Showing 51001 words to 54000 words out of 73133 words

Chapter 18 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5416

mintina goma a haka sannan ya dago ya zuba idanunshi a kanta,
Itama ta dubeshi a raunane, gabadaya ya sauya, idanunshi sun zama abin tsoro har wani red suke badawa da orange dan huci, kan hancinshi da kunci da labbanshi ma sunyi orange orange, ta sunkui da kanta hawaye ya digo mata
"Nasani ko nawa en uwan idan suka san result din nan bazasu bar wannan alaqar tamu ba, yanxu an waye se da genotype kafin ayi aure a mafi yawan lokuta..." Ya katseta
"Me kike nupi nerhnerh?
Ki dubi tsabar idona kice zaki rabu dani,
Ta shiga girgiza kanta,
Wannan kuma nayi karya
Yadda nakejin zuciyata namin zafi watakil ko rabin haka bakiji, bazan rabu dake ba, ni ne mijinki, ina qaunarki ina sonki nerh nerh, jeki gida
Kmaar an hankada ta
Ta bude kofar da sauri ta fice taja ta tsaya har ya bar gurin sannan ta goge hawayenta ta shiga gidan




Kusan sati biyu bayan nan bata sakejin wani maganar genotype daga bakin faruq ba, harkokinsu kawai sukeyi, itama kuma bata ko tmbyeshi ba, da kanshi yazo ya sanar mata
"Nerh nerh dady ya amince da auren mu, ya yarda muyi aure in muka kammala karatu"
Da rashin fahimta ta kalleshi, irin suspicious look dinnan, like mganar daya fada gaibu ce
Sai ta dauke kanta ta cigaba da danna wayarta, dayake kan kujeru suke a sararin school din, ya tsugunno gabanta yana kallanta,
"Nerh nerh pls say something" ta miqe tsaye kawai, shima ya miqe da sauri,
"Me kake shirinyi ne?, me kaje ka shirya ka fada musu? Domin dani da kai duka mun sani ko momy ko dady bazasu goyi bayan wannan auren ba"
Ya saka hanky ya goge gumin dake tsattsafowa a goshinshi dukda iskar dake kadawa a gurin,
"Tsorona Allah tsorona karki ce zaki barni, my life will be empty, pls zee wannan ba wani abu bane da har ze saka mu sadaukar da soyayyar da muka gina da kyakkyawar niyya"
A hankali ta koma ta zauna ta tallafi chin dinta da dukkan hannayenta,
Ta girgiza kai "ya akayi soyayya ta rufe maka ido har haka FUJ?, sukuma yaranmu fa? Se muna sara muna duban bakin gatari fa"
Be zauna ba yana tsayen "wai meyasa bazaki gane irin son da nake miki ba, meyasa bazaki gane irin loneliness din danake ciki ba kafin shigowarki rayuwata,, haduwar mu ta samamin abubuwa da dama dana rasa, zainab kin cike min gurabe dayawa a rayuwata, kin haska rayuwata, wallahi ke alheri ce a rayuwata, na rasa ummee na bana so na rasaki pls zainab"
Ya karasa yana mai zaunawa a sanyaye
Ta dubeshi "she feels for him, yes she love him, itama kanta datake maganar batajin zata iya rabuwa dashi din"
Har kin manta sanda kika ce min u're ready to fight the world for me, ko kuma dama duka zance ne?
A sanyaye tace "ko kadan kalamai na ba iya labba suka tsaya ba har zuwa jini da tsoka zuciya da ruhi tareda ilahirin jikina" ta hadiyi yawu mai daci "now tell me, me kacewa su momy da har dadyn ku ya yarda?"


Dont forget to follow my wattpad page, comment and share
@AyshabNasir


💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 34: For how long


Yace "i just bribed the doctor not to reveal the real result to them, and he agreed" yayi pausing da rashin son karasa fadin abinda ya soma tace
"So u lied fuj? U lied to them? And whose idea was that?"
Ya shafa kanshi "Anty safiyya"
Sai kuma ya kalleta da kyau, "hav faith in our love zainab, stop worrying about the future, its all in the hands of the Almighty, we shall continue praying for the best and i hope u re my best, i know u re"
Komai ya cigaba da tafiya watarana farinciki watarana kuma akasin hakan kwana a tashi babu wuya ga mai rai da lpia, su zainab suka kammala jarabawar first semester na level 3, babu abinda yaa ragu a soyayyarsu sai ma shaquwa mai karfi dake kara danko tsakaninsu


Yau sukai last paper ya kaita har gida sannan ya dakko abinda ya saka a mota a back seat, ya miqa mata ki rike da kyau kuma se kinje daki zaki bude, my regards to zakiyya and Anty"
Tace okay bye take care and thank you,
Sukai waving juna ya tapi, haka ta dauki katon abin datake kyautata zaton frame ne ta wuce dashi har daki kuwa, dayake su zakiyya sun gama exams dinsu tun last three days da suka wuce ta tadda ta a dakin,
Zee ta shimfide shi a kan gadon ta soma kiciniyar budewa da zumudin son sanin menene,
Daidai sanda ta karasa unwrapping, hoton data gani a gidan faruq ya bayyana a fuskarta, amma wancan half done ne wannan kuwa cikakke ne ya kammala zana ta zane mai kyau so smooth fully blended, zakiyya ta karaso tana karewa zanen kallo
Muryar zakiyya ce ta dawo da zee daga duniyar tinanin data tapi,
Wow amma wannan F.U.J dinnan sun iya zane, ya akayi suka zanaki?
Zee tace "uhm, ehhh, sun iya sosai wlh, nima faruq ne ya bani as a gift,"
Daidai nan waayar faruq ta shigo, zakiyya tace "oh dan halak yaqi ambato, zee ta dauka tana kara kallan zanen zakiyya kuma ta fice a dakin
"So how do u like it my dear"
Tayi smiling, "i dont just like it, im so much inlove with it"
Tohm so nake ki bani dama kiyi placing dinshi cikin dakinki a saman bed ko a side, yadda duk sanda kika gifta zaki ganshi,
Tace wannan ai abu ne mai sauki,
"Tunda kin manta ni bari nayi reminding naki, "its our anniversary gift, look closely at the frame, akwai rubutu a jiki, i love you nerh nerh"
Se yanxu ta tuna today 10th june is exactly their anniversary, Gosh
Taa rike goshi, bayan sun gama wayan da faruq ta zuba ma frame din ido, yes akwai rubutu kam dagaske written in a golden shinning colour amma se mutun ya zuba ido ze gano shi a gefe yake kasa,
"It's exactly 10th of june, its exactly the day i met the only person in the world that I want beside me every day and every night for the rest my life. Having you by my side makes me the happiest, most grateful and luckiest person in the world. Here is my vow to you, i vow to be with you until the end of forever.... Happy anniversary soul mate
Gurin "i vow to be with you until the end of forever" sai yayi bold kuma yafi fitowa akan sauran rubutun, ba karamin nishadi kalamnshi suka saka ta ba, ba kankanuwar kwanciyar hankali da nutsuwa suka kara mata akan relationship dinta da faruq din ba,


Watanni hudu suka shude bayan nan, hakama rayuwar na cigaba da garawa, sun kammala level 3 successfully hakama zakiyya ta kammala level 2, kubrah da usama sun gama college dinsu, khairi kuma itama level 4 zata shiga yanxu
A wannan semestern data kare babu wani abun daga hankali daya faru se wata jarabawa da sukai ta human genetics, a ranar ba guri daya suka zauna ba, cos faruq yazo late time din har an fara ma, ya zauna daga baya, wani dan P.G aka barwa yayi supervising nasu sukuwa dalibai da sukaga sun sami salala sai akaita bude waya kuma mostly en baya ne keyi inda faruq yake, en gaba ma basu san wainar da ake toyawa b, se bayan sun gama ne faruq ke bawa zee lbarin abinda ya faru a exam hall din taita mamaki, ai bakiga yadda suka dinga fidda waya naked bama da kinsha mamaki, yanxu karatu duk ya baci, yai ta mata mita....


maneman su kubrah sun nemi gaanin Abbah jabir tun kwanaki, se Abbah jabir din ya saka rana zuwa ending september in shaa Allah ze zo gida dan yana saka ran an kusa mishi transfer zuwa guri kusa, to shima faruq se yace in Abban yazo zeje ya gabatar da kanshi
Anty shirye shirye take sosai na tarban Abban dan gidanta ze sauka saboda ita keda girki a wannna lokacin, tareda maman su khairi ya dawo ya fara sauka wancan gidan sannan ya dawo gidan ta, minnatullahi bata gidan a lokacin taje Abuja gidan yayansu, dama service din nata suna ne kawai, tunda harkar nigeria a saki kudi ne kawai a wuce gurin
Rana daban daban ya basu, iyayen Bashir (meson kubra) su suka fara zuwa, sun yi magana sosai dan har da niyyar kawo kudi ma sukazo amma abbah yace su bashi wata daya zeyi bincike ya kuma sanar da en uwa, sai na khairi (Bukar) shima same Abbah ya sanar dasu dan duka a shirye suke dama, sai kuma ya mujahid (na zakiyya qanin uncle muzakkir), shima Abbah ya fada mishi hakan dukda yasan ta bangarenshi ba wani matsala tunda yasan en gidansu tun kan uncle muzakkir,
Faruq ne yazo a karshe saidai shi nashi ba kamar na sauran ba, ya sanar da Abbah shi ba da wurwuri yakeso ba dan be kammala shiryawa ba, se sun gama karatu tukunna, shima Abbah yacemishi ba matsala zeyi bincike kanshi,
Zee tai shiruuu tana tunani
Tunda faruq ya sanar mata Abbah yace zeyi bincike taji jikinta yayi sanyi, indae kuwa za'ayi bincike kan faruq da prof. to akwai matsala tattare da gidan nan...


Wata daya bayan nan, Abbah yayi bincike kan maneman, komai na biki ya cigaba da tafiya aka saka bikin kubrah da khairi da zakiyya, duka rana daya za'a daura auren on may na sabuwar shekara me kamawa,
Kafin Abbah ya koma ya samu transfer din kuwa amma zuwa kaduna ne hakan yayi ma kowa dadi dan ko ba komai yapi kusa,
Komai na tafiya kaamar flash lokacci babu wuya a gurin Allah, level 4 first semester tayi musu sauqi sosai, dan courses sun ragu duk kamar karashe ne, ba kullum ma suke shiga school din ba,
Sukayi duk jarabawarsu suka kare, shagulgulan bikin su kubrah aketa faman shiri,
Sunyi kamu kawai sannan aka daura aure, kubra a nan kano zata zauna, zakiyya ma haka, khairi ce dai aka kaita katsina,
Zakiyya aka fara kaiwa tunda itace karama, sannan daga baya akayi asubanci aka kai khairi, sai kuma kubrah itama
Tun da suka dauki hanyar katsina kai khairi, zee taji gabanta nata faduwa, bata samu damar kiranshi ba har suka dawo, suna dawowa ma kubrah suka tapi kaiwa, zee tai jigun tana lissafa tun ranar kamu dayazo yace mata bejin dadi ya tapi be dawo ran daurin aure ba, ta kirashi sau daya wayarshi a kashe, bata samu lokaci ba suka kai zakiyya sai khairi yanxu gashi sun kai kubra,
Ta jawo wayarta ta danna lambobinshi, tayi ringing ta katse no answer ta kuma dialing tai ringing ta kusa katsewa sannan ya dauka, da wata murya da batasan faruq da ita ba yace zee, shima kamar da kyar ya fada, tana dai jin numfarfashi sama sama, sai kuma wayar ta katse, ta miqe a zabure
Innalillahi faruq mene ya sameka, sai tai realizing a gda tke ta yi kokarin calming kanta, sannan ta dauki gyalen dake kan gadon ta dau wata 500 ta fita da sauri dan nutsuwar ma taki zuwa, batasan sadda ta fara hawaye ba, ta saka gyale tana gogewa amma yaqi goguwa, dan tana gogewa wani na fitowa
Ta dau napep ta fadamishi inda zai kaita, ta zabga tagumi tana hawaye "ashe ni ina can ina shan shagalin biki shi yana nan wayasan ma mene ya sameshi" haka suka karasa tana ta bama kanta laipi, ta sallami mai napep and without thinking twice ta danna kai cikin gidan, bata tsaya ko ina ba sai bakin apartment dinshi, ta tura kofar
Silent taji dakin, falourn very neat komai a tsaftace, ta subale takalmanta harda er sassarfa ta wuce bedroom dinshi, yana kwance marabarshi da gaawa kadan ne, ta rike bakinta saboda kada kukan ya fito,
Ta karasa bakin gadon da sauri ta zauna tana kallanshi, idanunshi a lumshe suke ya budesu a hankali yana kallanta,
Ya kara haske akan wanda tasanshi, labbanshi sun bushe fuskarshi ta rame, idanunshi sunyi ciki kamar wanda yayi jinya ta watanni,
Muryarshi ce ta ja hankalinta
Ta dan kara tauri da karfi yace "taimakamin na zauna, batayi wani tunani ba ta riko kafadarshi kusan gabadayanshi a kirjinta yake, ta taimaka mishi ya zauna sannan itama ta zauna gefenshi, tari ne ya rikeshi, wanda har saida idonshi ya fidda ruwa sannan ya sauka
Itama taji nata idon ya kawo ruwa amma ta hadiye kukanta, kai kana kallan faruq zakasan yana jin jiki,
Da muryar tashi da ta sake rashin dadi yace "nerh nerh ya gida? Ya hiddima?" Ta gyada mishi kai kurun
Mene ya sameka? Kuma bazaka iya kirana ba, kaje asibiti?"
Ya lumshe ido tarin ya sake yi sannan yace "mura ce kawai sai ciwon kai, na kira wannan doctorn na momy yazo ya dubani har ya bani magunguna kuma masu aikina na kulawa dani ba wani abin damuwa"
A kufule ta dubeshi "har ni zaka cema babu wani abin damuwa"
Yayi shiru yana kallanta a kasalance bece komai ba, sannan yace ki jirani a falour zan shiga bandaki
Tace to, ya miqe dakyar kamar iska zata kadeshi ya fadi, jallabiya ce jikinshi, sai lokacin ta lura ramar ma har jikinshi ne,
Ganin yana tangadi kamar dan maye, yasa ta zuba mishi ido cikin tausayawa, kasa yayi luuuu
Saukinta a tsaye take ta tafi da sauri ta riko kugunshi
Dukansu sai suka zube a kasa, gyalen nata ma ya riga yayi nashi guri, numfashinshi takeji gaba dayaa fuskarta da kirjinta shine yayi saurin tashi a kanta sannan itama ta miqe, im... Im sorry
Ya fada tace "are u sure u can manage, ya lumshe ido i will
Sai wajen la'asar ta tafi tayi mishi girkin rana, first time daya ci girkin zee a nan ya banbance me ake nupi da girki me dadi, dukda beda lpia amma yaci abincin dayawa, sai ta gane rashin lpiar nashi harda loneliness ma, rashin samun wanda zeyi hira dashi, wanda ze tsaya ya kula dashi ya bashi abinci,
Saida tamishi girkin dare kapin ta tafi,
Ya tsaya jikin curtains din yana hangota har ta fita sannan ya dawo ya zauna,
Hawaye ya biyo kuncinshi "how would she feels in ta gane asalin abinda ke damun faruq dinta? Wanann shine Abu kwalli daya daya boye mata tun ba yanxu ba kuma har a yanxu bejin ze iya fada mata shi,
Devastated, heartbroken, heartache wadannan duk sunyi kadan su fassara azabar da zatajii a kokon ranta, radadin da zataji a fatar jikin, da kuma zafin da zataji cikin nama da kashi da bargon jikinta,
For how long zan iya keeping wannan secret din daga gareta?.......
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 35: Heartbreak


A week after
Komai na tapiya normal, saura sati daya hutunsu na first semester ya kare su koma second semester, wanann lokacin ma kamar kowanne lokacin suna ta6a karatun next semester danma babu wasu course project ne ma me dan wahalar kuma already sunyi proposing topics anyi approving sunma fara chapter 1, jikin faruq yayi sauki tari ne kawai har yanxu akwai saura da er rama amma bame yawa ba,




Zee takan ziyarci gidan zakiyya lokaci zuwa lokaci,
Next month zasuyi anniversary dan haka wannan karan zee ta shirya suprise ma faruq
A haka suka koma school suna ta kaaratunsu da project abinsu dan kusan course dinma duk sunyi covering, zeena ma an fara maganar bikinta da Imran, to nata course din dayake 5years ne yasa suka tsaya kan idan ta gama level 4 za'ai bikin se ta karasa final year a gidanshi


Ranar laraba ana gobe anniversary dinsu, Anty ta hana zee zuwa school da cewar ta taimaka mata da girkuna zatai baki, zee bata damu ba tace to tunda itama bason zuwa school din take ba sakamakon suprise din datake shiryawa goben,




Sun sha ayyuka da kusan duka zee ce karfin aikin, tayi abincikan masu dadi da kamshi,


Tana daki ta fito a wanka suna waya da faruq guraren karfe 4 taji sallamar su a falour, dama taji tsaiwar motocinsu,


Ta cigaba da shan soyayyarta, saida suka gama wayar ta nemi kayanta ta saka atampa ce brown da pink ta kashe daurinta na zahra buhari
Anty ce tayi kiranta ta amsa,
Mutun uku ne da yara biyu,


Wadanda ke facing dinta sanda ta fito ta gani alamu mata da miji ne manya, sai mace daya da bataga fuskarta ba sai gashin kanta kasancewar ta juya mata baya,
Saida tazo inda zata gansu duka ta gane ai minnatullahi ce, zee ta gaidasu duka
Anty tace
"wannan shine babban yayanmu wanda ke abuja" zee ta sake kallanshi babba ne kam dan akalla ze haura 40, se matarshi


Ta sake gaidasu sannan ta gabatar musu da abincin da ruwa ta koma daki,
Sai bayan isha'i suka tapi suka bar minnatullahi, a daren wata mata itama tazo gidan da wasu kayayyakinta
Jin anata amarya amarya yasa zee gane cewar bikin minnatullahi za'ayi
Aikuwa tana shiga daki ta tadda zakiyya nata kwala mata kira, ta dauka
"Ina kika shiga ne haka labari mai zafi na neman hucewa"
"Fadamin mene ne ya faru?" Ki bari gobe kizo gidana kawai musha labarin, zee tai jimm eh to gobene anniversary dinmu kuma akwai shirye shiryen danake but still i will squeeze tunda kece"...


Da en kudaden da suke hannunta ta shirya musu candle light dinner, taje tayi booking sannan ta kirashi tace mishi by 6 yazo tana jiranshi yace okay, sannan yace
"Nima level coordinator ne yake nemana yanxu xan shirya naje befre the time
Tace okay to seka dawo daga nan ta wuce gidan zakiyya,
Bayan sunyi settling take ce mata "kinsan wani babban business tycoon a kasar nan ummm" tai shiru tanaa kokarin tuno sunanshi yawwa "yusuf Abubakar As-siddique" zainab itama ta shiga nazari ta tabajin name din amma a inaa, zakiyya ta katse nazarin nata ta hanyar nuna mata hotonshi a wayarta kinganshi
"Yes yanxu ta tuna shine bakon uncle muzakkir zuwanta saudiyya na farko da Anty hawwer tace yayi satar hanya,
Ta gyada kai "yes yes na sanshi" yawwa
To in gaya miki shine wai zai auri minnatullahi" zee ta wara idanu wai dama beda aure? Zeyi 30 fa koma fiye, kuma ina ya ganta yace yaanaso kodaayake ai kina ganinta kinsan dole se gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login