Showing 30001 words to 33000 words out of 139707 words
yabi ya isheta ji take kamar ta nitse 'kasa....
Junaid yana farkawa yaga a halinda suke a razane ya mi'ke tsaye yana maida numfashi, itama Ayush tashi tayi ta tsaya a gabansa,
Wani irin hankad'a yayi mata ya tureta baya sauran kad'an ta fad'i 'kasi amma ta bugu da jikin gini
Yana fad'in "whattt! Are you crazy, ni zaki runguma? Ni zaki bawa kunya a cikin mutane? Banza 'kazama fool like you..."
Yana magana yana nuna jikinta da hannunsa, sannan ya kuma cewa
"As from today kika 'kara gwada mun wannan iskanci saina murd'e miki wuya,
Are you going to rap me? Eh answer me nace kinaso kiyi mun fyade ne? Karo na biyu kenam Ina samunki a jikina because you are a useless, mtsswws shameful girl...."
Yana gamawa sai fuuu yayi hanyar fita daga cikin room d'in da sauri nurses dake wajen suka bashi guri ya fice..
Yana fita kuwa nurses suka kwashe da dariya
Suna fad'in "woo gaskiya kinji kunya har ki kawowa namiji hari kin ganshi gantsalelen saurayi....." Basu 'karisa ba Dr. Hasheem ya daka musu tsawa sukayi waje suna gutsiri tsome
Inajin d'aya daga ciki tana cewa "muma munyi kwad'ayinsa mun bari, ina ma ace nice na rungume shi haka wayyo dad'i amma sai dai Ina gudun naushi......." Suka 'kara tintsirewa da dariya.......!
Bayan fitar su kuwa
Ayush fashewa tayi da matsanancin kuka ta dur'kusa gwiwowinta a 'kasi ta kifa kanta 'kasan tiles tana sheshshe'ka kukanta mai cin rai......
Girgiza Kai Dr. Hasheem yayi Sam baiji dad'in abunda Junaid yayiwa yarinyar nan ba
Shi kansa Dr. Yasan lalurace tasa kuma banda iskanci irinta Junaid shine fa yake rungume da ita..
Mommy itama 'kololuwar ba'kin cikine yasa ta kasa yin magana
Kamar zata fashe da kuka itama...............
*๐ค SDEENDTM DATA SERVICES๐ค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โฆ300. 1GB = โฆ350
2GB = โฆ600. 2GB = โฆ700
3GB = โฆ900. 3GB = โฆ1000
4GB = โฆ1200. 4GB = โฆ1300
5GB = โฆ1500. 5GB = โฆ1600
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โฆ350. 500Mb โฆ250
2GB = โฆ700. 1GB โฆ500
3GB = โฆ1050. 2GB โฆ1000
4GB = โฆ1400. 3GB โฆ1500
5GB = โฆ1750. 4GB โฆ2000
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ
*๐ช08066268951*
*ASMEETAH* *CE* โ๏ธโ๏ธโ๏ธ
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
*FREE* *BOOK*
๐
*MATAR* *DAMUSA* ๐
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โ๏ธโ๏ธ
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦalaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
๐ซ๐ซ *{{N W A}}* ๐ซ๐ซ
ุจูุณูููููููููููููููููููููููู
ู ุงููููู ุงูุฑููุญูู
ููู ุงูุฑููุญูููู
*BOOK* *ONE*
*PAGE* โก๏ธ 35 & 36 โฌ
๏ธ
A ranar a asibiti suka kwana mommy da Ayush,
Dakyer Mommy ta iya rarrashin Ayush akan wulakancin da Junaid yayi mata, zuciyarta ya sosu sosai sai dai duk fad'an dayafi karfinka saika mayar shi wasa!!
Inda sabo ai an saba indai akan halin Junaid ne.
Zuwa washe gari da safe Ayush ta mance da Abunda Junaid yayi mata, zuciyarta wasar yake, Ayush bata saka abu aranta sannan da wuya tayi fushi akan abu, duk abunda Junaid ke mata ko sau d'aya bata ta6a tsanarsa ba saima 'Kara sonshi da take yi!
Tin ranar da Baba tsoho ya sanar mata shine Junaid d'in da Umanta take magana akai
Saita fara jin tausayinsa da kuma sonsa domin tabbas an cutar da rayuwarsa ...
Shirye-shiryen komawa gida suke, sun kuma shirya tsaff, Junaid ne ya shugo hannunsa ri'ke da key d'in motor
Fuskar kuwa a murtu'ke ba alamar annuri ga idon yayi wani irin jaa, hatta fuskarsa sai data canza yayi kamar wanda aka watsa masa ruwan zafi duk ya yi wani iri kamar kamar dai gashi nan dai an canza masa kamanni, ga wani birtsi-birtsi akan fuskar kamar tabon duka, gaskiya yadaiyi muni a wannan karan..
Sai huci yake shi kad'ai
Mommy na ganinsa a haka tayo kansa tana fad'in "My son lafiya kuwa? Meya faru da Kai? Dambe kukayi ne?......." Bata 'karisa maganar ba ya katseta da cewa "please mom nazo d'aukanki ne bawai sauraron Questions d'inki ba" yana kaiwa haka ya kawar da kansa gefe fuska a cur6une.
"Innalillahi Junaid meya sameka akan wuyan ka? Kamar yagunin kare, wallahi faratun kare nee... Tana shirin kuka tana fad'in "dan Allah my son talk to me meya faru dakaii???"
Juyowa yayi yana kallon Mom kamar zaiyi kuka yace "ba kare bane, Damusa ne!"
Cikin firgici Mom tace "Damusa kuma aina? Aina kaga Damusar? Jiyan ka sake mafarkin Damusan ne?" Ta karisa maganar tana kallon fuskar sa wanda hawaye ke tsiyaya daga cikin idon jarumin sojaa!
"Mom! Ba mafarki nayi ba, a zahiri yazo mun, ya kawo mun hari, amma na samu na ku6uce masa karki damu.."
Fashewa Mom tayi da kuka ta kifar da kanta akan kirjin Junaid tana fad'in "Allah ka kawo mana d'auki a cikin al'amuran mu, ka dubi yarona ka kawo masa agaji ya Allah ka warkar dashi daga wannan cutar, ka kawo karshen azzaluman da suke azabtar mun da shi!.." Kuka ne yaci ranta sosai har ta gagara maganar.
Shi kuwa bubbugan bayanta yake a hankali yana rarrashin ta cikin kulawa....
Duk halin da suke ciki kuwa Ayush na tsaye ta gefe guda tana sauraronsu, ta fahimci suna cikin tashin hankali itama sai data zubda hawaye ganin halin da Mommy take ciki da kuma Junaid..
A ranta take fad'in "kuyi hakuri nasan duk wannan halin da kuke ciki iyayena ne suka jefaku ciki, Damusar daya fitowa Junaid kuma tayi tunanin shine ya fitowa mahaifiyarta tana gudu tana ambaton Damusa! Damusa!! Har Junaid ya bugeta da mota ta rasa rayuwarta..
A hankali abubuwa suna dawo mata kwakwkwalwa,
"Tabbass wannan Damusar da ya sha jinin Junaid dashi mahaifina yake amfani waran cutar da Junaid, shine yake zuwa wa Junaid a mafarki har kuma ya fara fito masa a zahiri.."
Fashewa Ayush tayi da matsanancin kuka, ita kad'ai tasan rad'ad'in da takeji a zuciyarta
Bataso ace mahaifita ya zamto a haka ba, tayi tirr da halin mahaifinta!!
Hannu ta d'ora a kaa tayi wani irin ihu na gaske
Tana fad'in "wayyoo Allah na, na mutu na lalace,
Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un," kuka take sosai
Wai abun ba'kin ciki ta hanyar fasi'kanci aka sameta
Abun yanayi mata ciwo a rai...
Mommy ce ta nufo waranta tana fad'in "lafiya kuwa Ayush meya sameki"
Ita kuwa cewa take "mutuwa zanyi na huta, rayuwata batada wani amfani,
Um Um Um Umaaaa naah wayyo nagaji da ganin takaicin nan, bazan iya cika miki alkawarinki ba, I can't, I can't wallahi.....
Umanta ne ta fara yimata gizo a cikin fararen kaya da hawaye kwance saman fuskarta,
Hannu Ayush take mi'ka mata alamar tazo ta tafi da ita.......
Muryarta ne ya dishe ta gagara yin kukan ma!
Sai idonta daya fara kakkafewa, yawu ne yake gangarowa ta gefen bakinta
Daga nan aka nemi hankalin Ayush aka rasa ta sumaa!!
Shima Junaid ne yayo kanta yana bubbugan gefen fuskarta amma ba numfashi ya tsaya cakk sai ido a bud'e ya 'kafe....
Lokaci guda Junaid ya rikice yana fad'in "mo mo momm moomm Doctor zata mutu fah," ya nufi waje da gudu yana kiran " Doc Doctor! Doctor!! Doctor!!! Gaba daya ya fita hayyacinsa.....
*****
Abunda ya faru da Junaid kuwa a daren jiya
Shi kad'ai ya kwana a gida sai kuma mai gadi dake d'akinsa wanda yake bakin gate...
1:00am yana cikin baccinsa yaji wani irin gurnani a cikin baccin a hankali yake bud'e idon a tunaninsa mafarki yake kamar Wanda ya Saba, ashe abun ba haka yake ba a zahiri aka fito masa wannan karan!
Idonsa ya bud'e sosai still bai daina jin gurnanin ba
Yakai hannu ya kunna ligh d'in d'akin
Haske ne ya bayyana idonsa ne ya sau'ka akan wani ba'kin Damusa 'katoto dashi ga idonsa jawurrr daga gani kasan na tsafine,
Junaid ja da baya yayi ya manne a jikin karfen gadon,
Tsorone ya bayyana akan fuskarsa gaba daya ya mance da Addu'o'in da akace yanayi, jikinsa 6ari ya soma yi!
Shi kuwa Damusan kansa yake yowa da wasu fikokinsa a waje
Wani irin sufa yakai wa Junaid
Shima Junaid yun'kurawa yayi da 'karfin gaske ya cafki wuyan Damusa.....
Ido cikin ido suke kallon juna idon Junaid ne ya Fara komawa na Damusa sai dai shi nashi Blue eyes ne,
Wani irin yakushi Damusan nan yakaiwa Junaid a wuya, jin zafin yakushin ne yasa Junaid yayi wulli da Damusar jikin mirrow saida madubin ya dagargaje,
Cikin karfin hali Junaid yayo kan Damusan zai kai masa naushi rashin sa'a yasa Damusar zamewa Junaid kuwa ya doku a 'kasi, hakan ya bawa Damusar daman hawowa kan Junaid ta baya yakai bakinsa saitin wuyansa zai cije shi,,,
Wani irin juyi Junaid yayi ya cakawa Damusan glass d'in jikin mirror a wuya....
Wani irin Ihu Damusar yayi ya 6ace 6aatt!
Jinin Damusan daya zube a tiles shima kamar Wanda aka goge waran ba alamun jini...
Damusar ya tsani ganin jini a jikinsa domin yana had'e da jinin Junaid ne hakan zai bada matsala sosai daga 6angaren su,
Hakan yasa Damusar yayi saurin 6acewa....
Junaid kuwa kansa ne daya bugu a 'kasi ne ya fara ciwo sosai ga jinin da Damusar ya yakushe shi a wuya sai zuba yake ga rad'ad'i ga ciwon jiki, gaba d'aya jikinsa ne yahau yin ciwo
Abu kamar a mafarki!!
Sai a yanzu Junaid yake furta
"Innalillahi wa inna'ilahi raju'un, wannan wani irin masifa ce.."
Dakyar ya tashi ya shige toilet yayi wanka ya fito ya shirya ya nufi falo d'akin medicine ya nufa yaje yayi treat d'in ciwon dayaji a wuya,,,
Daga lokacin bai samu yin bacci ba har asuba
Yayi sallah.....
Ya wayi gari da mungun 6acin rai, bayason kula kowa, da haka har yaje hospital d'in, yana tsananin mamakin kansa "how comes Zan iya ya'kar Tiger?" Abunda yake yawo masa a rai kenam.........
Sorry my fans kuyi manage da wannan banida time ne ๐๐๐๐
*๐ค SDEENDTM DATA SERVICES๐ค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โฆ300. 1GB = โฆ350
2GB = โฆ600. 2GB = โฆ700
3GB = โฆ900. 3GB = โฆ1000
4GB = โฆ1200. 4GB = โฆ1300
5GB = โฆ1500. 5GB = โฆ1600
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โฆ350. 500Mb โฆ250
2GB = โฆ700. 1GB โฆ500
3GB = โฆ1050. 2GB โฆ1000
4GB = โฆ1400. 3GB โฆ1500
5GB = โฆ1750. 4GB โฆ2000
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ
*๐ช08066268951*
*ASMEETAH* *CE* โ๏ธโ๏ธโ๏ธ
*FREE* *BOOK*
๐
*MATAR* *DAMUSA* ๐
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โ๏ธโ๏ธ
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦalaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
๐ซ๐ซ *{{N W A}}* ๐ซ๐ซ
ุจูุณูููููููููููููููููููููููู
ู ุงููููู ุงูุฑููุญูู
ููู ุงูุฑููุญูููู
*BOOK* *ONE*
*PAGE* 37 & 38
Ganin Junaid a wani irin yanayi yasa Dr. Hasheem tasowa da sauri yana fad'in "Kai lafiya kuwa Junaid meya faru haka"
Karasowa wajen Dr. yayi yana huci yace "She's die, Please go and check her"
Shima kansa Dr. ya razana yace "Who? Kodai jikin mommy ne?"
"Noo not my mom, tana nan kwance zata mutu"
A cewar Junaid gaba d'aya baya cikin hayyacinsa.
Dr. gaba d'aya ya kasa motsawa sai cewa yake "ba mom ba to wace ce?"...
Cikin zafin rai Junaid ya finciko hannun Dr. suka nufi room d'in da Ayush take a kwance.....
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un meya sameta....?"
Dr. ne yake fad'in haka tareda sa hannu zai d'auketa....
Junaid yayi saurin dakatar da shi yana fad'in "Leave her.."
Yasa hannu ya d'auketa ya d'orata akan gadon da aka kwantar da mom, Dr. murmusawa yayi a ransa yake fad'in "Toh me hakan yake nufi? Ya hanani d'aukarta sai shi! Allah yasa dai ba wai sonta yake ba, na tabbata ba abunda zai hana zuciyata bugawa"