Showing 135001 words to 138000 words out of 139707 words

Chapter 46 - Matar Damisa book Complete by Asmita .txt

Asmeetah   

16 Dec 2024

9959

Ajiyar zuciya Hasheem yayi sannan ya ɗago yana kallon Maimoon cike da mamaki yana maganar zuci "wai yaushe yarinyar nan ta canza haka ne? duk irin son da take mun amma yau itace take gaya mun maganganu har da zagi?..."


katse masa tunani tayi da cewa "malam Hasheem kaban wayata na ƙira iyaye na su zo su fidda ni daga cikin wannan akurkin ɗakin kajin ku...."


ƙayataccen murmushi yayi yana kallon kyakykyawar fuskarta sannan yace "baza ki bar gidan nan ba har saikin warke gaba ɗaya..."


a fusace ta jefa masa pillow tana faɗin "ƙarya kake wallahi mungu kawai Azzalumi, ai ɓoyeni dakayi bashi zai sa asirinka ya rufu ba, wallahi saina bazawa duniya cewa kai ɗan ta'adda ne mai yiwa mata fyaɗe..." ta ƙarasa maganar tareda fashewa da matsanancin kuka.


shi kuwa girgiza kai yayi sannan ya tashi yabar ɗakin tareda murɗa key ya rufeta, daman already an kawo mata abinci da kuma ruwan sha..


bazai iya juran kalaman Maimoon ba, tabbas yasan yanzu ta tsane shi shi kuwa har yanzu tana cikin zuciyarsa, yana son maimoon sosai abunda ya faru kawai tsautsayi ne da ƙaddara, kuma tausayinta yake ji..


yana zuwa harabar gidan ya tarar da Laylah tana tsaye a jikin motar,
shigewa sukayi ya tada motar suka tafi....
(to sai mun haɗu a gidansu Junaidu...)


shima Doctor Hasheem ba ƙaramin kyau yayi ba, yasha gizna sky blue da hularsa shima sky blue, ga kuma takalminsa mai sawu ciki shima kalar kayan, sai ƙamshin turare yake ga kuma ƙamshin gizna shima yana bada nashi ƙamshin, domin sabin kayane bai taɓa saka su ba..




☆☆☆☆☆☆




mutane har sun fara hallaruwa, sai shugowa ake da wasu manya-manyan motoci maka-maka, zafafan mutane ne suke fitowa daga cikin motocin masu kuɗin gaske, da ƴanmata kala-kala,
ƴan uwa daga wasu garuruwa har sun ƙaraso wasu daga ƙasar waje,
abun baƙin ciki shine babu ƴan uwan mahaifin Junaid ko ɗaya, abun yana masa ciwo sosai a ransa, hakan yasa bai damu da ƴan uwan Mommy ba, saboda kullum mitarsu akan ba'a san asalin mahaifin Junaid ba,
kuma ba'a son ransu Alhaji Junaidu ya haɗa Auren ɗiyarsa Doctor Fatima da kuma mahaifin Junaid ba...


Junaid yana tsaye a gaban madubi yana sanye da gajeran wando da farar singlet ya gama kimtsa jikinsa tsab sai ƙamshin turare yake, ya gyara sumar kayinsa ya kwanta luf-luf har waran kafaɗarsa..
yanzu iya kaya kawai zai saka shima an kawo masa yana ajiye akan gado,


yana tsaye yaji an zagayo da hannaye ta gabansa, ta cikin madubi ya ga Angel ce ta kwantar da kanta a bayansa tana kuka,
riƙo hannunta yayi ya zagayo da ita ta gabansa ya riƙe haɓarta sannan ya ɗago da fuskarta sama suna kallon juna yace "meyasa kike kuka?.."


murya na rawa tace "Mommy ta sanar mun baikon da za'a maka kai da Ayushert, ta gaya mun komai.."


rungumarta yayi sosai a jikinsa yace "sorry my Angel, nasan zakiji wani abu a ranki koh?.."


ɗagowa tayi tana kallonsa tace "Mommy ta fahimtar dani komai, saboda haka ba abunda naji a raina saima ƙarin farin ciki, Ayushert tana masifar ƙaunarka kuma kaima nasan kana sonta, ni daman bansa a raina cewa zan Aureka ba, ni dai abunda na sani shine ina sonka..."


murmushi yayi sannan yace "ina ji da ke my Angel, and i will never forget you in my life, we will stay together forever..."


Kuka ne yake shirin kuɓuce mata ta ƙwantar da kanta saman ƙirjinsa,
yace "abun kunya ne naga soja tana kuka..."


kwashewa tayi da dariya tana dukan faffaɗar ƙirjinsa tareda faɗin "ai ɓangaren aiki da ban, ɓangaren soyayya ma daban,
my man! ina tayaka murna sosai, Mommy ta ce da zarar anyi baiko za'a yanke ranar bikinku, amma shawarar da zan baka shine ka daina hurting heart ɗin Ayushert saboda naga macece mai haƙuri da hankali, kuma she is a younger lady tayi dai dai da rayuwarka kuma kunyi matuƙar dace wa da juna, amma kaje ka ƙwaso waɗancan tsofin ina zaka kaisu marasa ɗa'a da tarbiya, daman ni babu maganar Aure a bookless ɗina...."


ɗago haɓarta yayi yana faɗin "daman yaudarata kike yi?.."
tana dariya tace "see this man wai yaudara..."
suka haɗe goshinsu guri ɗaya suna dariya,


Angel ta ture shi tana faɗin "lokaci fa zai ƙure naga mutane har sun taru, ta nufi gaban gadonsa ta ɗauko kayansa,


daman ita ta kammala shirin ta, tana sanye da doguwar riga Abaya milk mai duwatsu a jere daga sama har ƙasa ta gaban rigar, tayi rolling gyalen rigar a kayinta sai tudun sumar gashinta da ya fito kamar wacce tayi acuci maza sakamakon tuƙeshi data yi,
ƙafarta tana sanye da farin thorns mai ɗan tudu, Angel ta fito tayi kyau sosai tayi shigarta na musulmai, kamar balarabiya haka ta fito ga ta farinta ɗan dai dai ruwan tarwaɗa domin bata kai sauran haske ba, ko rabin Ayush bata kai haske ba balle su Aunty baturiya da Aunty china, daman Angel asalinta ƴar misrah ce amma kuma iyayenta ba musulmai bane, aikin soja ya kaita ƙasar California, yanda iyayen Ayush suke, kuma Angel ta tafo da tarin bayanai akan su...


a gurguje Angel ta taya Junaid ya saka kayansa, suit ne masu kyan gaske baƙaƙe da kuma farar riga ta ciki mai dogon hannu, ta ɗaura masa wannan abun wuyan nan na ado (na dai manta sunansa🙄).


ya saka takalminsa baƙi na kayan, ga kayan yanda suka kama jikinsa ya fito yayi kyau sosai, sumar kansa har wani sheƙi yake ya yi laushi yanda kasan gashin jarirai har kafaɗarsa,
fuskar nan yayi fari sol,
Angel ce ta sanya masa agogon hannu sannan ta ƙara feshe shi da turare..
(ku hasasho yanda Junaid yake domin bazan iya tsara irin kyan da yayi ba, nadai tsara shi kaɗan😹😹)..


Bayan sun kammala Angel ta miƙa masa new phone ɗinsa tace "ga saƙon Mommy tace na baka, sim ɗinka yana ciki.." da murmushi a fuskarta ta kuma cewa "my man kayi kyau sosai saika fito kamar ɗan indian.."
hannu ya kai ya kamo lips ɗinsa yace "zan cire bakin maganar fa..." suna dariya da haka suka bar ɗakin, tace masa "kai na gama shirya ka, kaje abokanka suna jiranka, sauran ita Ayushert zanje itama na shirya ta..."


murmushi yasau mata ba tareda yace komai ba ya sauƙa downstairs, ita kuma ta wuce ɗakin Ayush...


Angel tana shiga ɗakin Ayush ta tarar da abun mamaki, baki ta sake tana kallon Ayush wacce take ta shan baccin ta ko wanka batayi ba, gashi har an taru,
sai kuma ta tuno da maganar Mommy yanda take cewa Ayush bata san da maganar baiko ba amma kar a sanar mata anaso ayi mata bazata ne!!!


rufe ƙofar ɗakin Angel tayi sannan ta nufi yanda Ayush take kwance saman gadonta, zama tayi a bakin gado tana bubbugar sawayen Ayush a hankali,
a gigice Ayush ta tashi tana faɗin "dan Allah kayi hakuri Yaya Junaid wallahi bazan sake ba, wayyo Allah nah....."

zaro ido waje Angel tayi tana kallon ta cike da mamaki tace "sorry ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru da ke.."
Ayush tashi tayi zaune tana kallon Angel har ta haɗa gumi,
ta kwanta ne da tunanin yanda taga Junaid yana dukan Adity kamar bazai barta da rai ba, tayi tsammanin yayo ta kanta ne yanzun,


da murmushi a fuskar Angel tace "daman mommy ce ta turo ni akan nazo na shirya ki, kinji hayaniyar mutane har sun taru a guest house...."


Ayush tsaya wa tayi tana kallonta cikin rashin sanin ko ita wacece,
batayi tunanin Angel bace saboda tasan su ɗin ba musulmai bane ita kuma wannan da shigarta na musulmai,
Angel ce ta katseta da cewa "ki hanzarta ki shiga wanka yanzun nan, please.."
tayi hakan ne domin tasan dole za'a nemeta a wajen taron kuma yanzu kowa ya shirya ita kaɗai ta rage,
Ayush tana shirin tashi saiga mommy ta shugo tana riƙe da doguwar riga wedding gown da takalmanta da sarƙoƙin wuya, ganin Ayush a haka yasa mommy ta tsaya cak tana kallon Ayush tace "subhanallahi Ayush daman bakiyi wanka ba? dan Allah ki hanzarta yanzu kowa fa ya hallaru acan guest house, shima Junaid an ƙira shi sun tafi da abokansa, nima yanzu can zan tafi saboda akwai gabatarwar da za'ayi,
Angel yanzu zan turo muku wata inyaso saiku shiryata ku biyun zakufi sauri...."
Mommy tana kaiwa nan ta ajiye ledar kayan sannan ta juya da sauri ta fita,
itama mommy ba ƙaramin kyau tayi ba a cikin wata danƙararriyar gizna water fruit mai tsadar bala'i tasha ɗinkin doguwar riga ya baje sosai har jan ƙasi yake, ta hau takalmi mai tudu yanda tsayin rigar zai ɗan ɗage,
ga anyi mata zigzar wuta a giznar mai style, ta ɗauko gyale water fruit shima mai duwatsu, tasha makeup sosai tayi matuƙar kyau, ga sarƙar ya zauna mata a wuya kamar wanda aka ƙeroshi dan ita, ga ba ƙashin wuya ko ɗaya,
sai ƙamshin turaren da yake tashi a jikinta,
(nifah mommy tafi burgeni yaciin😘)...


Ayush jin mommy ta ambaci sunan Angel yasa ta tsaya tana kallonta,
Angel kamar zatayi kuka tace "kiyi sauri mana Ayushert, muma fa munaso a buɗe taron damu, please too pass..."


haka ta tashi da sassanyar jikinta ta nufi toilet, ita har cikin zuciyarta bata kawo komai a ranta ba,
bata san da maganar baiko ba..


♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎


Anan fa ake taro na manyan mutane, kowa yana zazzaune a kujerarsa da lemuka kala-kala a gaban kowa,
ta can saman hall kuma tsararrun kujeru ne a jere na mutane namusamman, Mommy tana zaune akan ɗaya daga cikin kujerun sama, sai ta gefe kuma Rumana ce tasha rigar kanti wato riga mai haɗe da dogon wando, kayan roba ne amma jikinsa duk gashi-gashine mai colour purple, hannun rigar kuma ɗaya mai dogon hannune ɗaya kuma gajeran hannu ne, amma kuma wandon ta ƙasi a baje yake, rigar tayi kyau sosai kuma itama mai rigar tayi matuƙar kyau ga farin gashintan nan ta kwantar dashi har gadon bayanta, ga goshinta kuwa ta 6angare guda yayi jaa yanda Junaid ya wurga mata wayarsa, ƙafarta kuwa tana sanye da takalmi thorns mai tsinin gaske, dan dai sun iya tafiya da takalmin amma idan mu mukasa kam ai sai dai mu karya ƙafarmu...


ta ɓangare guda kuma Adity ce take zaune itama tayi kyau a cikin wata baƙar riga dogo har zuwa gwiwarta mai ɗinkin bubaa da dogon wandonta mai fela ya ɗan baje ta ƙasi, ta toshe da baƙin glass a idonta, sumar gashinta kuma ta kwanto wani ta gaba, itama takalmi mai tudu ta saka,
can jikinta kuma a farfashe da zaku cire rigar 🤣,


sai kuma wasu manya-manyan ogannin sojoji,
ta tsakiyan kuma doguwar kujera ne yasha kwalliya an tanadar wa Junaid da Ayush ɗinsa...
warai ya cika da zafafan mutane duk kuma sunada pass a hannunsu,
wani irin ganga ake bugawa mai ratsa zuciya da kuma sojoji masu hura sarewa, abokanan Junaid ne suka rinƙa tashi ɗaya bayan ɗaya suna gafatar da kansu tareda jawabai na musamman da kuma murnar samun lafiyarsa..


Mommy ce ta taso itama ta bada cikakken tarihin Junaid da irin gwagwarmayar da suka sha kafin ya samu sauƙi,
wasu har da kukan su tsabar tausayi,
Rumana da Adity duk ba wacce bata zubda hawaye ba, sannan Mommy ta sanar wa al'umma cewa yau ne ranar Baikon Junaid tareda wacce yake so kuma zai Aura nan da wasu ɗan kwanaki kaɗan...


dake da turanci mommy take magana duk ba wacce bata razana ba acikin ƴanmatansa su biyu wato Rumana da Adity,
Laylah itama tana zaune a kusa da Yayanta Doctor Hasheem tsabar rikicewa da sauri ta miƙe tsaye daga zaune,
Doctor ne ya riƙo hannunta tareda zaunar da ita yana girgiza mata kai,
tinin ƙwalla har ya soma gangaro wa Laylah..


mutanen waran ne suka fara tafa hannayensu cikin farin ciki da jin daɗin lamarin,
tare da buga ganga mai bada sauti, komawa mommy tayi ta zauna cikin jin daɗi, duk a cikin manya-manya mutanen nan ba wanda bai tashi ya sanyawa Junaid albarka ba da kuma nuna masa farin ciki..




saida aka gama gabatar da kowa kafin aka buƙaci ganin Amarya domin su sanyawa junansu zoben ƙauna,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login