Showing 24001 words to 27000 words out of 139707 words

Chapter 9 - Matar Damisa book Complete by Asmita .txt

Asmeetah   

16 Dec 2024

9943

tana tunanin Mommin Junaid dake kwance a gadon asibiti
Abun duniya duk yabi ya isheta!
"Allah Allah ka bawa Hajia ta lafiya, nasan na tabka babban kuskure da ban sanarwa Junaid kiran da akayi masa akan rashin lafiyar mahaifiyarsa ba, wayyo Allah nah, ban san da mai zai d'aukeni ba, gashi ba wani sha'kuwa mukayi ba"
Zama ya gagareta ta tashi tsaye tana ta zarya a cikin falon,
"Naga ya fita a firgice Allah yasa ba mutuwa tayi ba!"
Hawaye duk ya wanke mata fuska, ga gumin da yake kwararowa daga cikin suman gashinta ko kwali babu a kanta
Gashin nan ya kwanta a kan gadon bayan ta, zirin gashin yana gogan tudun duwaiwayan ta ๐Ÿ˜
Tana cikin wannan iftila'in kamar daga sama taji muryar mutum yana fad'in "ki kwantar da hankalinki insha Allahu babu abunda zai sameta, zata samu sau'ki"
Murya na kakkarwa yake maganar..
Saida Ayush ta tsorita ta waiwaiya da sauri ta kalli bakin 'kofa mai gadi ne tsaye jiki na rawar sanyi alamar yana cikin jinya!


'Karasowa yayi gaban ta yana fad'in "Dan Allah ki taimaka mun da abunda Zan ci tin jiya bansa komai a bakina ba"


Ayush cike da tausayi take kallon Dattijon mai gadi tace "toh Bari na duba maka"
Ta kalli wajen da ta ajiye bread ko rabin ci bata yi ba tin lokacin da Junaid ya fita ta tsayar da yin breakfast...
Dauka tayi ta mi'ka masa tare da kakkauran tea!
"Zauna anan kaci" ta fad'i haka a lokacin da itama ta zauna.
Zama yayi shima ya soma tura biredin nan a bakin sa
Ta zuba masa ido har saida ya kammala, yasha ruwa yana fad'in "alhamdulillah"


Gyaran murya tayi sannan tace "Dan Allah Baba kafin ka tafi inaso zanyi magana da Kai"
Shima gyara zamansa yayi yace "inajinki yarinya, fadin duk abunda kike son fad'a insha Allahu Zan sanar miki komai"


Ayush ta d'ago cike da damuwa a fuskarta tace "inason sanin tarihin gidan nan"


Baba ya kalleta yace "ke kuwa meyasa kike son sanin tarihin gidan nan?"


Ajiyar zuciya Ayush tayi sannan tace "jiya da daddare naga abun mamaki akan yaron gidan nan kuma naga idanuwan sa sukan canza kala su koma na irin namun daji shin sun had'a dangantaka da namun daji ne??"


Jinjina Kai Baba yayi yace "tabbas zakiji komai daga bakina, nayi shekara aruruwa ina aiki a tare da mutanen gidan nan tin kafin a haifi Junaid wato yaron gidan nan, Junaid ya samu jinyarsa ne ata sanadiyar wata karuwa wacce Alhajin gidan nan ya taimaka, munafukar mata, arniyar banza arniyar wofi da zan sameta ni da kaina zan fille mata wuya da takobi na 'yar banza ita tayi sanadiyar mutuwar mai gidan nan sannan tayi sanadiyar kamuwar ciwon zuciyar hajia ga Junaid tayi sanadiyar fad'awarsa cikin masifa da bala'i, duk da basu tabbatar da cewa ita bace AMMA ni Malam shehu Aljanuna sun sanar mun cewa itace munafuka,
Wai ita sunanta AGAZA (Aghata) ko wacece oho sunan yaren su ne haka Alhaji ya sauya mata suna da BURA'ATU (Bara'at) taje tayi cikin shege ta kawo mana Algunguma ta ce Alhaji ne yayi mata, wannan mutuwarta bazaiyi kyau ba......."
Ya tsayar da maganar yana huci.


Ita kuwa Ayush fashewa tayi da matsanancin kuka jin tsohon akan mahaifiyarta yake magana....
Tabbas jikin ta ya bata cewa anan gidan Umanta ta zauna!
Sai kuma a yanzu ta 'Kara tabbatarwa,
"Wannan shine Junaid d'in da Uma taketa ambato, kuma shine ya kasheta har lahira, shikenam ya d'auki fansar mahaifinsa, babu abunda zance yanzu,
Amma duk lokacin da suka ganeni cewa ni diyar Bara'atu ce tabbas kashina ya bushe....."

Duk wad'annan maganganun a cikin raanta takeyinsu...


Shi kuwa Baba ganin kukan da takeyi ya'ki tsayawa
Yace "Allah sarki dole kiyi kuka da tausayi mana
Bari na tashi najeni kar masu gidan su dawo...


Yana fita kuwa yaji Ana horn da motor
Da sauri yaje ya bud'e,
Ganin Junaid ya shugo da gudun gaske yace "Allah yasa dai lafiya, oh Allah ya baka lafiya yaron kirki"


Zuciyar Junaid kuwa cike yake da takaici da kuma tsananin tsanar Ayush domin a tunaninsa itace silar rashin lafiyar mahaifiyarsa tinda har ta iya kashe masa waya ta wurga cikin wardrobe
Kuma ta gagara sanar masa, alhalin Doctor ya sanar mata ana nema nah,
"tana son kashe mun Uwa, yau saita bar gidan nan, abunda ya faru a baya bazai 'Kara faruwa ba, mahaifiyata bazata mutu ata sanadiyar wata ba,
Anyi akan mahaifina,,,,
I can't trust anybody again, daman ban yadda da ita ba......"


Haka ya dinga sambatu shi kad'ai, ya sauka daga cikin motar ko rufe murfin motar baiyi ba
Yayi cikin compound da sauri.............






*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600


*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000


*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*




*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ


๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)


*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ




*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________


https://www.facebook.com/103637491942644/


๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ




ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…


*BOOK* *ONE*
*PAGE*โžก๏ธ31 & 32




Shigarsa cikin falo ya tarar da Ayush zaune tana ta faman rera kuka!
Da sauri ya 'karasa gurinta ya ri'ko hannunta yayi filli da ita 'kasan carpet, a razane take shirin tashi ya cabko sumar gashinta ya ri'ke sosai ya d'agota 'Kara tasau take fad'in Dan Allah kayi hakuri Yayana bazan 'kara ba, nayi kuskure a gafarce niiii ta fashe da matsanancin kuka tana ri'ke da hannunsa wanda ya ri'ke gashin.

................."Mahaifiyata kike so ki kashe? metayi miki haka har kikeso ki d'au hukunci, matar data taimake ki??" Bud'an baki tayi zatayi magana ya darara mata tsawa "Shut up" har saida dodon kunnenta ya girgiza ta toshe kunnenta da hannayenta biyu tsabar karfin tsawar....
Yayi wulli da ita gefe yana fad'in "kina son cewa wani abune? Daman kinada bakin magana? Shameful girl"
Ja da baya take dasauri tana fad'in "wallahi bani bace, ni ni niiii bansan komai baa, kai kainee......." Bata 'karisa maganar ba ya cabko wuyanta ya d'agata sama da hannu d'aya "ni ne mai??" Har idanunsa sun fara canza colour zuwa tiger eyes, jijiyoyin jikinsa sun fara bayyana...
Ayush ganin haka yasa jikinta ya soma kakkarwa da bakinta hakoranta suka fara dukan juna da 'karfi, ga kuma 'kafar ta dake lilo ga yayi mata kyakykyawar sha'ka ga kuma yana shirin zama tiger tsabar firgici saida ta sau fitsari a jikinta..
Ganin numfashinta ya soma d'agewa ya yi cilli da ita sai yarabb ta fad'i 'kasi, a tsorace tayi wani irin razanannen ihuu ta mi'ke da gudun bala'i tayi waje! Shima bin bayanta yayi yana fad'in "I will kill you, foolish girl you want to kill my mom."

Ita kuwa compound d'in dazai sadata da harabar gidan ta taka adai den lokacin da tsantsin tiles ya d'ebeta tayi sama zata fad'i 'kasin floor wani irin 'karan gaske tasau harta saddakar kwatsam taji an ri'ke kunkuminta mannata yayi a jikinsa sosai,
Gumi duk ya wanke mata ilahirin jikinta ta d'ago da kanta a hankali tana son ganin wanda ya ceceta lokaci guda ta zaro manya-manyan idanuwanta waje ganin 'kwayar idonta a cikin na tiger eyes! Eyeballs d'insa sun zama blue sosai, gashi yanda yake za'kami kamar kuntaccen zaki, ido cikin ido suke kallon juna ganin kwakwalwarta bazai iya d'auka ba yasa ta sume masa a saman chest d'insa.

'Daukarta yayi kamar wanda ya d'auki jaririya ya nufi harabar gidan kai tsaye ya nufi gurin mai gadi,
Baba mai gadi ganin yanda Junaid ya koma gashi d'auke da yarinya, jikinsa ne yahau 6ari yana fad'in "innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi rahmanu rahim, Ku kuke ganin mu bamu ke ganin Ku ba, don Allah don Annabi Junaidu ka rufa mun asiri karkayi mun komai wallahi banida 'karfin ri'keka, wayyoo kakan goggo" Junaid duk yana jin abunda mai gadin yake fad'a saboda bai gama fita hayyacinsa ba,
Katsar da mai gadin yayi tareda fad'in "lafiya klau nake, wannan Yarinya inason kafin na fito tabar gidan nan bana son sake ganin fuskarta a wannan gidan, idan ba haka ba Zan kashe ta har lahira" yana fad'in hakan tare da kwantar da ita asaman daddumar baba tsoho wacce take a sume,
Juyawa yayi ya koma cikin compound ya shige cikin falo daganan upstairs ya haura cikin bedroom, toilet ya shiga shap-shap ya watsa ruwa a jikinsa domin bayaso hankalinsa yabar jikinsa saboda in har hakan ta faru duk wanda yake gidan sai ya raunanasu, amma saka ruwa a jikinsa zai taimaka masa ta wani 6angaren....


Baba mai gadi jin abunda Junaid yace kuma ga a halinda yake ciki yasa ya yi saurin d'auko ruwa yana zuzzubawa Ayush, a razane ta tashi tana fad'in "wallahi ban mata komai ba, Dan Allah kayi hakuri karka kashe ni....." Ganin mai gadi a kanta tsaye yasa tayi shuru ta zuba masa ido tana maida numfashi sama-sama.
Shima mai gadin kallon ta yake cike da mamaki
"Kiyi hakuri Yarinya nasan kina cikin matsala, amma Allah yana tare da ke". A cewar mai gadi..
Ayush bin gidan tayi da kallo gaba d'aya kanta ne yake juyawa da kyer ta iya motsa la66enta tace "aina nake?"..
Mai gadi ya kalle ta yace "ah daman baki san a yanda kike ba? Ni kuwa bar mun ke akayi akace da zaran kin farfad'o kibar gidan kar a kashe ki"
A tsorace ta kalli mai gadi tace "Damusa koh? zai kashe ni wallahii wayyo Allah gashi nam, sai take ganin kamar shine yake nufo gurinta
Kuma gizo yake mata..
Da gudu ta tashi ta bud'e get tabi layi tana gudu tana waiwayen bayan ta, haka ta hau kwalta tana gudun ceton rai ba takalmi a 'kafarta ba kwali a kanta balle mayafi
Haka take gudu kamar mahaukaciya murara!


Shi kuwa Baba mai gadi girgiza kai kawai yayi bashida bakin magana sai abunda yake sa'kawa a ransa
"Oh yanzu Ina ta nufa sai Allah abun tausayi, haka Junaid yake korar duk wata yer Aikin da aka kawo gidan, amma banga laifinsa ba abunda akayiwa mahaifinsa babu dad'i sam,
Gashi shima a sanadiyar cutan nan tashi yasa mahaifiyarsa kwance a gadon asibiti, Allah ya bata lafiya" haka ya zauna akan daddumarsa yana wannan maganar zuci....


Ayush tafe take a tsakiyar kwalta bata san Ina zata ba, duk fuskarta ya tuje yayi jawurrr tanata sharar kwallah sai ji tayi 'katuwar mota trailer ya yi wani irin hornnnn a bayanta a tsorace ta juya bayan ta da wani irin ihuu ta toshe kunnuwanta da hannaye biyu ta 'kame 'kamm a waran, idonta kuwa ta 'kan'kamesu a rufe!
Ganin anyi wani irin hajijiya da ita an rungumota ne yasa tayi saurin bud'e idonta
Ana kawar da ita daga tsakiyar kwaltan kuwa 'katuwar motan nan ta wuce ko seconni ba'ayi da kawar da itaba!!!!
Zuciyarta kuwa wani irin bugawa take tsabar ta gama tsorita
Sai ji tayi ance "ke ashe bakida hankali, waya gaya miki ana wasa da rayuwa?" Ya kalleta da kyau a hankali ya furta "ke ce Ayusha wacce kike tare da Doctor Fatima?" Ya karisa maganar tare da 'kura mata eyeballs d'insa.
Itama kallonsa take baki na kakkarwa ta kasa cewa komai sai idanunta wad'anda suka canza launi zuwa light red tsabar azaba da firgici.....


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login