Showing 3001 words to 6000 words out of 73133 words

Chapter 2 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5410

buqatar wani abu just dial Bashir's number (security din daxu) ta jinjina kai okay sir, dan sanda tazo duk muhimman ma'aikatan gidan sun bata mumbers dinsu incase of emergency
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer




Episode 03: His father's Son


Zainab ta tashi da annashuwa, kodan tasan zatai girki ne oho, as early as 9am ya kira wayarta, tai picking da sallama meet me at my apartment tace okay sir, ta rike wayar tana jujjuyawa, anya tasan falournshi kuwa ta dae san bangaren datake zargin nashi ne amma batada tabbas
Ta zira hijab da slippers dinta, ta karasa waje, ta wuce bangaren minnatu sannan ta isa last part, a hankali ta tura kofar, falour ne kamar na minnatu, tayi tsaye tana kallon kofofin dake cikin falourn wayarta tai ringing, yace ta shiga kofar hannun damanta, ta juya ta tura kofar, sai stairs, yace "descend down" ta soma taka steps din tana kaiwa karshe taga wani hadadden falour an kwatashi da Arya sofa and dining set (the pic is on wattpad)
Shi kadae ne zaune yana kallan tv da spec din a idanunshi, ta karaso ta tsugunna ta gaidashi ya amsa ya nuna mata kusa dashi yace ta zauna, ta zauna
Tunda yanxu kin zama personal cook dina u need not to worry about the FC zamu cigaba da aiki tare, and by 4 yayye na danake fadamiki zasu zo,
A nan falourn zaki dinga serving duk girkin da kikayi, breakfast, lunch and dinner zan dawo cinsu a gida, zee tace to
Daga nan yace taje tayi planning girkin da zatama yayyenshi gobe se ta fara nashi
Har ta juya zatabi ta inda ta fito yace "no zoki bi ta nan and ta nan zaki na shigowa ko yaushe" ya nuna mata wata kofa anan kasa, databi kofar sai gata a wannan corridor din da aka shimfida carpet, inda kofar conference room yake, karshe ya sadata da main falour din,
Everything went smoothly as planned, abu hudu ta mishi presenting tace ya zabi wanda zata musu atlast ya zabi grilled fish da barbeque,
Komi ya kammala tayi serving nasu kan dining (pic on wattpad), minnatu ma tace akai mata nata daki dan babu yadda zakaji kamshin nan baka fara salivating ba,
Sunyi dogon meeting shida yayyen nashi kuma kowannensu ya yaba da girkin da akayi presenting...


Yana tsaye yana tsane ruwan dake kanshi, fitowarshi a wanka kenan ta karaso dakin nashi, she's dressed attractively in nighties, yayi placing brief smile a fuskarshi, dan yasan wani abu tazo buqata
"My Star ya su yaya sukaje gida" ba mutun ne mai riko ba yace "lpia qalau", meyasa bakizo kun gaisa ba kuma kinsan na fadamiki zasuzo
Ta yatsina fuska kaina ke dan min ciwo, yace Allah ya sawwaqe
"Star ya maganar komawata makaranta? Da kuma aikina zaman gidan nan ya gundireni"
Yace don't worry im working on that
Amma bakya ganin abin zeyi yawa, ga aiki ga school, musamman profession dinku da kin rabu da masters din ko kuma ki haqura da aikin for now,
"Karka damu i can handle them all, beside 2nd degree is not that stressful i can manage"
Yace "okay good, yanxu suna arranging hospital dinnan kinsan aikin dayawa, so da zarar sun gama zaki fara aiki ne, nd for the 2nd degree sedae kiyi nan abuja tunda kinaso ki hada harda aiki, taji dadi sosai sannan ta qarasa gadonshi ta kwanta, "yau anan zan kwana" yace next week zamuje gaida mami daga nan zamu tsaya mu sauke umarah... Tayi diff kamar batasan yana mgana ba...


Kashegari tun asuba yayi mata tex na abinda yakeso, da time din dayakeso tayi serving nashi, ganin da safene yasata tashi da wurwuri, ma'aikata duk sun gama aikinsu na safe, ta shiga kitchen tayi preparing pancake din kamar yadda yace dayake ba abu ne mai wahala ba da wuri ta kammala, ta koma daki tai wanka dukda batai wani datti ba, ta dan dora hijab mai saukin nauyi sannan taje ta dauki pancake din da kamar ya balle kamar baze balle ba kuma dan laushi da taushi,
Baya falourn dan haka tai mishi matsuguni a dining area ta juya,
Har takai kofa taji motsin sakkowarshi daga sama, ta juyo ta rissina tana mai gaidashi ya amsa looking cool as always,
Karfe 8 ne daidai amma har ya gama shirinshi tsaf da alama fitar dazeyi mai muhimmanci ce yayi kyau in blue ya karasa kan couch ya zauna ya lankwasa kafa daya kan daya sannan ya dan juyo ya kalleta
(Pic on wattpad)


"Dakko breakfast din"
Ta dakko tazo tai serving dinshi ya sakko daga couch ya baje a kasa, ta miqe zata tapi yace a'a ta zauna becin abinci shi daya, last cook dinshi ma tasaan da hakan koda bazataci ba buh ta zauna... Ta zauna amma hnkalinta be gurinshi, be bar komi a plate din ba datai serving, yayi hamdala sanann ya miqe




Tana serving lunch minnatu ta sakko cikin falourn, zee tace "barka da warhaka ya mint" yawwa barkanmu dae, ta qarasa gurinshi yana zaune kan couch din ta zauna kusa dashi, "ina kwana star" yace lpia qalau kin tashi lpia" tace lpia lau
Zee ta gama serving din yace "bata wannan" ta miqa wa mint "doramin shi kan dining ya mutun zeci abinci a kasa ga dining" zee ta qarasa ta ajiye ta dawo ta soma seving nashi,
Har minnatu ta miqe yace "jiya na miki mganar tafiya saudi bakice komai ba, kuma kinsan tunda akayi bikin nan bakije kun gaisa da mami na ba" ta bata rae taja kujera ta zauna "nipa bance maka bazanje ba" yace good
Wani dadi ne ya tsirga zuciyar zee dan tasan dole itama zae tapi da ita, kuma zata roki alfarmar ya barta taje gidan aanty hawwer,
Haka kawae murmushi ya subuce mata, ya kalleta "why is she smiling all alone"?


Gurin yayi kama da library saboda yadda aka kawatashi da qananun kujeru da glass cabinet, saedae yayi kama da bolcony saboda yadda yake daga gefen falourn,
"Wannan gidan wae ashe har yanxu ban gama kallo ba" zee ta ayyana hakan a ranta, ta taho da mug of coffee din dayace ta hada mishi, he smiled at her, zee ta tsinci kanta da tunanin why is he smiling?, dukda zata iya cewa this is the first time dayayi smiling a gabanta, ta ajiye mug din yace "sit
Batayi musu ba ta zauna, "tell me dazu da rana naga kina smiling why?" At once murmushin ya bayyana a face dinta, and he couldn't stop looking at her innocent face, "she's a natural" ya fada a ranshi,
"Am excited by the fact we re going to visit my most beloved land"
A hankali yayi recalling haduwansu na farko cikin plane, she's blushing all alone
"Zakiyi visiting sister naki shiyasa right?" Ta gyada kai feeling so much happiness
A ranta tace he don't know Anty hawwer is more than a sister she's a mentor, a friend, a mom,
Tell me the secret behind ur cooking skills, i must say i like every bit of ur food how each and every dish taste, smell, the aroma is simply amazing,
Zee tai dariya a hankali tana tuna yadda Anty hawwer tace ya yabi girkinta sanda ya faraci,
This man and food.....


Satin tapiyarsu ya zagayo, sukayi duk shirye shirye, gidansu Suka fara biyawa dats gidan iyayen Assiddique,
Motoci biyar sukayi convoy, zee tana ta biyu ita da bashir (head of securities)
Assiddique da minnatu na motar bayansu, ranar zee tasha kallo, mansion ne mai kama da royal one, apartment apartment,
Haka suka dinga ketawa da motocin har daga karshe suka tsaya wani apartment dayafi dukkan sauran kyau na ban mamaki,
Suka fito duka, amma basu motsa daga bakin motar ba, sai da yayi appearing


Ba tsoho ne can sosai ba, amma akwae shekaru tattare dashi, yana rike da wata stick mai azabar kyau, gabadaya bakinshi ya kasa rufuwa, dayake fuskarshi ba boyayyiya bace yasa zainab ta gane shine the real Assiddique wato mahaifin yusuf,,, shi yayi musu jagora har falournshi, minnatu ta gaida shi haka zainab ma,
Maimakon yusuf yabi matan daidaya yana gaidasu a'a sune suke zuwa daidaya suna gaidashi, su hudu ta karshen itace sukayi hira mai tsayi kuma bata bar gurin ba sabanin sauran da kowacce tazo sai ta tashi ta koma tana yatsine yatsine,
Yayyenshi maza da mata haka suka dinga zuwa suma suna gaidashi wasu suyi musabiha wasu su dan daga mai hannu dan ji suke kamar su shake shi, zainab dae a yadda ta dinga irga yayyenshi saida mutun goma sha daya maza da mata, kuma magidanta,
Abu daya dayake a bayyane shine irin tsananin qauna da mahaifin yusuf ke nuna mishi bama iya wannan ba harda fifikon da yake nunawa karara, a bayyane yake cewa yapi sonshi fiyeda duk sauran yaranshi, wannan yasa momy ta samu gurbi mai karfi a zuciyar yallabai, dan duk wanda ze nuna yusuf yace yana sonshi to ya zama abin kauna gurin yallabai,
Dukda momy itace amaryarshi amma tapi sauran matanshi wayau, taja yusuf sosai a jikinta sakamakon mahaifiyarshi bata gidan duniyar ma gabadaya


A bangaren yusuf kuwa sam bejin dadin yadda yallabai ke nuna karara yafisonshi akan yayyenshi ba, dan yasan hakan ba karamar kiyayya ze jawo mishi ba a matsayinshi na Auta a gidan, kuma wanda ya pita dabaan da sauran en gidaan domin mahaifiyar shi ba er kasar nigeria bace er ethopia ce, shiyasa sam be cika zama cikin gidan ba ko kafin yayi aure, yau yana waccan kasar gobe yana wannan
Gidan mami (qanwar mamanshi dake saudi) ne kadae yake zuwa ya dade ya sake,,,
Sai yamma Yallabaai ya barsu dan su tapi shi a cewarshi bai gaji da ganinshi ba, sun tattauna business matters a inda yallabai ke jaddada mishi lallai ya cigaba da kula dan kusan rabin kasuwancinshi a hannun yusuf yake, danma shi yusuf din yaki yarda ne da tuni ya sakar mishi kusan komai, amma sai ya nuna mishi ai ga sauran en uwanshi nan kuma mostly maza ne suma suna buqata....
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 04: Mint's Husband


Private plane sukabi shida dumbin securities dinshi, tarbar mai kyau mami tayi musu sai nan nan take da minnatu a matsayinta na matar yusuf, Abincin da akayi serving nasu ya dan taba kadan duk yaji be mishi dadi, dandanon nata yapi mai kowanne yanxu,
Sae bayan an kwashe abincin yace da mami ta nunawa zainab (wacce ya gabatar da ita matsayin qanwar minnatu kuma personal cook dinshi a yanxu) kitchen ta dafa mai abu mara nauyi yaci kamin ya kwanta, haka kuwa akayi seda tayi mishi girki sannan ya samu yaci ya koshi, kashegari shi da kanshi yace ta shirya ze kaita gidan Anty hawwer, ya shiga dakin da aka sauke minnatu "zanje nakai zainab gidan yayarta ko zaki rakamu?" Ya tambayi mint tace a'a taja blanket ta rufe fuskarta alamun bacci bae isheta bama, ya girgiza kai kurun,, shima yanaso yaje su gaisa da muzakkir din dan haka suka tapi da mota daya, shi dama ba wani son wannan convoy din yake ba yallabae ne be yarda dole se ya dinga yawo da securities


A waje suka tsaya yace da zee ta shiga ta musu iso, zee kamar ta sa gudu tadae yi sassarfa ta qarasa, saedae babu kowa gidan sai nihal da binafat er aikin Anty hawwer
Zee tai murmushi "gidan en boko kenan" ta koma tace dashi ya shigo, ya shiga yana cewa "muzakkir din baya nan ne" tace eh duk basa nan
Ya dau waya yace da securities din su tapi ze taho anjima,
Ruwa da lemo ta kawo mishi ya sha ruwan kadan, sai taga yayi relaxing kan kujerar yana kallon news, harda daukan remote ya kara volume, tace "kana bukatar wani abu? Yace no, so nake na dan huta ni kadae na gaji da hayaniyar securities, duk inda kayi suyi ta binka" ta jinjina kai tana dan jin nauyinshi
Lura da hakan dayayi ne yasa yace "zo" ta kalleshi, zo? Ta maimaita a ranta, sae kuma ta miqe daga kujerar datake ta koma kan capet kusa da kafarshi, yayi en danne danne a wayarshi sannan ya miqa mata wayar, garin karban wayar hannayensu suka hadu, taji taushin fatarshi it was wow


"Dubamin apartments dinnan wanne ne ginin shi da tsarinshi sukapi kyau a naki ra'ayin" ta soma dubawa a hankali, da gani kasan bana kasarmu bane,
"Sir wannan yapi kyau" ya gurgiza kai, "don't call me sir again" ta daga ido ta kalleshi yayi nodding ta sauke idanunta, to me zata kirashi idan ba sir ba, Ina kallonki matsayin er uwar matana, bugu da kari u re my personal cook, nd that makes u someone close to me.


A haka ya saka zainab ta saki jiki dashi, ganin lokaci ya dan ja yasa tace zata hadamishi lunch mai sauki, haka kuwa akayi ta kammala ta kawo mishi ya sakko ya baje ya ci abinshi cikin jin dadi, abin mamaki duk dadewar da yayi gidan Anty hawwer minnatu batama san bai cikin gidan mami ba balle ta daga waya ta kirashi, ta dauka ya dade da dawowa, kammala cin abincinshi keda wuya sae gasu su biyu sun dawo Anty hawwer da Uncle muzakkir,
Wani tsalle zee tai ta fada jikin er uwarta, suma su Assiddique suka yi musabiha, nan suka zauna aka danyi hira sannan yace ze wuce,


Zainab ke sanar da Anty hawwer yadda zaman ta ke gudana gidan minnatu da kuma matsayin personal cook daya bata, Anty hawwer tace "kice kin sha kwana, lallai ki rike amanarshi dan naga ya saki jiki dake" zee tai murmushi "amma seda na sha gwaji ai, kuma fa ko a kitchen din nashi akwae cctv"
"Yes ai yanada gaskiya, danma yanada taka tsantsan da kuma kariyar ubangii amma wadaannan en uwan nashi ai da tuni sun batar dashi, to zakaran da Allah ya nupa da chara ko ana muzuru ana shawo sai yayi"


Kwanakinsu hudu gidan mami itakuma tana gidan Anty hawwer, yakan lekota lokaci zuwa lokaci idan yaji yayi kewar girkinta, daga nan sukayi ziyara suka kuma wuce makkah, sati daya sukayi bayan sun sauke umrah suka dawo gida, a lokacinne kuma barrister shima ya dawo,


Komi da suka tsara da minnatu ya tapi smooth, aka kammala shirya hadadden asibitin da akayiwa ado da kayan aiki wadatattu, hakan yasa aka budeshi sannan ta fara aiki, makaranta ma ana jira sunfara diban sabbin dalibai
Dadi kam gurin minnatu kamar kamar me,


Satinta daya da fara aiki, duk taji yusuf ya gundireta babu damar tayi bacci zezo ya dameta, a nashi bangaren shima halin minnatu yana damunshi babu damar yazo neman hakkinshi zata fara complain ita a gajiye take blah blah blah....


Suna falournshi tana danne danne a system, zainab na serving dinner yace
"Sweetheart inada labarin da zan baki" ta dago a kufule "haba star wae meye haka, Allah ka fiya surutu" he was stunned, ya miqe a zuciye yace da zainab "serve me upstair" zee ta bishi da kallo, ko ba'a fada ba ranshi ya baci amma mint ko damuwa batayi ba ta cigaba da abinda take


Zee tai serving mint ta ajiye kan dining nashi kuma ta dauka ta haye sama dashi, ta kai mishi har inda yake tana mai yi mishi murmushi, lokaci daya duka bacin ranshi yayi disappearing, yaji tamkar ta zuba mishi ruwan sanyi ne kan tafasasshiyar zuciyarshi dake hayaki, ta zauna ta tankwashe kafa kamar yadda yayi shima tana facing dinshi yana cin abincin yana dagowa lokaci lokaci yana kallonta, yana kammalawa sae ga mint ta shigo a shirye harda jakarta tace "star inada emergency zanje na dawo maybe kuma a can zan kwana" ya jinjina kai "a dawo lpia"
Daga haka ta fice, zee ta miqe ta kwashe kwanukan dayaci abinci, tana kitchen tana ajiyewa sae gashi, ya jawo kujera ya zauna, ta dan kalleshi kadan tae murmushi sanda ta gama sannan yace tazo palournshi na sama
A kan couch ta sameshi yana danna system hannunta rike da bowl na fruit salad ta karasa ya jawo dan karamin table ta dora a kai, taje ta dakko pick ta ajiye mishi, ba dan qaramin birgeshi tayi ba, shikam duk me kula da cikinshi ya gama mishi komi,
Ta zauna kusa dashi with a smile on her face shima yayi murmushin calmly and brief, "so how do you know this Assiddique need something to taste while working" tai er dariya "afterall its my duty, added to that its my pleasure to serve a unique person like you"
Ya kalleta sannan ya soma kai fruits din baki "tell me more how unique am i?".... "U re not only unique, u're amazing, u re simple, kindhearted, and u re cool" ta karasa fada muryarta low
Interestingly yake nodding, ko mint bata ta6a yabonshi haka ba, kuma a yadda yake kallon zee sanda tana fadi he knows the words re coming straight from her heart, she's the first person da cikin kankanin lokaci taga farinshi har take yabonshi with outmost sincerity,
Ya dan dauke hannunshi daga kan system din sannan yace "na maida ke personal cook dina and u didn't inquire about ur salary why?" Zainab answered him with
"U told me u spoke with my uncle (Abbah jabir) about me being your personal cook, hakan yasa ban ja ba bankuma ce komai ba dan nasan duk abinda ya yanke daidai ne" ya gyada kai sannan yace come closer, ya fada yana matsawa shima gun system din,zee ta matsa ya soma mata explaining aikin dayakeyi da en abinda zata tayashi, sun shafe kusan 1hr suna aiki, hakan ya tabbatr mata he trust her, shima yasan yayi trusting dinta yanxu tunda already ya gwada ta kuma ya lura da motsinta, yayi observing nata from the first day she came to the house dukkuwa da cewar bai nan....


After like a month komi na mint ya kammala ta soma zuwa school kuma tana aikin data kwallafa duk wani buri na rayuwarta a kanshi, babban burinta bae wuce taje interview gidan tv ba sunanta ya rabu dana Assiddique kuma a medical doctor itakm burinta ya cika, jin kanta take tamafi Assiddique din, dan ita kadae tasan abubuwan datae dan ta ganta cikin gidan Assiddique
Tafiya ce ta taso mishi ya sameta a daki tana shirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login