Showing 93001 words to 96000 words out of 139707 words
"hakan bazai taɓa yuwa ba domin wannan masarautar ya fara ne daga tin kakanun kakanun iyaye na kuma haka zai cigaba da tafiya har kan jikanu na, wanda zai mulki wannan masarautar shine ɗan ɗan-uwana koda bayan rai nane......." tin kafin ya ƙarasa maganar Munafurr ya wurga masa sandarsa lokaci guda sandar ta zama maciji ya naɗe wuyan sarki Raamud, ga ido kuma a ɗaure da farin ƙyalle baya ganin abunda ke faruwa...
Munafurr ya kalli Damusa sujjur ya tintsire da dariya sannan yace "jinin yaron da kake son bawa mulkin maƙarƙashe yana jikin Damusaaa...." yana nuna Damusar tare da jann maganarsa cikin salo da isgilanci,
ya kuma cewa "tayaya maƙiyinka zai zamo masoyinka Raamud? shin ka manta da yarjejeniyar da mukayi ne?...." ya ƙara tintsirewa da dariya yana ambaton
"Junaid! Junaid!! Junaid!!! yau kwananka ya ƙare, tinda maƙiyinka ya fara ƙaunarka ai lamarin ya ɓaci, saboda haka zan kashe Junaid tare da shi wannan Damusar, kaima idan kamun tirjiya zan hallaka ka in mayar da matarka baiwa ta..."
Sarki Raamud yana karkaɗa hannayensa alamar bada hakuri, babu halin magana sakamakon sandar macijin daya zagaye wuyansa ya shaƙe sosai ko yawu baya iya haɗiya..."
shi kuma Munafur gashin kansa da ya zama na macizai ne suke ta buɗe baki suna kaiwa sara abun farmaka suke nema,
hannu yasa ya figi ɗaya daga cikin macizain gashinsa ya wurga wa Damusa, macijin ya shige cikin gashin Damusan...
cikin zafin nama Munafurr ya tashi yana faɗin "zan tafi amma zan juyo bada daɗewa ba, ganan Damusar ka ga can Junaidu ka cecesu idan zaka iya...."
yakai hannunsa ya ciro sandarsa daya zamo maciji daga wuyan Sarki Ramud yayi ficewarsa,
kai tsaye harabar masarautar ya nufa yanda wata ƙatotuwar mujiya take a tsaye, girman mujiyar yakai raƙuma haka Munafur yayi tsalle ya hau kan mujiyar suka bar masarautar....
a gaggauce sarki Raamud ya finciki ƙyallen daya rufe idonsa da shi, ya dubi yanda Damusar yake, da gudu ya nufi gurin Damusar yana faɗin "Sujjur! Sujjur!! Sujjur!!! ka miƙe kada ka mutu dan Allah.."
Damusar yana kwance sai shure-shure yake tayi yana shirin mutuwa ga jinin dake zuba a bakinsa, idon Damusar ya koma launin Jaa daga blue...
*****
Ayush ce take taka matakalar beni a hankali, tana ɗangale hannun data ƙone!
ta nufi ɗakinta zata shige ji tayi gabanta yana ta faɗuwa, jikinta ba ƙwari, ɗan tsuka ta ja sannan ta rufe ɗakinta kai tsaye ɗakin Junaid ta nufa...
itama Mommy tana zaune akan sallaya yanda ta idar da sallah bata tashi ba,
ƙirjinta sai bugawa yake yi, gabanta na faman yanke wa,
a hankali tace "mai yake shirin faruwa dani ne?.."
kafin ta kai ƙarshen maganar zucin ta tajiyo ihun Ayush ta ƙwallawa Mommy ƙira,
a gigice Mommy ta zabura tana faɗin
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kunta mina zalimin,
Allahumma ajurni fii musibati wa akhlif lii khairan minhaa...."
Mommy ta gagara tashi jikin ta sai kakkarwa yake sai faman jero addu'o'i take...
Shi kuma Junaid shima ya yi irin abunda Damusa yayi, sai shure-shure yake bakinsa yana bleeding jini, idonsa yayi jawur yana ta kakkarwa,..
Ayush ta durƙusa ƙasi sai faman jijjigar sa take tana ihu...
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*
typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*Laifin Daɗi qarewa*
*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*
*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*
*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*
*OR*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*
*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ ------->81 & 82 <-------
Daƙer Mommy take taka upstairs tana dafe da kanta sakamakon mungun ciwon da yake mata, tura ƙofar ɗakin Junaid tayi da fargaban abunda zata gani, gaban ta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske baki na kakkarwa take ambaton sunan Allah, a ruɗe tayo kan Junaid tana faɗin "yaro na meya sameka haka, na shiga uku nah so ake aga bayanka ba tare da ka aikata wani laifi ba, yaa Allah ya kawo mun ƙarshen wannan mummunan zalincin da ake wa ɗana..."
fashe wa tayi da matsanancin kuka,
ita kuwa Ayush tayi kukan har ta gaji, kifar da kanta tayi saman bed hannun ta riƙe dana Junaid...
Junaid yana kwance jiki ya sake ko motsawa baya yi idonsa sun ƙafe yana kallon sama, duk ya ɓata bedsheet da jinin dake bleeding a bakin sa,
Mommy ta saddaƙar da tayi rashin Junaid ɗinta, zame wa tayi ta zauna a bakin ƙofar ɗakin tana hango fuskar Junaid,
ita ma Ayush tin tinin tasan Junaid ya mutu....
*SAHARA*
warai ne da babu komai sai farar ƙasa ga kuma feshin ƙanƙarar da ake yi, hatta bishiya babu balle ɗan tsuntsu,
sai wani matashin saurayi yana zaune akan dadduma,
(ban iya hango shi ba sakamakon juya mun baya daya yi..)
nadai hango wani makeken Damusa mai launin fari, sai uban gudun da yake ta tiƙa,
bai tsayar da gudun ba har saida yazo gaban matashin da yake zaune, shima Damusar zama yayi a kusa da shi,
ya ɗauki hannu ɗaya ya ɗora kan Damusar yana shafar gashin jikinsa a hankali,
(gulma tasa na zagaya ta gaban matashin dake zaune akan dadduma ga kuma Damusa ta gefensa, na haska shi da camera ta 🧐🧐🧐)
Junaid ne a zaune fuskarsa ta ƙara haske sai sheƙin da yake, ya kalli Damusar sa da kyakykyawar murmushi a fuskarsa yana shafar gashin Damusar tare da faɗin "my Sujjur sauran mana daƙiƙa 5 mu bar doron duniya gaba ɗaya, akwai wacce ruhin mu yake jikinta kuma ta kasa ceton rayuwar mu, Daƙiƙai 5 suna cika indai bata ceci rayuwar mu ba shikenam munyi bankwana da duniya..
wannan maganganun da yake yi a Damusar yake yinsu, shima Damusa sujjur kamar mutum har da hawayensa, Junaid ne ya rungumi Damusan yana ƙirga mintunan da ya rage musu a duniya....
******
a ɓangaren sarki Raamud shima zama yayi a gaban Damusa ya kifar da kansa akan gwiwowinsa ganin Damusar ya daina shurawa ko motsi baya yi, hakan yasa Sarki Ramud ya fidda rai akan Damusar kuma yana takaicin rashin Junaid da akayi domin ya tabbatar shima Junaid ya mutu tinda har Damusar ya mutu,
Bara'at itama kuka take sosai na rashin Junaid da kuma Damusar, tin tinin ta farfaɗo daga doguwar sumar da tayi, tashinta ta tarar da mummunar labari! duk a cikin su ba wanda ya motsa,
Bara'at ce kawai tayi ƙarfin halin cewa "toh yanzun ya zamuyi da Sujjur?"
Sarki Raamud katse ta yayi da cewa "idan dare yayi zanje na bisine shi.."
******
Shigowar malam cikin ɗaki kenam ya tarar da su Mommy a wannan halin,
shima ya dawo ne domin ya duba jikin Junaid, ƙiran sunan Mommy yayi yace "Hajia Fatima, meya farune na ganku a wannan yanayin?.."
shuru tayi ta kasa cewa komai sai idonta da yake kan Junaid,
Shima Malam ganin Junaid yasa gabansa faɗuwa Rassss!
ya nufo gurin da Junaid yake a kwance yana jijjigarsa amma ko motsi babu, hannu Malam yasa ya rufe masa idonsa sannan yaja masa mayafi ya rufe shi gaba ɗayansa yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un,
Kullu nafsin zaa'ikatul maut, kuyi hakuri wanda ya fimu sonsa ya karɓe abunsa, Allah ubangiji yasa can tafi masa nam🙏🙏,
Mommy tana zaune hawaye ne kawai yake go slow akan fuskar ta, daƙer take haɗiyar yawu, zuciyar ta kamar ya fito haka take jinsa...
Ayush ce ta ɗago kanta tana bin Malam da kallo, ga idanuwan ta sunyi lufu-lufu sun kumbura ga sunyi wani irin jaa tsabar kuka,
Miƙe wa tayi ta cakumi gaban gariyar Malam murya a disashe take faɗin
"waya gaya maka Junaid ɗina ya mutu, duk wanda yace Junaid ɗina ya mutu bazan yafe masa ba, ni ce fa zan rigashi mutuwa, ka tasar mun da shi bazai mutu ya barni ba, bacci fa yake yi,....."
Riƙe hannunta Malam yayi yana faɗin "ki kwantar da hankalin ki, kowa ma zai mutu, kema wata rana zaki iso shi idan kwananki ya ƙare.."
daga tsaye ta doku akan gwiwowinta tare da fashe wa da wani irin matsanancin kuka mai raunana zuciya,
a tunanin ta mahaifinta ne ya kashe Junaid, wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarta, lokaci guda taji tsanar mahaifinta bata ƙaunar sa, bata haɗa hanya da mungu!
tashi tayi ta fice a ɗakin da gudun gaske tana kuka,
Mommy baki na kakkarwa tace "Malam a ƙira ƴan uwa da abokan arziƙi a sanar musu mutuwar Junaid, ka ƙira sauran malaman su zo a suturta shi, bana so ayi jinkiri, gidansa na gaskiya yafi nan gidan"
murya a sanyaye take magana tana zaune a yanda take ta kasa motsawa,
Malam yayi ajiyar zuciya sannan yace "haka ne, kiyi hakuri daman Allah ya rigada ya rubuta Junaid yana daga cikin matasan cann.."
hawaye yana zubo wa Mommy tace "Malam idan banyi hakuri ba ya zanyi, ban isa na dawo masa da ransa ba, saboda haka hakuri ya zama dole......"
Mommy bata ƙarasa maganar ba suka jiyo ihun Ayush na lokaci guda,
da sauri Mommy ta miƙe ta fice daga ɗakin,
Malam shima bin bayanta yayi yana faɗin "subhanallah me kuma du ya faru.."
Ɗakin Ayush suka shige suna duba ta ganin babu kowa a bedroom Mommy tace "Ina take kuma, ina tsoron kar a kuma rasa rai a cikin gidan nan, mutuwar Junaid ma kaɗai ya isheni.." tana ƙarisa maganar tana kuka sosai,
Malam yace "to ko tana cikin toilet ne ki dubo ta,
Shi dai malam tsoronsa kar Ayush ta cire wannan zoben tinda Junaid ya riga da ya mutu, kar itama ta rasa tata rayuwar..
Bayan Mommy ta shige cikin toilet abunda ta gani ne ya tayar mata da hankali, ta dafa ƙirji tace "nashiga uku, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Malammm!!!..."
shima da sauri ya shige cikin toilet ganin Ayush kwance a ƙasan tiles ko motsi babu ga kuma jini ta ko ina,
jini ne yake ɓulɓulowa daga cikin cibiyar ta duk ya wanke cikin toilet gaba ɗaya, itama tana kwance cikin jinin tayi jarab da jinin,
hannun Mommy ne yake kakkarwa kamar wacce aka jona wa shocking,
Malam ne ya ɗago ta yana faɗin "mu hanzarta hospital jinin jikinta zai ƙare fa, ɗaukar luɗa yayi mata sannan yayi waje da ita, itama Mommy bin bayansa tayi duk tabi ta ruɗe da haka suka isa harabar gidan suka shige motor gaba ɗayansu, miƙar hanyar da zai sadasu da gate yayi da gudun gaske,
har zasu fita Malam ya sanar da mai gadi cewar