Showing 102001 words to 105000 words out of 139707 words
kowa yasan ka mutu, ganin haka yasa Ayushert itama tayi ƙoƙarin kashe kanta, gata nan a ƙwance, har anzo za'a maka wanka ka tashi, ya za'ayi kowa bazai yi gudunka ba, shin kasan irin tsananin jinyar da kayi ne? ko motsawa baka iya yi, gashi lokaci guda ka tashi bayan doguwar sumar da kayi, toh yanzu kaji dalilin da yasa mutane suke guduwa maka..."
Hawaye ne yake zuba a ido Junaid yana karkaɗa kai ya maida kallonsa kan Ayush, yakai hannunsa yana shafar fuskarta...
ita kuwa Mommy ƙarewa Junaid kallo take gaba ɗaya ya canza mata, kamannin mahaifinsa sun fito a fuskarsa, har tsayin gashin kafin ya aske, da kuma ƙirar jiki na jaruman sarakuna,
hawaye ne ya fara gangaro wa mommy, tana kallon Junaid da suffar mijinta,
Bata taɓa ganin fuskar mahaifin Ayush bane amma fuskar Junaid yafi kama dana Sarki Raamud,
(kodan saboda tsayin gashin Junaid ne yasa nake ganin haka oho😅)
duk da mahaifin Junaid da kuma mahaifin Ayush twins ne masu kamanni iri ɗaya shiyasa bazaka banbanta kamannin wa yaran suke yowa ba,
inka lura Ayush da Junaid suna ɗibar kama, Mommy ta daɗe da fahimtar haka sai dai bata kawo komai a ranta ba....
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*
typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*Laifin Daɗi qarewa*
*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*
*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*
*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*
*OR*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*
*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ ------->87 & 88 <-------
******* Daƙer Mommy ta lallami Junaid yake cin abinci, ita da kanta take feeding ɗinsa ko loma biyar baiyi ba yace "na ƙoshi da tuwon ni milk nake so" Mommy tace "bazaka taɓa ferfesun kifin bane?" kawar da kai gefe yayi sannan yace "idan naci kifi ba halin shan milk, ni kuma idan ban sha milk ba bazan ji daɗin baki na ba.."
Ajiyar zuciya Mom tayi sannan tace "toh ga kayan fruits yanda na haɗo maka"
tasan indai yasha milk bazai buƙaci wani abu ba,
taɓe fuska yayi ya ɗan turo ƙaramin bakinsa yana kallon haɗin fruits, yana yatsine fuska yace "indai ba milk ba bana son komai." Mommy tana jinjinawa wannan miskilanci na Junaid ba yanda ta iya dashi haka ta buɗe murfin flask tana tsiyaya masa milk mai kaurin gaske a glass cup tace "to gashi nidai in har zaka ƙoshi ai ba wani abun tada hankali.."
Hannu ya miƙa ya karɓi cup ɗin milk, idonsa kuwa yana kan Ayush wanda har yanzu bata farfaɗo ba..
Kai ya kifa yana kurɓan madaran, a hankali yake motsa sweet lips ɗinsa, da haka har ya shanye,
bayan wasu mintuna suka ji anata ƙiraye-ƙirayen sallar mangarib, Mommy ta kalli Junaid sannan tace "kaje kayi sallah daga nan kuma saika wuce gida kaima ka kwanta ka huta ko..?"
girgiza kai yayi sannan yace "bazan yi nisa da Yushert ba a halin nan da take ciki, zan zauna tare da ita har Allah yasa ta farfaɗo, kula da ita ya rataya mun a wuya..." ya ƙarisa maganar tareda miƙewa tsaye ya kuma cewa "zanje nayi sallah amma kuma zan dawo.."
Jijjiga masa kai kawai Mommy tayi ta kasa cewa komai,
har saida Junaid ya fice daga room ɗin kafin Mommy ta kawar da kanta daga kallonsa da take, ita har yanzu ta gagara gasgata wa shin Junaid ɗinta ne ko kuma sauya shi akayi aka maido mata da mai siffar mijinta, haka ta wuni tana wannan tunanin, dogon numfashi taja tareda sa hannu tana buga goshin ta alamar ciwo yake mata, daƙer ta iya motsawa ta tashi tana jan ƙafa da haka ta shige toilet ta ɗauro alwala, sannan tasa hannu ta murɗe mariƙar ƙofar toilet ta fito tana jero addu'o'i,
ƙarisa shugo wa cikin ɗakin tayi tana hamma tasa hannu tana kare bakinta ido a lumshe, tsananin bacci ne yake damun ta, ga yunwar da take ji! shimfiɗa sallaya tayi ta zura hijab ɗinta sannan ta tsaida sallah, har tayi nisa cikin sallar ta taga wani irin haske ya bayyano, haske mai kashe ido, tsabar tsananin ƙarfin hasken nan Mommy tana sallah ta ƙanƙame idonta sosai kuma Allah bai nufe ta da katse sallar ba haka ta cigaba da yinsa ido a rufe,
irin hasken da ya taɓa fito wa Ayush lokacin da ta ajiye littafin tarihi a ƙarƙashin gado shine ya ƙara fito wa a yanzu ma,
wani mutum ne ya bayyana a cikin hasken nan, shi ba mutum ba kuma shi ba biri ba, gashi nan tsayayyen mutum ne jikinsa duk gashi, daga kayinsa zuwa fuska har wuya irin na biri ne sak sai tarin gashi sannan yana da jelaa!!!
Wannan shi ake ƙira da *NARASIMHA* mai bada kariya a masarauta, tsohon biri kuma ƙirƙirarren tsafin Sarkin Zaid wato Mahaifinsu Sarki Raamud, baya cutar wa aikinsa shine temako da zaran an nemi temakonsa, har iyau a masarauta yake zaune yana rayuwa ne a cikin madubin tsafi,
NARASIMHA Amanar Sarki Zaid ne, yana kallon duk tsiyar da Sarki Raamud yake aikatawa har Allah ya kawo ƙarshen ta'addanci,
A yanzun ma an turo shi ne don yazo ya temaki Ayush, bazata iya tashi ba har saida temakonsa,
hannu yasa ya yi wa Ayush ɗaukan luɗa sannan ya ɓace da ita, yana tafiya kuwa hasken ya washe daiden lokacin da Mommy ta idaar da sallah da sauri ta miƙe tsaye a ruɗe tana ware manya-manyan eyes ɗinta, ta waiwayo bayanta a tsorace ganin gadon da Ayush take ƙwance wayam babu kowa a kai taja da baya a kiɗimai ta dafa ƙirjinta tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, ina Ayush take, wayyo Allah na.." ta fara kuka tana surutai ta fara dudduba wurare tana ƙiran sunan Ayush amma shuru ta leƙa ƙarƙashin gado bata ga kowa ba ta nufi toilet da gudu tana ƙwalla mata ƙira nan ma babu kowa, ganin bata ganta ba yasa ta saddaƙar tasan wannan hasken data gani ne ya ɗauke ta, zama tayi a bakin gado tana kuka ta kifar da kanta saman pillow..
tana cikin wannan halin taji an turo ƙofar ɗakin a razane Mommy ta ɗago tana kallon wanda ya shugo, a tunaninta Ayush ce! da sauri Junaid ya ƙarasa shugo wa ya zauna a bakin gado daf da Mommy yana faɗin "Mom why are you cying?.." yana riƙe da hannayenta, ya kuma cewa "please Mom ki sanar mun mana, kinsan bana son ganin hawayen ki..."
cikin kuka tace "Ayushhhh."
ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa, juyar da ƙwayar idonsa yayi ta gefen ido ya kalli saman gadon ba tareda ya juyar da kansa ba,
tsabar kiɗimewa har zuwa yanzu bai ɗauke idonsa akan gadon ba sai gumin dake gangaro masa, lokaci guda yaji garin yayi masa zafi, duk da sanyin A.C dake ɗakin amma gumi ya yi masa sharkab, a hankali ya miƙe tsaye leɓensa na kakkarwa daƙer ya iya cewa "Where is her? Mom where is my Yushert?.."
Idonsa ya sauƙar akan Mommy ya durƙusa ƙasi hannayensa suna kan lap ɗin mommy ya kuma cewa "Yushert ta warke ne? ina taje ta? and meyasa kike kuka? kada fa ki sanar mun cewa ta mutu ko an sace ta..." ya ƙarasa maganar yana zaro Manya-manyan eyes ɗinsa waɗanda suka cicciko da ƙwalla..
Mommy ta ɗago da hannayenta biyu suna kakkarwa ta riƙe fuskar Junaid tace "am sorry my son, Ayushert we are lossed her..." kafin ta kai ƙarshen maganar ya katseta da cewa "whattt?" ya tashi a gigice yana ja da baya yana huci yace "Mom yanzu ba lokacin wasa bane, inaso ki faɗa mun ina Yushartttt take..?." cikin wani irin gigitaccen tsawa yake maganar har saida Mommy ta toshe kunnuwanta da hannaye biyu, tana kuka a cikin ranta kuwa tana tunanin taya zata fara sanar da Junaid abunda ta gani, tasan ba lallai ne ya yadda ba..
haka tayi ƙarfin halin taso wa tana faɗin "ka ƙwantar da hankalinka zan sanar maka amma saika nutsu, ta ɗora hannunta saman ƙirjinsa tana bubbuga masa a hankali tana ce masa "kayi haƙuri karka tayar da hankalinka kaga baka daɗe da tashi ba, inaso kabi abun a hankali..."
"toh mom ki sanar mun mana tana ina?.."
Mommy gaba ɗaya ta rikice ta rasa ya zatayi, tana kuka tace "Haske ne ya ɗauke ta.."
cikin rashin fahimta Junaid yake kallon mommy, yamutsa fuska yayi yana mata wani irin kallo yace "bangane haske ya ɗauketa ba, ni ƙwata-ƙwata ban fahimci abunda kike nufi ba, try to understand me please🙏.."
Hukunci ɗaya Mommy ta yanke a ranta tinda har ya kasa fahimtar ta,
rufe idonta tayi ta tafi luuu zata faɗi ƙasi Junaid yayi saurin taro ta yana faɗin "Mom! Mom!! Mom please wake up,." yana jijjigan ta amma ko alamar motsi babu, ya ɗauke ta ya kwantar da ita saman gadon da Ayush take kwance before, gaba ɗaya ya ruɗe ya kiɗime zama yayi a bakin gado yana harhargutsa gashin kansa da hannayensa biyu, daga bisani ya riƙe kansa sosai yana kallon ƙasi,
shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji a ransa,
badan ya warke ba babu abunda zai hana ciwonsa tashi...
ita kuwa Mommy da saninta tayi sumar ƙarya saboda ta tsira daga tashin hankalin Junaid da kuma yawan tambayoyin da zai biyo baya wanda bazata iya amsa su ba..
yana zaune yana tunanin neman mafita ga babban damuwarsa shine aina zai ga Ayush? shin farfad'owa tayi ne ko kuma sace ta akayi?,
abubuwan nan suna masa yawo a kwakwalwarsa, tunaninsa yana shirin juyewa,
tashi yayi da sauri kamar wanda aka zabure shi ya nufi hanyar fita daga cikin room d'in,
Bayan fitarsa kuwa bud'e ido Mommy tayi tana ajiyar zuciya tare da dafa 'kirjinta tana fad'in "washh nagode Allah dana tsiratar da kaina, domin nasan wannan yaron inya dinga mun kururuwa har saina shiga uku, bansan mezance masa akan Ayush ba, nima kaina bansan meya faru da ita ba, hasken daya bayyano ma ban iya ganinsa ba balle nasan abunda ya faru, wayyo kaina Ina aka kaimun Ayush d'inta..." ta 'karasa maganar tana kuka,
jin motsin mutum yana shirin turo 'kofa ne yasa Mommy tayi saurin kwanciya ta koma yanda take daman tayi tunanin Junaid ne,.
Shi kuwa Junaid da sauri ya shugo kamar zai fura yayo kam Mommy da wasu manya-manyan Allurai a hannunsa , yana tsaye yasa Allura yana zu'ko ruwan magani dake cikin 'karamin kwalba,
Mommy ido d'aya ta bud'e tana kallon abunda Junaid yake shirin yi,
juyo wa yayi yana daideta dantsen hannun Mommy, yazo zai burma mata Allura tayi saurin ri'ke hannunsa ta d'ago tana fad'in "ha'a Junaid ya rayuwarka a haka, ya za'ayi baka karanci 6angaren likitanci ba kace zakayi wa majinyaci Allura.."
Junaid tsayawa yayi ya wani tur6une fuska yana kallon Mommy hannayensa a goye ta gaban chest d'insa, shi gaba d'aya ya rasa mai zai ce mata,
Ita kuwa hannu tasa ta kar6i 'kwalbar maganin tana duba wa, sai ji yayi tace "subhanallahi, Junaid ai wannan maganin family planning ne na Allurarsa, kuma hakan ma yayi expired..."
'Dagowa tayi ta kalle shi tana turo masa baki kamar wata yarinya,
fuskarsa a tur6une yake kallon Mommy cikin yanayin tausayi yace "Mom Yushert rayuwata ce, meyasa kike son wasa da rayuwata, kodai kinaso nayi asalin mutuwa ne?.."
Girgiza kai Mommy ta shiga yi tana fad'in "a'a ka kwantar da hankalinka, Ayush zata dawo soon..."
kafin ta 'karasa maganar ya katseta da cewa "Mom bangane zata dawo soon ba, shin ina taje? abunda nake son sani kenam!."
itama Mommy ta koma kalar tausayi, domin ba 'karamin matsala take ciki ba,.
mi'kewa tayi ta kamo hannun Junaid tace "muje.."
amsa mata yayi da "Ina.." tace "gida mana"
fizge hannunsa yayi yana fad'in "I will not going anyway without Yushert.."
Bata tamka masa ba saima d'aukar wayar ta datayi tana dialing number ma'aikatan asbiti tana sanar musu abunda ya faru da Junaid na cewar bai mutu ba doguwar suma yayi, ta kuma sanar musu da su dawo bakin aikinsu saboda majinyatan da suke nan,