Showing 9001 words to 12000 words out of 73133 words
Chapter 4 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt
break tace "yayana kaga wani abin mamaki, an turo min kudi kuma na rasa gane waye" ta dan daga mata hannu sae ta tuna in yana cin abinci bae magana, ta cigaba da cin nata abincin itama, sae bayan sun gama yace "first salary dinki ne as the personal cook of this YUSUF ABUBAKAR ASSIDDIQUE"
sae yanxu ta tuna jiya fa ya karbi Acct. Details dinta, tae shiru tana so tayi korafin yawan kudin sae yace "karkiyi tunanin na karamiki ne haka kudin suke, ko waccen cook din tawa ma haka nata albashin yake" a cikin ranshi kuma yace saedae nakki harda karin allowance, u re more than a personal cook,
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 07: more than personal cook
Godiya sosae tayi mishi sannan yace "kinfi karfin haka gurina, i feel like u re my best friend someone i can feel free with, kinsan harkar manyan nan se a hankali, u don't have time, u dont have friends, babu wani lokaci da zakayi spending naka na kanka its all on bussiness, buh still u manage to make me feel good all the times"
Kwanaki biyu bayan nan suna hirar wani film da daddare yace "off the tv i want ask u something" ta kashe tvn sannan ta maida focus dinta gareshi yace "baki da sha'awar kara karatu i mean second degree" zee har ranta bata wani muradi amma take taji ra'ayinta ya chanja sakamakon wani tunani daya fado mata, tace ina muradi, munyi magana da Anty hawwer kuma tace idan na gama service na koma gurinta se na cigaba" yayi shiru ya zuba mata ido
"Noo bazakije gurinta ba zanyi kokarin settling sae na nema miki school"
"Gobe akwae bakin da zamuyi na gayyacesu suzo nan muyi meeting din dan na gaji da cin jagwalgwalon da suke serving gurin meeting so nake ki zage ki mana snacks masu dadi, yadda zasuji kamar su taune hannunsu, i know u offer the best" tace "in shaa Allah"
Zama tai ta nutsu ita daya tayi list na abubuwan da zatae sannan ta mishi presenting yace duk sunyi, sae ki duba abinda babu a kitchen kiyi magana na bada a siyo, itakam daso samu ne suje tare da me siyan amma tasan baze barta ba, ta nemi takarda tayi list na abinda take buqata ta bada,
komai ya kammalu, ranar tun da safe ta shiga kitchen ta saka Apron sanin datai aikin ba na mutun daya bane, dukkuwa daba yawa garesu ba amma ta shirya yin varieties iri iri, tana cikin rolling flourn ya shigo tace "yawwa pls taimaka min ka dauremin" ta fada tana nuna mishi Apron din data kwance kuma hannunta duk flour, ya karaso, a hankali yasa hannu ya kama igiyar, sannan ya daure idanunshi a kanta,
Bayan ta kammala wadannan ne ta koma kan drinks ta debo wasu chocolates din da suka siyo tayi garnishing chocolate milkshake din da tai, sannan ta ajiye a fridge dan lokacin yamma maa tayi, gabadaya baya gidan ma shima yana da aikin tun kafin azahar ya fita da tuni yana nan yana tayata koda surutu ne,
Sae after magrib ta tapi yin wanka duka komai ya hadu ta kowanne bangaren,
Shikuma tunda ya shigo yaji kamshin dadi ya koma nashi dakin yayi wanka ya fito ya sauya ammaa daya fito falour be ganta ba, waayarshi tae kara bakin suka sanar dashi sun karaso, ya fita yaje ya tarosu, yaa kaisu kebantaccen gurin dayasa aka danyi decorating sannan ya dawo still bata falour ya kira sunan ta amma shiru, ya kwankwasa kofar dakinta still shiru ya murda kofar dakin abinshi, tana zaune kan dressing mirror da waya a kunnenta suna ta hira tana nishadi da batama san ya shigo ba
Towel ne a jikinta, gashin kanta data wanke ya kwanta a gadon bayanta yana digar ruwa ya rufe bayan nata ma, ta sauke wayar a kunne tana kallonshi ta cikin mirror, tayi gyara murya tana jawo wani towel din ta rufe kanta,
yace "ki dan hanzarta sun iso fa" sae ya juya ya fita da sauri kamar zeyi tuntube,
Tai saurin miqewa ta shirya, dan ko mai ma bata shafa ba, tunda ta fito a wanka zeenat(her bestfriend) ta kirata suke ta waya saboda sukan jima basuyi waya ba dan bata nigeria tun watannin baya da akae bikinta, mostly sunpi haduwa ta chat
Suna zaune ta karaso tana ta kamshi mai sanyi na arabian perfumes din, ta musu presenting snacks din sannan tayi plating ma kowansu cikin jan hankali, tana cikin aikinne dayansu yayi magana da yaren nasara "your wife is gorgeous, i like the colour of her skin" ta dago a hankali ta kalli yusuf, shima ya kalleta fuskarshi babu yabo babu fallasa, bayan ta gama ta wuce suna mata godiya, ta tsaya gaban katon mirror n dake falourn, gabadaya jikinta a rufe yake ruf, face dinta da tafikan hannayenta ne kawae a waje, kenan fuskarta ya kalla har ya gane skincolour dinta. Kuma yace his wife amma be gyara musu da cewar ba matarshi bace....
Rannan suna falour sunata faman aiki, ya kalli yatsanta yace "your ring" ta dago da sauri ta rike yatsan da zoben yake, "who gave you" ta saki yatsan tace Ammi
Be sake tofawa ba se can yace "yau zamu fita and in the next three days zamu koma gida" farinciki ya bayyana karara a fuskarta Allah ma ya sani tana son komawa nigeria ta gaji da kasar turawan nan
Suka shiga katon mall din, zee tayi iyakacin kokarinta kar tayi kauyanci ya dinga lodo mata kaya dan ta tabbatr ba nashi bane saboda idan ya dakko abu guda biyu ze tambyeta wanne tapiso in ta zaba ze debi irin shi kamarr guda 4 ko 5, atlast suka karasa gurin perfumes, yace "i like ur scent, zaki iya fadamin sunan perfumes dinki inaso nima na dinga amfani da irinsu"
Nan ta nuna mishi su harda wadanda suka fi nata kamshi da tsada ma duka ya siya da nata da nashi, haka suka dawo gida
Sun kammala duk shirye shiryensu ya fadamata wadannan kayan natane yanaso tayi tsaraba dasu taita godiya kuwa har saeda yaji dadi a ranshi
As scheduled suka koma gida nigeria kamar yadda suka tsara, ranar sunsha tarba daga jama'ar yallabai se kace ba business trip yaje ba, a gajiye ya koma gida ya tadda mint tana ta bacci, ya dubi wristwatch din hannunshi, karfe 4 ne na yamma, kuma tasan sarae ze dawo amma ta kama bacci, ya shiga bathroom yayi refreshing ya fito, abincin dare yayi musu ordering dan yasan zee ta gaji kuma beson takura mata, a bangaren zee itama wanka tayi ta kimtsa wasu kayan da suka dawo dasu, ta ware wanda zata bada laundry,
Tana cikin aikin raba tsaraba ya kira wayarta, its after isha'i ta dauka yace taje, tana zuwa ya bata abincin ta cikin takeaway ta karba tayi godiya tayi mai saeda safe, yace no coffee? Tai murmushi tace later? Yace yeah... Ta koma ta cigaba da aikinta sae da tagama warewa kowa nashi tsaraban sanana ta zauna taci abincin, tana kammala wa wayarshi na shigowa
Tasan tuni ne zeyi mata dan haka taqi dagawa ta tashi ta tattara gurin ta wuce kitchen, tana cikin aikin ya shigo, ya zauna suna hira jepi jepi, ta gama ta bashi nashi itama ta zauna tasha nata a nan, ya ajiye mug din da fadin "jazakillah bi khair" ta amsa da Amin, sannan yace "goodnight"
Yana shiga dakin mint ya taddata falour tana cin abincin tayi mishi killer smile datasa ya manta da duk haushinta dayakeji, welcome home Star
Yace "thanks my dear ya zauna kusa da ita, bayan ta kammala ta jawo system yace bacci nakeji, ta fahimci me yake nupi sae ta share da fadin to kaje ka kwanta, yayi shiru yana kallonta "ke bazaki kwanta ba" ya tambaya tace eh inada aiki da zanyi ai ban dade da tashi a baccin ba,
Ya matsa kusa da ita yayi whispering a kunnenta, tayi murmushi wanda yayi kama da na mugunta tace sedae na rakaka kai bacci se na cigaba da aikina yace eh naji,
Suka tapi daki, yayi juyin duniya duk abinda zeyi yaja hankalinta amma taqi tana bashi uzurin seta gama aikinta, daga karshe yace ya yarda to ta gama aikin ze jirata, ta koma falour ya biyota amma ko a gefen slippers dinta, atlast se bacci ne ya daukeshi kanshi a kafadarta.....
Kuyi haquri da wannan, biki tinz
💍 *AL_HUBB* 💍
The love 💘
By Aysha b. Naseer
Episode 08: Asma'ul Husner
Gabadaya yusuf ya fita harkar mint dan yaga alamun aikin ta da karatunta sunpi mata komai,
Yinin yau zee bata saka yusuf a idonta ba, ko breakfast baice ta hadamishi ba, ta tura mishi list na abubuwan da zatae ya zaba kamar yadda suka saba amma beyi reply ba, kuma da alama be gidan, mint ma bata gidan se ita daya,
Da yamma likis mint ta dawo, lokacin zee na kitchen, suka gaisa sannan tace "girki ake tayi kenan in kin gama ki kawomin nawa falourn Star na kasa"
Sae after magrib ta kammala taje ta kai ma mint nata sannan ta koma daki, tana shiga taji alamun shigowa cikin gida tae saurin fita bolcony ta leka, motocinshi ne suka shigo, taji dadi a ranta dan ta damu da bata ganshi yau din ba, tun kafin ya shigo gidan ta fita kitchen tayi warming hadaddiyar rice din da tayi sannan ta soma yanka salad
Ta kammala hadawa duka ta tapi taje falournshi inda yace ta dinga serving ta ajiye a spot din datasan suna zama cin abinci, tana cikin jerawa taji karan steps, ya sakko sanye da kaya masu sauki, ya karaso har gabanta fuskarshi dauke da murmushi, ya zauna ya tankwashe kafa itama ta zauna tana mai gaidashi ya amsata sannan ta soma serving, ya kusa kammala cinhe abincin tace "ya aiki ya gajiya, yau gabadaya banyi aikina a kitchen ba sae yanxu" ya dago tana goge bakinshi "naje gurin yallabai ne tun safe, na dauka zan dawo da wuri amma abin yaci tura" tace "Allah yayi jagora ya bada sa'a cikin al'amura" ya amsa da amin, ta debe kwanukan zata wuce yace ki kai ki dawo tace to
A gaban system ta sameshi yana ta aiki, ta karaso ta zauna gefenshi tana tayashi da jera wasu taakardu, dan yanxu ta san mafi yawan ayyukanshi yadda yakeyinsu, suna tsaka da aikin ne tace "ina neman alfarma ne" ya janye idanunshi daga kan screen din ya kalleta "gameda me fa?" Ta cigaba da aikin tana mai bayani "inaso naje kano ne na kai tsarabar da ka siyo min saedae kuma bansan ya za'ayi data anty hawwer ba"
Be ce komai ba har suka kammala guraren 12 na daren yace "i will think about it"
Mint kuwa tun sanda taji alamun shigowarshi ta shiga wanka, saboda tana so tayi spending quality time dashi amma data fito ta leka se ta tadda shi yana cin abinci tare da zee, taita jiranshi shiru shiru, ta leqa again taga suna aiki, ta koma ta cigaba da jiranshi amma be zo ba har tayi bacci
Sae sannnan mint ta lura yusuf ya pita harkokinta gashi en kwanakin nan wata kewarshi take ta rasa dalili, kuma sae ta soma jin haushin zainab,
Tana zaune tana mamkin jin gidan yayi shiru, sanin da tae aikinta sae yamma yasa tun asuba ta koma bacci bata tashi ba sae yanxu karfe 1 na rana, ta fita kitchen amma babu alamun anyi girki yau, ta shiga part din zee taga ba kowa a gyare tsaf, yusuf kam bataa nemeshi ba dan tasan ya fita ma,
Wayarta tai soma ringing, ta dauka tana murnar fanin kiran Anty siyama, suka gaisa tace "meyasa baki biyosu ba?" Da rashin fahimta mint tace "su wa?"
Anty siyama tace "mijinki mana shida zee, yanxu suka bar gidana ta kawomin tsaraba ta bawa Abbah jabir kudade dayawa wae albashinta na farko ne" wata ashariya mint tayi
Amma yarinyar nan se naci ubanta kuwa, harni zataci amana, duk security babu wanda ze bita in gida takeson zuwa se shi, ni zataiwa bariki, kan ubaan can" haka taita zage zage kamar zautacciya daga karshe ta kashe wayar batama tsaya jin abinda Amty siyaman ke fadi ba,
Su zainab kuwa shi da kanshi ya dinga rakata suna bawa en uwa tsarabarsu, har gidan zakiyya ma sunje dasu kubra, khairi kuma da bata garin aka bada nata itama anty hawwer aka aika mata nata ta plane,
Plane sukabi suka dawo,
Itakuma mint data kashe wayar anty siyama sai ta soma tunanin me zataiwa zainab ta huce, hankalinta ya koma kan abubuwan da suka faru, yadda yusuf ya chanja mata a kwanakin baida abokin hira sae zee
Wayarta tai pinging alamun shigowar notification ta dan jawo tana dubawa, a hankali akalar tunaninta suka koma kan calendar ta datai notifying dinta, she's been so busy da tama sha'afa shaf, ta je gaban mirror tana jujjuyawa tana kallan kanta, "what?" Ta fada daa dan karfi ganin zarginta na tabbata, bata tsaya testing a toilet ba ta dau driver suka wuce clinic, da kanta taje lab tace su debi jininta ga test din datakeso suyi mata, nan sukayi kmaar yadda tace, babu jimawa result ya fito, ta karbi takardar tana jujjuyata, wani kyakkyawan murmushi ya subuce mata "she has been pregnant for the past 4 month amma bata sani ba"
Ta fita a asibitin tace da driver ya kaita gidansu Assiddique saboda tasan yallabai baya nan, tun a hanya kuma ta kira mami, harda dan kukanta ta hada karya da gaskiya ta fada mata wae Anwar (haka suke ce mishi a gida) bae kula da ita ya maida hanakli kan cook dinshi, sae su kwana biyu bae mata magana ba, wani sa'in in tayi mishi se yana amsa mata ciki ciki,
Mami ta bata haquri sanann tace zata kirashi ta mishi fada "yanxu yana ina ke ma kina ina"
Ta dan ja numfashi muryarta na cracking tace "ni mami na gaji gsky na taho gidan yallabai, kuma naje asibiti nayi test ina dauke da juna biyu, tun safe yau bani da lpia ashe yabi ta sun tapi kano wae rabon tsaraba" ran mami ya sake baci, ta lallaba ta sanann tace taje gurin momy
Taji dadi soaae dan tasan mami wanke shi zatae tas, suna hanyar karasowa gida yaga wayar mami, ya dauka yana murmushi "amma se fadanta ya tadamishi hankali yadda take ta fada kan mint ta kawo kararshi be kula da ita, sannan a karshe ta kare da fadin yaje gida ya dakko ta tana tareda momy" ta kashe wayar baice uffan ba kuma bata sanar dashi maganar cikin ba saedae har ranta tana farinciki da cikin
Yayi biting lower lips dinshi cikin rashin jin dadi, wanann abu da me yayi kama, yana shiga gida ya wuce nashi bangaren, zee taga chanji karara kan fuskarshi, ta girgiza kai ta wuce nata bangaren,
Ya fito a wanka yaga wayarshi na haske, over 4 missed calls duka kumaa momy ce, ya lumshe ido ya salam, ya girgiza kai "mint shouldn't hav done this, komi ya haqura dashi in tayi mishi amma ya zata hadashi da iyayenshi, ya zauna ya nade kafa abinshi,
Kwana biyu amma shiru yusuf baeje ko inda mint take ba, yasan idan yaje yanxu momy se tayi mishi fada, shikam ya za'a na mai fada kan abinda baeyi ba, wacce kula ce be bata ba kuma, koda cewar aurensu hadi ne amma be rage ta da komai ba infact he likes her tun a farkon ganinta dashi sae dae ita zuciya tana son mai kyautata mata, she already wiped all the love,
Gobe ake saka ran yallabai ze dawo kasar dan haka sae goben zeje gidan, ya san kuma dole yallabai bayanshi zebi, yayi murmushi, a bangaren mint tunda taji labarin dawowar yallabai a gobe ta hada ya nata ya nata ta komo gidan yusuf ta sani sarae beson lepin danshi Allah yasa randa ce da ita ba ciki ba, babu abinda ya mai zapi indae kan yusuf ne
Yana wanka ta shigo gidan dan fita ma zeyi, ta je ta ajiye kayanta sanna ta dawo bangarenshi lokacin ya gama shiri, ya tsaya yana kallonta ta taho gurinshi tana murmushi ya tabe baki ya dau turarenshi ya soma fesawa, tayi hugging dinshi ta amshi turaren ta ajiye ta soma shafar sumar kanshi, im back ta fada yace u're welcome, sae ta bashi takardar dake hannunta, ya karba yana dubawa at once kuma ya mance da komai yana mai bayyanar da faffadan murmushi, "are u serious?" Four month pregnant? Tayi nodding with a smile,
Ya yi hugging nata da kyau yana godiya ga Allah, masha Allah, ya xaunar da ita yana matsa kafarta... Da yallabai ya dawo kasar da kanshi yaje yayi mai Albishir zo kuga bakinciki karara a fuskar mafi yawan mutan gidan, shikuwa yallabai ya mata kyautar kujerar makkah guda biyar sannan a take ya zuba mata 5mil a acct. Ranar mint taga gata,
Dadi ya isheta ta rikice jin uban kudaden da aka zuba mata a acct., tun daga nan mint ta dinga rashin mutunci a gidan, kuma duk abinta kan zee yake karewa ko zee tapi mai kaulayin shan wahalar cikin wasu abubuwan kuma duk mint tana sane duka dan ta kuntatawa zee dinne se kace ba itace ta nemi tazo gidan ba, se zee ta dafa abinci kala shida mint tana cewa beyi mata ba, amma baiwar Allah bata nuna mata ta damu, dukkuwa da takanji babu dadi
Inma sharar dakine sae ta hana kowa shigowa ta dage se zee ce zatai mata, har tausa take mata amma batayi a gaban yusuf se baya gidan, a haka cikin mint yayi ta girma zama da kyar tashi da kyar, addu'a kuwa sosae yusuf ya dage da ita yakuma tilastawa mint yinta dan sanin yawan makiyan dake harin wannan cikin, kujerun makkan da yallabai ya bata kuwa tuni ta rabarma yan uwanta tana fadi wai ita matar billionaire, sanda lokacin haihuwar yayi ta saka aka gayyato wani mashahurin likita daga india yayi mata c.s ya fidda babynta katuwa mace, zokuga farinciki gun yusuf sae hamdala yake wa ubangiji akwae shi da son yara sosae...
Wannan yarinya tasha gata