Showing 30001 words to 33000 words out of 73133 words

Chapter 11 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5428

ta jawo note din nata cikin sakin fuska da sanyi "dagaske fa nake ban san komi gameda blood and body fluid ba, physiology is not my fav"
"Are u serious?, oh u re d first person dat i met who dont like physiology"
Tai murmushi, "the course is not dat interesting" idanuwanshi ya kura mata cike da mamaki "lady u re different"
Furucinshi ya sata dan darawa kadan,
Yes if physiology is not interesting den wat would.... Biochemistry? Or Anaatomy?"
Yadda yayi furucin yana zare ido yasata fashewa da dariya.....
"Damn cute"
Furucinshi kenan wanda shi kanshi baisan ya furta ba, itakuma batama jishi ba
Zee ta kare dariyartata da placing wani dakakken murmushi, he just couldn't take off his eyes, ya ilahi
Furucinshi ya sata zuba idanunta cikin nashi tana neman karin bayani,
Gabadaya he feels uncomfortable ya miqe da dan hanzari yace "i gotta go chat later" ya dauki key da phone nashi daya ajiye yayi gaba da sauri
Da dumbin mamaki ta bishi da ido, he's doing okay just now and wat happen all of d sudden"
Tayi furucin a fili tana kallonshi yana kule mata da gani,
Ta sauke ajiyar zuciyar "i hop everything is ok and good... Atleast he made my whole week not a day for dat matter"
Wayarta tai kara ta duba taga sunan zeena ta dauka ranta wasai, "kina ina?"
Ina libry but am done" zeena tace okkay i tot ma ko kin tapi already
"No yanxu dai nakeson kiran drivern"
"To ki sameni a waje akwai labari" zee tai dariya to ganinan da gudu ma" sukai cutting call din
Kiran zeena na katsewa na zakiyya ya shigo
Ta dauka da murna
Zakiyya tace "er uwa kin bar makaranta kuwa?" Zee tace a'a
Zakiyya tace to jirani dan Allah akwai story nasan beje miki ba zee tace "too lallai se kinzo din" itama daga haka sukai cutting
Zee ta juya kwayar idonta "mene abin bakinciki gaa wanda ke zagaye da mutane kamar su zakiyya da zeena"


******
A wajen ta samu zeena zaune tana waya murya caan kasa kan wasuu kujerun gini a kasan bishiyar darbejiya, ta karasa gurin tana sake kallan zeena dake sallama dana wayar, zaman zee yayi daidai da ajiye wayar tata
Ita kanta zeena seta bawa kanta Dariya ta kuwa kyalkyala abarta
Zee ta tsaya kallon ikon Allah
Da kanta ta nutsu tace "ke nayi sabon kamu" zee ta tabe baki au shine dama labarin yo inde kece ai bakya gajiya da sabbin kamu, inaga sekinyi samari dubu tukun zaki zabi na aure"
Zeena tace "gara ni dai akan ke da kike korarsu, amma wlh ki tsaya kiji dagaske nake miki... Allah nima na fara sonshi"
"Tooo waye shi din haka me sa'a" cewar zee
Zeena ta gyara zama sunanshi Imran, abokin yaya ne (daama na fada muku gidan yayanta take zaune), amma ya taba aure matar ta rasu gun haihuwa ita da baby tun shekaru hudu baya,
Zee jin tai shiru yasata fadin shikkenan labarin? Ko dai ba'ason fadamin wani karin bayanin? Uhm to masoya Allah ya bar love"
Haka suka kare tana tsokanarta, har zakiyya tazo saiga driver shima, duka su ukun suka dunguma,
A hanya ne zakiyya tace "kinsan kuwa an sake yiwa Abbah transfer" zee tace "daga jigawan? To zuwa ina?" Zakiyya tace har port Harcourt pa, yaso zuwa nan kafin ya wuce amma be samu halin hakan ba wai akwai abubuwan dazeyi a can din"
Zee tace to Allah yasa haka yapi alkhairi,
Ni bama wannan ba ai baakisan meke faruwa ba, cewar zakiyya
Zee tace meke going kuma?"
Ai in gaya miki da akayi maai wannan transfer din yanxu bayan yabi jirgi yaje, to anty siyama ce da zuwa se abbah yace ai kikoma cikin mu ma'ana ki dawo gida a rufe nata, ta tubure wallahi babu inda zakije wai bazata rufe gida ba ya lalace har wata guda"
Wata guda kuma? Zee ta tambaya
"Eh sun kara kwanakin yanxu tunda garin da nisa"
"To Allah ya kyauta kuma ya aka kare"
Zakiyya tace "ai kin amincewa tayi shine tace akwai yayarta suna ce mata ya_bilki mijinta ya mutu sai 'danta daya yana bording itace zata dawo ta zauna dake, nima mama take fadamin wai na shirya kayana mu tapi yau tunda a BUK nake tapiyarmu zatai daya"
"To yaushene tapiyar antyn?"
Zakiyya tace a yadda naji ma yanxu yaci ace ta tapi tunda ya rigada ya mata booking flight, nima ai yanxu in mukaje gida dakko kayana kawai zanyi mu wuce dan na gama shirya su"


Maganganun Anty siyama na daxu da safe suka fadowa zee datake fadin "Wallahi ya_bilki bazan bar gidana ya mutu.... babu inda zee zataje, in kuwa ba haka ba nima ba inda zani wallahi"...


Haka suka miqa zeena gida zee na fadin "to tattabara uwar alqawari a gaidamin sahibin" zeena ta mulmula mata dakuwa me zakiyya zatai kuwa in ba dariya ba, itama zee ta dara


Zakiyya taje ta debi kayanta ta saka cikin booth sukai sallama da mama da umman halipha suka wuce du yaran gidan basa nan na islamiya na can en boko ma na boko...


Yadda zakiyya ta fadi kuwa haka zee ta gani a gidan Anty siyama
Dattijuwa ce takai shekaru arba'in da en kai, ya bilki da suke cewa yaayaa, bama ita kadai ba har da minnatu autarsu
Anty siyama kuwa already ta rigada ta tapi,. A dakin zee zakiyya ta saka kayanta, koda suka shiga gidan ma babu wanda yace ci kanku, dan mint ma sam batasan ma sun shigo ba, hankalinta naga wayar salulanta dataketa faman latsawa tana tauna chewing gum tana fasa kwai iri iri,
Yaayaa kuwa waya take yi, bata tarbesu da komi ba se kallon banza
Zakiyya ta zauna kan gadon tana yaye gyalenta ta zuba tagumi
"Munga ta kanmu mukam, zee kinga kallon da yaayaa ta mana kuwa"
Zee tai takaitaccen murmushin dole tace "se haquri daga haka ta shige bayi
Wata sabuwa cewar zakiyya...


"Motar tazo fa sis"
Ya fadi calmly
Ta daya bangaren tace "Allah yaa sanya alkhairi my fuj" yace Amin
Duka sukayi shiru na seconds
Ta katse shirun
"Fuj tell me wats wrong, u sound dull"
Ya zame daga zaman kujerar dayake yayi relazing sosai, ya luma yatsunshi cikin gashin kanshi yana mai hura iska waje
"Sis akwai matsala fa"
I know, ta fada
Tell me wats d prob.
Ya dan ciji lips dinshi kadan ranshi babu dadi yace
"I think am falling"
"Falling? Falling where, falling on wat?" Ta tambaya cikin rashin gane inda ya dosa
"For her"
Dukda baya ganinta saida yaji yadda ta mirgina akan gadon
"Ya ilahi.... Fuj Are u serious?"
Yai ajiyar zuciya,
"Seriously its killing me"
Muryarta wasai sounding excited tace
"Pls just drop everything and love her, fuj continue to love her pls dont kill urself,"
Ya dafe fuskarshi "and dad?"
Ta sauke ajiyar zuciya "we'll see to that later just love the lucky girl"
Ya girgiza kai kawai "u re not serious"
Ya katse wayar cikeda confusion, haka taita kiranshi amma yaqi picking


X x x x x x
Bayan zee ta fito a wanka aka soma kiraye kirayen sallah magrib, already ta dauro alwala ta sa kaya wando da riga sakakku, sannan ta zumbula hijab babba har kasa ta tada sallah, zakiyya kuwa tuni rabar A.C ta sata bingirewa bacci ya kwasheta,
Idar da sallar zee yai daidai da shigowar yaayaa,
Tai tsaye bakin kofa ta kama kugu, zee tace "barka da warhaka yaayaa"
"Sannu ku shafaffu da mai ko, kun shigo bako gaisuwa kuma kun kule cikin daki to wallahi iskancin da kukewa siyama ni baza'ai minshi ba"
Hayaniyar fadanta ya tada zakiyya ta soma mittsike ido tana hade rai cikin jin zapin tada ta da yaayaa tai bayan duk uwar gajiyar data kwaso,
"To ku fito kowacce aikinta na nan yana jiranta tunda banice zanyi muku aikin ba"
Ta fice daga dakin
Zee ta miqe ta cire hijab din tace kije ki watsa ruwa ni bari naje nayi aikin,
Zakiyya tace "ba yanxu zanyi wankan ba se zan kwanta yanxu dai zan sauya kaya ne kurun"
Daga haka zee ta fice
Kitchen Anty ta nuna mata, zee ta shiga taga yayi dakal_dakal, du a tsakude, tiles din yayi shatin sawayen kafafuwa da datti ga kwanukan abincika birjik da alama tun fitarta da safe ba'a gyara ba,
Haka ta hau gyarawa ta wanke kwanukan tai mopping sannan ta fita falour ta tadda zakiyya na goge dining ta gama sshara,
Yaayaa tace "jeki maza ki wanke bandakinmu" zee tace to ta wuce
Koda ta shiga dakin anty siyaman da suka sauka, minnatu ce gaban mirror tana shafa foundation a face dinta da alama makeup takeyi zata wani guri,
Zee ta wuce zuwa bandakin ta gyara musu se tashin kamshi yake ta fito, yanxu kuma tana tsaye tana daura turban
Tasha wata black fitted gown data fidda tsantsar kyau da halitta da ubangiji ya zuba,
Tabbas ko wace kuma ko wane ya kalli minnatu se ya sake juyowa ya dubeta,
Fara ce tas kamar ka taba nono ya zubo, tana da dan jiki, irin wanda bature ke cewa chubby, shape dinta kam shine muradin kusan kowanne d'a namiji, full option coca-cola shape
Har zee takai kofa taji minnatu tace
"Kinga zoki share nan ma"
Kamar bazata juyo ba amma seta juyo tace to sanan ta fita dan dakko broom, fitowar zee ba dadewa minnatu ma ta pito, tashaa makeup kam abinta kamar wata baby dull, idan ka dubeta zaka rantse bazataji yaren hausa ba, zakiyya da zee suka bita da ido, taiwa yaayaa sallama ta fice.....
X
X
A gajiye zakiyya ta shiga daki itaama zee ta shigo ta tadda ta, zakiyya tace "nipa yunwa nakeji" zee tace nima haka wlh dan ko lunch banyi bama ni"
Zakiyya tace to bari naje na nema mana abinda zamuci dan naga couscous a dining dazu, a dining ta samu plate, zata fara zubawa taji yaayaa na fadin
"Ke mene haka"
Zakiyya ta kalleta tana bata rai
Wannan abincin na mint ne pa, malama in yunwa kikeji ki shiga kitchen mana ki dafa...
Dire plate din zakiyya tai ranta a bace wlh badan yaayaa zatai sa'ar mama ba da seta gaggaya mata bakaken maganganu, tana kunkuni ta wuce fuuu


Itakuwa zee tun fitar zakiyya tunanin shi ya fado mata, haka kurun speed din zuciyarta kan kara gudu inta tuno wani abu nashi ko shi kanshi, innalillahi ta furta, what's all this? Ta tambayi kanta amma ba amsa sai ma shigowar zakiyya data katse mata tinani
Zakiyya a kufule take zazzagewa zee yadda sukai da yaayaa
"Kuma fa kiga minnatun taci kwalliya ta fita da daren wai taje birthday, a can din inace ai akwai abinci ne, Allah zee badan ke ba da tuntuni na tattare kayana nayi gaba, haba duk uban aikin da mukayi bayan gajiyar makaranta sannan ace abincinma babu"
Zee ta kammala sauraran zakiyyaa sannan tace kwantar da hanakalinki, ni bari na dafa miki abu mai sauki, beside dama ni kodaa kin kawo abincin ma ba lallai ya birgeni ba nafiso na dafa da kaina, ai shiga kitchen abin jin dadi ne.....




X


Kashegari Tare da zakiyya suka tafi school, aka ajiye zee,, sannan aka wuce da ita sabuwar jami'a,
Tana sauka wata arniyar bakar mercedes tai parking dan nesa da ita, kyawun motar ya ja hankalin zee ta zuba ido tana son ganin me saukowa, bangaren me zaman banza aka fara budewa,
Wata budurwa ta fito tana magana da na ciki kuma ta wuce
Babu jimawa aka bude bangaren drivern, faruq ya fito cikin shigarsu ta farare da suke bal'in amsarshi, sai kamshi yake,
Yana fitowa idanuwanshi sukai tintibe da fuskarta tsaye tana kallonshi,
Fuskarta a hade yai saurin jaanyewa daga kallonta, itama zee ta juya ta wuce


"Basabanba yau ba'a yi latti ba"
Taji muryarshi a kanta sanda take zaune daga baya cikin ajin da babu dalibai dayawa"
Ta danyi yake "bamuyi ba zakace" yayi wata dariya cikin makoshi
Sannan ya zauna gefenta, "ina friends din naki?"
Basu karaso ba tukun"
Shiru ya ratsa na dakikai kafin ya katse shirun da cewa
"Nikuwa in bazaki damu ba zainab inaso ki kara ganar dani biochemistry, yana daga cikin courses din danake faduwa kuma ban ganewa ko da can"
Zee tace
"Inace yanxu ne farkon yinmu ko ka tabayinsu?
Ya amsa da "eh na tabayinsu tace
"To Sedai idan nima zaka koyamin physiology dan yana bani wahala bansani ba kodan farkon yi na ne"
Ya lumshe ido kamin yace "karki damu da wanann"


Tun daga wannan rana kusancinsu ya sake karuwa fiyeda baya, a sati sukan ware rana daya suyi karatu bamai yawa ba yadda kowanne ze gane yana jin dadin karatu da ita yadda take farfasa mai komi daki daki, itama tana jin dadin karatunsu, har takai dalibai suka fara gulmarsu
Wasu suce ai en uwa ne wasu suce saurayi da budurwa kowa dai da abinda ze fadi
Zeena ma saida ta zaunar da zee amma finfiris zee taqi cemata ko kala domin ita kanta zee ta kasa gane mene tsakaninta da faruq balle har taiwa wani bayani
Ana haka ne aka tapi hutun sati daya na mid semester break


Xxxxxx
"Anty hawwer nidai Allah inaga kamar na fara sonshi"
Zee ta fada tana kara jaddadawa anty hawwern
Ta cikin wayar tace
"Nima jikina ya bani yana sonki kamar yadda kike sonshi koma fiye".... This is the first time danaji kin firta wai kinason wani da namiji,,, kuma hakan bawai ya nuna gazawarki bane a'a dat makes u a human with emotions with feelings, nidai koma mene i ll still support u as a sister as an elder, fatanmu shima ya soki kuma ya furta miki yana sonki, dan tunda har kika firta nasan ya chanchanta ne i hop ur intentions towards him are clean"....


Ghost readers 😕 kunsan kanku


💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 22 : propose




Bayan sunyi cutting call din
Zee ta mirgina akan gadon
Asking her self
"Why do i even love him?, how and when did i fall for him?"
Zee ta lumshe idanunta tana hango siffarshi tun daga kasa har sama
Faruq? Faruq is a tall guy, his complexion? yanada haske sosai sekace mace, dan sajenshi dayayi daidai da face dinshi his nose, lips and his lazy eyes,
Ita kadai take ma kanta tambaya kuma take amsawa,
Tai saurin bude idanunta "what am i doing?" Wani bangaren zuciyarta yace "u re asking why u fall for him"
Ta sake lumshe idanunta
"Sassanyar muryarshi, dabi'arshi ta kama kanshi daga kula en matan banza, shigarshi ta mutunci, furucinshi dake nuna tarin hankalinshi.....


X x x x x x x x
"Er uwar fuj, fuj fa ya rasa ya zeyi"
Ya fada very low
Tace ta cikin wayar
"Nida aka watsar dani kuma shine ake sake nemana yanxu, na kirakaa har seda na gaji na dena kira baka tashi nemana ba se yanxu kuma"
Ya dan goge zufar dayaji tana taruwa a goshinshi
"Dan Allah karki bar dan uwanki lokacin dayake matuqar buqatar shawararki"
"Shikkenan naa tausaya yanxu me fuj yakeso"
Yai shiru yana jimami
Tace zan kashe wayata fa in bazakai magana ba
Ya hadiyi wani yawu kamin ya ce
"Zuciya batai min adalci ta fada soyayya a sanda bai dace ba sam,"
"Inji waye yace maka be dace ba... Kaga shawarar dana baka kwanaki itace zan sake baka, kaje ka sameta ka sanar mata sakon ranka, na tabbata bazatayi denying ba,"
Yai ajiyar zuciya
"Amma kinfi kowa sanin halin daanake ciki a yanxu, bakya ganin furta mata so kamar yana nupin zanyi wasa da rayywarta ne, idan na cusa soyayyata a ranta kuma mene makomar soyayyar tamu a gaba, yaya kike tinanin dady zeyi dani? Kina ganin nata iyayenta zasu barta taa cigaba da zaman jirana akan wannan mummunar akidar"
A sanyaye tace
"Bawai banyi tinanin wadannan bane yasa nace ka fada mata, banaso ka tsinci kanka cikin irin halin dana tsinci kaina, banaso ka biye wa mummunar akidar ta tarwatsa taaka rayuwar kamar yadda tai gaba da nawa farincikin ta kuma barkaa da danasani da tarin nadama kamar yadda ta barni"
Ta fashe da kuka mai ciwo wanda yasata tsinke kiran
Gaskiyar Anty-Safiyya ne.......
*
*
Kwanci tashi babu wuya gurin Allah, haka sati dayan hutunsu ta kare, duk su biyun babu wanda yayi contacting wani bawai kuma dan basuyi kewar juna ba, a'a saidan kowanne na tsoron kara fadawa soyayyar dan uwanshi in yaji daga gareshi...
*


Dayake gidan nasu estate ne kowa da nashi bangaren gidaje ne kusaan 8 iri daya, faruq nashi gidan a kasa yake, yayinda na sarah ke gefen nashi,


Yauma a tare suka fito dan haka suka wuce makaranta cikin motar tashi da bai dade da siyanta ba...


Tana tsaye bakin department din nasu ta hangi motar, tasan tabbas ta faruq ce, ta kasa janye idanunta daga kan motar, kamar ko wacce rana cikin kwanakin nan haka yau ma ta fito daga cikin motar sannan shima ya fito, who is she? Ta tsinci kanta da fadin hakan,
Sam bata lura ya karaso gurinta ba seda taji kamshin perfume sannan ta ankara Allah ma yasa bai jita ba,
Yayi mata cikakkiyar sallamarshi, itama ta amsa a sanyaye, sannan suka jera zuwa class
Sai bayan ta zauna sanann ta tina tsaiwar jiran hudiyya takeyi a wajen ta tabe baki"Allah dai ya sawwaqe min" ta fadi a ranta...
Muryarshi ta tsinkayo yana fadin
"Yau da karfe nawa zamuyi karatu naji an fara scheduling test's"
Tace "inaga bayan wanann lecturen babu wani, duk sunyi postponing so we hav enough time"


*
*
Ta dakko note dinta ta bude zata soma bayani sai ta daga kai
Yana zaunen amma ya zuba mata kasalallaun idanunshi,, wani kasala ce ke shigarta idan tana kallon fishy-like sleepy eyes nashi
"Faruq" ta fadi a hankali
Ya sauke numfashi kadan ya shafi beard dinshi
"I want to tell u something" ya fada
Ta rufe littapin "am all ears"
Ya sake gyara zama idanunshi kyam a kanta
"Zainab as i told u ealier am faruq usman jabbar, my mom is no more, Allah ya mata rasuwa tun banyi wayo sosai ba, my dad is a professor...."
Sai kuma yayi shiru na wasu dakikai yana tinanin ta ina ze lalubo bakin zaren ya soma warware mata"
A hankali ya cigaba da cewa
Mahaifina dan asalin jihar katsina ne, su hudu ne gurin kakanninmu
"Mu biyar ne gurin ummee da dady, Anty safiyya itace babba tana da shekaru 35 yanxu, se ya halisa tanada shekaru 31, sannan ni sai kuma Aisha kanwata shekarunta 25 da auta Hamra dake 20yrs of age... Duka basa kasar nan, suna europe sauran danginmu kuma suna katsina wasu kuma Abuja"
Shiru ne ya sake ratsawa
Shi da kanshi ya katse shirun gabadaya muryarshi ta chanjaa ta sake low and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login