Showing 60001 words to 63000 words out of 73133 words

Chapter 21 - AL'HUBB (the love) Complete book document .txt

09 Nov 2024

5420

yana mata uzuri da girki, duk yadda yakai ga son girkinta yakan haqura saboda mafi yawan lokuta bata tashi da wuri saboda kwana datake tana ibada, har ya fita, hakan yasa yapi missing breakfast da lunch amma takanyi kokarin hadamishi dinner


Bangaren mint kuwa ta koma school da aikinta halayan na nan dai saidai yanxu tana damuwa na yadda star din nata ko kallon inda take beyi, in kuwa tazo inda yake ma yakan tashi ya bata guri ko ya soma fake call
Satinsu faruq daya da zuwa aka kammala komi na aikin, akayi mishi zainab tana zaune ta rike waya a hannu gabanta na dukan tara tara,
Tafi awa uku a zaune a wajen in ta gaji ta tashi ta dan zagaya sannan ta sake dawowa ta zauna, a haka wayar datake ta jira ta shigo mata
Ko ringing daya batai ba tai picking da fadin "ya safiyya an ida? Anyi sa'a? How was it?"
Se taji shiru ya biyo baya tace "hello"
Ya safiyyan tayi sighing da fadin Alhamdulillh zee it was successful sun mashi lobectomy kuma zasu dorashi a chemotherapy afterward"
Zee ta fidda haki mai kara tana mai dafe kirjinta
sannan wasu siraran hawayen farinciki suka zubo mata "Alhamdulillh"


Asibitin sunso discharging faruq saboda expenses da kuma yadda jikinshi ke responding ma treatment yadda ya kamata domin ana samun progress yadda ya kamata, ga kuma uban kudaden da ake kashewa
Amma sai Assiddique yace "kar a sallameshi tukunna nafiso ya warke sumul yadda ze iya takawa yazo har gaban zainab da kafafunshi, kuma to avoid further complication a barshi ya huta da kyau"


Ya safiyya ta kira zee tana sanar da ita abin Alkhairin da Assiddique yayi na barin faruq din "nima kamar yasan abinda ke raina kenan, idan akace za'a dawo dashi a yanxu jikin ze iya rikicewa ko kuma a samu delay na progress, dan Allah ki sake mishi godiya zee ubangiji Allah ya faranta mishi ya biya mai buqatunshi yasa ya cika da kyau da imani" zee bakinta har kunne amsawa kawai take da Amin Amin




Zee taje ta samu Assiddique shi daya yana aiki da system ya dago ya dubeta, tana tsaye da katon murmushi kan fuskarta tama kasa tsaiwa dakyau se rausaya take, sai ya samu kanshi da murmusawar shima, sannan ya nuna mata seat din kusa dashi yace "zauna
Ta zauna tana mai kallonshi and for the first time taji abu cikin zuciyarta gameda shi, ta sunkui da kai tana murmushin ita daya, ya girgiza kai sannan yace tunda kinzo, ga aiki ki tayani, ya fada yana dora wasu papers kan cinyarta
Har lokacin murmushi take ta rike takardun sannan ta sauka daga kan kujerar ta zauna tana facing dinshi ta dubeshi amma sai taga ya mata kwarjini ta maida kanta kan takardun a hankali ta soma fadin
"Allah ya saka da Alkhairi, mungode ubangiji Allah ya biya maka bukatunka na Alkhairi ya baka zuri'a dayyaba"
Yace "Amin a takaice dukda yaji dadin addu'ar har ranshi, cikin ranshi yake fadin "inama zaki ji yadda nakeji gameda ke zainab"...
Tunaninshi ya katse sakamakon ganin mint dayayi kamar an jehota, ta tsugunna ta watsar da takardun kan ciyar zee sannan taja hannunta ta tura waje ta rufe kofa, ya tabe baki yana kallonta sai kuma ya cigaba da abinda yakeyi,


Zee ta sa dariya dan ita abinma dariya ya bata, a yadda take cikin farinciki batajin wani abu da mint zatai mata ze bata ranta


"Amma star idan aiki kake buqatar ayi maka ni yafi cancanta ka saka, ita girki ne kadae aikinta cikin gidan nan"
Yayi shiru be tankata ba,
Magana fa nakeyi, yace "eh ina sauraronki
Tayi kwafa
Amma dai kasan nafi karfin wulaqanci ko, ka dubeni da kyau wlh nafi karfin ka hadani da zee
Beson yi mata magana amma yanxu kam se yayi
"dama ai ke da zee babu hadi ma" ya fada yana mai murmusawa
Ita ma tai murmushi dan da alama dukkansu da yadda kowannensu ya fahimci maganar, a ranshi yace "zee tafiki komai minnatu, a yanxu ma ta fiki matsayi cikin raina"


Jikin faruq na sauki sosai dan yanxu yakanyi abubuwa da dama da kanshi batareda an taimaka mishi ba, dukka update daga gurin ya safiyya zee ke samunsu, duk sanda tace ya safiyyan ta bama faruq suyi magana se tace yana bacci ne har abin ya fara damunta
Dan indai da gaske jikin faruq yayi kyau kamar yadda suke fada amsa waya dai ai baze gagara ba...


Comments dinku na sakani nishadi... Alhub novel Group dina ina yinku
Bama kamar in naji team faruq da team Assiddique na ja'inja kuna dan lukutin birgeni a cigaba da gashi
#team faruq
#team Assiddique
Which team 're u?


💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Asslm alaikum inaso na danyi clarifying abubuwa kamin mu cigaba saboda wasu na cewa basu fahimta ba se nake ganin bayani nada dadi
1. Ana cewa Assiddique baya magana lokacin data fara bashi labari amma bayan ta kammala labari sae ya cigaba da magana
Ai idan me karatu ze tuna abinda na fada a page din data kare bashi labari, ita kanta zee dayayi maganar seda tai mamaki tace yayana kaji kana magana shima kanshi murmushi yayi sannan ya sunkuya ya miqa sujudusshukur
Ma'ana yana godewa Allah da bakinshi ya bude yayi magana
2. Maganar mint da a ke cewa an saketa kuma ya akayi ta dawo, ai kafin zee ta soma bawa Assiddique labari yallabai mahaifinshi ya kira babanta har sukayi magana yace baya kasar amma in ya dawo ze dawo da mint din
So shine dalilin zuwan Anty siyama gidan tunda Anty siyama ai a kano take amma dalilin dawowar mint tazo abujan har tayi ma zee kashedi ta rabu da mijin mint


Episode 40: Married




Watanni biyu cur suka dauka a UK kuma Alhamdulillh jiki yayi sauki sosae, dayake ta hanyar Assiddique ne sai aka hada shi da wani doctor a nan nigeria daze cigaba da kula da lafiyarshi,


Ta zauna gaban mirror din a gajiye, gabadaya ma ta rasa gane wanne irin kwalliya zatai ma faruq din tun sanda ya safiyya ta sanar mata da dawowarsu a yau din takejin feelings iri iri,
Ta dubi kan gadonta da tai mishi kaca kaca da kaya ta rasa wacce irin sutura zata saka ji take komi ma beyi ba, ta kalli fuskarta tana tunanin wanne irin makeup zatai da ze faranta ran faruq din nata
Tapi awa daya tana wadannan sake sake daga baya dataga lokaci na sake kurewa sai ta sami wata black abaya mai adon flower red and white, ta sami black veil tayi rolling ta kalli face dinta babu kwalliya kamar mafi yawan lokuta ta saka lipgloss sannan ta dauki purse dinta,
Lambar Assiddique ta shiga nema sakamakon fadamata da yayi da kanshi ze kaita, dan zeso yaga farincikin daze sauka kan fuskarta idan taga faruq, bazeso missing ba
"Ya dauki wayar da sallama, bai bari tace komai ba yace "pls kiyi haquri wasu en ayyuka sun tsareni nayi ma driver magana ze kaiki, tace to yayana
Ta sauka batareda tayima mint sallama ba dan gabadaya damuwanta be wuce taje taga faruq ba, hankalinta na gareshi, saida ta fito farfajiyar gidan taga garin yayi duhu hadari ya hadu sosae, tai murmushi tana jin dadin iskar dake kadawa tana kada kayanta da flowers din gurin a hankali
Zee ta dubi agogonta tabbas ta makara tace da drivern dake tuki "dan Allah kayi sauri nasan sun sauka yanxu" Koda suka isa ta fito da hanzari har tana gurde kafa, driver shima ya fito ya soma vedio kamar yadda ubangidan nashi ya sakashi dan a cewarshi bazeyi missing kyakkyawar fuskarshi zee ba in tana murmushi


Daga nesa ta hangeshi cikin katuwar farfajiyar filin jirgin, dukda bayanshi take ganni amma tasan shi dinne, yau ya saka wasu sutura da ba farare ba, iskar gurin take kada gashin kanshi fuskarshi na fitar da annuri, juyowa yayi kadan hakan ya bata damar ganin gefen fuskarshi yayinda murmushi mai taushi ke fita a fuskarshi, bayanshi ya safiyya ke tahowa gurinshi ta gabanshi kuma wasu mutanene da ta tabbatar su dady ne, itama tana tunkarar inda yake, cak zainab taji kafafunta sun kasa karasawa kamar an saka kusa an kafeta a gurin,Take wani abu ya tokare mata makogwaro, sakamakon furucin ya safiyya dataji tana fadin
"Hamra dama kin haihu shine dady be sanar mana ba, wow faruq ka zama dady yanxu, Allah yayi kaine zaka fara bawa dady jika"
Zee ta hadiyi yawu mai daci, akan idanunta faruq yasa hannu ya amshi yaron dake hannun daya daga cikin kannen nashi biyu wanda bata gane wacce Aisha ba wacce hamra
Jaririne jawur dashi, dady ya karasa ya rungumesu tare duka su biyun, ya dan bubbuga bayanshi yace "welcome back my son"


Ruwan saman daya soma sauka ne yasa kowa na wajen ya fara neman mafaka harda su faruq ma suka bude umbrella, zee ta bisu da kallo batareda tayi yunkurin hana zubar ruwan a jikin ta ba.. tana kara gasgata murmushin dake kan fuskar faruq da yadda ya kama hannun hamra ya hada da nashi,
Denajin dukan ruwan tai a jikinta hakan yasa ta gane umbrella ce aka saka mata ta daga ido ta kalleshi a raunane, sai kuma taji kamar an sassauta rikon da akaiwa kafafunta ne, ta kuwa kwasa da gudu batareda ta damu da yadda ruwan yayi mata sharkaf ba, bata tsaya ko ina ba sai a gaban faruq wanda ke tsaye cikin wani glass place hakanan inda ruwa baze tabasu ba, haki take fiddawa tana ajiye tagwayen ajiyar zuciya,, ya safiyya ce tayi saurin karasowa ta lulluba ma zee wani showel da aka raba musu cikin jirgi, faruq ya saci kallon dady yaga suna magana da doctor din dasukazo tare sannan ya kalli hamrah yaga tana zaune comfortably itada Aisha suna hira, ya miqawa ya safiyya babyn sannan yaja hannun zee da sauri
Tana ta kokarin fizge hannunta amma bata cimma nasara ba seda suka sha kwana ta fizge tana huci tana kallonshi
Sai kuma hawaye masu dumi suka kwaranyo kan kuncinta masu sanyi, taja numfashi tana mai lumshe ido,
Ita ce tai breaking silence din ta hanyar fadin "Faruq dagaske ne kayi aure harda d'a?"
Ya lumshe ido ya bude sannan yace "gobe by 4 ki sameni a garden palace we'll talk" ya juya ze tapi sai kuma ya dawo yace ki tayani yima Assiddique godiya ya safiyya ta fadamin komi" yayi mata brief smile sannan ya fice ya tapi, ta bishi da kallo kamin ta zube kan guiwowinta tasa hannunta ta rufe fuskarta,
Kamshin turarukanshi taji yasa ta dago da fuskarta ta kalleshi yace tashi muje, ta tashi amma sai taji jiri ya debeta tai saurin dafe bango, ya akayi? Ya tambyeta ranshi be mishi dadi, ta daga ido ta kalleshi sannan ta murmusa cikin karfin hali tace bakomai yaya_na ya jinjina kai


Kan hanyarsu ta komawa dukansu sunyi shiru jigun jigun, is it true? Taji ya jeho mata tambayar unexpectedly, kawae sai ta saka mishi kuka ya furzar da iska waje, saeda tayi mai isarta dan kanta ta dena, motar ta tsaya alamun sun iso, yace "goge hawayenki banasonsu" ta daga jemammun idanunta t kalleshi taji wasu ruwan hawayen na taruwa
Ta bude kofar ta fita kawai, ya bita da kallo "ko kadan bayason damuwarta, dayasan abinda faruq ze mata kenan dabai soma barinta taje inda yake ba, yakasa gane indai a kanta ne be iya controlling kanshi, duk yawan ayyukanshi amma ya tsallake ya taho gareta dukda yace mata baze samu damar zuwan ba amma ya gaza nutsuwa..."


Zainab ta kira Anty hawwer muryarta very low alamun sun bayyana gabadaya she's depressed,
"Mene ya faru zee ya naji voice dinki haka"
Zainab ta soma mata bayani tanayi tana shessheqa
Shiru ya biyo baya, dan iskancin faruq ya matuqar bata haushi, daga alama kuma cikin abinda ta fada mata ta gane Assiddique na son zee din, tayi murmushin takaici
"Yanxu me kike ganin zakiyi?" Zee tace "bansani ba Anty shiyasa na kiraki
"Kin sani zainab, wallahi kinsan mene ya dace kiyi, wannan karan bazan cemiki komai ba na barki ki yanke wa kanki hukunci, saidai ki sani komene zakiyi kiyi abinda ze samar miki da kwanciyar hankali zainab"


Kashegari Ta shirya cikin sanyin jiki ta fita ta samu driver babu abinda yake dan haka tace ya kaita anguwa, bataso assiddique yasani shiyasa bata sanar mai ba,
Karfe 4 da mintina 10 ta isa palace din, can gefe ta hangeshi zaune kan wani dan dutse da aka maidashi kamar bench yana zagaye cikin kananun duwatsu da bishiyu
Ta karasa tana mai yi mishi sallama, kukan tsuntsaye na tashi yayi mata murmushi amma sai ta samu kanta da jin haushin murmushin nashi
Ta samu guri ta zauna yadda zata fuskanceshi, nana zainab kin wuni lafiya, ta gyada mishi kai kawae
Ya lumshe idanu ya bude, ya dubi en tsutsayen dake shawagi a gurin yace "its been a while"
Nan ma tai mishi shiru
Duka sukayi shiru tsayin mintuna kafin daga baya yace "ina fatan bawai fishi kike dani ba" ta girgiza kai kawai,
Then talk mana zainab, talk, tell me how much you've missed me
Sai ta samu kanta da zubda kwalla
"So kake na fada maka nayi kewarka dan ka sakejin dadin kuntatawa zuciyata,
Dududu watanni nawa ne?, Watanni goma sha takwas ne, shekara daya da rabi amma har kayi aure har ka rufe babin zainab a rayuwarka, harda yaro"
Ta lumshe idanunta yayinda hawaye suka sauka kan lashes dinta
"Pls don't cry zainab i never deserved your tears"
Ta miqe a kufule, idan baka da abin fada ni inada abinyi, yayi saurin shan gabanta
Nike da abubuwan fada zainab ki bani kadan daga lokacinki dan Allah, ta koma ta zauna tana mai hadiyar yawu lokaci lokaci


Ko kadan nasan ban kyautata miki ba zainab, hakane nayi aure na auri hamra bayan komawata europe, ki fahimce ni dan Allah nayi hakanne a bisa umarnin dady
Ta katse shi da fadin na fahimci wannan sai kuma wanne?
"Kema kinsan ke nakeso dake nake son karashe rayuwata amma a bisa kaddara da kuma dalilin rabo yasa alakar mu da hamrah ta kai haka, zainab ina nan a kan baka ta har yanxu ina sonki nasan kema kina sona ko?....."


Uhmmm nayi shiru bakina akwai goro #Aysha b.


Ina mai farincikin sanar da ku ni marubuciyarku Ayshab, nayi attending fashion school ta @malaabis_by_mymz inda nai syllabus dina a yanxu haka kuma nake dinki, mafi yawan wadanda ke garin kano nasan kunsan dinkunan malaabis base na tofa ba


kira na gareku masoyana musamman mutanen garin kano, ku kawo dinku nan ku, be it ankara, or material that will look like ready to wear i assured you wont regret in shaa Allah, ur fabric re in the right place n safe.. Patronize ur writer show love


And dont forget follow my IG page @Ayshabnaseer @Aysha_bee_couture
💍 *AL_HUBB* 💍


The love 💘


By Aysha b. Naseer
Episode 41: Breakup


Kema kinsan ke nakeso dake nake son karashe rayuwata amma a bisa kaddara da kuma dalilin rabo yasa alakar mu da hamrah ta kai haka, zainab ina nan a kan baka ta har yanxu ina sonki nasan kema kina sona ko?....."
Ta zuba mishi idanunta batareda ta ce mishi komai ba, ganin da tai baida niyyar fadin komai ya sakashi fadin
"Yanxu me kikai deciding" ta lumshe idanu taja ajiyar zuciya, batareda tasan me zata ce mishi ba gabadaya kanta ya kulle, sai kuma yace "zainab let's end everything"
Kwarewa tai jin kalaman nashi, sai kuma ta dan saita kanta dukda speed na heart beat dinta be ragu ba sema karuwa dayayi da tsananin gudu, yayi shiru yana kallonta, da dumbin tausayinta cikin ranshi, kiyi haquri zainab amma ina ganin hakan shi ne mafita, ya miqe itakam tana nan, "anya wannan faruq dina ne?"
ma'assalam taji ya fada tai saurin tashi tasha gabanshi, anya kaine faruq din dana sani, ina duka alqawarukan mu, ina batun soyayyarmu, ina kuma batun auren mu, duka kayi watsi da komai"
Ya hadiyi yawu sannan a hankali ya zagayeta ya tafi, ta zube kan guiwarta "ya ilahi what's all this" Ko zatai expecting komai daga faruq batai expecting kalmar rabuwa ba,
A nashi bangaren ya tabbata suyar da zuciyarshi ke mishi ya fi wanda nata keyi mata, "soyayyar dayake mata ce yasa baze jure kallanta cikin bakinciki haka ba, ko a baya ta sadaukar da abubuwa sosai saboda shi, tayi mishi halacci, bata taba cin amanarshi ba, ta dauki duka hope dinta ta saka a kanshi, to mene amfaninshi indai zaina saka ta kuka, mene amfanin soyayyar da bazata sama mata farinciki ba, bayaga wannan ma dalili na biyu shi ne, shi yanxu baida abubuwan da zasu sama mata farinciki, shi be kammala makaranta ba, baida certificate, bashi da aikinyi ta ina ze fara aurenta ya kula da ita da hamrah, baze iya sama mata jin dadin daya kudira ba, he lacks and na uku kuma, danginshi basu sonta tayaya ze so kanshi yaa jefata inda yasan ba dadin zaman zataji ba saidai tayi ta haquri ana cutarta
Wadannan dalilai dama wasu suka sakashi haqura da ita a ranshi bawae dan baya sonta ba, tun komawarshi babu abinda yake se fafutukar yadda ze kula da ita yadda ze dawo ya aureta amma dady ya bijiro mishi da zancen hamrah, babu yadda zeyi in yanason auren zee kuma idan yanaso dady yayi supporting dinshi financially ya bashi abinyi sedai ya aureta, sanda akai auren kuma yaga batada wata matsala, zaman nasu sai ya zama babu hayaniya saboda tana sonshi sai take avoiding duk wani abu da tasan bayaso..


Zainab tana komawa gida ta sulale kan gado a take ta soma jin zazzabi da ciwon kai, ta jaawo blanket ta lullube jikinta sai can dare bayan isha'i ya kwankwasa kofar dakinta, ta bude idanunta da sukai mata nauyi bibbiyu take gani dukda a kwance take amma jiri takeji, ta maida idanun ta rufe, ganin da yayi babu alamar akwae mutun cikin dakin ya sakashi bude kofar ya shiga, duhu ne cikin dakin dan haka ya nemi switch ya kunna fitila, haske ya gauraye can ya hangota ta dunkule guri guda cikin blanket, yayi saurin karasawa gareta
"Zainab mene ya sameki?" Baki da lafiya ne?
Ya tambyeta
Bata iya amsashi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login