Showing 36001 words to 39000 words out of 73133 words

Chapter 13 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5421

motan sannan shima ya fito yana locking motar zakiyya ta karaso tana mai shimfida murmushi a fuskarta, ta gaidashi ya Amsa sannan duk su ukun suka shige su biyu a gaba, faruq na biye dasu a baya, gefen garden din gidan ta kaishi ya zauna kan kujerun Alfarmar dake gurin, sannan ta koma ciki dan tuni zakiyya ta shige,
Batareda ta damu ba ta shiga ta watsa ruwa ta saka bubu peach mai ratsin coffee ta daura turban mai sauki sannan ta dauki gyale bayan ta fesa turaruka duka batafi 15 mins ba, ta shiga kitchen dan tun tana bandaki ta yanke shawarar hada mishi fruit salad kawai, tai turus tana kallan zakiyya da ta kammala yanka fruits din in cubes, zee ta karaso,
"Ke kuma haka akeyi se ki bar bako babu ko ruwa" cewar zakiyya taana juye salad din cikin mazubinshi na tangaran mai garai garai,
Zee ta karasa bakin window din kitchen din dake dan lungu ta hangi faruq zaune yana sipping juice,
Ta dawo tai hugging zakiyya ta baya "godiya nake er uwa, "kinfi haka ai a gurina zee"
Kije zan kawo wannan din ko bayan shi akwai abinda za'amishi" zee tace a'a
Har ta kai kofa zakiyya tace "he's perfect" zee tai displaying wide grin sannan ta fice tana blushing


Ta kofar kitchen din tabi ta baya yadda zepi mata sauki, yana zaune ya dago ya dubeta "she's looking cute in d attire" yaji zuciyarshi na mishi gulma, ta karaso ta zauna
"How re u feeling now?" Tace "na warke ai dama na dan lokaci ne gajiyan"
Yace to Allah ya sawwake, daidaai nan zakiyya ta kawo bowl din fruits salad da pick biyu, ta ajiye a table din tsakiyansu, sai sanaann zee tai musu introducing juna, sannan zakiyya ta koma ciki,
Zee ta dubeshi ta kama idanunshi cikin nata sai ta bude bowl din ta dau pick daya ta mika mishi daya, ita ta fara sha sannan shima, its really good, faruq ya fada yana kallonta, tai murmushi sannan ta ajiye pick dinta
In serious tone tace "i never deny loving you, even if i do is just a big fat lie"
"I loved u when i gave up my heart will love someone, not like i hav been inlove before, i truly don't even know how the emotions are, all i know about love is the love of my Ammi, my Abbah, and sibling affection"
I hav got all the care i needed from them, my best friend, my secretkeeper, my first love, duka Ammi ce, so am never lonely, shiyasa ban taba maida hankali kan guys ba" tai shiru
"I understand nernerh"
"Saidai kuma abinda ya sakani yin jinkirin amsar soyayyarka saboda bani da tabbas kan soyayyar da zamu gina, ban sani ba ko mai riba ce ko mara riba, idan nace mai riba shine am talking about the future, sincerely i don't want to love someone without getting married, wannan soyayyar shirmen irin ta en makaranta wacce ana kare karatu shikkenan an rabu banajin zan iya yinta and i want to know more about u"
Now he understand,
"Se yanxu ne na fahimci dalilin dayasa kikamin shiru har na tsayin wadannan kwanakin, u re afraid, u think i ll just love u, waste ur time without making u my wife.... Never zee never, dukda bamusan future ba, but wlh ban taba kallanki da wata manufa ba inba na aureki ba, kuma in shaa Allah i promise I'll do all what it takes to make u my wife,"
And about me what is it u want to know? Cos i think i've told you who i am, from where and about my family but dont worry ull get to know everything slowly, tunda wani abun ma mancewa akeyi"
Duka bayanan daya mata taji ta gamsu, ta kalleshi kadan, "now u already know my answer den" yace "noo say it" tai murmushi shima yana murmushin
"Dont tell me kunyata kikeji" ta rufe fuska da hannayenta, ba karamar dariya ta bashi ba yai dariyar sannan ya miqe yana kallan wrist watch nashi,
Itama ta miqe smiling slowly, "i ll be on my way we'll talk" ya fada yana kallanta ta miqa mishi wayarshi, ta rakashi har wajen motar sannan tai waving ta koma ciki


Ko karasa shiga ciki batai ba wayarta dake hannunta ta fara ringing, ta duba taga sunan faruq, ta dan yamutsa fuska sannan ta ja second kamin ta dauka
"Nerhnerh ince dai yanxu bakya jin kunya ta tunda phone call ne"
Tai dariya tai hanyar komawa bolcony din, so tell me nerhnerh, not now ta fada tana mai kashe wayar da sauri, faruq dake tuki yai mirmusshi ya ajiye wayar ranshi fes, bai karasa gida ba seda ya kira Anty safiyya ya fada mata yadda sukai da zee ba karamin dadi taji ba, tace "FUJ Allah ya barku tare ya kauda idon makiya yace Amin Anty na....


Zee da zakiyya suna kitchen sunata aikin abincin dare "wai meyasa yau baki kira driver ya dawo dake ba" zee ta tambayi zakiyya, "kawai nagama da wuri ne kuma banason zaman school din nace bari na d'ana hawa napep"
"Zee wannan shi kuma waye? Shine wanda ke dawo dake kullum shiysa kikace in na gama na dinga kiran driver kawai" zee tai nodding... Shine faruq kenan,
"Ya akayi kikasan sunanshi" zee ta tmbyi zakiyya
"Kinmanta sanda zeena tazo tace kuna soyayya kikaqi yarda harda mana kuka" zee tai dariya kawai
Amma yayi kam he's handsome.... From which state is he? Cos he look like pure Fulani
A takaice zee tace katsina... Good,, wish u best of luck.." Zee tace. Thank you"


Tun last week minnatu ta koma U.S inda tke krtu, sai yaayaa cee kawai a gidan itama bata fiya zama ba in suna nan,


Tun jiya da faruq ya kirata sukai wayar nan bayan fitarshi be sake kira ba, agogo ya buga karfe 12 na rana, kamar ta kirashi amma se taki, tana fadama kanta "maybe he's busy"
Ta idar da sallar azahar tana zaune bisa dardumar tana kare lazuminta, wayarta tai ring, tasa hannu ta jawo wayar dake kusa da ita kan mirror, sunan Anty hawwer ta gani bata wani ji dadi ba ta dauka, sai kuma hira ta barke zee ta sanaar da ita komai yadda sukai da faruq jiyan....


Tayi juyi kan gadon nata batajin bacci sam, zakiyya dake dayan bangaren a kwance itama ba baccin take ba tace "zee zamuje saudin kuwa a wannan hutun dan naga beda yawa 2 weeks ne kawai" a kasalance zee tace "no Abbah jabir yace se mun gama session din kamar last time, koni naso zuwa"....


Karfe takwas na safiya suna ta ayyukan gidan, sukaji karan shigowar motoci dan yaayaa ma bata tashi ba, window zakiyya ta leka, zee na karasa mopping,
Zo ki tayani ganin abin Al'ajabi kamar motocin gidansu Anty siyama, ai bata rufe baki ba ta gano Antyn na fitowa daga mota,
Keee dama yau Anty zata dawo?
Zee da sam batamaji me take cewa ba, gabadaya tunaninta naga faruq, yanxu kam ya fara bata mata rai, atleast he should hav called she's patiently waiting for his call, she missed dat cracked voice of his," jijjigata da zakiyya keyi yasata kikkifta idanu cikin jin gajiyar zuci,
Bata kaiga cewa komi ba Anty siyama ta bayyana gabansu ta kofar falourn, duka suka tsaya suna kallonta kamar sunga abin mamaki,
Zee ce tai karfin halin karasawa gareta tana gaidata dayi mata sannu da zuwa, ta dubi falourn sama da kasa babu abinda ke tashi sai kamshi, tai murmushi tace yawwa sannunku da aiki,, yaayaa ce ta fito jin karabniya, nan suka bude sabon babin yiwa juna sannu da jin dadin ganin juna.. Ranar Aikin dasu zee sukeyi se da ya karu, dan ko wanki daya anty bata bada ba na kayanta saida ta dawo ta basu suka saka a engine suka dinga aikin wankewa, ga girki da ta dinga saka zee
Abinka da mai ciki se an girka tace kamshin be mata ba, Allah sarki zee haka taita wahala dan zakiyya daki ta rufe tai kwanciyarta...


Karfe 6 na magriba, zee ta kammala girkin daren ranar, a gajiye take ta koma daki. Turus tai bakin kofa tana kallan zakiyya dake hada kaya a trolley, ta karaso da sauri kuma,
"Kardai tapiya zakiy ki barni" zakiyya tace zanje gida nayi sati daya se na dawo nan zance mama tayiwa Abbah magana yama Anty siyama magana na cigaba da zama a nan tunda mkrntarmu daya ne karatun da tapiyar zatapi sauki" ba karamin dadi taji ba tace "to sai kin dawo Allah yasa ya amince" zakiyya tai er dariya, ze amince ma sedai kiyi addu'ar Allah yasa me gidan ta amince" zee ta jinjina kai...
Bayan tapiyar zakiyya zee tana kwance a dakin ko dinner bata fita tayi ba, gabadaya ma ta rasa mene ke mata dadi,
Wayarta tai ringing ta zabura tana son ganin sunan faruq kan screen din, cikin sa'a sunan nashi ya bayyana, wani dadi ya ratsata ta dauka da sauri ta rike har zatai picking kuma se ta tuna kawai haushin takeji, wato ma duk kewarshi datai shi beyi ba ai da ba haka yake mata ba dan basu taba kwaana biyu basui waya ko kuma ta ganshi ba,
Ta yatsina fuska ta ajiye wayar gefenta raanta wasai, tana kallan wayar kiran farko ya katse na biyu ya shigo, shima ya katse na uku ma, seda ya kirata sau 5 bata dauka ba
Ya haqura, sai a sannan wata yunwa ta dameta ta mike ta fita neman abinci, ko ba komai tasan yanason magana da ita kuma ya tina da ita wannan ma kadai ya wadatar dukda har ranta tanaso ta dauka taji ya yake,
A haka ta tuttura abincin ta koma dakin, anan ta sami wayar tana ta ringing kuma shi dinne, ta karasa ta dauka sannan ta gyara zama tai picking call din,
Da sallamarshi da ko yaushe ya fara, wani sanyi mai kamada na kankara ya ziyarci zuciyarta, ta lumshe ido sannan ta gyara muryarta ta amsa mishi sallamar,
"Nernerh kuma shine inata kiran wayar kika sha re ni" ya fada muryar nan kamar wani mai shagwaba, ta hadiyi yawu tana maida numfashi akai akai, ta gaza fadin komi,
"Nayi laipi ban kira ba ko nernerh?, can kasan makoshi tace "uhm"
Yace "to nerhnerh meyasa baki kirani ba" har yanxu muryarshi kamar ba ta faruq din data sani ba he sound emotional
A wannan gabar kam batada Amsar dazata bashi,
"Nasani nine ya dace na kiraki but idan kinji shiru seki kiraa kiji ko lpia" ta gyada kai tmkar yana ganinta,
Ya cigaba da fadin "naje katsina ne cikin dangi acan zanyi hutuna" tace ohh, to ya kike? Ya gida? Ta amsa da lpia qalau, a hankali ya soma janta da hira tun bata amsa mishi sosai harta ware ta cigaba da amsa mishi, sunfi 1hour suna waya yana bata labarai kala kala duk dan ta sake dashi, daga karshe sukai sallama yayi mata saida safe sannan yace ta kula da kanta...
Kashegari da tex dinshi ta tashi, taji dadin tex din daya mata ta mishi reply da thank you, dukkuwa da ba sune kalaman da suka dace tayi mishi reply dasu ba,, tana ta ayyukanta na yau a cikin gidan amma hankalinta naga wayarta... Faruq kawai take tunani gashi ita nata jin kan ya hana ta kira taji ya yake shima tun tex din safe be kira ta ba, duk tabi ta damu wayarta nayin motsi kadan zata duba, tana zaune bakin mudubin tana juya wayar tana tunanin kawai gwamma ta kirashi, kiran sallar magrib akayi duka babu wata nutsuwa a tare da ita ta tashi tai sallah, bayan ta idar ko addu'ar kirki batai ba ta jawo wayar, sai kuma tai wurgi da ita kan gado cikin jin haushin kanta, duk tabi ta damu kanta akan wanda bema damu da ita ba, hawaye taji sun silalo mata meyasa zuciyarta zatai mata haka wanne irin fadawa so ne haka tafar daya, meyasa be damu daa ita kamar yadda ta damu dashi ba.... A hankali ta kwantar da kanta jikin gadon dake gefenta, hawayen idanunta basu tsaya ba, kewar Ammi takeji sosai, tun rasuwarsu bata ji kewarsu ba kamar yau bama kaamar Amminta, da tuni suna hira ko karatun qur'ani, ta share hawayenta ta dago ta jawo qur'anin ta soma karantawa amma sam babu nutsuwa a tare da ita, ta rufe ta dakko wayar ta saka karatun ta kwantar da kanta tana saurare, har akayi sallar isha'i tana nan ta miqe itama ta gabatar da nata sallar sannan ta hau gado dan sam bata jin yunwa ma, a haka har bacci ya sureta, cikin baccin ta dingajin ringin din wayarta ta tashi a dan firgice tana ambatan sunan faruq a bakinta, aikuwa sunan nashi da tai saving da dear ya bayyana kan screen din, wani sanyi taji a ranta, atleast tasan bai manta da ita ba, a matuqar sanyaye ta jawo wayar tai picking ta kara a kunne cikin sleepy voice ta Amsa sallamar tashi,
"My queen har kin kwanta" cikin makogwaro tace "uhmm" yace "to ya kike? Ya yau din?" Tace Alhamdulillh yace "masha Allah"
"I hope kinyi dinner" tai shiru a ranta tace "ko ya d'ance ma yayi missing dina, bata ida karashe maganar ba yace "yau nayi missing dinki dayawa" tai mishi banza ta fada a ranta "liar"
Ya cigaba da cewa "kinsan abinki da family issue, wlh ban samu zama ba i was very busy, daga a aikeka can se a aikeka nan... Haka yaita mata hira tana binshi da umm har kuma daga baya ta saki jiki dashi suka dinga labarai ranta yai fes,, ita har mamaki take ko nawa yake kashewa a sayan card? Wacce sana'a yake kodayake daga ganinshi kasan he's from a wealthy family, daga karshe chats suka koma dan ce mishi tai ta gaji da wayar amma bawai ta gaji da hira dashi ba nan ma suka bude sabon babi, datace mishi bataci abinci ba ya sakata gaba saida tai snapping abincin data hada ta turamishi kuma ta zauna taci tana mai jin annashuwa... Ba zee tai bacci ba se wajen 12 ta gota ma, a tarihinta kuwa wannan ce rana ta farko data kai ya wannan lokacin batai bacci ba saidai in karatu take ko kuma batada lpia....


Assalamu alaikum
Ina mai baku haquri jina shiru da kukayi jiya, hakan ya faru ne saakamakon rashi da muka samu, Allah yayiwa yayan Abbanmu rasuwa, pls ku sakashi cikin addu'o'inku
Ubangiji Allah ya kai rahama kabarinshi Allah ya jiqanshi Amin
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 26: message


Haka lamura suka cigaba da garawa tsakanin faruq da zee, a satin biyun da sukai na hutunsu kuwa ba er qaramar soyayya suke xubawa ba dukkuwa da wani sa'in se ya yini ya kwan be kirata ba itakuma ya barta da tinaninshi, idan kuma ya kira ya bata uzuri a haka suka dawo makaranta, A bangaren zakiyya ma Anty siyama ta yarje mata dawowa gidan da zama, yanxu su uku ne cikin gidan dan yaayaa ta koma gida tuni,
Karatu zee tayi daidai gwargwado dan wannan seemestern ma tanaso tayi abin arziki dukkuwa da result din wancan semester din be fito ba amma tanaji a jikinta tayi abin kirkin,,
A satin da suka koma a satin ya dawo garin, kuma yana shigowa garin be zarto ko ina ba sai gurinta dan ko apartment dinsu beje ba,, yauma zakiyya ce tayi mai iso sannan daga baya zainab din tazo, tun daga nesa take kallanshi, yayi haske akan wanda tasanshi da, siririn sajenshi ya sake kwanciya saidai bai kara kiba ba kuma bai rame ba, amma kuma yau ba fararen suturar bane jikinshi, besan ta karaso ba yanata pressing wayarshi saida sanyin breeze din data taho ya hurashi hadi da qamshin arabian perfumes dinta suka hade da scent din flowers dake gurin, a matuqar sanyaye ya lumshe ido yana sauke numfashi, a hankali ta mishi sallamar shima ya amsata sannan ta zauna gefenshi, sai sannan ya daga idanunshi ya kalleta, ya kai mintuna 2 kwarara yana kallanta, wanda yasata takura gabadaya, ta dan yi gyaran murya tace "anzo lpia ya hanya"... Ya dauke kanshi bai amsata ba, bata damu ba ta sa hannu zata zuba mishi lemon da zakiyya ta kawo, ya amshi lemon yana girgiza kai... "Banda abinki wake saka sarauniya aiki" ya zuba nashi itama ya zuba mata ya miqa mata dukkansu murmushi sukeyi,, kurba daya tai ta ajiye ta bata fuska "ni ka dena kallona"
Wani murmushin gefen baki yayi "baki isa ba" a mamakance tace "ikon Allah",
Sai kuma ya kalli jikinshi ya kalleta, "shine har da yin irin shigar da nai ko" ta kalleshi itama tana murmushi, dukkansu black sukayi shi yasa black getzner se shining take itakuma ta saka black Abaya tasha duwatsu tana shining,
A hankali murmushin fuskarshi yayi fading sounding serious yace "u really look good nerh_nerh"
Har wani melting zuciyarta keyi in taji yace mata nerh nerh nan wlh,
Ta kikkifta idanu kamar mara gaskiya "ai ban kaika ba"
Ya zare idanu "karkiyi sa6o dan kin fini nesa ba kusa ba," hakan ya sakata displaying wannan murmushin dayake mata kyau, har ya bayyanar da haqoranta dake shining
"So bright" ya fadi
"' shine abinda ya fara sanarmin da feelings dinki a kaina, zainab kina da wani silent beauty ba kowanne idanuwa ke gani ba se mai idon basira"
Wait wani ya taba fadamin haka, zee ta ayyana a ranta, a hanakali kuma ta tuna sanda zakiyya ta fadamata tun a wancan gidan a lokacin ta dauka wasa ne kawai, amma gashi still faruq ya sake fadamata"....
Basu dade va suka karkare hirar tace yaje gida ya huta tunda yayi tapiya, suka kuma tsaya a kan next week zasu koma lectures sanin halin malamai dasukayi in an koma hutu akan dan kara lokaci akai....


A falour ta tadda zakiyya, ta karasa kusa da ita ta zauna tana facing dinta, zakiyya tai tsaki, wai mene haka ne kina gani fa kallo nakeyi, zee ta juya ta dubi tv din da ake wani indian film a starlife, ta karasa ta kashe tvn sannan tace we need to talk, ihu ne kawai zakiyya bata kurma ba dan seda ta ma zee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login