Showing 15001 words to 18000 words out of 139707 words
ki taimake shi........!
Tana kaiwa karshen maganar ta 6ace 6attt.
A firgice Ayush ta tashi zaune tana fad'in "Umaa! Umaana!! Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, mafarki Ayush tayi kwanciyar da tayi tana kuka ashe bacci 6arawo yayi awun gaba da ita, zuwan da mahaifiyar ta tayi acikin mafarki ta zo mata.
Ta waiwaya ko Ina bata ga kowa ba ga hawayen da ya bushe mata akan fuskar "tabbas mafarki nayi, Uma tazo mun" a lokacin ta fara tariyo maganganun mahaifiyar tatan lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, Junaid ne ya fad'o mata a rai "Uma mutumin da ya rabaki da rayuwarki shi kike so na taimaka?" Kuka ne ya kwato mata sai wani tunani yazo mata a cikin zuciyarta take fad'in "Mahaifiyar shi ta taimake ni, ba don ita ba bansan Ina zan nufa ba, shin itama tana raye ne ko ta mutu? Tabbas suna bu'katar taimako a wannan halin" ta mi'ke tsaye cikin sauri lokaci guda kuma ta tsaya cakk
Alamar ta tsaya tunanin wani abu "amma meyasa naga shi wannan mutumin a manne da jikin gini ba tare da an d'aure shi ba, kuma jikinsa a faffashe kamar ma ya mutu"... 'Kirjinta ne yayi wani irin bugawa ta zabura da gudu ta nufi hanyar d'akin takawa d'aya biyu taji kamar an ri'ke 'kafarta ta doku a 'kasi danma carpet ne mai gashi da tunin taji ciwo,
Tana shirin d'agowa kunnuwanta suka jiyo mata kukan mujiya π¦π¦ mai firgitarwa a tsorace ta kalli saman cilling yanda ta jiyo kukan kenam, wutar nepa gidan ne ya d'age sai duhun daya biyo baya ko hannunta bata iya gani wani irin tsoro ne yabi jikinta, kamar daga sama tajiyo wata 'katuwar murya ana cewa "AYUSHHHH KADA KI KUSKURA KI TAKA 'DAKIN NAN, WANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA ZAKI TAIMAKA? TO LALLAI KEMA ZAI KASHE KI KAMAR YANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA, KIYI TUNANI SHI BA MASOYINKI BANE MAKIYINKI NE, YANA NEMAN AHALINKU NE DOMIN YA GAMA DA RAYUWAR KU GABA DAYA HAHAHAHA, HAHAHA, HAHAHAHA haka ta ringa jiyowa dariya marar dad'in ji,
Jikinta ne ya hau 6ari murya na kakkarwa tace "waye Kai?"
"NIIII MAI BAKI KARIYA NE, still ya 'kara tintsirewa da razananniyar dariyar shi mai ban tsoro....
Lokaci guda kuwa haske ya bayyana ta daina jin kukan mujiyan.
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'unnn wannan wani irin bala'i ne a cikin gidan nan, Aljanu da mutane duk suna rayuwa a gidan nan" zuciyarta ne ta soma magana kamar haka "Ayush kar ki manta wannan Addu'ar da malamin nan ya koya muku ke da mahaifiyarki" anan ta tuno da Baba tsoho wanda yayi hijira zuwa dajin da suka zauna yayi tsawon shekara biyar atare da su, Babban malami ne na gaske shi ya koya musu karatun al'qur'ani mai girma tare da addu'oi ya koya musu alwala da yanda ake sallah su wankan janaba da haila ba abunda bai koya musu ba ta 6angaren addini, Ayush lokacin bata wuce 15yrs ba ita kuma mahaifiyarta tana 'kara koyan karatun ne domin wad'annan karatuttukan mahaifin Junaid ya koyar mata su tin suna GHANA.
Damuwar dai Ayush ta samu ta koya duk da itama tana koya mata wasu abubuwan!!
Anan tayi firgitt ta soma jero manya-manyan addu'o'i....
π. "Allahumma laa sahla illaa maa ja'altahu sahlan wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan"
(Yaa Allah! Babu wani abu mai sau'ki sai abin da ka sanya shi ya zama mai sau'ki, kuma Kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sau'ki)
"'Kadrul laahi wamaa shaa'a fa'ala"
(Kaddarar Allah ce, kuma abin da Allah ya so, shi ne yake aikatawa, domin da-na-sani tana bud'e 'kofar aikin shaid'an).
"Laa ilaaha illallaahul aziimul haliimu,
Laa ilaaha illallahu rabbul arshil aziim,
Laa ilaaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kariim"....
Bayan ta kammala addu'o'in ta ta shafa ayatul kursiyu, duk wani tsoro da fargaba da 'kuncin zuciya ya wuce mata ta 'kwarin gwiwarta ta mi'ke tsaye ta nufi d'akin da ake bu'katar taimako!
Upstairs ta fara takawa a hankula har da iso bakin 'kofar d'akin tasa hannu zata ture d'akin...
Aka daka tsawa "kada ki kuskura ki bud'e" amma kash duk wannan maganganun kunnen Ayush ya toshe bata jin maganar
Tana bud'e d'akin kuwa wani irin duhu ne a d'akin babu haske kwata-kwata tana shiga d'akin haske ya bayyana ta ko Ina, still yanda taga mutanen nan a kwance haka ta same su
Ta d'aga kanta ta kalli yanda Junaid yake a manne a jikin gini ganinsa yasa ta tsorita naman jikinsa duk ya farfashe ciwon yanzu yafi na d'azu hakan na nufin har yanzu basu daina azabtar da shi ba,
Girgiza Kai tayi tana maganar zuci "bazan iya kusantar ka ba, ka rigada ka mutu". Toilet ta nufa ta d'auko bucket da ruwa a ciki duk bodyguard d'in da suke kwance ta bisu da ruwa tana kwakwkwara musu cikin sa'a kuwa suka tattashi a firgice suna ajiyar zuci, bayan sun dawo hayyacin su kowa rige-rigen fita yake daga cikin d'akin har mai gadin!
Ta dawo kan Mommy itama ruwa ta yayyafa mata, ajiyar zuciya tayi tana Jan numfashi sama-sama tana ambaton "Junaid! Junaid my son, ya mutu ko? Kamar wata zararriya haka take magana tana bin Ayush ta kallo, mommy bata san waye akan ta kawai dai tana sambatu ne,
Ayush ta tsaya tana tunanin aina ta ta6a jin sunan nan!
Tana cikin wannan tunanin tajiyo kukan mommy ya tsananta sosai tana kuka tana nuna gurin da Junaid yake da yatsanta, kafin kace mai Mommy ta tashi da gudu tayi kan Junaid
Da karfin gaske aka hankad'o mommy baya da sauri Ayush ta tareta badon haka ba fad'uwa 'kasi zatayi.
Lokaci guda idon Mommy ya 'kakkafe ta dafe 'kirjin ta tana shure-shure ciwon zuciyar ta ta tashi,
Ayush ta tsorita sosai da ganin haka da kyar ta iya d'ago Mommy suka fita daga d'akin
Falo ta nufa tana zuwa ta tarar da bodyguards duk sunyi cirko cirko kowa yaji jiki sai ajiyar zuciya suke sau'kewa
Da sauri sukayi kan mommy
'Daya daga cikin bodyguard ne ya d'aga mommy cakk yayi waje duk sauran ma binsa sukayi a baya
Motor suka shiga gaba d'ayansu
Motor biyu suka d'auka
Biyu suka shiga d'ayan motor and order car shima mutum biyu a ciki,
Kafin one minute sunbar harabar gidan, iya Ayush da mai gadi kawai aka bari a gidan, da sauri Ayush ta nufi gurin mai gadi tana fad'in "Ina zasu Kai ta?"
In short amsa mai gadi ya bata "Asibity" yana fad'an hakan ya shige cikin d'akinsa zallar tsoro ne a tattare dashi...
"Anya kuwa ba Aljanu a cikin d'akin nan? Junaid kuma? Uma ta ta6a bani labarinta akan Junaid, a'a ba wannan Junaid bane, to aina Zan samu Junaid d'in da Uma take so na taimake shi??
Waye wannan Junaid d'in? Innalillahi wa ina'ilaihi raju'un shi na gani acikin mafarki na idon sa kamar na namun daji,
A'a sharrin mafarki ne bashi bane......
Haka ta rin'ka sa'ke-sa'ke a raanta!...
(KASHH HABA AYUSH KIJE MANA KI TAIMAKI JUNAID MIJIN ASMEETAH πππ )
Yawwa dan Allah masoya kuyi hakuri a bisa jinkirin da ake samu waran yin posting, ba NEPA kullum chaji 100 naira, still i'am a student Ina bu'katar yin karatun exam, still I'm married not a single Ina wasu ayyukan gida da kuma Oga worker π
π
π
π
. Hhhhhh amun uzuri please πππ
*π€ SDEENDTM DATA SERVICESπ€*
*MTN* . *Airtel*
1GB = β¦300. 1GB = β¦350
2GB = β¦600. 2GB = β¦700
3GB = β¦900. 3GB = β¦1000
4GB = β¦1200. 4GB = β¦1300
5GB = β¦1500. 5GB = β¦1600
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = β¦350. 500Mb β¦250
2GB = β¦700. 1GB β¦500
3GB = β¦1050. 2GB β¦1000
4GB = β¦1400. 3GB β¦1500
5GB = β¦1750. 4GB β¦2000
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½
*πͺ08066268951*
*ASMEETAH* *CE* βοΈβοΈβοΈ
*FREE* *BOOK*
ππππππππ
π
*MATAR* *DAMISA* π
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* βοΈβοΈ
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alΖalaminmu Ζ΄ancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
π«π« *{{N W A}}* π«π«
Ψ¨ΩΨ³ΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩ
Ω Ψ§ΩΩΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΩΩΨΩΩ
ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΩΩΨΩΩΩΩ
*BOOK* *ONE*
*PAGE* β‘οΈ23 to 24.
Tana cikin nazarin duniya kamar wacce aka zabure ta tayi cikin falo da gudu kamar wanda taga abun tsoro, daga nan ta haura upstairs ta shige d'akin Junaid, da sauri taje gabansa ta tsaya tana ajiyar zuciya! Still a yanda ta barshi anan ta dawo ta same shi, lokaci guda taji wani irin tausayinsa ya kamata ta wani 6angaren kuma tarin tsanar sa ne acikin kwayar idanunta, bata kaunar ganin fuskar shi sunkuyar da kanta 'kasi tayi tana tariyo lokacin da ya buge mata mahaifiya da kalar wulakancin da ya yi mata itama yaso ya rabata da duniyar a lokacin, zazzafar hawaye ne yake gangaro mata ta d'ago da manya- manyan idanuwanta wad'anda sukayi jawur lokaci guda, kallon tsana takeyi mishi tana maganar zuci "saboda mahaifiya ta zan taimakeka, ba don haka ba ba abunda zaisa na ceci rayuwarka a halin yanzu sai dai ka hallaka! Allah yasa ka mutu" a halin yanzu mutuwar Junaid shine farin cikin Ayushh.
Rufe idonta tayi sosai ta d'ago da hannayenta biyu zata jawo shi, wani irin murya ne mai ban tsoro ya daki dodon kunnen ta
"KEE AYUSH KADA KI KUSKURA KI TA6A SHI, UMARNI NAKE BAKI, KAR KI KARYA MUN DOKATA, YANA CIKIN HUQUBA TA" tan fa ta bara jin kukan namun daji dana mujiyoyi π¦ cikin firgici da tsananin tsoro yasa ta rungumi Junaid ta 'kan'kame shi cikin rashin sani,
(Ita da ake bata dokar kada ta ta6ashi amma tsananin tsoro yasa ta rungume shi gaba d'aya) dogon numfashi yajaa tare da d'ago kansa sama ya bud'e jajayen idanuwansa wad'anda suka canza launi tsabar azaba, wani irin sanyi yaji a cikin zuciyar shi kamar wanda aka watsa masa ruwan sanyi, sakin shi akayi daga sama ya tafo luuuu ya fad'a kan Ayush atare suka fad'o 'kasan lallausar carpet 'Kara Ayush tayi saboda jin yanda Junaid ya fad'o akan ta ga ciwon breast d'inta da ya fame mata shi!
Shi kuwa sai 'Kara narkewa yake ya 'kara 'kan'kameta, shi yasan kalar nutsuwar dayake samu daga gareta ba tare da yasan ko ita wacece ba, haka yake maida numfashi sama-sama!
Guri kuwa yayi tsitt ba alamar motsi sai numfashin da suke ja a tare.
(Ayush itace samun nutsuwar Junaid, itace kuma samuwar warakar sa indai ta samu rauninsa wanda yake jikinta, in har ta kusanci yanda Junaid yake to babu wani abun cutarwar da zai sameshi, a yanzun mah itace ta ceceshi daga azabar da ake gana masa, domin suma kansu Aljanun tsoronta suke,
Ita d'in dai itace AYANAR JUNAID π§ββοΈπ§ββοΈ ).
Dakyarr Ayush ta tattaro iya 'karfinta ta ture Junaid gefe tana mai da numfashi duk ya kashe mata jiki, ta d'ago zata mi'ke ta nufi yanda yake kwance da rarrafe ta Isa waro ido waje tayi tana 'kare shi da kallo abun mamaki duk ciwon dake jikinsa babu shi, jikinsa ya koma normal kamar bashi ne wanda akaita azabtarwa ba babu tabo ko 'kurzune d'aya sai tarin gargasar dake kwance saman kirjinsa,
Abun ba karamin bata mamaki yayi ba aranta take fad'in "Anya ba Aljani bane, nashiga uku nayi gamo" a tsorace taja da baya zata gudu yayi caraf ya ri'ke hannun ta, a hankali yake bud'e idanuwansa yana ganin Dishi-dishi har idon ya washe nan ya sau'ke kyawawan idanuwansa akan ta idon ya washe ya komo fari soll, a hankali yake lumshe ido still hannunsa yana ri'ke da nata a hankali yake motsa 'karamin bakin shi murya Ciki-ciki yake fad'in "Wace ce ke?" Murya na kakkarwa tace "Ni ni ni ni" ta rasa mai zata ce tsabar tsoro kuma lokaci guda yayi mata kwarjini ga wani shakkar sa datake ji! Tana cikin motsa baki ba tare da yasan mai take fad'i ba ya katsar da ita "please can you carry me to go inside bathroom?"
Yayi maganar da harshen turanci, waro Manya-manyan idanuwanta tayi waje tana binsa da kallo, seriously taji abunda ya ce! Duk da batayi karatun boko ba amma ta iya turanci sosai ta koya agurin mahaifiyarta domin Umanta sai data zo Nigeria sannan ta koyi Hausa amma yarenta daga Ghananci sai turanci ta kuma iya yaren French, haka itama Ayush duk ta iya yaren sai dai yaren mahaifinta ne bata iya ba wato fulatanci.......
Ita dai bazata iya maida masa da amsa ba sai dai tayi magana da zuciyarta "How comes Zan iya d'agaka kana nam gardi da Kai, amma sai dai kyakykyawa ne mutumin" tana cikin maganar zuci taji ya ri'kota zai tashi ai tunin ta fad'a jikin shi 'karfinsa ya ninka nata sau goma π
Shima komawa yayi ya kwanta yana binta da kallo, d'agowa tayi a hankali suna fuskantar juna, numfashin su yana dukan na juna, ido cikin ido suke kallon juna! Dakyar Ayush ta iya cewa "you're a