Showing 90001 words to 93000 words out of 139707 words
"ok kinyi ƙoƙari fah, na gaishe ki.." tana kaiwa haka ta juya ta cigaba da yin haɗin kayan abincin da take son ci..
ran Laila ne yayi matuƙar ɓaci tace "ke matsiyaciya banda ƙaddara mai Yayana zaiyi dake ma har yake wani nace miki, idan kinga budurwarsa haɗaɗɗiyar balarabiya sai kin kama baki saboda ta fiki komai, kuma nazo naga kinata shishshigi wa Oga Junaid, toh wai ke banda ƙwacen samarin mata ba abunda kika iya ne? kin ƙwace wa Maimoon Doctor Hasheem sannan nima kina shirin ƙwace mun Junaid to ina zaki kai su...."
Ayush juyo wa tayi tana dariya,
dariya sosai take yi har da kama ciki,
kuma darinyan yayi matuƙar mata kyau tinda take bata taɓa yin dariya irin ta yau ba duk da damuwar da take ƙunshe dashi haka ta cigaba da yin dariyan tana nuna Laila da yatsa, da ƙer ta iya dakatar da dariyan ta kama kugu tana juyawa cikin salo kamar wacce take gaban namiji tace "toh ya kika ganni! shin akwai mata macen data fini komai? gaskiya bana tunanin haka domin inda ace yarinyar can ta fini komai da Doctor Hasheem bai gujeta ya koma kaina ba, kodai farin jini nane yayi yawa haka, wow gashi inata rikirkita mazan mutane wasu suna barin ƴan matan su suna dawowa kaina wooo ni Gimbiya Mayushert Ɓingel Abbanta ta ƙarasa maganar tana ƙwashe wa da dariya.."
Baƙin ciki duk yabi ya ishi Laila ji take kamar ta shaƙeta , ta ja dogon tsuka tana faɗin "da ba'a san asalin ƙarago ba sai ya ce shi ɗan kamfani ne, meye haɗinki da masarauta har kina ƙiran kanki da wani Gimbiya matsiyaciyar banza, to inaso ki sani Oga Junaid yafi ƙarfin ki, gwara ma ki kama Doctor shima manage zaiyi da ke wannan kuma ki kiyayi haɗuwar ki da Maimoon domin kararayaki zata yi, munafukar banza son maso wani ƙoshin wahala..."
Ayush murmushi tayi sannan tace "eh naga alama Yaya Junaid yana matuƙar ƙaunar ki tinda har kika bashi abinci a baki yaƙi ci ya kawar da kansa gefe idonsa kuwa akaina.."
Kawar da kai Laila tayi gefe cikin takaici ta nufi gurin electric gas ta tsaya sannan ta kunna! idonta yayi jawur ga hawayen dake tsiyaya daga cikin eyes ɗinta tace "idan kina son ranki da lafiyarki ki rabu da Oga Junaid domin shiɗin nawa ne...."
ita ma Ayush matsowa daf da Laila tayi ta zazzaro manya-manyan eyes ɗinta sannan tace "idan kuma naƙi fah?..."
Laila ce ta hura iskar bakin ta sannan ta juyo a wahalce ta cafki hannun Ayush ta ɗora akan electric gas wanda ya yi jaaa kunnawan da tayi,
wani irin ƙara Ayush tayi sai da Mommy da Doctor suka razana da gudu suka sauƙo downstairs kai tsaye kitchen suka nufa,
banda Junaid wanda aka barshi a zaune saman gado, shima saida ƙirjinsa ya buga jin ihun Ayush gashi ba halin tashi balle yaje yaga abunda yake faruwa ba kuma magana sai hawayen da ke zuba daga cikin ƙwayar idanuwansa,
shigar su kitchen suka tarar da Laila ta danna hannun Ayush kan electric taƙi ɗaga hannun,
ita kuwa Ayush har ta fara shiɗe wa da ƙer Doctor ya finciki Laila ya zabga mata mari har sau uku ya jefar da ita ƙasi, bakin ta kuwa ya gagara mutuwa sai cewa take "sai dai ka kashe ni wallahi indai akan Oga Junaid ne, sai na hallaka ta! akan wannan matsiyaciyar zaka dake ni....." ta fashe da kuka.
Mommy kuma rungumar Ayush tayi sosai tana riƙe da hannunta duk fatar hannun ya ƙoƙƙone, sai naman hannun kake gani ta gagara yin kukan ma sai shiɗewar da take yi, ta kwantar da kanta saman kafaɗar mommy....
miƙewa Laila tayi tana faɗin "wannan raɗaɗin da kike ji a hannunki haka nima nake ji a cikin zuciyata da zarar an kusanci Oga Junaid, tana kaiwa haka tayi ficewar ta daga cikin kitchen....
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*
typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
*WhatsApp me 09065443871*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ -------> 79 & 80 <-------
💫✨.
"A gaskiya Laila baki kyauta ba, saboda rashin Imani da kuma rashin tausayi ki ɗauki hannun mutum mai rai ki ɗora akan wuta? ina ganinki mai hankali..."
A wannan lokacin ran mommy yayi matuƙar ɓaci, ta rinƙa surutai tana balbalawa Laila masifa,
cikin ɓacin rai Laila ta tashi tana gunaguni ta yi hanyar waje zata tafi,
ita kuwa Ayush tana can medicine room ita da Doctor yana duba mata hannun...
yana riƙe da hannunta ya gama ɗaure mata shi da bandeji bayan ya yi treat ɗinta,
"kiyi hakuri Ayushert bansan haka zata faru ba wallahi da bazan barta ta biyo ki ba, yarinta ne yake damun Laila! please forgive her.."
murmushi Ayush tayi sannan tace "babu komai ya wuce, nasan duk akan Yaya Junaid tayi mun haka, but shawarar da zan bata shine taso mai sonta, ta daina son maso wani ka sanar mata saƙo daga Ayushert, na barka lafiya..."
ta fizge hannunta da ya riƙe tayi ficewar ta daga cikin room, zuciyarta cike da ɓacin rai,
kuma abunda ya ƙara ƙona mata rai shine abunda Doctor ya gaya mata wai Laila yarinta ne ke damunta,
tana tafe hawaye na zubo mata ta rasa mai ke mata ciwo a jiki,
shigar ta cikin falo kenam ta tarar da mommy zaune tayi tagumi, ganin Ayush yasa tayi firgitt ta tashi tana faɗin "Ayush yadai hannun nakin, anyi gyaran ko mugani.." mommy ta kamo hannun Ayush ta kuma cewa "Allah sarki ki duba kiga fa duk da an manne hannun da bandeji amma wanda ya gani yasan ba ƙaramin ciwo bane...
Ayush tana kwance saman sofa a falo kanta kuwa yana kan cinyar mommy tana mata wasa da sumar gashin ta, Doctor ne ya shugo idon sa kuwa akan Ayush, yana faɗin "toh mommy ni zan wuce, dan Allah ayi hakuri akan abunda Laila ta aikata..."
Mommy tace "ba komai tsautsayi ne, kuma kowa baya tsallake ƙaddararsa,
kayi mata allura ne..?"
"Eh nayi mata allurai guda biyu sai maganin da tasha insha Allahu zuwa gobe zata samu sauƙi.."
Mommy tace "toh shikenam Doctor, Laila ta yi zuciya ta tafi gida, amma ka rinƙa mata nasiha akan sha'anin rayuwa kar ta rinƙa biye wa zuciya domin zata kaita ta baro ta ne..."
Doctor ya amsa mata da "to ba damuwa Mommy insha Allah zanyi iya ƙoƙarina akanta, nagode" cikin girmamawa ya yi mata sallama idonsa kuwa akan Ayush wacce ta kifar da kanta saman cinyar mom ko kallonsa batayi ba...
*****
Sarki Raamud yana zaune a saman gadon su ya naɗe ƙafafuwa kamar mai zaman cin tuwo, ya riƙe hannunsa na hagun, shi kaɗai ne yake jin wannan raɗaɗin da yake ji bayan Ayush!
tafin hannunsa ya yi jawur, ƙonuwar da Ayush tayi ne shima ya shafe shi sai dai shi bai nuna ƙonuwa ba amma gurin yayi jawur dashi,
Bara'at tana zaune daf dashi sai dumama masa hannun take da ruwan zafi, tana faɗin "kayi hakuri shugaba, wannan ciwon nakan lokaci guda ni na rasa gane maka..."
yana ajiyar numfashi yace "meya faru da Ɓingel ɗina? na tabbata akwai wani mummunan abu daya faru da ita.." ya ƙarasa maganar yana duban hannunsa wanda ya nuna alamun ƙonuwa.
Da mamaki a fuskar Bara'atu idonta akan sarki tace "daman Ayush bata mutu ba??"
kallonta sarki yayi da ɓacin rai yace "Ɓingel bata mutu ba, kuma bata cire zoben dish a cibiyar ta ba, idan kuma kinason ganin bayanta bismillah.." ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanya.
miƙe wa Bara'at tayi daga zaune tana zazzaro ido tace "ya akayi hakan ta faru? nidai nasan Ayush ba yanda za'ayi ta bar zoben nan a jikinta indai har Junaid ya mutu, idan kuwa Ayush tana raye to tabbas Junaid ma yana raye..." ta juyo tana kallon sarki da murmushi kwance saman fuskar ta.
Shi kuwa hannunsa yakai ya dafe goshinsa kansa yana sunkuye, murya a sanyaye yace
"Hmmm! Bara'at kenam kina tunanin sarki Raamud ɗin baya kamar yanzu yake, na canza tin daga lokacin da Allah ya nuna mun cewa shi kaɗai ne mai mulki kuma shine mai juyar da komai, haƙiƙa na tafka babban kuskure a rayuwata, na zalinci al'umma wanda bansan iya adadinsu ba,
ga kuma ɗan uwana twins ɗina nine nayi sanadiyar barinsa duniya, ina zan ganshi na nemi yafiyarsa? ga mahaifina shima ni nayi sanadiyar hallaka shi shima ina zan sameshi na nemi yafiyarsa? ga Junaid ina zan kai tarin zunuban da na ɗauka, na tabbata alhakinsu ne yake ta bibiyata,
na rasa komai nawa inada manya-manyan aljanu masu bani kariya sun kai trillions amma gashi tashin farko duk na rasa su..." yana zubda hawaye ya tashi ya tsaya a gaban Bara'at yana faɗin "a koda yaushe mutuwa tana ƙara kusanto ni, za'a iya kawo mun hari a ko wani lokaci saboda bani da mai bani kariya...."
kafin ya kai maganarsa ƙarshe Bara'at ta katse shi da cewa "sai Allah, Allah shine mai bada kariya, inda ace tin farko ka riƙe Allah a zuciyarka da baka shiga wannan halin da kake ciki yanzu ba,
su waɗanda kake tunanin zasu baka kariyar suna ina yanzun? babu su asalin mai bada kariyar ya tarwatsa su kuma shi kaɗai ne mai baka kariya, inda ace bai baka kariya ba da yanzu babu kai a doron ƙasa..."
Sarki Raamud fashe wa yayi da kuka ya rungumi matarsa Bara'at yana faɗin "Allah na tuba ka gafarce ni, na aikata babban kuskure, ɗiyar dana haifa a cikina ma gudu na take.."
suna cikin wannan halin suka jiyo kukan mujiya 🦉🦉 a harabar masarautar.
jin hakan yasa sarki ya zabura yana faɗin "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, *MUNAFURR* yazo shi.."
Bara'atu ta ɗago tana kallonsa ido sunyi zuru-zuru tace "wa ne ne Munafur ku ma.." ta ƙarisa maganar cikin ƙinƙina baki na kakkarwa, ita tsoronta kar a farmake su..
Sarki Raamud jan hannunta yayi yace "muje mu.."
suka nufi wajen masarautar,
a falon masarautar suka tarar da Munafur a gaban Damusa Sujjur yana shafar gashin bayansa tare da rera waƙar isgilanci,
Munafur wani mutum ne mai hatsarin gaske kuma mungun maciji ne, idanuwansa baƙi ƙirin ne ƙananu na maciji, hatta sumar gashinsa zirin macijine ƴan ƙananu, duk yanda ya taka maciji ne yake fitowa, farin mutum ne irin buzayen nan yana tafe da sandarsa mai ƙiran maciji kuma sandar zai iya komawa macijin gaske!
Munafurr ba'a haɗa ido biyu da shi domin makance wa mutum zaiyi.....
Bara'at ganin yanda mutumin yake a take ta faɗi sumammiya,
shi kuma Sarki Raamud farin ƙyalle ya nema ya ɗaure idonsa dashi gudun kar ya haɗa eyes da shi,
Munafur cikin salo ya yi wani irin juyi ya zauna akan kujerar mulki wanda inba sarki ba babu wanda ya isa ya hau kan kujeran nan,
ya tintsire da wata iriyar dariya mai kama da kuka yana faɗin "Masarautar Maƙarƙashe daga yau ya zama nawa!!!
daga yau na koma Sarki Munafurr...."
gaban Sarki Ramud ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, ya durƙusa gaban Munafur yana faɗin "Munafur taya hakan zata faru? bayan ban sauƙa akan mulkin ba.."
wani irin kallo Munafur yake yiwa sarki Raamud yana jujjuyar da kansa, cikin dirarriyar murya yace "haka naso kuma haka naga dama, wannan masarautar ta zama na Munafur..."
Sarki Ramud cikin ɓacin rai yace