
I cherished every moment we spend together, i love you even more in the moments when we re apart. Tonight As i write this letter it's like you are right here with me. I miss you my omar" ta rufe jottern ta maida cikin drawern tana mai jin tarin kewar shi
Ta kurawa kanta idanu ta cikin mirror din wondering how can love be so deep, ta lunshe ido..
Turo kofar dakin zakiyya tayi tana sallama zainab ta amsa tana mai juyawa fuskarta dauke da murmushi
Dukka suka hada baki gurin fadin WoooW
Zakiyya ta riga cewa "zee kinga kyan da material dinnan ya miki" dariya ta subuce ma zee tace "ke kinga kyan da less din ya maki, dukka dariyar suke
Ita zee material ne pale pitch yana da yanayin santsi da sheki aka mishi ado da duwatsu bakake masu dan girma da suka qara mishi kyalkyali, se gyalenta dark Ash da yyi bala'en shiga da kayan, kanta kuma ta daura head pale pitch, sarka da dan kunnenta duka black ne, makeup din face dinta kuma nude babu wata hayaniya,
Ita kuma zakiyya lace ne royal blue da ratsin sky blue se touch din plain white kadan kadan, tayi dinkin buba da zani da sukai mata kyau dan ta sakeyin er kiba, dankwalin lace din ta kashe daurin zara buhari, sannan tayi ado da silver jewelries, hakama gyalenta da jaka da takalmi...
Tare suka jera suka fita falourn suna annashuwa, babu kowa a gidan se anty dake dakinta da alama wadanda ke gidan antyn sun tapi gurin event din, zakiyya ta zauna kan kujerar snn tace jeki ce mata mun shirya fa dukda tasan mun shirya din dan na gaisa da ita,
Zee batai wani yunkuri ba sega Antyn ta fito itama a shirye, ta kashe kala, har gida me makeup tazo tayi mata ta tapi, dan seda tace zee ma tazo a mata tace a'a saboda batason makeup me yawa a face dinta, ta iya simple one kuma yayi kyau
Ko ban fada ma me karatu ba nasan yasan labari yazo karshe...kiris ya rage
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 38: He's back
Tare duka suka dunguma gurin event din, saedae da sukaje mutane dayawa sunje dukda bikin na manya ne amma da mutane dukda haka kuma komai a tsare akeyi kuma a nutse, sai karfe 10 amarya tazo, akayi kamu sannan aka sanar da shigowar Ango da abokanshi, karkuso kuga idanun jama'a bama kamar kawayen amarya daketa rangwada ko wani abokin ango ze kyasa
Ya shigo tare da abokanshi, gabadaya idanunshi naga kan amaryarshi da take ta walwali, tayi makeup kai baka ce a kasar nan take ba, a lokacin ne mutane dayawa suka fuskanci Assidduque mutun ne mai fara'a daga yadda yake ta murmushi yana blushing, barima inya dubi amaryarshi se wani nishadi ya taso mishi itama a nata bangaren kanta ya sake girma ji take babu ya ita a fadin duniya, ace ta hada zuri'a da dangi kamar na assiddique,
A tsakiyar filin ya tsaya yayi folding hannayenshi, daya daga cikin abokan angon wanda ya kasance barrister mijin zakiyya ya amshi mike ya soma fadin "ango na jiran amarya tazo ta tareshi" (barrister bawae abokin Assiddique bane, yana mai aiki ne kuma yana jin dadin aiki dashi, yayanshi wato uncle muzakkir mijin anty hawwer shine abokinshi kuma shi ne ya hadasu)
Qawayen amarya suka tapi gurinta suma suka zagayeta sannan cikin isa ta taso tana taku bride's maids na take mata baya, 'dan nesa kadan dashi taja ta tsaya itama, shi da kanshi ya karaso inda take, ya hade hannayensu suka karasa gurin zamansu. Bayan sun zauna yayi whisper a kunnenta "u re more than beautiful"
Tayi blushing
Haka aka kare taro cikin annashuwa dajin dadi..
Bayan daurin aure da kai amarya abuja wanda zee bata je ba, aka hada mother's eve a can ma suka rakashe,
Abubuwa suka cigaba da tapiya smoothly da taimakon mai duka, har zee ta kammala semestern data rage mata a makaranta, lokacin service dinsu akayi posting dinta a camp a garin Abuja, shine mafarin zuwanta Abuja kamar yadda na fadi a first page
Zee ta karkare labarin tana mai duban Assiddique wanda ya sunkui da kai
Tace "kaji yadda ta kasance tsakani na da faruq, shi ne masoyina wanda na rigada na bama zuciyata ba tun yau ba"
"Nikuma ya zanyi da tawa zuciyar" a bazata taji kalamnshi sunzo mata
Ya dago yana kallonta a nutse tareda shauqi mai yawa
Ta dubeshi batareda ta kula maganar da yayi ba "yayana kaji kana magana" ta fada excitedly... Be amsata ba se murmushin dake kwance kan fuskarshi, a hankali kuma ya zame kasan falourn ya miqa sujudus_shukur
Ganin da sukai dare ya tsala ya sakasu neman makwanci tareda barin sauran batutuwa ma gobe idan mai duka ya kaimu..
Zee kuwa ta kasa kwanciya dakyau se juye juye take kan gadon dakin nata, damuwanta da hankulanta sunaga faruq ne "batasan mene ke damunshi ba amma abin ya tsaya mata a rai, bayan tsayin watannin data dauka tana kewarshi yau gashi gareta amma cikin wani yanayi,
Akalar tunaninta ta karkata ga Assiddique, sarae taji furucinshi na daxun "Nikuma ya zanyi da tawa zuciyar"
Da sassafe ta tashi kai da ganin idanunta kasan ko kadan bacci bai isheta ba,
Ta kammala wanka da shirinta kenan idanunta suka sauka kan wayar farruq data taho da ita jiya, ta jawo ta ta kunna
Abinda ta fara gani shine wani hadadden hotonshi kan wallpaper
The first time data ganshi da kananun kaya, ba irin namu na gida nigeria ba, kai da ganin hoton kasan ba anan kasar aka daukeshi ba
(Pic on wattpad)
A hankali kida mai taushi ya soma tashi daga wayar na waqar Alan Walker "lily" amma se ta fara daga gurin
"Follow everywhere I go
Top over the mountains or valley low
Give you everything you've been dreaming of
Just let me in, ooh.......
Everything you wantin' gonna be the magic story you've been told
And you'll be safe under my control
Just let me in, ooh.......
Just let me in, ooh"
Har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa sannan ne zee ta ankara kira akeyi ta dauka tana mai gyara muryarta
Gaisawa suka somayi da ya Safiyyan dan taga sunanta jikin screen din
Surprisingly tace
"Zee ko ba zainab bace?" Zainab taji heart dinta tayi melting tace "nice Anty har muryarta na shaking,
Nan ta sanrma ya safiyya abubuwan da suka faru jiya sannan ta dora da fadin yanxu ma asibitin zamu wuce, itama ya safiyyan tace yanxu zata shirya su hadu a can.. Tayi cutting call din, zee tabi wayar da kallo does that means tana garin nan?
Tare da Assiddique suka tapi asibitin, suka fara duba jikin faruq har a lokacin be farka ba, da alama an mishi allurar bacci ne, zee tayi kokarin danne kukanta ta hanyar rufe bakinta, duk abinda take Assiddique na lura da ita,
Sanda suka sami doctor ya soma musu bayanin abinda ke damun faruq
"Matsalar hunhu (lungs) ce, da alama ta dan jima a jikinshi dan har cancer din tayi developing takai matakin da dole sai an mishi aiki kuma in so samu ne kawae a fita waje a mishi aikin saboda hadari da aikin keda shi..."
Suna fitowa a office din doctor sukai kacibis da ya safiyya, ai zee me zatai, se hawayen dataketa riqewa suka soma bulbulowa, "na shiga uku Anty, faruq keda lung cancer"
Rarrashinta ta shiga yi daga baya suka nemi guri suka zauna inda take zayyane mata abubuwan da suka faru shikuma ya barsu ya wuce gidan yallabai saboda nemanshi dayakeyi
"Faruq ya koma europe ba a son ranshi ba, school authority sun mishi sharrin yin exam malpractice sakamakon sunanshi daya fado cikin wa'anda suka zauna a gurin da akayi na wata exam wai human genetics"
Sarai zee ta tuna sanda faruq ya fada mata anyi malpractice amma ai shi beyi ba, tana da tabbacin faruq be satar amsa dan da yanayi da ta sani duk dadewar da sukai, da baze na karatu sosai haka ba
"Wannan lung cancer din kuma bata jima da tashi mai ba, shi ne dalilin zuwanshi amsar wannan award din domin ya saida ya biya expenses na aikinshi"
"Dady ya samu matsala da harkokinshi na europe, duka muna nan Abuja gurin momy, yanxun ma hada kudin tafiyarshi aketa famanyi amma dake aikin me tsada ne sosae yasa kudin basu hadu ba"
Zee tace
"Kenan yasan da ciwon a jikinshi?" Ya safiyya tace eh"...
Zee ta koma gida devastated, abu daya ke zuwa kanta taje ta samu Assiddique ya biyawa faruq kudin aiki, tasan ko nawa ne yanadashi, kuma yanada kirki tasan ze bada kudin, ta tura kofar falourn ta danna kai ciki, har ta soma hawa sama taji kamar muryar mutane cikin gidan, tasan Assiddique be gidan tunda ya sanar da ita zeje gun yallabai,
Ta wuce dayan part din datake jin kmr magana, cikin falournshinna kasa ta tadda minnatu da Anty siyama, mamaki tai ya akayi ko motarsu bata gani ba, kodayake hankalinta be gurin ba lallai ta lura ba
Gaisawa suka shiga yi
Minnatu se wani hade rai takeyi tana cika tana batsewa, zee ta tashi
Anty siyama tace "zainab dawo kiji mana" zee ta koma ta zauna
"Kinga dai a gidan nan aiki kikeyi kuma biyanki akeyi, to dan Allah ki tsaya iya boundaries dinki, banaso na cigaba da jin kananun maganganu, gida dai minnatu keda gida, babu ruwanki cikin abinda ya shafi itada mijinta in sun ga dama su daki juna babu ruwanki, dan naji kece kika ingizashi ya rubuta mata takarda, ba haka nasan halinki ba kuma bana fata ki sauya,, tun ina miki ta lallami ki kyale mata mijinta suyi zaman lafiya"
Zee ta jinjina kai kurun ta tashi tabar gurin
A ranta take saqa maganganun Anty "ita sam yanxu bata da lokacin wannan abinda ya dameta ma ya shallake tunanin wata minnatu, fatanta Allah yasa Assiddique ya amince da buqatarta, tana son faruq dinta dadin dadawa tana matuqar qaunarshi....
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 39: fishy
Ta zabga tagumi da hannaye biyu sam bata ji maganar dayake tayi mata ba sai da ya zuguri fuskarta da spoon
Ta kifta idanu tana mai hadiye kukan dataji yana kokarin tahowa, ta sunkui da kai batareda tayi wani tunani ba ta soma fadin
"dan Allah yayana ka taimaka min ka taimaki faruq, dan Allah badan ni ba, yadda Allah ya taimakeka..."
Se ta kasa karasa maganar ta sunkui da kai cikin jin zafin zuci,
Tashi yayi daga gaban abincika sannan yace ta biyoshi,
Wannan gurin mai kama da library ya karasa sannan ya jawo kujera ya ce da ita "zauna, zee ta zauna tana sauke ajiyar zuciya
"Kiyi kokarin kwantar da hankalinki, in shaa Allah faruq ze samu lafiya, kinji" ta gyada kai
"Good, munyi magana da doctor and yayimin recommending UK so yanxu ma mun soma processing ne, karki damu by God's grace ze tashi"
Zainab ta tsaida idanunta kanshi tana mai jin wani dadi na ratsa ta
Tayi hour daya a kwance kan gadon amma juye juye kurun take faman yi abubuwa dayawa ke yawo a kanta
A bangaren ubangidan nata, lokaci daya taji yayi furuci bayan ranakun daya kwashe bai magana a sanda ta ida bashi dogon labarin, shi kanshi a yadda ta lura furucin nashi ya bashi mamaki,
Kuma koda be fada mata ba tasan me maganar tashi ke nupi, yes tasani sarai yana sonta, amma tai ignoring ta lumshe idanunta tana qara hasko fuskarshi daxun dayake mata bayanin shirye shiryenshi gameda faruq,
A yadda ta fahimta Kawae yana danne feelings dinshi ne yana dora nata saman nashi, maybe zata iya kiran haka a matsayin asalin qauna, saidai ita da shi ta sani sam abu ne da bama zeyu ta hango ko ta hasaso ba, tamkar hada ruwa da wuta ne guri guda,
Challenges take hanga ta ko ina, bama kamar bangaren uwargidan nashi, All she can do is to keep ignoring his feelings for now koda hakan zeyi hurting dinshi ne, ya kamata ya fahimci inda akalar zuciyarta ta tapi, shima ya maida hankali ya kula da gidanshi, bazataso ta zame mishi tashin hankli ba sam, zata cigaba da mishi addu'a Allah ya bashi farincikin duniya da lahira hadi da gamammiyar kwanciyar hankali..
Kafin kace me shirye shirye sunyi nisa, saidai Assiddique yace kar a sanarma da familyn faruq cewa shi ne ya dau nauyin aikin da sauran expenses, ya fadama zee kar ta fada musu nan ma,
Amma still seda ta sanar da Ya safiyya kadai tace "yace beso a sani to dan Allah kar ki fada, a barshi a matsayin wata foundation ce ta dau nauyin komi"
Ranar Anty safiyya har kwalla ta zubda, tayi murmushi duka lokaci daya " dama seda na fadama FUJ kedin Alkhairi ce" sukai hugging juna
Mutane biyu suka tapi tareda faruq, safiyya se wani likita da Assiddique yace ya bisu saboda sauqin abubuwa, dan dady beda ishasshiyar lafiya shima, zee taso ta bisu amma Assiddique yace ta kwantar da hankalinta ta zauna har su dawo, haka tana kuka tayi waving dinsu a airport, shikuma yana daga bayanta yana kallon komi,
Yana sonta sosai amma ba yadda zeyi dole zeso abinda takeso, salloli ta maida hankali sosae tanayi ba dare ba rana, rokonta da addu'arta Allah yasa ayi aikin a sa'a faruq ya dawo lafiya, har takai ma yanxu Assiddique