Showing 18001 words to 21000 words out of 73133 words
Chapter 7 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt
duniya ta saki wani kuka mai cin zuciya, haka take kukan tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi lokaci lokaci.....
Dan kansu suka dena kukan, sai bayan kwanaki biyu aka sallami Zee, ta rame sosai, dan kasa dena zubda hawaye tayi, gabadaya jitai duniyar ta fita a kanta babu abinda keyi mata dadi, gidan Anty hawwer ta koma ta zauna, Abbah jabir (kanin Abbansu) shine ke ta dawainiya dasu, matanshi ma duk sunzo duba Zee sanda tana asibitin, zeena kuwa kusan koyaushe tana hanyar asibitin har aka sallameta dayake a gidan yayanta take, dan har matar yayanta ma tazo tayi musu ta'aziyya dan kowa ya zauna da Ammi yasan halayyarta ta dattako, haquri da tsananin Addinin islama dukda tayi boko kuwa, shiyasa duk wani d'a da Ammi zata raina to ze taso a nutse ne dan ya samo tarbiyya tun daga tushe, dan ma Allaah bai azurta Ammin da yawan 'ya'ya ba....
A gidan Abbah jabir ake zaman makoki, dayake Zee battada lpia yasa Anty hawwer tace tai zamanta kurun a gidanta itakuma kullum zataje da safe ta dawo da yamma, har akayi sadakar bakwai,
To dama kamata yayi tun kwanaki hudu baya, Anty hawwer zata wuce saudi, inda mijinta ke karatunshi na masters degree kuma ze dora da PHD itama antyn zatai masters din tunda shi yama kusa kamamla nashi, to se kuma wannan kaddara ta faru, mijin Anty hawwer yaso zuwa gaisuwa amma Anty hawwern ta hanashi dan yana tsakiya da yin jarrabawa ne, yaqi yarda sam saida ta hadashi da Abbah jabir sannan ya haqura, dan shim Abban be goyi bayan ya taho din ba, bayan sadakar bakwai din ne Abbah jabir da wasu en uwa na nesa suka hadu dan tattaunawa, dayake duk babu wani dan uwa na kusa daga bangaren ammin har Abbah se Abbah jabir duk sauran cousins ne ko na Ammi ko kuma cousins din iyayensu Ammi da Abbah haka...
Kowaa ya hallara su biyune kadai mata sai kuma nihal dake hannun Zee, wacce ta rame tai duhu dama ba farar bace amma kuma ba baka sosai bace, sabanin Anty hawwer datake da haske
Abbah jabir ne ya soma musu bayanin abinda ya tarasu
"Bazamuja da tsayi ba, muna sakeyi muku ta'aziyar rashin iyaye da enuwa, dan ni kaina sun wuce yayuna saidai nace musu iyaye, yadda suka kula dani tun rasuwar namu iyayen, to dama haka rayuwar take, dududu nawa take, kuma babu komai cikinta sai zallar haquri ga wanda keson cin riba, Allah yajiqansu ya gafarta musu muma ya kyauta namu zuwan, saida aka sakewa su Abbah addu'a sanan Abbah jabir ya dora
"Hawwer munyi magana da maigidan naki, yacemin kun gama tattaunawa kan zaki dauki Zee ki cigaba da riketa a can gurinki,
Anty hawwer ta gyada kai alamun hakane, Zee ta dubesu dan ita batamasan da wannan mgnr ba,
Maganar Abbah jabir ya cigaba
"Muma nan mun tattauna bayan munji ta naku bangaren, Hawwer se muke ganin kamar zepi idan Zainab ta zauna nan gurina" lokaci guda gaban Zee ya tsinke ya fadi tana mai jin hawaye na taruwa cikin idonta, Allah sarki rayuwa, sati daya baya bazata taba cewa har lokacin da za'a dinga neman inda zata zauna zezo ba, amma gashi iyayenta tmkr basu wanzu ba komi ya kone, gida, mota, su kansu komi ma,
A wayance ta saka gefen gyalenta ta share er kwallar dake zubowa, bawai zaman gidan Abbah jabir ba amma matan Abban duka sedai hamdala kuma kowa yasan da hakan
Maganar Abbah jabir ya cigaba da fadin
"Mun duba ne munyi la'akari da karatunta, tunda yanxu suna karshen semester karshe a level one idan ta kammala wannan semestern sukayi hutu setaje gurinki din tayi hutu in aka dawo kuma seta dawo ta cigaba da karatunta har itama lokacin da Allah ze kawo nata mijin"
Wannan hukunci na Abbah jabir shida sauran manya yayi daidai a kunnen kowa har da Anty hawwer hakan yasa itama Zee ta amshi kaddararta tana mai fatan Allah yayiwa iyayenta rahama,
Daga haka aka cigaba da maganar gadonsu, Abbah jabir ya sanar dasu dukiyar Abba ta cikin gidan sun rigada sun kone kamar yadda kowa ya sani, abinda ya rage sune kudade cikin account da wasu filaye da takardun ke hannun wani Abokin Abbah dukda haka suna cigaba da binciken wasu...." Bayan an kuma tattaunawa su Zee suka koma gidan anty hawwer wacce itama gobe zata koma saudi, tunda suka taho a hanyar babu wanda yayi magana, Zee ma zamewa tayi takwanta sosai kan kujerar tana rungume da nihal dake bacci, itama ta lumshe idanunta,Anty hawwer tace "Zee" Zee ta dan bude idanunta da sukai mata nauyi sannan ta kalli gefen da Anty hawwern take tana tuki ta dan kakalo murmushi sanda Antyn ta dan juyo ta kalleta
Ajiyar zuciya kurun Anty hawwer ta sauke tana mai maida kanta ga titin , basu dadeba a hanya suka isa gidan Anty hawwern, madaidaicin gida da aka tsarashi tsari irin na en boko,
Har anyi sallar la'asar ma sanda suka iso, hakan yasa suna shiga Anty ta amshi nihal ta wuce daki, Zee ta ajiye hijab dinta sannan ta shiga bandakin falourn dan bata muradin shiga ciki, a ciki tai Alwala ta fito, ta nemi dadduma ta shimfida tai sallah, bayan ta idar da sallar ma ta dade tana addu'a sosai ga iyayenta har ta kare da kukan dayaci karfinta ta kifa kanta kan abinsallar tana mai tsananta kukanta,
Anty hawwer ta durquso tana mai dafata ganin ta tsagaita da kukan tana ajiyar zuciya, ita kanta anty hawwern tausayin Zee takeji, tasan tanada haquri sosai hakan yasa inma abu ya bata mata rai bata fiya kulawa ba, abinda ze sakata kuka kuwa ba karamin abu bane, musamamn sanin irin shaquwar dake tsakaninta da Ammi.... Zee ta dago sanda sukai ido hudu da Anty hawwern sai ta sake rukunkumeta, cikin kuka take fadin "Anty ke kinji dadi, ko ba komai Ammi da Abbah sunga aurenki, nikuma fa?, burin Ammi bai wuce taga ranar da zataga bikina ba, Anty hawwer kema tafiya zakiyi ki barni!!!
Rarrashi sosai Anty hawwer take saida tai kuka takoshi sannan ta share hawayenta
Anty hawwer ta soma mata nasiha kadan kadan
"Rayuwar gabadaya nawa take ma Zee dita, komi sai kinyi haquri zakiga yazo ya wuce babu wani dawwamammen abu a duniya komi se ya wuce wlhy kmr yadda muma din zamu shude watarana, meyasa bazaki dauki kaddara ba Zee, kigafa har faduwa kikai Zee, nikuma ya kikeso nayi da tawa rayuwar, all the expections danake yi gameda su Ammi, duk tanadin danayi musu ashe babu wani rabo, to ki kwantar da hankali ki dau komi ba komi ba Zee ta, we hav to be strong, muci jarrabarwarmu Zee, mu fawwala lamuranmu ga ubangijin talikai,
Kukan Zee ya tsananta amma babu sauti cikin jimammin wannan rayuwa, yau kaine gobe kuma bakai bane,
"Dududu ma kwana nawa ne kun kare semestern kinzo gurina, in kuma kinaso na fasa tafiya ne wallahi zan fasa Zee, banida wata data fiki yanxu, idan kin ida semestern se mu koma tare"
Zee ta dago ta share hawayenta dan tasan tsaf Anty hawwern zata iya kuma tasan zata shiga hakkin Abban nihal ne, "a'a anty hawwer "
A sanyaye antyhawwer tace "Zee" Zee ta dago da kanta tana kallan Anty hawwern,
Ta dafa kafadar Zee tace "ki Zama jaruma, babu abinda Ammi da Abbah sukke bukata kamar Addu'arki idan kuma kinje gidan Abbah jabir, ki maida komi ba komi ba, kiji kiqi ji, kuma ki gani kiqi gani, dan sai kin toshe kunnuwanki kuma rufe idanuwanki, ni kuma na yarda Zee din danasani , Zee rainon Ammi, Zee one and only sistern hawwer zatayi overcoming duka wani diffuciultie with faith kimin alqawari Zee"
Zee ta kamo hannun Anty hawwer, tayi rapping hannunta cikin nata tace "nayi miki alqawari Anty hawwer, na kuma karbi kaddarar rashin Ammi da Abbah, Allah ya musu rahama"......
Kashegarin ranar tun wajen 12 duka suka kammala shirinsu dan anty hawwer tafiso takai Zee da kanta sannan ta tafi, kulle ko ina sukayi dama already sunyi waya da Abbah jabir kan karfe 1 zasu zo dan haka yace to ze jirasu, en sauran kayan Anty hawwer dake gidan na sakawa da wasu na amfani ta kwashe duka suka zuba komi a mota, saida suka kulle ko ina sannan suka fito, suka kulle gidan ma, suka shiga motar suka hau titi, boutique suka biya Anty hawwer ta saiwa Zee wasu kayan sakawa tunda battada su, wanda take sakawa ma a kwanankin na Antyn ne, sannan ta siya mata atampopi, ta kuma ce zata tura mata kudi cikin account dinta, Zee taji dadi taita godiya kuwa, #the sister's love
Bayan sunje gidan Abbah jabir, sukaa tarar dashi a driven din gidan ya kafa wata kujera yana karanta jarida, sukayi parking suka fitto, nan suka shiga gaisawa sannan yace su shiga daga ciki, jakar kayan Zee aka futar a motar da wasu en kayan da Anty ta bar mata, aka bar na Antyn a motar,
Idan ka baro driven din gidan ma, tsakargida zaka tarar, sai kuma falour a gefe, sannan dakunan yaran gidan, na matan gidan kuma yana saman benen,
Duk yawancin su suna falourn a zaune dan nan suka fi zama, gidan kam ba'a cewa komi dan a jagalgale yake nan buta, nan kwanukan wanke wanke, ga bandaki a hangame kudaje kuwa ta ko ina, hmm Zee tai ajiyar zuciya kurun dan abin ma ba'a magana, saida suka huta aka kawo musu abinci dukkansu babu wanda yaci abincin,
Bayan sunyi sallar la'asar ne, Abbah ya kirasu falournshi dake can gefe cikin gidan, suka sake gaisawa,
Duka yaran gidan sun hallara mata 8 ne sai kuma maza 4, nan Abbah ya sanar dasu zuwan Zee kuma zata cigaba da zama a gidan, babu wanda yace ko kala, haka ya gama jawabinshi,
Anty siyama itace amaryar Abbah jabir kuma matarshi ta uku, kasancewar bikin nasu bai wani dadeba yasa battada 'da ko 'ya a cikin gidan, wannan dalili yasa Abbah fadin "na damka alhakin komi na Zee a hannun siyama" tunda dama dole se an sama mata uwar daki itama kamar kowanne 'da,"
Anty siyama da bata fiya surutu ba tace "Allah ya tayamu riko" duka sukace Amin,,,
Anty hawwer ma ta dora da fadin "Abbah jabir, nima ga tawa motar nan se Zee ta cigaba da zuwa makaranta da ita dukda bata iya ba amma tana koya kadan kadan" Abbah jabir yace to ba matsala zai sama mata driver kurun se su dinga tafiya tareda sauran yaran gidan" (babu motar yara a gidan Abbah jabir dan ba wani dukiya ce mai yawa gareshi ba, mota daya ce kuma tashi ce)
Sai magariba sannan Anty hawwer ta soma shirin tafiya filin jirgi, Abbah jabir da Zee ne kurun suka mata rakiya,
Koda sukaje rabuwa Zee ta rike hannun anty hawwer kamar karta saki, sai kuma tai murmushi tace Allah ya tsare ya kaiku lpia, sannan tai kissing nihal tana mai murmushin da baiyi mata dadi,
Anty hawwer ce ta kalleta tace "haka nakeson jarumar kanwata, idan na sauka zan kiraki" daga haka sukai waving juna... Wasu en hawaye suka dan digo daga idanun Zee tana murmushi cikin tunanin sabuwar rayuwar dazata tsinci kanta a gidan Abbah jabir da kewar iyayenta da er uwarta...
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 14 & 15 : first glimpse
Kashegarin wannan rana Abbah jabir ya soma shirin barin garin dan komawa gurin nashi aikin (yana aiki ne a garuruwa daban daban kasancewar shi mai aikin dan sanda mai mukamin D.P.O. yasa akanyi mai transfer zuwa garuruwa daban daban lokaci zuwa lokaci, kuma yakan dauki matar dakeda girki ya tafi da idan idan tayi kwanakin ta wato sati daya se wata taje),
Abbah jabir seda ya tabbata ya wadata iyalanshi da abinda suke bukata kamin ya tafi shida uwargidanshi dasuke kira umman Halipa, ita tanada yara 7, Halipa ne babba wanda yaci sunan Abbanshi shekarunshi 25 se tahir shekarunshi 24, Usama (22yrs), Kubrah (19yrs), Hassana & Hussaina (15yrs), da Kausar (11yrs).
Sai kuma matar Abbah jabir ta biyu, tanada yaranta 5, suna kiranta maman khairi,
Khairi ce babba (18yrs), sannan Zakiyya (17yrs), iklima (15yrs), Ammar(13yrs) da Hindu (10yrs)
zee ma ranar talata ta koma makaranta, batada matsala da duka takardunta dukda sun kone amma already they are scanned on gmail..... tun Asuba da zee ta tashi ta share dakin da suke bacci itada Kubrah da Khairi dukda su basu tashi din ba, sannan tai karatunta na safe da sukanyi da Ammi, zee ta rike littafin tana mai tuno nasihun Ammi kowacce Safiya.... "zainab ki kasance mai haquri da duk halin da zaki tsinci kanki a rayuwa, ki kula kuma ki nutsu ke macece, dabi'unki, mu'amularki da mutane, kalamnki, suturunki sune zasu fadawa mutane ko ke wace, dan haka ki kiyaye harshenki, ki tauna magana kafin ki fidda ita, ki kiyaye tufafinki su zamto masu nuna darajarki ba masu fidda tsaraici ba...." bubbuga kofar dataji ne ya sakata dawowa tinaninta ta dubi agogo karfe 6:30 ne gari bai kammala wayewa baa kuma dukda haka babu wacce ta tashi kaf gidan, dan ko da Asubahi bataji motsin kowa ba se mazan da suke can boysquaters, baba maigadin gate din gidan yazo ya budema ladi kofar kamar yadda ta saba zuwa tana aiki tazo da sassafe ta shirya en makaranta tayi breakfast sannan ta tapi wajen 12 inta gama duka ayyukan gidan, sai kuma wajen 3 ko 4 ta sake dawowa tayi ayyukan yamma da wanke kwanukan da akaci abincin rana da yamma, girkin rana dana dare kuma wacce keda girki ce zatai in kuma tana da yarinya se ta sakata, in kuma suna makaranta tilas tayi dakanta.... Wannan kenan
zee ta dade tana jerama Ammynta da Abbanta addu'o'i kamin ta miqe taje dan yin wankan safe kmr kullun, ta tarar har ladi ta ida wanke bandakin kuwa, sai karfe 7:45 zee ta kammala dukka shurinta dan tanada lecture ta 8 kuma gashi ma ta makara, lokacin dukka kowa ya tashi, wasu na wanka wasu na shiri, wasu kuma na breakfast, haka suka gurgunda suka gama karfe 8 suka dunguma cikin motar da Anty hawwer ta bada su kusan rai 7 (ba dukansu ne keda lecturen safe ba wasunsu zasu bi zeen ne saboda samun bati dan Abbah jabir ya shaidama drivern iya hidiman zee ne kurun wanda kuma ze fita a lokacin dazata fita se su tapi tare tunda dai ba shine ya sayi motar ba ta gado ce).
Usama ne a gaba (shima yana zuwa wata private college), zee, khairi, kubrah, hassana da iklima kuma suna baya, sai hussaina data zauna a gaba kusada Usama dan babu waje a bayan,
Ammar, hindu da kausar kuma makarantarsu babu nisa su qananan, zakiyya kawai aka bari a gida, ita ta gama sec. Schl amma bata fara wata schl ba tukun se nxt session in za'ayi sabon diban dalibai
Hassana da hussaina da iklima aka fara saukewa a wata private sec. Schl, sannan aka sauke kubrah a school of nursing sai kuma usama a Aminu dabo college of health, ya rage daga zee se khairi, tun kan su karasa Zeena keta faman kiran zee, zee da wayarta ke cikin jaka ma sam bataji ba dan mostly a vib. Ko silent take saka wayarta
Dayake tafiyar akwai d'an tsayi kafin a karasa yasa zee ciro wayarta dan debe kewa, ganin kiran Zeena rututu yasakata bin kiran amma se zeena tai rejecting, zee ta tsaya tana kallan wayar da mamaki, can kuma babu jimawa sakon zeena ya shigo yana fadin "ki hanzarta zee malamin har ya shigo" zee tai shiru tana kara kallan time takwas harda talatin da biyar ta sauke boyayyiyar ajiyar zuciya, zata iya cewa tun da ta fara makaranta wannan shine karo na farko data taba makara haka, dan Ammi jajirtacciyar uwa ce, wacce take kulawa da dukkan al'amuran gidanta danma bata samu haihuwa da wuri ba wasu yayun zee da anty hawwer kuma sun rasu, wasu ma tun suna ciki suke barewa, iya su biyu kadai Allah ya tsayar mata,
zee tai murmushi tuno Amminta da tayi lokaci guda kuma idanunta suka ciko da kwallar tunowa da tai bazata sake ganinta ba... Allah sarki, Rayuwar kenan...
zee aka kai har cikin makarantar... Tsohuwar jami'ar Bayero dake kano, sannan aka wuce da khairi jami'ar maitama sule (northwest uni).
Qarfe 2 suka kammala lecture itada Zeena da sukeyi tare dama already driver yasan by 2 zata gama dan ta fada mai, suka taho itada zeena aka kai zeena har gida, itama ta shiga ta gaida matar yayan zeena datake gurinsu sannan suka wuto gida, kasancewar zee ba raguwa bace dan ko sanda tana gida tareda Ammi itake girki indai babu abinda take, and there's something special about zee's cook...
Tana shiga dama already tayi sallar zuhr dinta tun a school ta cire kayanta ta shiga ta watsa ruwa dan gidan shiru yake yaran duk sun tapi islamiyar karfe 2:30, zakiyya bacci take hakama matan gudan kowacce na dakinta dan haka itama ta koma daki tana mai jin kadaici, dan da ace da ne da tana jikin Amminta suna hira ko shawarar abinda za'a dafa da daddare, tashi tayi ta shiga kitchen din gidan fot th first time, kitchen is d best place in d world dake daukewa zee kewa, is the best place that makes her feels comfortable and okay, shiyasa girkinta ma dabanne da wani sinadarin da idan kaci sai kaso ace baie kareba u ll be craving for more and more babu kosawa babu ginsa (secret na girkin zee wanda ta koya da taimakon Ammi da kuma nata soyayyar da girki)
Gyara kitchen din tayi saboda ladi batazo ba tukun kuma zakiyya da tai girkin rana bata gyara ba, coffee ta shiga hadawa, the best drink of hers, bayan ta kammala ta juye cikin wani karamin cup data gani, sannan ta fita a kitchen din, its been a while since she had it, al'adarta ce itada Ammi basu kwanciya bacci basu sha akalla 2 mug of coffee din da zee ta kware wajen hadawa, yanxu kuwa kusan more than a week ma batasha ba, hakan yasataji wani dadi bayan tasha coffee din
Dukka yaran gidan wadanda suke higher institute se kusan magrib suka soma dawowa,
zee ta cigaba da zama gidan Abbah