Showing 69001 words to 72000 words out of 73133 words

Chapter 24 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5422

tsayin shekaru sun sake haduwa kuma ya aureta din
Allahu Akbar ta furta tana ganin iko irin na ubangijinmu maiyi yadda yaso, shikuwa dady yanxu ya saduda a yadda Anty hawwer ta bata labarinshi ya halisa kuma ana kwance ana jinya rae a hannun Allah, an ma kasa gane mene ke damunta


Zainab tace da Assiddique bata buqatar wani event amma Anty ta shirya musu kamu iya mata zallah, yace "to shikkenan"
Tayi mamaki dayayi saurin yarda ma, ranar kamu kuwa ana mata makeup an kusa kammalawa Anty tazo ta sameta tace "kuyi sauri zainab ango yana waje yana jiranki zaki karbamin sako"
Aka kammala ta lullube fuskarta da gyalen rigar me kamar net, complete white tayi sai touch na sky blue, ta fita ta sameshi cikin mota yace ta shigo
Ta shiga motar ranta bayaso dan bataso ta dade gurinshi, da tarin mamaki taga yaja mota sun soma tafiya,
Ta zare ido "banfa dakko clutch ba ina zaka kaini" yace kiyi shiru kawai mu tafi cikin salama
Ta dan harareshi
Sai gasu gurin katon gurin event, basu dade da zuwa ba su Anty ma suka karaso tazo ta kawo mata clutch
Nan fa guri ya dauka ai amarya da Ango sunzo
suka shiga ciki kawayenta da abokanshi na take musu baya, sai taga sam wannan ba kamu bane tamakar wata mashahuriyar dinner ce, duk taku daya da zatai camera man yana fitar da hoto fitacce,


Mint bata san me akeyi ba, tana can gidan yayanta dake Abuja itama tana sake gyara, dan kin zama tai a gidan tun saura sati biyu da bikin, a cewarta gara taj cikin en uwa zatafi jin dadi,
Anty siyama tana daga cikin taron, dan ita kadai ce tace zataje cikin matan Abbah jabir sauran duka cewa sukai ai abin na en mata ne, tun saura wata 1 bikin ta gane Mijin kanwarta zee yake nema kuma zai aura, amma gudun husuma yasa tai shiru koma mene sune suka kai zee gidan yanxu basuda bakin yin complain, tana tausayawa mint dan idan ta gane abinda ake ciki kowa bazeji dadi ba


Duka yaran Abbah jabir daidaiku ne basu halarta ba, bama kamar su zakiyya da ake ta rawar kai dan ji take tama fi zainab jin dadin wannan auren


Mint na zaune matar yayan nata ta kkwalla mata kira babu kakkautawa,
Jin kiran dai yaqi karewa yasa ta nupi dakin da take, ta wulla mata wayar hannunta "dama wannan ce matar mijin naki, ni kamar na ta6a ganinta ma a gidan siyama"
Mint ta dauki wayar tana son ganin amaryar mijin ta "
Ta rike wayar baki bude domin ba wata high makeup ne a fuskar zainab din ba,
Dariya tayi amma mai tafe da hawaye, "Anty zainab ce fa"
Sai ta saki wayar ta dora hannu aka
Wallahi Anty sai na musu rashin hankali, dama amanata suke ci ban sani ba"
Sai dure duren ashariya ya biyo baya


not edited
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 46: knotted


Matar yayan nata ta kada kai kana tace "to ke yanxu dan Allah mene haka, ji abubuwan da kike fada" mint ta dubeta idanunta sun fara cikowa da kwalla tace "Amma Anty idan banda namiji ma, mene ya rasa tattare dani, kalleni fa, babu abinda bani dashi"
Ta tabe baki tace zauna mint kiji
Kamar bazata zauna din ba amma ta zauna ranta na mata k'una
"Naga alama duk cikin yayyanki babu wacce zata fadamiki gaskiya mararanta shiyasa ni zan fadamiki minnatu, na lura sam bakisan me ake nupi da zamantakewa irin ta aure ba, abinda kikeso kuma kikaga yayi miki shi kike aikatawa wanda hakan kuma ba daidai bane, akwai sadaukarwa akwai haquri akwae hidimtawa juna akwae juriya dukka a zamantakewa irin wannan,
Ko ita siyama da kikaga tana zaune gidan mijinta lafiya dole tana haquri ne saidai in bazata fada miki ba, inaso ki sauke wannan girman kan da kika dorawa kanki domin baze amfaneki da komai ba, shifa aure bauta ne ta ubangiji ki tsaya ki kyautatawa mijinki tayu ki samu rabauta duk wadannan kyale kyalen da kike dauka shi ne aure sam basu da wani muhimmanci,
Minnatu ki sani shi fa zaman tare dole saida kyautatawa kuma ita zuciya an gina ta abisa son wanda yake kyautata mata, indai dagaske kina son mijinki kamar yadda kike ikirari to sai kin mishi biyayya, shi namiji shi ne shugaba, kuma wallahi badan mijinki me haquri ne bama baxe taba jurar wannan cin kashin da kike mishi ba, da tuntuni yayi waje dake
Abinda nakeso dake shi ne ki yarda kina da laipi, domin idan kika yarda kika amshi laipinki shi ne zaki samu ki gyara alaqarku keda mijinki
Itafa gaskiya a bayyane take ke da kanki kin san abinda kikeyi ba daidai ba, idan mijinki na kyautata miki kinsani idan ma kece kika tura shi bango ya dena kyautata miki kinsani, idan mijinki na ganin kimarki wallahi kinfi kowa sani, balle ma kuma Assiddique
Ke da ace wani ne keda wannan dukiyar kuma kike mishi abinda kike ma yusuf ke kinsan wulaqancin da zaki fuskanta ba kadan ba ne dan ba er kankanuwar wahala zakisha hannunshi ba
Shawarata anan ki kwantar da hankalinki, karki sake ki tadawa mijinki hankali domin indai kikai asararshi ko kika bari ya subuce miki a tunaninki na zaki sami wani to wallahi kece zaki kwana a ciki ke mutunce kuma mai cikakkiyar hankali ki tsaya ki gyara halayyarki dan ke kanki kinsan zama dake abu ne mai wahala,
Dan Allah ki saka kanki a mazaunin Assiddique idan shi ne yake miki abinda kike mishi ya zakiji? Zaki iya jurewa"


Mint tayi shiru tana sauraren maganganun Anty hakika ita gaskiya dama daci gareta, taji dacin maganganun Anty amma can kasan zuciyarta tana ji kamar gaskiya ne, idan da ita ke da matsayin yusuf a kasar nan, da bazata ma soma auren yarinya a nigeria ba, gani zatai duk ta girmi tunaninsu, da ita keda matsayin yusuf kuma matarshi ta mishi abinda ni nayi mishi bazan zauna da ita na sscond guda ba....


Anty ta katse mata tunaninta da fadin to shiyasa a alaqa irin wannan uzuri yake da dadi, yanxu naki turn dinne ki saka wa Assiddique da haqurin da yayi na zama dake kowa idan yayi aure kwanciyar hankali yake nema, amma du kinbi kin tada naki hankalin da nashi kin hana muku zaman lafiya, kije gurin malaman islamiya su kara sanar dake zamantakewa dan ni ba malama bace kuma ki nemi yafiya gurinshi dan kin dauki hakkinshi..


A bangaren Amare kuwa ana can ana shagali, ba kananun kudi aka liqawa zee din ba, bama kamar angon nata daya bude bakin aljihunshi yayita watsa mata nera da doollar saida t rike hannunshi a kunyace tana blushing shima ya dan murmusa sannan yace "ur wish my command my queen"
Hotunan bikin nan sunbi social media sosai, zakiyya ji take ina ruwa ta zuba a kasa tasha, yau zainab dinta ta auri mijin minnatu


An daura auren daya samu halartar dumbin jama'a manyan mutane na kasar sannan aka soma shirin kai amarya dakinta, zainab na daki itada su zakiyya Anty ta kira wayarta tace "ta fito" ta saka gyale a kai ta fita, tana sanye da atampa Ash and white, da farin gyalenta, ta sami Anty itada Abokiyar zamanta ya safiyya suna hira abinsu kai kace ba kishiyoyi bane abin sha'awa
Gefe ta ga faruq zaune kan kujerar dayake ba anan ake daura aure ba yasa babu jama'a gidan sosae ba kamar gidan Abbah jabir ba


Ta gaidasu suka amsa, Ya safiyya tace "zainab ina tayaki murna Allah ya sanya Albarka a aurenku" sai tayi murmushi ta daga kai ta kalli faruq yace "na tayaki murna qanwata"
Fuskarta da dumbin farinciki tace "Nagode yayana"
Daga haka ya tashi ya basu guri dama yazo yi mata Allah sanya Alkhairi ne, su Anty suka saka ta a gaba da nasihu kala kala gameda zamantakewa, daga karshe akayi shirin daukan Amarya


Komai ya tapi lafiya aka kai amarya gidan yallabai gurin kowacce matarshi, sannan aka kaita gidan mint, tana waiting falour a zaune tasha ado itama aka ajiye amarya a gabanta aka gama nasihu suka tashi batace dasu ko uffan ba
Zainab ta danyi mamakin mint, sai taji dadi da batai tashin hankali ba kamar yadda tayi tsammani,


A gidan yallabai zainab da wadanda suka kawo amarya suka kwana, da shirin kashegari amarya zata wuce gidanta dake UK, su Anty duk sun niyyaci zuwa ganin gidan Amarya amma fafur Abbah jabir ya hana yace babu wanda zaibi amarya,
Hakan nan suka haqura suka koma gida a kashegarin,
Zainab na zaune a dakin da aka saukesu, ta dubi kanta a mudubi sai sheki take exactly yadda Amarya ya kamata ta kasance, sai taji tayi kewar yusuf, tun ranar dinner dinnan rabonda ta ganshi dukka sun shiga busy ko waya basu samu sunyi ba, ta rike wayarta tana jujjuyawa kamar ta kirashi amma sai t kasa,
Kwankwasa kofar dakin akayi, ta bada izinin shigowa,
Daya daga cikin hadiman gidan yallaban ta shigo ta ajiye mata Accessories din tace "hajiya tace "ki shirya Anjima Angonki zaizo" tana kaiwa nan ta fita,
Zee ta matsa kusa da kayan tana kallansu, ta jinjina kai lallai wannan kaya kowa ya gansu yaga zallar dukiya,
Ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin less din da aka kawo mata, ta daura dankwali fuskarta fayau babu makeup ta dora gyalen dake ta walwali a kanta, ta jawo wayarta taga lokaci karfe hudu harda mintuna, ko ba'a sanar mata ba tasan lolacin sallah yayi ta tashi ta gabatar da la'asar dinta
Daidai ta idar wasu en mata suka shigo dakin, daya tace "ki fito wai ana jiranki", ta zura kafafunta cikin rufaffen golden shoe dinta sannan suka fita


Sai da suka wuce falour wannan bangaren aka kaita har falourn yallabai, a can taji presence dinshi dukda fuskarta a rufe take amma tasan yana cikin falourn,
En matan da suka mata rakiya suka zaunar da ita sannan suka koma,
Yallabai yayi musu tashi nasihar sannan yace zasu iya tafiya, zainab taji an kama kafadunta tasan ba maigidan nata bane amma batasan waye ba, har mota ta shigar da ita sannan tace "Amarya a dawo lafiya, daga jin muryar tasan ta mint ce


da sukaje filin jirgi taji motarsu ta tsaya a ranta tanata tunanin ina mijin nata ne wai, meya hanashi shigowar motar datake, bude kofar motar akayizee taji an yaye gyalen fuskarta, ta fara tozali da takalman kafarshi, ta daga ido ta kalleshi, looking exactly like Ango,
"To ai mun baro gidan yallabai kya iya bude fuskarki, tayi smiling, ya hada hannayensu ya fito da ita, sai lokacin zainab ta lura da tulin securities din da zasui masu rakiya tace "na dauka mu biyu zamu tafi" ya girgiza kai
"Yallabai baze taba yarda ba"
Sun sauka lafiya cikin birnin na london a ranar dukkansu baccin gajiya sukasha babu ma kamarshi daya tara uwar gajiya
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 47: His bride




Kashegarin ranar da magarib ya shigo gidan da leda a hannunshi, zee tana can falournta tana kallo abinta, sai taji kamar motsinshi ta ruga daki d sauri ta nemi hijabi ta saka ta koma bakin windown cikin dakin tana kallan wasu flowers a bolcony
Har cikin dakin ya shigo yana fidda kamshi, yasha ado bata juya ta kalleshi ba


Ya ajiye ledar hannunshi da cewa Amarya ga kazarki, tai shiru tana rarraba idanu, ya bude ledar kamshi ya shiga lungu da sako, ya taka ya karasa har inda take tsaye ya zagaye kugunta da hannayenshi, ta dan matse jikinta ya saka kanshi a kafadarta


Tun zee bata saki jiki ba ya saka saida ta saki jiki bayan sun kammala cin kazar yace "ki dan cire hijab din mana kisha iska, ta girgiza kai ai babu zafi, yayi murmushi
Nidai Ayshab na koma daga falour na jawowa amarya da Ango daki dan naga Assiddique niyyar kashe boss yake lol


Satin Assiddique daya gurin zainab ya koma Nigeria cikin sati dayan nan kuwa soyayya babu kalar wacce basu kashe ba, sanda zai tafi ma sai zainab taji gabadaya bataso, har da yi mishi kuka amma haka ya lallaba ta da cewar ta bashi 1 week zai karasa wasu abubuwan a Nigeria sannan ya dawo


Mint taji dadin dawowarshi, shima kuma yayi mamaki sauyi daga gurinta, ta chanja kamar ba ita ba, bakaken kalamai, ji da kai, rashin kulawa, duk ta rage su sosai, hakan yasa Assiddique yabonta, a lokacin ta nemi yafiyarshi kan abubuwan da tayi ta mishi, ya kuma ce ya haqura har ranshi


Zainab tana nunawa masu aikinta abubuwan da suka kamata taji wayarta na ringing ta dauka tana jin dadin ganin sunan Anty hawwer, sunyi er hira sannan tace mata "naga abin Alkhairin da mijinki yayi wlh na matuqar ji dadi Allah ya saka mishi da gidan Aljanna"
Zainab ta shiga nazari mene yayi din haka tace "Anty me kenan" zee tace duk yadda abin Alkhairin sa yayi ya bi social media ke baki sani ba
Tace "a'a Anty" Antyn tace "to ki duba news nasan zaki gani"
Ta shiga kafar news dake cikin wayarta, tana ta dubawa aikuwa saiga sunanshi
"Shahararren d'an kasuwar nan wanda ya kasance d'an gaban goshin yallabai wato yusuf Abubakar Assiddique yayi abin da ya bawa kowa mamaki"
Ta shiga cikin full labarin ta soma karantawa, har ta fahimci abinda angon nata yayi,


Har cikin kokon ranta taji dadin abinda mijin nata yayi, "zuciyarshi wankakkiya ce he's pure" ta tabbatar wa da kanta tana mai murmushi
Ashe abinda zaiyi kenan dayace na bashi sati daya, ta sauke numfashi cike da jin dadi, ta kudurce bazatai mishi maganar ba sai ya dawo


Ranar da zai dawo kuwa shiri ta maida hankli tanayi sosae, ta gama tsara duka abinda zatai mishi hatta da kayan da zata saka wajen tarbarshi sai da ta fidda su ta ajiye, cikin gidanta kuwa kamshin turaren wuta yake na musamman da Anty hawwer ta saka akayi mata hadinsu, su kajiji, damsu, sandal da sauransu, dayake kullun saita kona ta turara jikinta sai gidan ya kama sosai hakama jikinta
Ta maida hanakli ta shiga kitchen, karfe 2 ta soma girke girken itada wata baturiyar yarinya dake dan taimaka mata batai wasu abincika masu yawa ba dan haka da wuri ta kammala


Karfe 4 da mintina ta fada wanka dan sai 5 jirginsu zai sauka, ta fito taci ado bamai yawa ba looking as natural as always, tana jera abincikan a dining dinshi taji an murda kofar falourn, ta dubi wajen kofar tana jiran ganin mai shigowa dan kuwa tasan da dan sauran lokaci kafin karasowarshi,
"Yana so yayi suprising dinki" taji zuciyarta na rada mata, ta saki baki tana kallonshi ya tako yana mata murmushi,
Har ya karaso gurinta tana kallonshi, ya dan ja hancinta yace "bazaki amsa sallamar tawa bama" ta sunkuyar dakai "sannu da hanya"
Ta karbi briefcase din hannunshi, ta ajiye,
Tace "abinci ko wanka" yace zabamin tace muje na wanke ka to, yayi brief smile yace kafin nan muje kiga
Ya zagaya bayanta ya saka hannayenshi ya rufe mata ido yace muje
Tana murmushi ta dinga tafiya batareda tasan ina suke tafiya ba,
Sanda suka tsaya ta tabbatar harabar gidan ce saboda iskar dake kadata ya dauke hannunshi daga idanun nata hakan ya bata damar bude idanunta yayinda rantsattsiyar motar ta bayyana a gabanta ta karasa gurin motar sannan ta juyo tana kallonshi yana tsaye,
"Sabuwar amarya mukayi?" ya girgiza kai, kikayi dai matata, ta zare idoo
"Ni kuma" tasa dan yatsanta ta nuna kirjinta" yayi nodding "kwarai ma" ta bude bakinta widely "like seriously"
Ya saka mata dariya ganin yadda take acting, sai ta ruga zuwa gurinshi, ta fada kirjinshi...


Sanda sukaje wanka daga ita har shi sai da sukai wankan
Saida ya kammala cin abincin ta soma mishi maganar
"Naji Abin Alkhairin da kayi kuma naji dadi sosae Allah ya kara Arziki"
Yayi smiling "shiyasa ban fiyason yin abubuwan taimako dayawa ba, yanxu zai bi social media, sai ya zama kamar ma dan riya ne mutun yayi" tace "ka tsarkake niyyar ka ka kuma toshe kunnuwanka mijina, Allah ne zai biyaka ba mutun ba" yace "lokacin da najewa yallabai da maganar ki ya nunamin cewar bazan iya rike mata biyu ba saboda yanayi na ayyukana bana samun zama kuma ni kaina na yarda da hakan a lokacin ne nai niyyar yin abinda na dade inaso nayi, tun daga nan na soma duba cikin Al'amuran
Kasancewar duka harkokin yallabai na hannuna ne, shidai yakan duba wasu abubuwa ne lokaci zuwa lokaci amma jagoranci gaba daya a guri na suke wanda ni kaina hakan sunmin yawa, shi ne fa nayi analysis na fitar da abinda zan baiwa kowanne domin su tayani kulawa da harkokin tunda ba ni kadai ne d'anshi ba,"


Sanda ya ida bayaninshi zee ta ce "kuma yallabai ya aminta da abinda kayi?" Dafarko da na kira meeting yaqi yarda, daga baya da kanshi ya kirani yace "meyasa ban fara fada mishi abinda nake shiryawa ba" na bashi haquri, sannan yace shikkenan ya amince indai ina ganin hakan da nai daidai ne,
Na sake kiran meeting na musu bayani in details na kuma damkawa kowannensu dukiyar da zai cigaba da kulawa da ita a cikin dukiyar mahaifinmu"
Zainab ta daga thumb dinta, thumbs up Ango na, Allah ya kara girma yasa Albarka,
Ya sake mike kafarshi kan kujerar
"Kinga zamusha soyayyarmu cikin kwanciyar hankali bazan damu da ayyuka ba nima na samu sassauci"


Ya safiyya ta kira zainab tana mata godiya, zainab tace "mene kuma ya faru"
"Kinsan faruq is struggling da neman abinyi sakamakon baida certificate yasa gurare da dama suka dinga rejecting dinshi dukda abokan dady ne wasunsu, wannan raba dukiya da Assiddique yayi yasa daya daga cikin yayyen nashi ya dauki faruq aiki a masana'antar shi a bisa umarnin Assiddique


Zee taje ta sameshi da maganar daukan faruq aiki, yayi smiling "ina sane da duk moves dinshi ai zainab tun rabuwarku, kawae ina neman ways da zan rama miki abinda yayi miki amma sai na lura ba yadda na dauka yake ba, he's struggling to live, bayaga rashin wadatacciyar lafiya ga responsibilities na iyali, iyaye da yayye thats when nayi niyyar sama mishi abinyi atleast ya barmin ke" ya karasa fada yana pecking cheeks dinta tayi dariya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login