Showing 138001 words to 139707 words out of 139707 words

Chapter 47 - Matar Damisa book Complete by Asmita .txt

Asmeetah   

16 Dec 2024

9956

(magana ake ta rayuwar turawa to meya hwaru🤔😜)..


Ana tambayar Amarya daide lokacin aka shugo da ita,
Angel tana riƙe da hannunta na dama sai wata mata mai sanye da hijabi har ƙasi tana rufe da fuskarta da liƙab itama tana riƙe da Ayush ta ɓangaren hagun,

Ayush tayi matuƙar kyau bana wasa ba,
ta saka wedding gown fari na campany irin mai kama jikin nan, daga saitin gwiwarta kuma rafar ta baje sosai, ta bayan yana jan ƙasi, dirin jikinta ya fito bana wasa ba, ga hips ɗin nan kamar kamar dai....


a hankali take taka takalmin ta fari mai duwatsu ta sama ga tsini domin daƙer take taka takalmin a hankali gudun karta faɗi,
ga anyi mata gyaran gashi gaban goshin nan anyi style da gashin wajen ya kwanta, aka naɗa mata gwaggwaro da net ɗin kayan jikinta, sannan aka rufa mata ɗan ƙaramin gyalen net ɗin akan ta da fuskarta gaba ɗaya, ga an zuba mata makeup, Ayush bata ƙwalliya ma ya kuka ga kyanta balle yanzu da akayi mata makeup na amare, kyau iya kyau kam ba'a magana...


tinda suka shugo har aka zaunar da Ayush idon Junaid yana kanta, har maganar zuci yake "anya kuwa wannan itace Yushert ɗita? wannan kam aljanar kyau aka samo mun..." yana maganar zucin idonsa na kanta wacce take zaune ata gefensa,

photuna kawai aketa musu da masu wayoyi da camera man duk suna ɗauka ne a photo har da video domin ba ƙaramin dacewa sukayi ba, sunyi matuƙar kyau sosai...


ita dai Ayush har yanzu ta kasa gane mai hakan yake nufi ne, a tunaninta duk karramawa ne haka, an nuna an damu da ita tinda gashi har ɗaukota akayi aka zaunar da ita,
abunda yake cikin ranta kenam..


mata mai liƙab kuwa itama zama tayi tana bin kowa da kallo, itadai mommy ta turata ne akan taje su taho da Ayush ba tareda tasan ko wacece ita ba, domin tin zuwanta bata cire liƙab ɗin ba,
Ayush ce kawai taso ta ganeta amma itama bata gama wayeta ba, ita kaɗai sai murmushi take a cikin liƙab ɗin, tana cikin farin ciki matuƙa....


Ayush tana zaune sai ji tayi ance Amarya da Ango ku tashi tsaye,
zaro manya-manyan eyes ɗinta tayi tana faɗin "su waye Amaren kuma?.." tayi maganar acikin ranta, bata ankara ba taji an riƙota a tsayar da ita, Angel ce take kusa da ita daman ita ta tasar da ita..


Junaid ne ya riƙo hannayenta biyu suna fuskantar juna, cikin rashin fahimta Ayush take kallon Junaid, shi kuma sai faman sake mata murmushi yake..


wannan tsari ne za'ayi shi idan duk suka amince suna son junansu toh zasu sanyawa juna zobe koda bayan nan ne babu halin rabuwa dole daga baya za'ayi aure ba fasawa ba janyewa..




Mai gabatarwa ne yazo gabansu ya tsaya sannan yace "Captain Junaid shin ka amince kana son Ayushert?"
Junaid idonsa akan Ayush yace "na amince ina son Yushert..."


mai gabatarwa ya ƙara da cewa "ka amince komin daɗewa zaka Auri Ayushert babu janyewa?.."
yana murmushi yace "na amince, bana fatan na rabu da Yushert koda wasa..."


kafin kace mai mutanen wajen sun haɗe wajen da tafi da ihun farin ciki especially abokansa, harda su buga ganga lokaci guda, kafin wajen yayi tsitt..


zoben zinare aka bawa Junaid ya sanyawa Ayush, ya karɓa sannan ya zura mata a dogin yatsunta..


mai gabatarwa ya komo kan Ayush itama ya tambayeta,
"Malama Ayushert shin kin amince da soyayyar Junaid?..."
sai a lokacin Ayush ta fahimci wani abu, ita a tunaninta Aure ake ɗaura musu a hakan,
jin tayi shuru ne yasa aka sake tambayarta
"Malama Ayushert kin amince da soyayyar Junaid? kuma zaki Aure shi?..."


wajen yayi tsit ana sauraronta,
hannu tasa ta yaye gyalen kan natan tana kallon Junaid tace "Ban Amince ba, kuma bazan taɓa Auransa ba! dukan mata yake yi, yau ma saida yayi wa wata budurwarsa duka kamar zai kasheta, a haka zan aure shi? to gwara na mutu banyi Aure ba, idan na Aure shi zai iya murɗe mun wuya ya kashe ni, ga ƴanmatan ka nan ka zaɓi ɗaya ka Aura amma banda ni......"


tana kaiwa ƙarshen maganarta ta juya da gudu zata tafi, ta gurmuɗe da takalmin ƙafarta zata faɗo ƙasan floor da aka ɗanyi tudun beni a gurin da sauri Junaid ya cafko kunkuminta ya rungumota jikinsa har idonsa ya cicciko da ƙwalla yana kallon yawan mutanen da suke wajen mata da maza gasu nan, yana rungume da ita jikinsa na kakkarwa tsabar takaici da baƙin ciki tinda yake ba'a taɓa basar dashi a cikin mutane ba sai yau, gaba ɗaya ya rasa ya zaiyi kamar ya nitse cikin ƙasa haka yake jii,
hajijiya ne yake shirin ɗibarsa, ƙafarsa tayi masa nauyi yana shirin faɗuwa da Ayush da yake rungume da ita, abokinsa commander yusuf yasa hannu ya ɓanɓare Ayush a jikinsa ya zaunar dashi yana bubbugar kafaɗarsa alamar rarrashi,
Ayush zame jikinta tayi tana tattara rigarta ta bar wajen kwata-kwata...


idan aka ware Laylah da Rumana da kuma Adity duk wajen ba wanda zuciyarsa bai sosu ba, musamman abokansa tsabar takaici kasa cewa komai sukayi suna zazzaune kamar wanda ruwa ya cinyesu,

Mommy kam haɗa kanta tayi da gwiwowinta bansani ba ko kuka take yi...


Angel itama kamar ta rausa ihu tsabar takaici, domin duk abunda zai taɓa Junaid haka take jinsa a ranta,
babban tashin hankalinta shine ganin hawayensa, tinda take dashi bata taɓa ganin hawayensa ba sai yau...


suna zaune babu wanda ya motsa sai matar nan mai liƙab itace ta tashi da sauri tabi bayan Ayush,
tana shiga parlour kai tsaye upstairs ta wuce saboda taga daga nan aka fito da ita,
tana buɗe ɗakin Ayush ta tarar da ita kwance sai faman rera kuka take,
ta rufe ƙofar sannan ta ambaci sunata "Ayushh.." cikin ɓacin rai ta ƙira sunan..


Ayush ɗagowa tayi da manya-manyan idanuwanta waɗanda sukayi jaa, har yanzu ta kasa gane ko wacece,
matar hannu tasa ta ɗage liƙab ɗinta sama,
a razane Ayush tana kallon matar ta tashi zaune tareda faɗin "Umaa! Uma kece daman kika zo.."


Ayush tashi tayi da gudu ta nufi yanda Uman natan take zata rungumeta, ta riƙo Ayush ta zabga mata mari, tana ɗagowa kuma du ta ƙara zabga mata wani marin ta ɗayan ɓangaren ta saketa ta faɗi ƙasi tana kuka ta riƙe fuskar ta da hannu biyu.......






*ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFINA NA ƊAYA..*


*YA ALLAH KAMAR YANDA KA BANI IKON KAMMALA LITTAFINA NA FARKO ALLAH KA BANI IKON GAMA NA BIYUN*




*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500


*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500


*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login