Showing 33001 words to 36000 words out of 112373 words

Chapter 12 - AGE MATE'S Complete Document book by Momy Fareesa .txt

23 Dec 2024

12823

pm"bata rufe bakiba taji k'amshin turarensa da muryarsa yayi sallama"yana sanye da shigar larabawa"farar jallabiya da rawani da b'akin glass"sai takalmi rufaffu bak'ak'e da Agogo bak'a daya d'aura "yayi wani irin masifaffan kyau tamkar bak'in balarabe"karon farko Ahyaan ta kallesa taji fad'uwar gaba "ga wani kyau daya mata wanda yafi na kullum...mamy ga shi khaleel zaizo ki bashi"ya fad'a yana mik'a mata keys d'in shagonsa"yana kuma satar kallon Ahyaan "Anan ya lura da hijab d'in dake saman cinyarta"ko Ina zataje ita kuma?"ya fad'a Azuciyarsa yana juyawa zai tafi"tashi kuje mana"cewar mamy"juyowa yayi fuska Agimtse ya kalleta ta cikin glass d'in yaga ta mik'e tsaye tana warware hijab zata saka"wai Ina zamuje mamy?"kamar ya?"ba wajen wa'azin zakajeba?"eh can zanje "to kuje mana"nifa gaskiya ban tsara zuwa da ita wannan satin ba"haba broth harfa na shirya kuma"sai da ya wani yamutsa fuska kafin yace "Ina ruwana da shiryawar taki?"ba k'aramin shak'a tayiba dama kuma d'azun ma tana hak'e dashi "saita yi shiru fuska bbu walwala ta zauna"rai b'ace mamy ke kallonsa tace"wai nurah meke damun kane?"Ahyaan tashi kuje"idan kun tafi ka yarda ita kan hanya"ta k'are maganar cikin fad'a "k'in mgn yayi ya fita"mamy na hak'ura da zuwan ya barshi kawai tunda baya so yaje dani"ah ah" tashi maza kuje kema Ai zaki samu ladan"bata yi mgn ba sbd bata son musu da ita"jikinta A sanyaye ta mik'e tsaye ta fita "saidai Aranta taci Alwashin ta gama ganin zaije wani waje tace zataje"duk kuwa ranar da yace tazo suje saiya gane kuransa "ko zuwa wa'azin shine Ai last week yaje da ita bama tare da son ranta ba.tana wannan tunanin ta hangosa bakin get ya bud'e mota ya shiga"sosai ta daure fuska Ayangace cike da izzah take tafiyar da takalminta masu tudu ,ta rataye hand bag d'inta saman kafad'a"hijab d'in bata kai har k'asa ba tadai wuce gwiwa.... Azahiri idan ka kalleta zaka d'auka tsananin yawan shekarunta baza su wuce 23 yrs ba"sosai tayi kyau na musammun"Dr darma ya dake kallonta tun d'azun ya sauke numfashi sbd ganin zata shigo"saiya maida kallonsa ga waya"bayan ta shigo ta rufe batare data tankashi ba"shi kuwa so yakeyi ta kulashi Amma ya rasa ta Ina?"sai yaja motar suka d'auki saman titi"saidai fa A zuciyarsa beson zuwa da ita wajen wa'azin sbd kar mlm tasi'u ya ganta"besan kuma meyasa yayi hakan ba?"d'an cije baki yayi daya tuna da sak'onta dake Ajiye cikin motar daga gefen k'afarsa"saiya mik'a hannunsa guda ya zaro ledar ya Ajiye mata saman cinyarta "ita kuwa hankalinta na wajen waya tana chats da Khairiyyah"saidai tana ganin ya Azo mata ledar ta harari ledar dashi kansa daya Ajiye mata"hmmm! huta hararata ba wani abu bane turaren da kikeso ki fesa ne, shine na siyo miki sabo....bana so !ka rik'e Abunka"ba d'azun da nace ka bani ba mgn ka gayan?okay to saiki yadda tunda baki so *Aminatu*! shiru tayi sbd ta rasa meyasa duk idan yakira Ainahin sunanta takejin wani iri?"wai Ina zaka damu?"siyar dake zanyi"hmmm! Ai wlh daka shiga ukku ka siyarwa da mamy y'a" to yanzun zaki gani"wai mlm Ina zamuje?"gidan Hjy (mahaifiyar daddy)"shiru tayi sbd ta d'an kwana 2 batama je gidan ba, Amma da yake sarkin yab'a mgn ce sai cewa tayi dama nan mamy tace muzo?ko kuwa nace maka ka kawoni nan?"ban sani ba"wajen wa'azin ne dai bazaki jeba"in kuma kina so kiyi sabon saurayi Acan sai muje.....kaga ka dena mun irin haka bana so"d'an murmushi yayi bece komai ba "ita kuma ta maida hankalinta wajen waya"saida ya tsaya ta fahimci sun iso"bud'e k'ofar tayi saidai taji ya saka lock"fuska Atsuke ta juyo ta kallesa"kinsan Allah? na dawo na samu kin tafi saina miki Abinda baki tunani"kajima baka yimun ba"ta fad'a tana hararar sa"bece komai ba ya cire lock d'in,ita kuma ta fito tabar ledar nan"ya tab'e baki ya wuce Abinsa.....
sai wajen k'arfe 6:7 pm Dr Nura Darma ya dawo d'aukar Ahyaan" "ya soma ya kirata ta fito su wuce ,saidai rashin contact nata da baya dashi Awaya ya saka bisa tilas ya nufi cikin gidan kakar tasu". Ahyaan na zaune ta tak'ark'are tana cin kwad'on zogalen da Hjy tayi mata"yaji k'uli k'uli da kayan had'i"suna zaune tsakar gidan Hjy nata bata labari tana dariya"sosai ta manta da b'acin ran da uban gayyar ya hadda mata"dukda tajima rabonta da gidan Hjy d'in Amma yau taji dad'in zuwan ta gidan"musammun yadda tsohuwar ke nuna mata k'auna da yimata Addu'ar fatan Alkhairi"suna zaune kan tabarma hijab d'inta na daga gefe ta ninke ta,ta Aza hand bag d'inta da wayarta Asama....da kallo ya bisu hannayensa zube cikin Aljihun jallabiyar sa"sau biyu yana sallama Amma basu jiba"Ahyaan ce kawai da taji k'amshin turarensa ta juyo ta hangosa yana doso inda take zaune kai tsaye..... d'an nema na d'auka Ai ba zaka shigo A yanzun ba?"meye ne kika bata ni ban dani Hjy?"ya fad'a yana duk'awa gaban Ahyaan "da sauri ta Aza hannunta saman plate d'in zogalen zata janye"shi kuma yayi saurin rik'ewa cikin nutsatstsiyar muryansa yace kefa matsalata dake marowaciya ce"Hjy kin ganshi zai cimun Abuna ko?kaga nidai ban yi dakai ba, sbd haka saika rungumi na Annabawa"ke kin fara haka Hjy kiyi Abu ki hana mai gida?uhmm! mai gidana yana lahira"kai kuma Allah ya baka mace ta gari"Ameen to tunda ke bakya sona ko?"dariya Ahyaan ta dinga musu ,yayinda shi kuma yake cin zogalen"yana binta da kallon k'asan Ido"can tace" nidai ka barmun Abuna haka mana"yi yayi tamkar be jiba "ganin zai iya cinyewa ya saka itama ta dinga ci"ita dai Hjy tayi shiru tanata kallonsu"saida suka cinye tas ya kalleta,tashi muje mu wanke hannun"batayi mgn ba ta mik'e tsaye ta saka takalminta ta nufi bakin maguji wajen tape"d'an lumshe Ido yayi bayan ta wuce shima ya mik'e tsaye ya iso wajen,saidai tana ganin ya iso ta rufe tape d'in "wlh koki bud'e kona saki kuka"idan ka sani saina barka da Allah "tunda baki iya ramawa ko?"ya fad'a yana bud'e tape d'in ya d'ebi ruwan ya d'ago zai watso mata tayi saurin matsawa tana masa gwalo ta wuce ta d'auki hijab nata ta sanya ta d'auki wayarta da hand bag d'in tace"Hjy na wuce sai Anjima"to shikenan Aminatu ki gaidasu su Hjy zainab d'in "zasuji y'ar tsohuwa"cewar doctor yana yin gaba....tun kafin ta fito ya dinga danna mata horn, ta yamutsa fuska tana fad'in nida sabon shiga"ta k'are maganar tana fitowa daga cikin gdn ta bud'e gefen me zaman banza ta shiga"saidai taga babu ledar daya bata"Ina ledata?"yayi shiru Ak'ule tace "kana fa ji?kefa kikace bakya so?"wai meyasa kake son b'ata mun rai da maido Abinda ya wuce??"shikenan gashi nan"ta Amsa tace na gode tana bud'a ledar"turaruka ne guda biyu"broth shower jal d'infa?"bara muje na siya miki"ya fad'a suna hawan saman titi"shi yana driving ita tana chats"saida suka iso wata had'ad'd'iyar super market sannan ya tsaya yayi parking"ki jira zanje sashen kayan shafa na duba miki saina dawo"be jira cewar taba ya fita dg motar"tana hangosa ta glass d'in motar ya shiga wajen ta kauda kai"saidai befi mintina 2 da shigaba taji Ana mata knocking "ta zuge glass d'in motar Ahankali ta d'an lumshe Ido sbd wani irin k'amshi shigen na Dr darma da taji me sanyi da kashe jiki"Assalamu Alaikum! saida taji gabanta ya fad'i ta d'ago Idanunta Atake suka nutse cikin idanun *Abdallah Aliyu mashi*! matashin saurayi tuzuru d'an gayu"da sauri ta yamutsa fuska ta kauda kanta"saidai Ayadda ta kallesa da irin dressing jikinsa data gani ya tabbatar shid'in gogaggen d'an boko ne! pls madam ki d'an janye motar zan fita da tawa idan ba damuwa ko?"yafad'a yanata kallonta"kin tankashi tayi "ta fito daga cikin motar"ya zuba mata Ido yana kallo"saurayine da zaiyi 35yrs Aduniya bak'i dogo....tana k'ok'arin mishi mgn Dr darma ya iso wajen cike da shan k'amshi yayi kicin kicin da rai"meye kika fito kiyi Anan?"ya fad'a murya Adake "AA mashi ya bishi da kallo bece komai ba, ya d'auka yayenta ne"dama broth yazone sbd mud'an gyara parking ko zai wuce ne"kin mgn yayi ya mik'a mata ledar hannunsa yanufi gefen driver ya bud'e ya shiga"itama saita bud'e zata shiga....ranki ya dad'e babu sallama sai tafiya kuma?"banza ta masa ta shigo"Dr darma yaja wani kakkauran tsaki ya fisgi motar suka bar wajen"da mamaki Ahyaan ta kallesa tana son sanin meyasa yayi tsakin?"saidai ganin yadda ya had'e girar sama data k'asa ya saka yamata wani irin masifar kwarjini saita kasa masa mgn"ga wayoyinsa nata ruri ya musu banza kawai....tunda ta fahimci zafin kansa da izzarsa sun motsa sai itama nata suka motsa tayi biris dashi"suna isowa layinsu yayi parking "kallo be ishetaba ta bud'e k'ofar zata fito"...ita wannan ledar waye kika barmawa ya d'aukar miki?bana so ka rik'e Abinka "in sha Allah na gama cewa ina son wani Abu naka balle kamun yadda kakeso"tana fad'in hakan ta buga k'ofar da k'arfi ta wuce"ba k'aramin hassala shi tayi ba"sai kawai shima ya fito ya bud'e get ya koma ya shigo da motar ya wuce masjeed......tun mamy na zaton Dr darma zai shigo da dare harta cire rai"Ahyaan kuwa ko Ajikinta da k'in shigowar tasa, sbd ba k'aramin k'ullatarsa tayi ba.....


*****************
zaune take gaban wani malamin tsubbu cikin wata bukka"kansa Aduk'e ya d'ukufa yana bugun k'asa"yayinda tayi tagumi tana jiran jin Amsar bayanin data kora masa Ayanzun"can ya d'ago kansa yace"wanene likitah ?"da mamaki ummah luba ke saurarensa tayi shiru"sai kuma ta tuna da Dr darma "Atake gabanta yafad'i tace"cikin gidanmu yake ,yaron Abokin Mai gidanane"to shine ya b'ata mana Aiki"sannan ya saka Aka maida Aikin k'aik'ayi koma kan mashek'iya"bi ma'ana Abin ya dawo kanki"kai Amma matsiyacin yaron nan taya yasan meye mukayi?"to gashi nan dai naga ya lalata komai"sannan yanzun muddin kina so mijinki ya dena jin kina warin jab'a Tofa dole sai An binne Abin inda yaron ya saka Aka rufe"idan mgn zakiyi masa yaje ya binne zaifi, idanma yaya zakiyi shawara ya rage naki"hankali tashe tace" mlm inani Ina tonama kaina Asiri kuma?"to Ai ya riga yasan kece kikayi Abin sbd haka ke kika sani"yarinyar kuma dole itama sai mun canza wani Abun game da ita"sbd gata nan tana gab da zama wata irin tauraruwa"cikin fad'uwar gaba tace"ya za'ayi kenan mlm?"ki fara bada kud'i kiga Aiki mana"shikenan Abani kwana 2 zan dawo"dato ya Amsa ,tayi masa sallama ta tafi"Allah ya kyauta ya shirye mu gaba d'aya....


Tun daga lokacin da Dr darma da Ahyaan suka tafi suka barta tsaye Awajen"Ikkhee taci mummunan Alwashi Akan Ahyaan"tayi Alk'awarin ba zata koma zuwa wajen saba ko kuma kiransa ,koda sonshi zai kasheta"saidai muddin tana lumfashi bazata bar Ahyaan Ahaka bata mata wani gib'i ga rayuwa ba" wanda zai saka Dr darma yaji muguwar tsanarta Azuciyarsa"dukda Ayadda ta saka Aka mata bincike kansu da Alak'arsu taji suba masoya bane"Amma zuciyarta tak'i yadda suba masoya bane"tafi zaton suna son juna ne sunki fad'ama kansu"ko kuma shi Dr darma ke sonta yabdai b'oye ne game da gudun wani abu"sbd tun lokacin da taga sun hau mashin tana masa shakulkul ta hanashi ya kulata zahiri ta tabbatar Akwai wani Abu Ab'oye"wannan kenan.......
Ayau ya kama Friday"misalin k'arfe 4:11 pm Ahyaan ta fito sanye da dubai Abaya black me zanen flowers golden brown da Adon stones "saita yane kanta da mayafin"tana sanye da takalmi masu masifar tsini golden brown "yayinda hand bag nata itama golden brown ce"ta d'aura bak'ar tsadaddar Agogo ta saka zabba da wani d'an hannu"fuskarta da make up sbd ta shafa red d'in lipstick "tayi wani irin shegen kyau kamar wacce zata gasar fidda sarauniyar kyau"ga wani irin sanyayyan k'amshi ke ratsa jiki da zuciya tanayi"gudan hannun na rik'e da waya ta Kara gefen kunnanta tana mgn murmushi kwance saman kyakykyawar fuskarta.....shiko tun fitowarta ya zuba mata idanu, murmushin da take yi ya matuk'ar k'awata kyawunta da motsa rauninsa. Hakama kwalliyar tata ta d'auki hankalinsa matuk'a"duk da ita hakan normal ne a gareta badan wani birge wasu maza ko wani abu tayi ba....ita sam Ahyaan batama lura dashi ba"dukda koda ta lura dashi d'in ba tankashi zatayi ba"sbd jiya da yau data gansa be tankataba. ko jiya da yayi Azumi wajen cin Abinci yaje yasha ruwa"ta lura kamar ya tsaneta yanzun sbd daya ganta saiya had'e rai....Dr darma kuwa yana zaune kan resting chairs dake k'ofar d'akinsa "t shirt ce me gajeran hannu fara da wondo 3 quarter Ajikinsa "yana d'an shan iska ya cire kayan da yaje masallacin juma'a dasu"ganin tana k'ok'arin wucewa ya saka yataso batare daya san meye zaice mata ba idan ya iso wajenta?"saidai kawai yana son sanin Ina zataje? sallama tayi da wacce suke wayar ta kashe ta bud'e hand bag nata ta saka wayar"dagowar da zatayi da nufin ta iso bakin get taga mutum gabanta"saida taji fad'uwar gaba "saidai bata kallesa ba"ita yanzun bata son yawan had'a Ido dashi bata san dalili ba"saidai ta d'aure fuska tana k'ok'arin giftashi da nufin ta wuce"Ina zakije ne?"yafad'a kamar Ammasa tilas yana zuba mata Ido"cikin masifa tace inda ka Aikeni"na d'auka Ai yadda ka nunamun tsana zahiri bazaka damu da inda zanje ba"to kaima Awa da zaka ta sani gaba kana tambayata Ina zanje?"tunda dai mamy ta barni ta kuma bani kud'in transport me ruwanka da inda zanje??"tunda take masifar ya zuba mata Ido yana kallo lips nasa na k'asa na cikin bakinsa"idanunsa sun yi d'an ja"har cikin zuciyarsa bayaso suna samun matsala da ita, saidai bazai d'auki raini ba"kar taga yadamu da ita ta nemi gaya masa mgn"ganin yak'i mgn kuma yak'i bata hanya ya saka ta tab'e baki zata giftashi ta wuce yakoma tarewa murya Akausashe yace wlh koki sanar mun Ina zakije kona baki mamaki?kin Isa ki tasani gaba kina mun ihu ne?"har tafiyar saina hanaki naga yadda zakiyi....tunanin zai b'ata mata lokaci ya saka kamar zata had'iyi zuciya sbd b'acin ransa da takaicinsa tace" sunan k'awarmu data haihu zamuje nida Khairiyyah"idan kana yiwa Allah ka jaraba hanani zuwa mana"ta fad'a cikin zafin zuciya"sai yaja tsaki yabar wajen zuciyar na tambayarsa wai me yarinyar nan ta d'auki kanta ne?"Akanme zaka shiga sabgarta wai??"wata zuciyar ta tambayesa"gaba d'aya jinsa yadin gayi cikin b'acin rai"kawai saiya koma ya zauna"befi mintina 5 da zama ba Akirashi Asibiti Ana son ganinsa da gaggawa"hakan yasa ko kaya be sauyaba ya wuce ya shige mota ya tafi.... "sai bayan sallar magrib ya shigo gidan"zuciyarsa ta dinga in gizashi yaje yaga kota dawo?"saidai koda ya shigo mamy ce zaune kawai a parlourn "tana lura dashi yana ta y'an kalle kalle yak'i mgn sai kuma ya fita"bakin get ya fito yayi tsaye daga waye yana danna waya"kawai yaji motsin mota ,sai kuma yaji horn"Anutse ya d'ago kansa yana zubama motar Ido har tayi parking "sai Aka bud'e gefen driver Aka fito"kallo d'aya yayima matashin da suka gani shida Ahyaan last 2 days ya d'auke kansa cike da shan k'amshi "saidai yana kallonsa ta gefen Ido yaga ya bud'e gefen me zaman banza"saiga Ahyaan ta fito daga cikin motar.....��


wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba


#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: � *AGE MATE'S* ��♀�




*25&26*








*Littafin kud'i ne!*


.........wani irin fad'uwar gaba had'e da tsinkewar zuciya suka sami Dr darma duk Alokaci guda"tsaye kawai yayi turus Awajen yana binsu da wani irin shegen kallo"fuskarsa bbu yabo babu fallasa....k'amshin mayen turarensa da Ahyaan ta shak'o yasakata saurin kallon bakin get d'in gidan nasu"Atake taji k'irjinta yabuga sbd tozali datayi da kyakykyawar fuskarsa yana dannah waya tamkar besan da zaman suba"saita dake ta rufe murfin motar kawai"Adaidai lokacin AA mashi ke furta gashi zaki tafi baki bani contact d'in ba?"yamutsa fuska tayi tak'i yin mgn...yayan mu barka da dare! cewar AA mashi yana kallon Dr darma daya d'auke kansa daga barin kallonsu" saidai yana sauraren su"ya d'auki kusan second 5 kafin cikin shan k'amshi had'e da basarwa yace"barka dai Atak'aice"tamkar Ahyaan tace masa *Age mate* d'inta ne ,sbd ta fahimci AA mashi ya girmeshi"sai kuma taga rashin dacewar hakan" sai kawai ta nufi cikin gidan batare da kota gode tace masa ba...dama ya ganta bakin titi ne tana jiran Abin hawa ga magrib tayi"saiya tsaya ! kasancewar tunda ya ganta yarasa nutsuwarsa yana neman ta yadda Allah zai sanya yakoma had'uwa da ita"sai gashi ya taki sa'a ya ganta tsaye bakin titi"saida ya dinga yimata magiya sannan ta yadda ta shigo motarsa"tunda ta shigo kuma shine ke surutunsa ita dai tayi masa shiru, saiya dameta zata ce uhmm ko ah ah har suka iso gida....pls ji mana! ya koma fad'a sbd ganin zata shige ciki"saidai bata juyoba ta Ida shigewa cikin gidan"Dr darma ya tab'e baki ba tare daya kalli gefen da yakeba shima yabi bayanta"kusan Atare suka shigo cikin parlourn mamy"dandai ita ta rigashi shigowa"sai yanzun Ahyaan bayan nace karkiyi magrib??"wlh mamy matsalar nafef ce shiyasa kiyi hak'uri dan Allah"ba komai tunda kin dawo lfy"kije kiyi sallah,dato ta Amsa ta wuce ciki tana lura da Dr darma na zaune ya wani sha mur yanata y'an Harare Harare"saidai bata tankashiba ta wuce sbd wani irin haushi yake bata.....ba Abincin zaka cibane?"yayi shiru"baka jine?"na k'oshi"wai dan Allah mamy meyasa kike barin yarinyar nan tana yadda take so?"wani nefa ya sauketa daga cikin motarsa"yanzun haka tarbiya ce me kyau?"da kallo mamy ta bishi har saida yayi shiru kafin tace"sbd wani ya kawota ya Ajiye shine ke nufin batada tarbiya ko bamu bata tarbiya ba?"shin kasan kota sanshine ,ko kuma sbd kar tayi dare shiyasa ta shiga motar tasa??"kaifa malamine nurah yaka mata ka dinga uzuri da kyautata zato"Ahyaan ni banga laifinta ba"sbd haka idan naga tayi ba daidaiba Ina tsawatar mata "mgn ta dakai ta k'arshe karka koma ce mata yarinya sbd kaida ita sa'annin juna ne"idan bakaso tayi magrib d'in meya hana kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login