Showing 15001 words to 18000 words out of 73133 words

Chapter 6 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5428

wannan abu na kara dugunzuma mishi hankali, zee ta lura gabadaya walwalarshi ta ragu sosae duk soyayyarshi da abinci kuwa yana faraci zeji ya fita a kanshi, wani sa'in ma se yaji tmkar ya bar duniyar ya huta, gashi brothers dinshi na kara rura wuta, wajen yawan damunshi da kira dukda be dauka amma abin na bata mai rai, idan be dauka ba kuma se su mishi da tex da ya jikin Allah ya sawwaqe, zainab ta sanar da Anty hawwer duk yadda suke ciki a nan ne ta bata shawarwari gameda abinda zatayi
"Ki kyale duk wata harka ta asibiti, ki tuno karatukan ammi, zan turo miki da zamzam sae mu tsara yadda addu'o'in zasu na tapiya ina fata dae ze yarda" zee tai jinkirin amsawa kamin tace "eh a tunani na dae bazeyi musu ba"
Bayan kwanaki uku kuwa aka turo da zam zam din, da kanta taje ta sanar dashi abinda take kokarin farawa, beyi wani jaa ba ya bata go ahead,


Farko da laqad ja akum ta soma ta tofa mishi gwargwadon yadda zata iya sannan ta karanta suratu ra'ad kafa 7 da niyyar koma mene ke damunshi Allah ya saukaka mishi ya bayyana, ya karbi ruwan data tsiyayo a cup ta miqa mishi yasha da bismillah acikin ranshi, kwanaki bakwae suka jera sunayin wannan, kuma a kwanaki bakwan ta lura walwalarshi ta soma dawowa amma yakan zauna shi daya ya rike newspaper kamar yana karatu amma ba karatun yake ba,


Yauma yana zaune rike da news paper din ta karaso bema san da zuwanta ba ta amshe newspaper din sannan ta bude Al'qur'ani mai girma suratur rahman ta miqa mishi, ya karba ya soma karantawa, ta fita ta kyaleshi yana karatun a zuci, be dena ba seda ya kai nasi, ya kuma ji dadi, sae ya soma istigfari, shikam yaushe rabonshi da bude Al'qur'ani ya ruqe ya karanta shi haka saedae ya saka a audio ya saaurara ko yana mota yace da driver ya saka musu, amma wannan nutsuwar da ladan rikewar da kallar ma ya rasasu, gashi yanxu da beda wani abu dayakeyi ya dauko ya karanta, tabbas d'an adam ba abakin komi yake ba, yanxu gashi ya koma kamar mara amfani, yayi hamdala daya tuno wasu ni'imomin ubangijin...


Yallabai kuwa dayaji maganar tafiyar mint hankalinshi ya tashi dan bazeso taje ta tonawa d'anshi asiri ba, gashi bemaji labarin tapiyar tata ba sai da tai sati da tapiya, ya dau waya ya kira Abbanta, bayan sun gaisa yallabai yake sanar dashi abinda mint tayi, dan da alama ma be sani ba, Abban ta yace "karka damu yallabai in shaa Allah zata dawo, yanxu bana kasar ne shiyasa ma bansan hakan ta faru ba amma idan na dawo zamu ga yadda za'ai"


Next abinda zee tai shine ayatus_shifa da ayatul_rukiya, to dayake sunada yawa yasa ta dan dau lokaci mai tsayi ma tana tofasu, suma kamar wadancan ta bashi yakesha da kadan kadan, rannan sunyi sallar magrib itada shi suna zaune a gurin da aka kebe domin yin sallah cikin falournshi, bayan sun kammala addu'a ne ya juyo ya kalleta ta mishi alama da ya dan dakata da hannunta, ya juyo yana dubanta ya tankwashe kafafunshi, ta dakko Al'qur'anin ta soma rera mishi kira'a, hakan yasata tunawa da Amminta, yayi shiru yana saurarenta da annashuwa a fuskarshi, bayan t ida ne ta dago ta kalleshi kawai ya sakar mata murmushi a take zuciyarshi ta ayyana mishi muradinta,
Zee zata iya cewa yau ce rana ta farko dayayi murmushi har haqoranshi suka bayyana tun sanda wannan abun ya sameshi, ba karamin dadi taji a ranta ba ganin Assiddique din data sani yau da dawo,


Kwanaki biyu bayan nan barrister yazo ya sameshi da maganar wani award night da akayi organizing tun last month kuma sunce shine babban bako me bada awards, Assiddique yyi shiru ranshi babu dadi dan already sun fadamishi tun yanada lpia kuma yayi accepting.. ya rubuta ma barrister "i will think about it" daga haka suka gimtse maganar, ya kammala shan ayatur rukiya da shifa sae wasu ayoyi na warware sammu suma ta sake tofa mishi, rannan suna kitchen yana zaune kan worktop, gabadaya zee ta sha'afa beji, yanata binta da ido tana harkokinta ji yake kamar ya dakko takarda ya sanar da ita sakon zuciyarshi, sae yaji tace "yaya_na tea ko coffee" sae kuma ta dago tunawa da tae baiji amma sae taga ya jawo memo ya rubuta "i can hear u, i will prefer tea" taa kalleshi da dumbin farinciki batasan sadda ta dinga jera Alhamdulillh ba har saeda ya zuba mata ido yana murmushi, ta rufe bakinta cikin tsananin jin dadi, sae ya dau takarda da pen din yana rubutu "jiya bayan na saka karatu a daki na kwanta dukda ba ji nake ba, har bacci ya daukeni, banyi awanni biyu ba nayi mafarki mai tsoratarwa na tashi ina gumi, a lokacin naji sautin karatun yana ratsa kunnena, now i can hear ur sweet voice"
Tayi blushing tana kara godewa sarki Allah a nan ya sanar mata da maganar zuwanshi Award night nextweek ya nemi shawararta, itakam yanxu base ta rubuta mishi ba tunda yana jinta, tace mai eh yaje din tundaa har yayi alqawari kuma babu wanda ze gane baya magana tunda yanaji, ze miqa award din itakuma zatai speech" da haka sukayi concluding


Kowacce rana kowanne second kowanne minti sae Assiddique yaji kamar ya zauna ya rubutawa zee tsararriyar wasiqar da zata bayyana sirrin cikin zuciyarshi amma sae yake danne zuciyarshi akan har se ya samu lpia zepiso ya sanar da ita wannan muhimmin al'amari da bakin shi, tabbas ita zuciya tanason mai kyautata mata, zee ce ta zaba mishi kayan da ze saka in zasu tapi award night din, akwae labarae dayawa dayakeson bata gameda artist din da za'a karrama amma babu baki kuma yayi tsayi ya rubuta mata su, zee tana daki ta kammala kwalliya, sam ba ma'abociyar kwalliya bace ta dade sosai rabonda tayi kwalliya irin haka ta saba shafa lip gloss kawae da er powder shikkenan, ta sakke kallon kanta a mirrorn tayi murmushi (pic on wattpad), sannan ta dauki dan kwalinta ta daura


Bayan ta fito ta taddashi cikin motar a zaune, yayi kyau zee ta ciro wayarta tayi mishi hoto (pic on wattpad) ganin yau ba spec a idanunshi yasa tace "kafi kyau in bakasa wannan bakin tabaran ba" yayi dariya sannan ta zagaya baya ta shiga,
Sanda suka karasa ma an dade da fara taron, shine ya fara shiga itakuma ta tsaya amsa wayar zeena tana sanar da ita ta dawo nigeria, tace okay zamuyi waya anjima,
A lokacin har ya shiga m, ta bishi da dan sauri, akwae mutane dayawa a wajen, ta hangeshi yana bama wani matashin saurayi award, ta karasa ta samu guri ta zauna ta dauki lemo kenan, Assiddique ya matsa fuskar matashin saurayin ta bayyana, glass cup din hannunta yyi crashing lemon data saka a baki ya kwareta harda fitowa ta hanci, wannan ya jawo hankalin mutane ciki harda saurayin, amma se ya tsaya daga nesa yana kallonta, Yusuf ya karasa da hankali yana dan bubbuga bayanta idanunta suka kada ssukai jawur ta daga su ta zuba cikin nashi, yana nan tsaye rike da award a hannu,
Ta ture Assiddique dake gabanta ta karasa gabnshi sae yayi saurin fita waje, itama ta bishi a hanzarce, Yusuf kuma ya bisu da ido kawae amma ganin baze jure ba ya dagawa me taron hannu sigar neman excuse


Da dan duhu a inda suka fita suka tsaya ta kare mishi kallo tun daga sama har kasa "faruq" ta furta kamar bataso,
Be amsa ba kuma be dena kallonta ba, sae ta durqushe a gurin why, why faruq, ka tapi ka barni, u always make me missed u
Tana kuka sosae take wadannan maganganun, wanda ta kira da faruq din ya bita ya tsugunna a gabanta, da hannu biyu ta dinga dukan kirjinshi, "u left me, kayi tafiyarka on our anniversary without a goodbye, u always love it when u make me miss u"
Sae lokacin yace "zainab" da muryarshi mai bala'in dadi, ya cire hannunta daga kirjinshi, sannan ya fara tari mai karfi, Assiddique dake nesa dasu yana sauraronsu ya karaso
Zee data rikice ta koma gun assiddique pls help him, har jini ne ke fita a bakinshi, suka daukeshi suka saka a mota unconsciously,
Dukka sukai jigum jigum, sae shessheqar zee lookaci zuwa lokaci
Da suka karasa ma sae aka bashi gado dan za'a mishi gwaje gwaje sosae, zainab duk ta rude hankaulanta sun dugunzuma,
Shikuma Assiddique babu baki balle yace mata wani abu ko ya lallasheta ya zuba mata ido, da kanta ta kwantar da hankaalinta amma tana jin daci a ranta, ita tace mishi su koma gida tunda dare yayi,
Tun a mota ya rubuta mata who is he, idanunta suka taru da hawaye tace " the owner of this ring" ta daga yatsanta wannan zoben datace mishi ammi ce ta bata yayi shiru yana tunani, sai ya rubuta mata tel me about him, tai murmushi kadan sannan ta gyada kanta i will
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 12 & 13: Begining


Zee ta soma tuno masomi kuma mafarin lamarin
.
.
.
Gabanta ya sake faduwa a karo na barkatai,,,, sam bata gane lecturen da malamin keyi, kanta ya shiga sarawa, a hankali ta dukar da kanta kan desk din cikin ajin tana mai jin juwa na dibarta, Zeena ta dan rankwafo da nata kan saitin nata tace " zee mene ke damunki ne wai?" Zee ta daga mata hannu kurun tana mai maimaita sunan Allah akan labbanta, wayarta ce ta shiga vibrating ta zaro ganin sunan Anty hawwer yasakata dagowa ta kalli malamin dake karkare darasin dan ya fita, ta dan sauke numfashi sannan ta maida wayar jaka, malamin na fita ta zaro wayar ta kira Anty hawwer, tayiwa zeena alamun tana zuwa saboda hayaniyar dalibai, da sauri ta karasa inda keda saukin hayaniya lokacin Anty hawwer tayi picking, "Anty mene ya faru?" Anty hawwer tai dariya, "kamar ya mene ya faru, meze faru kuwa?" Zee tai shiru batareda sanin amsar da zata baiwa Anty hawwern ba, Anty hawwer ce ta katse shirun da fadin "ke tsiyata dake se ki shiru kinajin mutun na magana, ke kika jiwo, dama ce miki zanyi in kin gama lecture din ki biyo gun maman fatima naje wankin kai sai mu wuce gida kawai", zee tace to Anty hawwer, ta fadi a sanyaye sannan suka katse kiran,
Cikin ajin ta koma ta tarad da zeena da en tsirarun dalibai da basu fita ba, zeena ta kalli agogon hannunta tana miqewa, "zee karfe biyar (5) fa yanxu har da rabi, muje gida ko? Zee ta gyada kai itama tana karban jakarta sannan suka fita daga cikin theatren,
Bayan sun fito suna tafiya kan kwaltar cikin makarantar Zee tace
"Zeena Anty hawwer na gurin maman fati zan biya ta can sai mu wuce gida" okay to muje kawai, Zee tai murmushin jin dadi dan ta tsani tafiya ita daya,
Bayan sun futa cikin school din suka tsallaka titin sai gasu gaban wani tafkeken Beauty pala, gurine na gyaran jiki, gyaran gashi, kafa, fuska da duk wani gyara na mata, harda bangaren makeup a ciki,, sliding glass in sukayi suka shiga katon gurin, daidai shigarsu suka tarad da Anty hawwer na kimtsawa itama an kammala gyaran, zeena da Zee suka karasa gurinta, zeena ta Amshi bbynta mai suna Nihal, sannan duk suka gaidata
"Anty hawwer barka da yamma" tai murmushi yawwa barkanku daga haka suka fita zuwa motarta,"
Anty hawwer ke tuki, Zee na baya ta kwantar da kanta a kujerar ta baje abinta, zeena da nihal kuma suna gaba, hirarsu suke su biyu sai lokaci lokaci Zee ke sako baki
"Anty Abbah ya dawo kuwa?" Zee ta tmbya,
Eh ai tun wajen 2 ma yana kasar nan, dan na barosu a gida shida Ammi," Zee taji dadi jin Abban nata ya dawo,
Zeena tace "Anty yanxu dagaske jibin zaku wuce saudi?"
"Eh zeena ni kaina har na fara kewarku, ko na tafi ki kulamin da waccan shiru shirun kawartaki kinji zeena" zeena tai murmushi tana kallan fuskar Zee ta mirror, baki da matsala Antynmu,ku kula da karatunku dan Allah banda wasa, banda abokan banza da samari barkatai,
Haka taita musu nasiha har suka karasa unguwar mai titi a tsakiya da gidaje bangaren hagu da dama, tun farkon layin suka sauke zeena tana musu sai gobe zata shigo ta gaida Abbah ta mai sannu da hanya" sukuma sukai gaba, bayan Anty tace lallai sai Zee ta dawo gaba, haka ta dawo ta dau nihal,
Tafiya suka sake saida suka kai karshen layin sukai kwana sannan suka hangi dandazon jama'a hayaki ya saka gurin ya kara duhu,
Zee ta dan dafe kirji tana jin kanta na sarawa tamkar an buga mata karfe a tsakar ka,
Hasbunallahu wa ni'imal wakil ta furta a hankali,
Jikin Anty yayi sanyi ta dubi Zee dake dafe da kirji tana saita numfashinta, cikin dakewa ta taka accelarator kadan suka kara gaba, yawan mutanen dake gurin yasa suka toshe hanya dan haka a tilas Anty hawwer ta samu guri tai parking tana mai danne zuciyarta da fatan Allah yasa tunaninta ya zama karya, tun kan Anty ta ida parking Zee ta bude motar, a tsawace anty tace "ke kula dalla zaki yar min da 'ya" Zee da sam tama sha'afa akwai nihal kan cinyarta tai saurin riketa tana rungumewa a kirji gam kamar za'a kwace ta, babu wanda ya iya sake cewaa dan uwanshi ko Qala suka fito suka rife motar, sai kuma suka zama kamar masu san'da suke tafiyar a hankali a hankali, har suka ida karasawa,
Abbah jabir ne a tsaye yana waya hankalinshi a matuqar kidime, Zee ta daga kanta sanda ta ganta a gaban konannen gidan daya kone rumus,,, ta kada kai tana mai sake kallan gidan a karo na biyu, sai lokacin Abbah jabir ya kula dasu, Anty ce tai karfin halin fadin "Abbah jabir, gobara akayi?" Ya kada kai kurun,
Zee ta sake kankame nihal tanajin wani abu mai zafi na kuna a kirjinta,
Sama sama taji muryar Abbah na fadin "kuyi haquri Allah ya musu rasuwa"..... Shine kalmar dataaji ta karshe, wata murya taji a kanta tana fadin "sun rasu, sun rasu, Ammi da Abbah sun rasu, wayyo mun shiga uku",


"Ta rasu? Ammi rasu?, dan Allah karki tafi ki barni" ta kumajin karajin muryar tamkr zata fasa mata dodon kunne tana mai hautssinewa da dukkan neurons din cikin kwakwalwarta, sai aka fasa wani kuka mai azabar karfi da razanarwa, daidai nan ta bude idonta cak ta dena jin komi tsit
Lokaci daya ta bude dukkan idanuwanta tana mai kallon cieling din dakin datake, sai ta kalli gefen daga sama ta hangi abin karin ruwa, take ta soma motsa sassan jikkunanta, hakan yasa tabi karin ruwan da kallo har zuwa inda ruwan ke shiga wato hannunta, asibit? Shine abinda ya fado mata,
Zee ta maida idanunta ta kulle sannan ta bude, ta kalli gefenta, dakine mai girma babu kowa kuma a cikinshi, ta dauki tsayin seconds sai aka bude kofar dakin, su uku suka shigo
Zeena tai saurin karasowa gurinta tana mai danne kukan dayazo mata , Zee Zee, ta maimaita sunan nata
Sannu Zainab, Abbah jabir ya fada, Kallo daya Zee tayiwa Anty hawwer ta kauda kanta, saboda yadda fuskar Anty hawwern ta chanja, ya bayyana karara tasha kukane kuma tana kan sha,
Sun rasu ko? Zee ta tambaya a matuqar sanyaye,
Zeena dake zaune gefen gadon ta kamo hannun Zee ta hada da nata kurun tana mai shanye nata kukan, cikin dakewa Anty hawwer tace
"Zee baki da lpia kiyi kokari ki cire duk wata damuwa a ranki, daga haka ta fice da sauri,
A hankali hawaye suka gangaro gefen idanun Zee dake kwance, shima Abbah jabir din fita yayi,
Wani abu zeena ta hadiya kamin tace "hawaye kuma Zee, namene haka, kinajin dai abinda Anty ta fadi",
Cikin karfin zuciya Zee ta dan dago daga kwancen, zeena ta taimaka mata ta saka mata pillow a bayanta, bayan ta zauna ne, ta kuma matse hannun zeena dake cikin nata har saida zeenan ta kallin hannu ta kuma kalli Zee,
"Zeena na rasa Ammy shikkenan Ammy na ta tafi, zeena kinfi kowa sanin wace Ammi, kin kuma fi kowa sanin ya Ammy take," zeena ta sunkui da kai jin Zeen na kokarin karyar mata da zuciya,
Zeena Ammy zeena Ammy, zeena ta kalli Zee da bakinta ke ambata sunan Ammy idanunta babu hawayen kuma,
Ki kwantar da hankalinki Zee, Zee ta murmusa kadan dan akwaita da haquri kam, dukkansu shiru sukai yayinda Zee ta lula duniyar tinanin Amminta
A hankali take tariyo rayuwarta tareda Ammi,
Amminta mace ce mai hakuri, mace mai tarin ilimi, tundaga na boko zuwa na addini, ga ilimin rayuwa,
Her whole best moment in dis life is her moment with Ammi,
Kasantuwarta autar Ammi yasa tafi samun kusanci da Ammi, sukai muguwar shaquwar ko a bacci ta kanyi mafarkin Ammi
Wasu zafafan hawaye masu dumi suka gangaro mata,
Koyaushe kuma kowacce rana baza ta kare ba Ammi bata karar da ita da wani sabon ilimin ba, A gurin Ammi ta koyi karatunta na Alqur'ani wanda sukeyi duk bayan idar da sallar magrib har zuwa isha'i, duk wata rayuwa kamilalla Ammi ta nuna mata, kuma duk wani gata na duniya Abbanta ya sama mata
Ta sharce siririn hawayen da suke zuba sakamakon tuno iyayen nata da tai, mutane mafi soyuwa a gareta duk duniya, mutane datafi shaquwa dasu duk duniya, haka kuma mutane mafi daraja a rayuwarta
A bangaren zeena ma, sarai tasan halin Ammi halin dattako, koda ita ba diyar Ammin bace amma ta samu abubuwan karuwaa dayawa tun daga kuruciyarsu har zuwa yanxu da za'a iya cewa sun mallaki hankalin kansu tunda suna da shekaru 19 ne a duniya, Ammi ta sanar dasu darusan zaman rayuwa kuma tana kan sanar dasu, ashe zaman nasu bazaiyi nisa ba, ashe Ammin bazataga auren autarta ba
Duka su biyun basu an kara da junansu ba, basu san cewar duka hawayen suke ba,
Anty hawwer da shigowarta kenan ta tsaya tana kallonsu
Kasa jurewa tayi ta karaso ta rungumesu duka tana mai share kwalla
Sai a lokacin da Zee ta jita jikin yayarta kwalli daya duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login