Showing 81001 words to 84000 words out of 139707 words

Chapter 28 - Matar Damisa book Complete by Asmita .txt

Asmeetah   

16 Dec 2024

9964

ya koma yana mata barazanar idan ya ɓalla ƙofar zai ɗauki mataki a kanta duk da hakan Laila bata zo ta buɗe ba,
har zuwa ƙarfe 11 na safe Hasheem ya kuma dawowa yana ƙoƙarin ɓalle ƙofar ɗakin amma ya kasa, shi tsoronsa kar yaje ta mutu domin jiya yayi mafarkin mutuwa,

"ke Laila ina miki magana bakya ji ko? dan Allah ki buɗe mana Autar mu bansanki da fushi ba, kuma na baki hakuri ai, insha Allahu bazan ƙara dukanki ba nayi miki alƙawari, wannan ma tsautsayi ne, in har baki buɗe ba yau ba zuwa hospital,"
shuru Laila taƙi buɗe wa....


tin jiya ta rufe kanta a ɗaki take ta sharar kuka,
abun ya bata mamaki "wai Bros ne zai mareta akan budurwa??"
tana jin kiran da yake mata amma ta share,
Laila tana da zuciyar masifa, sai ta iya kwana uku bata ci komai ba saboda zuciya irin tata, ita fushin ta ma yana shafar abincin da zata ci!
Dalilin da yasa Doctor Hasheem yake damuwa sosai akanta indai tayi fushi domin yasan halin ta, tin jiya bata ci komai ba kuma haka zata cigaba da fushi indai ba lallamanta akayi ba..


Doctor Hasheem yana zaune a falo yayi tagumi Laila ba ƙaramin ƙona masa rai tayi ba,
sallama yaji anyi ya ɗago da kansa yana faɗin "Haydar ka dawo ne..??"
"wallahi kuwa Bros mun kammala exam, amma Bros ya na ganka a gida baka je hospital ba?"
Ajiyar zuciya ya yi sannan yace "na rasa yanda zanyi da Laila, tin jiya ta kulle kanta a ɗaki har yanzu taƙi buɗe wa.."


"Amma Bros mekayi mata ne..?"
Haydar yayi tambayar yana kallon Bros ɗin shi..
Shafa fuskarsa yayi da hannayensa biyu yana hura iskar bakinsa yace "Laifi tayi mun na mareta..."

zaro ido Haydar yayi sannan ya miƙe tsaye yana faɗin "shikenam yau Abinci ya huta, daman ita take cinye mana abincin gidan!
yau kam abinci inci in ƙara inci in ƙara, yana magana yana haɗawa da rawa..


Daman Haydar da Laila basa jituwa kullum a cikin faɗa suke, daman fifikon wa da ƙanwa ne a tsakaninsu,
ya wuce kitchen ya ciko plate da abinci ya dawo falo ya zauna yana ci yana kallon plasman ana showing MAZA A YAU acikin shirin Arewa 24, sai da yaci iya cinsa tukun ya ture plate ɗin gefe bai iya cinye abincin ba,
duk abunda yake yi kuwa Doctor na kallonsa sai daga baya yace "Haydar ya za'ayi Laila ta fito ne ?"
Haydar yace "kaima Bros kasan halin ta, kawai shareta taga an damu da itane shiyasa..
Amma abu ɗaya zanyi mata ta fito"


Dr ya zabura yace "please Haydar ka taimaka kasa ta fito.."

Yace "toh shikenam ina zuwa"
Haydar ya tashi ya nufi wajen ɗakin Laila yana faɗin "Ah Oyoyo Oga Junaid your welcome, ya kwana biyu....."
kafin ya ƙarasa maganar sai ga Laila ta fito da gudu tana washe baki tare da faɗin "yana ina?."
Jin yanda Haydar ya kwashe da dariya yana nunata da yatsa tareda faɗin "ƴar wahala ta fito, so shame wallahi.." ya na cigaba da dariyar sa....


Ɗaure fuska tayi tana hararar sa taja dogon tsuka zata koma ciki Doctor yayi saurin tare ta....


******


Mommy ce take zaune a bakin gadon Ayush, kanta ɗaure da bandeji ita yau ta samu sauƙi domin ba ƙaramin kulawa tasha ba.
ita kuma Ayush tana kwance ido a rufe ita tanada sauran numfashin ta, daga suma ta wuce da yin bacci sakamakon allurai data sha ga kuma an ɗaura mata drink na ruwa,
sai ji kake tana ƙiran Yaya Junaid, tana motsa lips ɗinta a hankali "Yaya Junaid! kar ka mutu ka barni, nima zan bika mu tafi tare..."
Mommy ce ta kira sunan ta "Ayushert."
a cikin baccin ta amsa da "na'am.."
Mommy ta kuma cewa "meya faru daku ne" still idon Ayush a rufe domin bata cikin hayyacinta tace "Abba na ne, Ab ba na, Abbana ya kashe shi kuma zamu tafi tare da Yaya Junaiddd..."

Mommy cikin rashin fahimta tace "wazai fahimci wannan maganar ki Ayush, ki buɗe baki kiyi mun bayani Dalla-dalla..." suna cikin wannan halin sai ga Doctor samuel ya shugo duba jikin Ayush yace "Doctor ki barta yanzu tunaninta yake fara dawo mata kwakwalwa, bata cikin hayyacinta zuwa anjuma kaɗan zata farka." duk wannan maganganun daya yi su acikin harshen turanci ya yi...


Mommy tace "okay what about Junaid??"

Doctor Samuel yace "yes abunda nazo sanar miki kenam, munyi iya ƙoƙarin mu kuma ya farfaɗo,
sai dai kwakwalwarsa ta juye sai wani gwalatu yake tayi!.. but Hajia kamar dai ya haukace..."


Mommy a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin "what?? yarona ya rasa tunanin sa, taya hakan zai faru." da gudu Mommy ta ratsa ta gefen Doctor ta fice, kai tsaye room ɗin Junaid ta nufa! tana shiga kuwa ta sameshi ya fisge jinin da ake ƙara masa ya zauna a tsakiyar gado ya naɗe sawayensa kamar mai cin tuwo yanata gwalatu kamar haka "ǧ'rēæñçüčæǰǰǰǰǰǰǰǰæ''rëžñœøœöøœæç..."
(Asmeetah ta baza kunnuwa domin taji meyake faɗi amma ta kasa 🤔🤔)


Subhanallahi Junaid fa ba mutuwa yayi ba haukatar da shi akayi,
Mommy ce ta nufi gurinsa da gudu tana faɗin "Nashiga uku Junaid ka haukace ne? ta ƙarisa tana kuka..


shi kuwa ganin tayo kansa yasa ya ƙanƙame jikin gini yana ihu, yana kukan jarirai tare da gwalatu wanda ba jin abunda yake faɗa ake ji ba,

Mommy tana rarumo shi, shi kuwa yana guduwa mata yana wannan kukan luɗa
"Innƴyaaa 😭! Innƴyaa😭!! Innƴyaaaa😭😭 !!!...
Duk wanda yaji wannan kalar kukan sai ayi tunanin haihuwa akayi a ɗakin saboda kuka tsakk irin ta jarirai yake yi..
bai daina kukan jarirai ba har saida Mommy ta tashi daga bakin gadon ta ɗan ja da baya tukun yayi shuru yana ajiyar zuciya irin yanda yara idan sunyi kuka suke ajiyar zuciya haka shima yayi ya ɗauki babbar yatsar sa ya zura a baki yana tsotsa, ga hawaye a saman fuskar sa sai tsotsar yatsa yake ta yi...


Kuka Mommy take sosai bazata iya ganin wannan takaici ba, haka yasa ta bar ɗakin da gudu tana kuka,


Oga Junaid dai haka ya zauna a cikin ɗakin yana tsotsar yatsa da zaran wani ya shugo ɗakin kuma sai ya fara kukan jariri,
cikin dare kuwa haka ya hana mutanen asibiti yin bacci ya damesu da kuka, da haka likitocin suke shiga suyi mata treatment amma abu ba sauƙi,
a cikin daren kuwa Ayush ta farka tana Kalle-kalle a hankali take motsawa ta tashi zaune daƙer, idon ta suka sauƙa akan Mommy tana kan sallaya ta ɗaga hannu sama tana ta Addu'o'i.
Kwatsam kunnuwanta suka jiyo mata kukan Jariri yana ta ihu, ɗaga kanta sama tayi tana kallon fanka dake juyawa iska ta ko ina ga na A.C haske ta ko ina amma a wannan lokacin ƙarfe 2 na dare ne...


jin kukan jaririn yayi yawa yasa ta sauƙar da ƙafarta ƙasi, tana tafiya a hankali ko takalmi babu a ƙafarta ta fice daga ɗakin,
ita kuwa Mommy bata sani ba.


tafiya take ita kaɗai tana bin yanda take jiyo kukan yaro,
ga gashin kanta a baje ya rufe mata gadon baya, itama kamar wata Aljana da blue riga a jikinta na asibiti zuwa gwiwar ta, sai ta tazo dab da ɗakin da take jin kukan tasa hannu zata buɗe taji a dafata ta baya har sai data tsorita ta waiwaya da sauri, wani Doctor ne wanda yake night duty ya kamo hannun ta yana faɗin "meya fidda ke a wannan daren, kije ki kwanta ki huta kinji ko.." ya kaita har ɗakinta, daiden lokacin Mommy ta idar da salla ita ma ta nufo gurin Ayush tana faɗin "Ayush ina kika je kuma? bansan kin farka a baccin ba ai" ta kamo hannun ta sannan ta zaunar da ita a kan gado...


Ayush ce ta buɗi baki tace "Mommy wacece ta haihu ina jin kukan jariri, kodai bashi da lafiya ne inaso inje na duba jaririn..."


Hawaye na gangaro wa Mommy tace "Ayush ki kwanta ki nutsu kinga baki da lafiya"
Ayush ce ta katse Mommy da cewa "Ina Yaya Junaid? ya mutu koh? daman na sani sun kashe shi, nima kuwa mutuwa zanyi..." ta fashe da matsanancin kuka,
Mommy ta jawo ta jikinta tana rarrashin ta, itadai Mommy Allah ne kaɗai yasan irin baƙin ciki dake zuciyarta...




*WASHE GARI*


wata mata ne take zaune da yaronta a kusa da room ɗin Junaid, kwatsam sai suka jiyo kukan jariri, daman ita awu tazo yi tanada tsohon ciki, yaron ta yace "mama an haifi jariri yana kuka a ɗakin can.."
ganin uwar bata kula shi ba yasa yaro ya nufi ɗakin yana zuwa ya buɗe ya shige ciki,
Yaro kam yaga Junaid a kan gado zaune sai kukan jaririn yake tayi, a tsorace yaro ya jefar da fidar hannunsa ya gudu yana faɗin "Mama ƙatoto ne yake kukan jariri, babba ne kuma yana kukan yaroro ƙarami..." uwar bata fahimci mai yaron yake cewa ba kawai ta fisgi hannun yaro suka tafi....


Doctor Hasheem ne ya shugo ɗakin Junaid ganin Junaid a wannan halin ya firgita shi,
daman kafin yazo an bashi labari! shine yanzun yazo ya tabbatar, gashi kuwa har yanzun bai daina kukan ba
Shi kuma Junaid ƙara volume kukan luɗan yake idan ya kalli Doctor Hasheem sai kuma ya kalli fidar da yaron nan ya jefar, Doctor Hasheem ne kawai ya fahimci kukan yunwa yake yi kuma bazai iya sauƙa daga kan gadon ba,

Hannu Doctor ya kai kan fidar dake yashe a ƙasi ya ɗauka gashi kuwa cike yake da madara, zuwa gabansa Doctor yayi sannan ya miƙa masa fidar..
Dariya Junaid ya farayi yana mimmiƙo hannayensa, yana ƙara irinta yara masu wasa ga kuma yawun da ke zuba a bakin sa irin mai yauƙin nan na yara, kafa baki yayi akan fidar yana zuƙan madarar cikin, ya rirriƙe da hannu biyu yana lumshe ido,
Doctor Hasheem ne ya taimaka masa ya kwantar da shi yana shan madarar fidar a kwance har bacci ya ɗauke shi...


Tsabar takaici da tausayi haka Doctor Hasheem ya fice daga ɗakin yana hawaye....


*MASHA ALLAH*


( *kuga fah jaririn aljani aka turowa Junaid😭😭🤣🤣🤣* )




*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500


*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500


*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*


*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*


typing📲


🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)


*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)




*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________


https://www.facebook.com/103637491942644/


💫💫 *{{N W A}}* 💫💫




بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم


*BOOK ONE*
🅿️ -------> 75 & 76 <-------


____________________________
mommy tana zaune a bakin gadon da Ayush take kwance tana kallon ceiling, da alamun tana tunanin wani abu ne ga hawaye kwance a saman fuskar ta..
Doctor Hasheem ne ya shugo da sallama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login