Showing 126001 words to 129000 words out of 139707 words
ware mata miƙaƙƙun hannunta alamar tana buƙatar kofin shayin..
Ayush miƙa mata kofin tayi kanta a sunkuye domin ba ƙaunar haɗa ido take da ita ba,
tana miƙa mata ta wuce zata haura saman stairs,
Rumana ta dakatar da ita tareda faɗin "come here.." tayi mata alama tazo da hannunta, a tunaninta Ayush bata jin yaren natan,
tana zuwa Rumana ta miƙa mata cup ɗinta tace "bazan iya shan wannan abun ba, ya yi kauri da yawa sannan sugar yayi yawa, go and find me coffee..."
Junaid ne ya buɗi baki zai maimaita wa Ayush abunda Rumana ta faɗa da hausa,
cikin zafin rai Ayush ta ɗaga masa hannu da sauri tace "ba sai ka fassara mun ba..."
tana kaiwa haka ta nufi kitchen,
abunda Rumana ta kasa ganewa kenam amma tasan akwai wani abu a tsakaninsu, just tayi shuru ne kawai amma tasan ba ƙanwarsa bace domin a saninta da shi bashida bros or sis...
Junaid bin bayan Ayush yayi da kallo cike da mamaki "taya Ayush tasan abunda Rumana ta faɗa?..."
yana cikin wannan tunanin sai ga mommy ta fito tana faɗin "Junaid ka kaita ɗakin ni zan wuce bedroom ɗina saboda ina jin bacci sosai, ya kamata kuma ku samu ku kwanta kafin sallar asuba, kunga gobe kunada hidima ba baccin rana..."
Mommy tana kaiwa haka ta wuce ɗakinta,
shima Junaid magana yayi wa Rumana suka nufin ɗakinta, yana kaita ya juya zai fito ta tsayar dashi tace "ina zaka je Beb?.."
yace "Girl i what to sleep.."
tace "ok before seat here and wait for me.." ta kama kafaɗarsa ta zaunar dashi a bakin gado..
a gabansa ta gama cire kakin sojan natan ta sanya sleeping dress sannan tazo yanda yake zaune ta hau saman cinyarsa ta zauna tana fuskantarsa tace "Beb you known i really miss you.." tareda da manna masa kiss a saman goshinsa tana shafar lallausar suman kansa,
Shi dai Junaid sai faman kakkauce wa yake saboda sun sani baya taɓa biye musu, kuma tinda yake da su bai taɓa yadda ya haɗa baki dasu ba, sai dai su gama iskancinsu na shashshafa shi amma bayan hug baya barin a kauce hanya saboda wasu dalilansa na farko su ba musulmai bane sannan shi ba irin mazan nan masu ƙwaɗayin mata ba ne,
mace ta farko daya taɓa sumbatar ta a rayuwarsa itace Ayush, kuma itace kawai yake biye mata suyi romance,
Rumana tana cikin kissing ɗinsa a wuya tana wasa da sumar kansa saiga Ayush ta turo ƙofa ta shugo hannunta riƙe da cup na coffee,
ganin halin da suke ciki ne yasa ta tsaya cak tana kallonsu nan da nan hannunta ya fara rawa, idonta har ya cicciko da ƙwalla tana kallon Junaid wanda shima ita yake kallo, gaba ɗaya ya rasa yanda zaiyi domin shima kansa baiji daɗin hakan ba, bai so ace Ayush ta zo ta sameshi a haka ba,
ita kuma Rumana ganin Ayush a tsaye ta kasa motsawa tace "you will not keep it?..."
Ayush jikinta a sanyaye ta ajiye cup ɗin tana jan ƙafa daƙer zata fice a ɗakin idonta kuwa na kan Junaid, shi ɗinma kallonta yake sun kasa ɗage idanuwansu daga na juna,
Ayush kuka ne yake shirin kuɓuce mata tayi saurin barin ɗakin,
hankalin Junaid ba ƙaramin tashi yayi ba,
ɗaga Rumana yayi daga kansa ya kwantar da ita yana faɗin "ki kwanta ki huta.." kafin tayi magana kuwa har ya bar ɗakin..
Ayush tangal-tangal take zata faɗi tsabar hajijiyan da yake ɗibarta da haka take haura upstairs a hankali gudun kar ta faɗo ƙasi, wani irin hajijiya ne ya fizgeta tayi baya zata faɗo daga saman beni,
ji tayi ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, ƙamshin turarensa ne yake bugan hancinta anan ta ƙara tabbatar da Junaid ne,
lumshe idonta tayi wani irin ciwon kai ne yake damunta, gaba ɗaya ta kasa motsawa duk jikinta ya mutu babu sauran ƙarfi a tattare da ita..
hannu yasa ya ɗago ƙafafuwanta yayi mata ɗaukar luɗa sannan ya ƙarisa haurawa da ita, kai tsaye ɗakinta ya wuce da ita, ya kwantar da ita saman katafaren gadonta,
har zai juya ya tafi saiya kai hannunsa yana taɓa saitin wuyanta yaji jikinta ya hau temporary sosai, har tiririne yake fita daga jikinta tsabar zafin zazzaɓi, a zabure ya tashi yana kallonta har ta fara rawar sanyi da sauri ya fice daga ɗakin yana sauƙa daga downstairs kamar zai dungura kai tsaye ɗakin medicine ya nufa yaje ya ɗauko boxes na pharmacy da gudu ya koma ɗakin Ayush tareda bottle na ruwa,
haurawa saman gado yayi ya ɗagota yana ƙiran sunanta, Yushert! Yushert!! please open your eyes,
a hankali take lumshe ido tana buɗe wa,
maganinnuwa ya ɗuɗɗura mata kafin kace mai ta yunƙura ta amar da duk maganin data sha, tana haki sama-sama ganin maganin da ta sha bai zauna mata ba ya ɗauki allura ya zuƙo ruwan maganin paracetamol ya saita dantsen ta sannan ya caka mata allurar hannunsa na rawa, ita kuwa nan danan gumi har ya yarfo mata tana jan numfashi da ƙarfi,
da sauri ya tashi ya shige cikin toilet ya jiƙo ɗan ƙaramin towel da ruwa yazo ya ɗora mata akan goshi, bayan wasu mintuna bacci yayi awun gaba da ita,
ajiyar zuciya yayi yana sauƙar da numfashi a hankali sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa da tinin har ya tsorita ganin halin da Ayush ta shiga cikin ƙanƙanin lokaci,
tashi yayi ya zamar da bedsheet ɗin da ta ɓata da amai yakai toilet sannan ya shimfiɗa wani bayan ya ɗagota saman kafaɗarsa, a hankali ya maida ita ya kwantar shima kwanciyar yayi a kusa da ita ya mannata a jikinsa tareda jawo musu mayafi suka rufu domin bazai iya barinta ita kaɗai a wannan halin ba, shima daga baya baccin ya ɗauke shi,
sai kace wasu ma'aurata🤔🤔...
ƙiran Asubar farko akan dodon kunnen Junaid, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa, ganin ɗakin yayi haske sosai yasa ya buɗe idonsa gaba ɗaya yana mamakin taya akayi aka kunna hasken ɗakin alhalin a kashe yake, hannu ya kai zai taɓo Ayush yaji gurin wayam da sauri yakai idonsa gurinda take kwance ata gefensa yaga babu kowa, miƙewa yayi ya zauna tareda kallon yanda Ayush take a zaune saman sallaya tana jan carbi alamu sun nuna tayi sallar dare ne, domin yanzu ake ƙiran sallar asuba ma...
a hankali yake motsa bakinsa yace "Yushert.." bata kula shi ba sai ɗagowa tayi ta kalle shi sannan ta kawar da kanta tana kallon gabanta bakinta na motsi alamar tana tasbihi..
tashi yayi ya sauƙa daga kan gadon zai fita a ɗakin har yazo daf da bakin ƙofa yaji tace "meya kawo ka ɗakina?.."
murmushi yayi sannan yace "nazo duba lafiyarki ne, ya jikin nakin?.."
daga nan bata ƙara cewa komai ba ko amsa bata bashi ba ta cigaba da jan carbinta..
ganin ta sharar dashi ne yasa ya girgiza kai sannan ya fice, kai tsaye ɗakinsa ya nufa yana shiga kuwa ya shige toilet ya yo alwala ya fito da sauri ya sauƙa down yayi ficewarsa ya tafi masallaci...
misalin ƙarfe 9 na safe mommy tana zaune a falo tana jiran shugowar Junaid tin fitar Asuba, tana so a fara shirye-shirye tin yanzu kafin a fara yin baƙi duk da tasan sai wajen la'asar a buɗe taron, kuma a cikin gidan za'ayi taron a babban hall wanda sai an buɗe wani ƙatoton get a cikin gidan kafin a shiga fili ne guda duk an mamaye gurin da floor, wajen daman an tanadar da shi ne saboda taro na musamman, an ƙayatar da wajen sosai ga kujeru a jere na musamman, ga wasu ƙayatattun kujeru kuma du a saman yanda manya-manyan baƙi zasu zauna da kuma shi kansa Junaid, ga wasu haske masu ƙayatarwa sai walwali suke suna bada haske kala-kala, duk an mammanna photunan Junaid a jikin bangon an tsara shi shima..
(wannan taron da za'ayi nima ina gayyatar members na group ɗin matar damusa dasu halacci gurin taro amma sai kunada card na gayyata domin tin jiya aka raba wa manya-manyan baƙi idan baku samu ba toh ba shiga gurin taron sai dai a baku labari ko kuma ku kalli video, ni kuma Asmeetah ga kujerar Oga Junaid ga nawa🤪🤪 kuma in baku labari raƙumi da saniyoyi uku za'a yanka..)
Mommy tana zaune a saman sofa saiga Rumana ta fito daga cikin ɗakinta tana sanye da gajeran wando zuwa gwiwarta mai kakin soja da kuma ƙaramin best sai dai ta saka breziya ata ciki kafin ta ɗora best akai, zuwa tayi ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falo tana faɗin "gud morning mom.."
Mummy da murmushi a fuskarta ta amsa mata dake yanzu da turanci tayi gaisuwar bada french ba..
Mommy tace "ga can kayan breakfast asaman dinning..." tayi mata maganar ne da turanci,
yamutsa fuska tayi sannan tace "where is Junaid?.."
"I don't known.." mommy ta bada amsa a takaice,
Rumana ta kuma cewa "ok bari yazo muyi breakfast a tare..."
daga nan basu ƙara cewa komai ba.
saiga Ayush ta fito sanye da zureren hijab har ƙasi ta fitar da hannunta waje dake hijabi mai hannu ne..
saida tazo gaban mommy ta durƙusa tana gaisheta,
mommy amsawa tayi da murmushi a fuskarta tace "antashi lafiya my dota?.."
Ayush ta amsa mata tareda miƙewa tsaye har fuskarta yayi fiyau farinta ya ƙara fitowa,
zuwa tayi gaban Rumana ta durƙusa mata sannan itama ta gaisheta,
tana turɓune fuska tareda yamutsa shi daƙer ta buɗe baki ta amsa mata,
dake tana zargin akwai wata alaƙa dake tsakaninta da Junaid tin a daren jiya, Rumana sarkin kishi kenam...
Ayush miƙewa tayi mommy tace "Dota ga can kayan breakfast kije ki karya kinji, nasan kina jin yunwa..."
Ayush ta ɗaga mata kai tareda cewa "toh Momy.."
taje ta zauna a dinning tana zuba fried chicken domin shi take sha'awar ci ta haɗa wannan la'anannen shayinta nan mai masifar kaurin gaske domin tana zuba madara kam bana wasa ba sannan ta zabga sugar,
haka take ci tana ɗibar tea da spoon tana haɗawa da shi,
ba ƙaramin yunwa ta tashi dashi ba,
tana cikin karyawa sai ta jiyo sallamar Junaid ya shugo yana jan trolly ta bayansa kuwa wata zankaɗeɗiyar mace ce domin wannan ta wuce ace mata yarinya,
Ayush dakatar da karyawa tayi tana kallon ikon Allah,
miƙewa mommy tayi tsaye tana faɗin "ina kaje Junaid tinda asuba?.."
bata ƙarasa maganar ba taga mata ta shugo tana bin falon da kallo tareda faɗin "wow nice this parlour is so fantastic.." tana magana da yaren china gashi kuwa tayi zubi da chinoni hatta ƙananon idanuwan da ƙaramin baki,
Junaid ne yace "Adity look at my mom.." ya ƙarasa maganar yana nuna mommy shima da yaren china yayi maganar, sannan ya kalli mom itama yace "mommy ganan Aditi fah ta ƙaraso.."
Mommy yaƙe kawai take tace "eah ai na gani, ganan zubinta kuwa irin na chinoni, wato zaka haifo mun jikoki masu kamanni daban daban kenam, a cikin akwai chinoni da kuma turawa.."
Dariya Junaid yayi sannan yace "ita kuma Angel fa?..."
mommy tace "ai wallahi gwara Angel duk ta fisu kyau, ita wannan ai kamannunta irin namu ne.."
Aditi ce ta katse mommy da cewa "mom you are so beatiful, glad to see you.." ta ƙarasa maganar tareda rungumar mommy,
mommy dai kawai ta biye mata ne tana dariyar yaƙe amma daga Aditi har Rumana ba wacce ta ƙwanta mata a rai..
Rumana tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana zabgawa Aditi harara kamar idonta zai faɗo ƙasi saboda tasan itama budurwar Junaid ce,
Adity ganin yanda Rumana take hararar ta yasa ta fusata tayo kanta zata naushe ta Junaid yayi saurin riƙota yana faɗin "don't allow if not you'll see what am going to do.."
Adity juyowa tayi tana kallon Junaid da fici-ficin idanuwanta, duk zafin ranta tana shakkar Junaid, ba china ba ko itace sarkin faɗan chinoni ce bazata iya gabzawa da Junaid ba...
turo baki tayi tace "nuna mun ɗakina.." tayi maganar da yaren china cikin sauri-saurin magana,
yana riƙe da hannunta yaja ta suka nufi ɗakin dake