Showing 75001 words to 78000 words out of 139707 words

Chapter 26 - Matar Damisa book Complete by Asmita .txt

Asmeetah   

16 Dec 2024

9957

larabawan makkah ne, suka baro makka zuwa nan nigeria garin Abuja,
Maimoon fara ce tas itama ga gashi tana da dirin jiki domin tafi Ayush dirin jiki gaskiya
sai dai bayan nan bata fi Ayush da komai ba,

Ayush da Maimoon farare ne sai dai launin fata ta banbanta,
ita Ayush fara ce tasss, Maimoon kuma farin ta launin jaa ne.
gashin Ayush mai murɗi-murɗi ne ga laushi gaban goshinta kuwa gashi ne a kwance har yaso ya haɗe da girar ta, yanada tsayi sosai zuwa tudun bayanta,
ita kuma Maimoon gashin ta tsantsi ne dashi a ware gashin yake itama ya rufe gadon bayan ta,
Ayush ta fi Maimoon Eyes da ƙaramin baki,
Maimoon kuma tafi Ayush tsayin hanci duk da itama Ayush tana da tsayin hanci,
Amma kuma Ayush tafi Maimoon tsayi nesa ba kusa ba domin ita fa Ayush da kaɗan Junaid ya ɗarata tsayi..

kowa da kalar suffar ƙasar daya ɗauko,
zuriyar mahaifin Ayush ƴan fulanin indiyawa ne dake ƙasar Oromia daganan kakanta ya samu mulkin ƙasar California....


Ita kuma Maimoon balarabiya ce ciki da waje,
duk ɗin su ba laifi ta ɓangaren kyau...


Mahaifin Maimoon babban abokin mahaifin Doctor Hasheem ne marigayi alhaji Bukar,
tin suna ƙananan yara suka fara soyayya da Dr Hasheem da kuma Maimoon, har Allah yasa suka mallaki hankalin kansu yanzu kuma Docter Hasheem yake so ya juyar da soyayyarsa kan Ayush haɗuwar sama...


*DALILIN YIN LESBIAN TSAKANIN MAIMOON DA LAILA...*


Akwai wata rana Maimoon da Laila suna tafe kan hanyar su ta zuwa hospital zasu je gurin Doctor Hasheem to daman Maimoon ita take draving motar ta suna tafe suna hira, kwatsam sai suka bugi wata tsohuwar mata da baƙaƙen kaya a jikin ta,
da gudu suka fito daga cikin motar suna faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, ta mutu ko?"
ita ko Laila fashe wa tayi da kuka dake lokacin yarinya ce bazata wuce 15years ba, ita kuma Maimoon ta kai 18years suna ƙoƙarin ɗaga tsohuwar nan suka ji ta tintsire da dariya ta ɗago tana musu wani irin kallo, lokaci guda kuwa ta rungumo su jikinta kowanne sai data zura harshenta a cikin bakin su, cikin lokaci ƙanƙani kuwa ta ɓace ɓatt, tin daga lokacin ta juyar musu da kwakwalwa wanda idan basu kusanci juna ba basa jin daɗi duniyar zafi take musu,
to tin daga wannan lokacin suke wannan harkar ba tare da son ransu ba, sai bayan sun kammala suke dana sanin aikatawa kuma suke faɗa a junan su, tsawon shekara uku yanzu kenam....


idan har ba tsafi bane ai Maimoon tafi ƙarfin zuciyar ta saboda kullum a cikin karatun kur'ani take, a yanzu ta kammala N.C.E, Laila kuma ta kammala S.S.E, shaƙuwar dake tsakanin su ne yasa Laila take ƙiran Maimoon da Besty ita kuma Maimoon ta ƙirata da ƙawas amma ai Maimoon ta girmi Laila sosai....



*MASHA ALLAH*


Rashin comments ɗinku ne yasa zamu tsaya anam.


ku gyara dan Allah🙏🙏




*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500


*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500


*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*


*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*


typing📲


🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)


*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)




*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________


https://www.facebook.com/103637491942644/


💫💫 *{{N W A}}* 💫💫




بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم


*BOOK ONE*
🅿️ ------->71 & 72 <-------


✈️✈️✈️ ƘASAR CALIFORNIA...


Sarki Raamud ne zaune akan kujerarsa ta mulki ya ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya yanata huci,
ga Mahaifiyar Ayush kuwa durƙushe a gabansa ya sata tayi kneeldown, tana kuka ga gumin dake yanko mata daga sumar kanta, tana faɗin "Shugaba kayi hakuri ka bar hukunta ni haka, nifa temako nayi...." kafin ta ƙarisa maganar ya daka mata wani irin gigitaccen tsawa "your very stupid, ni zaki munafurta? kin sace mun zoben Dish kin kaiwa Ɓingel kuna ganin shine hanyar da zaku bi ku magance matsalar ku, kin toshe mun kafar da zanga Ɓingel da kuma Junaidu! toh amma ina so ku sani cewa kafin ku aiwatar da aikin ku na rigada na tura Aljanin ƙudus yaje ya murɗe mun wuyan Junaidd...." Hahahaha ya kwashe da wani irin mahaukaciyar dariya..


tsabar tsoro da firgita sai da Bara'at ta faɗi zaune daga kneeldown ta dafe ƙirjin ta tana faɗin "shugaba ka kashe Junaid? Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!" ta fashe da kuka "meyasa ka ɗauki wannan tsatstsauran hukunci? shikenam nima kuwa zaka rasani yanzu domin rayuwata batada wani amfani tinda har na gaza ceton Junaid."

Da gudu ta tashi ta miƙi hanyar fita daga cikin falon masarautar kai tsaye ɗakinta ta nufa tana shiga ta danna key, zuwa tayi ta ɗauko poisen zata sha,
wani irin bugu akayi wa ɗaki ya buɗu, cafko hannun ta yayi sannan ya yi wurgi da ƙwalbar gubar ya zabga mata mari ya hankaɗata saman gado yana faɗin " ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, idan kika kashe kanki kin mutu kafura..."
katse shi tayi da cewa "wanda yayi kisan kai kuma fa?? ya kamata kaji tsoron Allah Abul Mayush, ka sani fa wata rana zaka mutu, bawai kai kaɗai za'a bari a doron duniya ba,
Ka kashe Junaid ita kuma fa Ayush shin zata rayu ne? bakayi tunanin haka ba, ka yanke hukunci saboda ita to ka sani ko da ran Junaid ko ba ran Junaid Ayush zata mutu ne,
an zo wajen da bazata iya rayuwa ba tare da Junaid ba....."
ta tinshire da dariya tana tafa hannayen ta biyu ta kuma cewa "shin baka san Junaid da Ayush jininsu ɗaya ba ne?
to ka ɓarar yanda ka kashe Junaid haka Ɓingel ɗinka ma mutuwa zata yi, bazata rayu ba......"


Ja da baya Sarki Raamud ya soma yi tabbas maganganun Bara'at sun juyar masa da kwakwalwarsa, zuciyarsa ne ta fara harbawa da ƙarfin gaske,
lokaci guda kuwa ya yi regret akan abunda ya aikata, "haƙiƙa Ayush itace mahaɗin Junaid, kuma jininsu ɗaya yanaso ya warware wannan al'amarin amma ya kasa..." haka ya tsaya cak yana maganar zuci, jikinsa ya sake baya jin daɗin jikinsa sosai, ga wani irin zazzaɓi da ya rufe shi..
lokaci guda kuwa ya zabura da sauri ya fice daga cikin room ɗin Bara'at wacce itama tsayawa tayi tana kallonsa cike da tsana da kuma mamaki ga hawayen da suke gangaro mata, kamar tasan abunda yake ransa ta furta cewa "yanzu haka nasan zai tafi ƙasar nigeria ne domin yaje ya dubo su Ayush...."
itama da gudu ta nufi waje, ta samu Sarkin har ya hau kan wani dokinsa mai ƙarfin gaske da kuma gudu, domin zai iya zuwa nigeria da wannan dokin ba tareda ya hau jirgi ba, domin yasan ta ko ina nemansa ake..
har ya fara tafi ta ƙwalla masa ƙira da ƙarfi tana faɗin " *kasa a ranka cewa kana barin cikin masarautar nan shikenam ka barshi har abada, kuma ba kai ba mulki! ƙa'idojin dokar kenam, na tunatar dakai...*


Sarki da jin hakan ya tsayar da dokinsa, gabansa na yankewa, idanuwansa
kuwa har sunyi jawur, fuskarsa ya nuna alamar damuwa ajiyar zuciya yaja sannan ya kanne idanuwansa sosai, yana so yayi kuka amma ba hali domin zubda hawayensa shima wani makaryin asiri ne a jikinsa...

Ba yanda ya iya haka ya juyo da dokinsa saboda mulkinsa shine babban abun tasirinsa kuma shine tushen sa na iyaye da kakanu...
Haka ya sauƙo yana tangaɗi hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfin bala'i, tabbas shima yasan idan babu Ayush shikenam tashi tazo ƙarshe,
saida yazo daf da Bara'at ya tsaya yana kallonta cike da tausayawa kansa, bazai iya control hawayensa ba haka ya durƙusa da gwiwowinsa sannan ya fashe da wani irin matsanancin kuka kansa a sunkuye....


zaro ido Bara'at tayi tace "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, nashiga uku *SHUGABA* tinda uwata ta haifeni ban taɓa ganin damuwa a fuskar ka ba balle hawaye uwa uba har da rera kuka, abun babba ne, shikenam ka korar da ALJANUNKA sunga hawaye a idonka...."


Aljanun da suke cikin masarautar sa kuwa haka suka rinƙa ɓacewa,
duk wani abun tsafi sai ɓacewa suke,
duk abubuwan tsoro dake cikin dajin maƙarƙashe duk sun ɓace daman shi ya ƙirƙire su da yarjejeniyar bazasu ga hawaye a idonsa ba har abada...
gashi kuwa yanzu komai ya rushe masa ata sanadiyar Ayushert!
Haka masarautar nan ta dawo babu komai na tsafi a ciki, daga shi sai matarsa Bara'at sai kuma DAMUSAR JUNAID wanda shi kuma makaryin tsafinsa yana jikin zoben cibiyar Ayush,
Shima Sarki Raamud akwai sauran tsafi a jikinsa wanda shima makaryinsa yana a tattare da wannan zoben cibiyar Ayush,

suna tsaye a harabar masarautar sai ga wasu tsuntsaye suna shirin shugowa, da gudu Sarki ya miƙi hanyar babban gate wanda ya buɗe yaje ya rufe ya danna ƙwaɗo
haka tsuntsayen suka juya ba halin shugowa domin akwai hayaƙin da suna shugowa zasu ƙone...

ita kuwa Bara'at jikinta ne yayi sanyi domin za'a iya kawo musu hari a koda yaushe idan aka fiskanci babu masu kula da masarautar nan, tana cikin wannan tunanin taji ya riƙo hannunta suka shiga cikin falon masarautar, gaban Damusa yaje ya durƙusa yana shafarsa
murya na kakkarwa yake magana da Damusar "kai kaɗai ne ka rage mun a halin yanzu daga kai sai matata, itama Allah yasa kar ta gujeni, ga shi na rasa ɗiyata tilo, nasan Ɓingel mutuwa zata yi! banaso na rasa masarautar nan saboda amanar mahaifina ne.."
Hmmm! ajiyar zuciya yayi sannan yakai idonsa kan Bara'at wacce take tsaye kanta a sunkuye, ya taso yazo gabanta ya riƙe hannayenta yana faɗin "idan bakya son zama dani akwai sauran tsafi a jikina zan mayar dake nigeria a yanzu, sai dai amma gurin zama zai gagare ki..."


Bara'at tana kuka tace "ba yanda zanje ina tare da kai, gurin wacce zanje a nigeria nasan ta mutu, ina zanje to? sai dai mu mutu tare...." ta ƙarasa maganar tana kuka ta rungumi Sarki,
shima hawayen yake zubar wa yana mamakin ta yanda al'amarin nan ya afko masa lokaci guda,
Abubuwa sun taɓarɓare masa, lokaci ɗaya ya zamo kalar tausayi,
kamar ba shi bane *SARKI RAAMUD, SARKIN MATSAFAN DUNIYA*....


(( *Yaaa Salam!*
*ku duba abunda ya faru da Mahaifin Ayush lokaci ɗaya,*
*ba'a jayayya da ikon Allah, duk abunda Allah ya tsara ba makawa sai ya faru kafin ƙiftawar ido,*
*Allah shine mai komai a hannu kuma shine mai mulki shine mai yin abunda yaso, duk tsafin mutum, duk izzar mutum, duk ƙarfin ikon mutum, duk zalincin mutum a lokaci ɗaya Allah zai gama da shi,*
*ya Allah kasa mufi ƙarfin zuciyar mu 🙏🙏* ))


******


Doctor Hasheem ne ya fito falo yana zaune akan sofa idonsa akan plasman,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login