Showing 39001 words to 42000 words out of 112373 words

Chapter 14 - AGE MATE'S Complete Document book by Momy Fareesa .txt

23 Dec 2024

12820

ya bita da kallo yana sauke numfashi "Ahankali ya sauka daga saman bed d'in ya zare kayan jikinsa ya d'aura towel"sannan ya zauna yayima kansa Allura "befi zaman mintina 5 yayi ba yaje ya murza key ya shiga bath room"Atsabtace yabsamu toilet d'in,ga ruwan wanka ta had'a masa cikin bath tub"saiya shige ciki yayi kwance ya lumshe manyan idanuwansa da suka yi d'an ja.....yafi mintina 15 cikin bath room d'in sannan ya fito yana tsane ruwan jikinsa "gaba d'aya jikin nasa da sauk'i sosai"babu jirin da murd'awan cikin"shima zazzab'in gashi ya sauka"rashin k'arfine kawai da babu Ajikin nasa"turarukan jiki kawai ya fesa yasaka k'ananun kaya mararsa nauyi yayi zaune saman bed d'in yad'an jingina yana tsotsar lip nasa na k'asa yana cijesa"gaba d'aya kyakykyawar choko face d'in Ahyaan yake hangowa"lokacin da take goge masa goshinsa da sadda take goge Aman babu nuna jin k'yank'yami, saima tsananin tausayinsa daya hango cikin k'wayar Idanunta"wanda yayi mamakin hakan sbd Aganinsa ta tsanesa! Ayanzun ko dariya takeyi data gansa take denawa"hakama idan tana murmushi ko mgn daya shigo zata gimtse Abinta"Afili ya furta komai girman namiji yaro ko babba yana buk'atar kulawar y'a mace "dubi yadda yanzun yakejinsa Alhamdulillah bisaga y'ar kulawar data bashi"ya tabbatar idanda beci wani Abuba yasha magani da yanzun yana nan kwance"yad'an lumshe Ido daya tuna d'azun yadda take ta rarrashinsa"gaba d'aya sai yaji fushin daya keyi da ita ya dena.... knocking d'in k'ofar da Akayi ya katse masa tunani "Ahankali ya Isa bakin k'ofar ba tare daya tambayi waye ba yabud'e"sbd ya d'auka ko itace"saidai yaga khaleel tsaye yana mik'a masa plate d'in data zuba yankakken lemon fata Aciki"Ina Ahyaan d'in?da barata iya zuwa da kanta ta kamun ba "ya furta ba tare daya shirya fad'in hakan ba"shi kansa Khaleel d'in yayi mamakin kalamansa"sai cewa yayi mamy ce data gama yankawa tace na Amso na kawo maka"bece komai ba ya Amshi plate d'in dan ya fahimci mamy tayi hakane sbd bata son yawan kad'aice warsu ne "kaje ka siyo kaza ka kai mata tamun farfesu" Amma ta saka yaji bakina ba dad'i pls"dato ya Amsa ya juya shi kuma ya rufe k'ofar d'akin.....
Ab'angaren Ahyaan kuwa tun bayan ta gama yanka lemon mamy tace" khaleel yaje ya kai masa"bata yi zaton komai ba ta wuce d'aki ta shiga wanka"koda ta fito sallar Azahar tayi sannan ta shirya cikin wani had'ad'd'en tsadaddan leshi me kyau daya haskata matuk'a "wanda sabo ne sawarsa guda"powder da maskara kawai ta shafa"saita gyara gashin girarta dake cike "sannan ta fesa turaruka ta saka y'an kunne kawai"ba k'aramin kyau tayiba "musammun datayi d'aurin d'an kwali goshi style d'aya bayyanah gashin gaban goshinta"fitowa tayi daga cikin d'akin"mamy ta bita da kallo tana fad'in Masha Allah "wuf d'aya idan ka kalleta zaka d'auka irin y'an matan Abuja d'in nan ce"mamyn nata kallonta Aranta tana mata Addu'ar zab'in Abokin zama na gari"mamy bara naje naga kosu Ammah d'in sun iso?"Ai Ahyaan sun jima da isowa gsky"sbd mama ta kirani tun d'azun tace sun iso"nima dama ke nake jira muje na gaisheta na dawo"to mamy muje ko?"dato ta Amsa ta d'auki hijab dake gefenta ta saka suka fito mamy ta rufe k'ofar parlourn da key"kafin ta rik'e hannunta Ahyaan suka fito"sai murmushi sukeyi suna mgn suka wuce....sam basu lura da Dr darma dake nufo cikin gidan ba"kasancewar dawowarsa daga masjeed kenan"ya bisu da kallo har suka bacewa ganinsa"ya lura koya Ahyaan ta saka sutura saita nuna kanta Ajikinta..... kyakykyawar motar daya gani Ajiye bak'a daga gefen tasa motar ya janye hankalinsa"wacce motar mata sukafi yawan hawanta"kuma itama bazata wuce sama da 8 million ba"sam be kawoma ransa motar Ahyaan ceba"sbd besan uncle mustapha ya siya mata mota ba"yadai san ta sami Aiki sbd saida iyayen nasu maza suka sanar masa....ringing d'in wayarsa yasaka ya d'auke kansa daga barin kallon motar ya wuce wajen resting chairs dake bakin d'akunan mazan gidan ya zauna yana Amsa kiran mu'az.....
Ummah na zaune a tsakar gidan itada Khadija"tayi duhu da y'ar rama"sbd gaba d'aya Abin duniya ya isheta "ga matsalar tsakaninta da Abba ba zaman lafiya,ga jin zafin Ahyaan ta sami Aiki"gaba d'aya ta lura yaranta ne kawai cikin gidan koma baya"musammun da taga ga Dr darma ya fara fantamawa"ga khaleel shima yanada Abin hannunsa"Isma'il na karatu shida Affan sun kusa gamawa"hakama Abdul Aziz shima yanada nashi Abin hannun"tun wayewar garin yau ta fahimci mamah bak'i zatayi"sbd ganin yadda taketa y'an Aikace Aikace da kai da kawowa itada Asma'u "kasancewar dama bata dogara da girkin luban ba"gashi itace keda girki yau"shiyasa tayi girkinta daban"sbd tanada komai da Dr darma dasu Affan ke Ajiye mata"saida k'arfe 1 saura tayi sannan su Ammah suka iso gidan, ta fahimci dalilin su ya saka Ake wannan hidimar"saidai ta lura mahaifiyar zainab d'in nada girman kai ko gaisuwarta da k'yar take Amsawa"tana wannan tunanin uncle mustapha ya fito daga cikin parlourn mamah da nufin yaje yayi sallah sbd sun huta sunci Abinci"saidai yana fitowa mamy da Ahyaan na shigowa tsakar gidan "Ahhh Anty maryam! yanzun nake tambayarki ,sai nace bara na dawo daga sallah na shiga mu gaisa "sbd wannan zuwan naki ne, k'arar y'arki nakawo miki"mamy na murmushi tace na d'auka Ai kamanta dani musty "ya kama murmushi yace" Nina isa na manta da Anty nah"ya fad'a yana hararar Ahyaan ta kama dariya tace" uncle Niko?"Eh mana ba rashin m kika mun ba"nidai Ina motata?"tana bakin get"sai kawai ta wuce d'aki "shi kuma yayima mamy sallama ya fita....kasak'e da kunne ummah tayi k'irjinta na bugawa jin Ance motar Ahyaan na bakin get "gaba d'aya ta lura babu wanda yabdamu da ita da yaranta "ko mamy daga Ina wuni ba Abinda ke koma had'asu "kan idonta ta shige parlourn mamah.....Hjy Ammah kyakykyawar tsohuwa"meji da izzah da Isa "tana zaune hakimce kan kujerah sanye da wata super me tsadar gaske"dukda tafara tsufa Amma son Adonta da kwalliyarta na nan"da Alama Anan wajenta Ahyaan ta gado izzah"fuskarta na mak'ale da medical glass fari, sai k'aramar waya baby Nokia na hannunta "yayinda kan Ahyaan ke saman kafad'arta tanata zuba mata shagwab'a"mama dai na zaune tana kallon su tana kuma kallon TV "Ahaka Mamy ta shigo cikin parlourn da sallama"Ahhh Maryam ki koma kawai"da Ina cewa bara nina zo na gaisheki"haba Ammah! Nina isa nak'i zuwa ne"na bari kud'an hutane shiyasa"ta fad'a tana duk'awa ta gaida ita cikin girmamawa tare da tambayar mutanan gida"ta Amsa da Alhamdulillah" Ina likitah bokan turai ?"gaba d'aya ya manta dani na rasa wane irin Aure ne wannan? mamy na murmushi tace"yana nan Ammah dole yazo yakawo gaisuwa"to da yake yatashi yau bejin dad'i "subahanallahi! meke damun sa?"cewar mamah"Ahyaan tace zazzab'i ne harda Amai yayima d'azun"Allah yasawaka ya bashi lafiya"cewar Ammah"mama na k'ok'arin mgn kiran Abba ya shigo cikin wayarta"saita d'auka tayi sallama"daga bisani kuma tace"Eh"daga haka ta yanke wayar suka d'an tab'a fira da mamy "kafin mamyn ta tafi"bata juma ba saiga hamza Autah yadawo rik'e da tray me marfi shak'e da snacks inji mamy Abama Ammah"baki washe ta Amsa tana godiya"bayan yaron ya fita ya sake komowa rik'e da leda bak'a ya kalli Ahyaan yace"inji yaya nurah yace" kiyi masa farfesu ki zuba yaji bakinsa ba dad'i"dato kawai ta Amsa tana karb'an ledar "Adaidai lokacin Abba da dr darma suka shigo cikin parlourn"Ahyaan tayima Abba sannu da zuwa "ta saci kallon mutumin nata Ashe ita yake kallo"broth ! uhmm "ya jikin?"da sauk'i "bata koma mgn ba ta mik'e tsaye tana d'an murmushi sbd jin yadda yaketa tsokanar Ammah da tayi kicin kicin da rai sbd ganin Abba"ita wlh tsohuwar har mamaki take bata"ta rasa me mahaifinta yakashe mata Arayuwa??.....sau kusan ukku Abba nayima Ammah sannu sai tayi kamar bata jiba ta biyema Dr darma suna surutu"mama tayi k'asa da kai gabanta na fad'uwa "lura da Abba na mgn yasaka Dr darma ya fita yana murmushi...Hjy sannu da zuwa"da k'yar tace yauwa"bayan sun gaisa shiru ya biyo baya"cike da isah Ammah tace"dama nazo ne Akan batun yarinyar nan Ahyaan"Alhamdulillah! tayi karatu ta gama ,gashi ta samu Aiki"to shima mijin ta samu"inaso ko bayan Auren Amata transfer d'in Aikin zuwa can kd sai ta dinga yi tun yaron Acan yake kuma nan zasu zauna"shidai Abba shiru yayi sbd yakasa fahimtar zancen nata"idanma ya fahimta to waye wanda takeso Ahyaan d'in ta Aurah?"....yauwa iliyasu Akwai yaron dana yaba da hankalinsa Abokin mustapha ne kuma yana sonta sosai"to shine nakeso yazo kuyi mgn yaji yaushe zai turo iyayensa?"yaro ne saurayi ya jima beyi Aure ba"yanada Abin hannunsa,kuma d'an boko ne"sanin kankane na tsayama Ahyaan tayi karatu bazan bari tayi Auren wahalaba kamar yadda zainab tayi.... d'ago kanta mama tayi sbd rashin jin dad'in kalaman Ammah"Abba na lura da ita tana girgiza mata kanta da kyafta mata Ido"ya saki murmushi me ciwo be furta komai ba"saidai yaci burin nunama surukar tasa iyakarta"jin tayi shiru Alamar tana son jin ta bakinsa sai yayi k'asa da murya cikin ladabi yace"to Masha Allah ! zan kira Ahyaan gabanki naji idan har tana sonsa "idan har yamata kuma nayi binciken halayen sa sun min to zan bashi ita"oh wato mu bamu iya bincike ba kenan?"sannan wayace sai Anji ta bakinta?"yayi shiru"dakai nake mgn"gaskiya Hjy saidai kiyi hak'uri sai naji ta bakin yarinya tukum"zancen yanada dukiya be dameni ba"dana bama me kud'i y'ata ya wulak'anta, gara na bama me rufin Asiri ya kula da ita da rik'e mutuncinta.... Ak'ule Amma ta d'ago kanta da nufin ta sauke masa kwandon masifar dake ranta sai uncle mustapha ya shigo"wanda daga shashen mamy yake, yana can shida ita sun tasa Ahyaan Agaba"harda kukanta da rantsuwar bata son Abokinsa Ahmed "kadawo ne?"Amma ka jima"cewar mamah"beyi mgn ba ya zauna suka gaisa da Abba cikin girmamawa har saida shi Abban da ita kanta maman suka ji dad'in hakan"kafin ya kalli mama yace"Anty zainab Ina can shashensu Anty Maryam Ina fama da Ahyaan ita bata son Ahmed"tsaki Ammah taja tana fad'in matsalarta ce"ita ta sani tunda tafi son tayita zama Agida ko kuma tayi Auren fatara"na rasa wace irin zuciya ce da yarinyar nan ana nuna mata gabas tana canza hanya?"to nidai bada gummu ta gado wannan mugun halin ba....Hjy ya Isa haka pls"cewar uncle mustapha sbd yasan halinta ba k'aunar Abba takeba tuni"sosai Abin ya faranta ran Abba"yaji dad'i da Ahyaan ta nuna bata son zab'in Ammah"Anutse yace"to Hjy kinji bayanin mustapha? sbd haka bama saina tambayeta ba"tundai bata so inaga Ayi hak'uri Allah yabata Wanda yafishi"sbd zancen gaskiya bazan yima y'ata Auren dole ba"mitsssssuww! kai tashi muje"Abba beyi mgn ba ya mik'e tsaye ya fita ransa Ab'ace "uncle mustapha na ganin ya fita ya fara fad'a rai b'ace yake cewa Alamomi sun nuna zancen kika masa bayan nace ki bari nazo Ayi mgn Agabana"wai meyasa kike haka Hjy ne hjy?"so kikeyi yaya iliyasu ya dena ganin mutuncinki.....saime idan ya dena ganin mutuncin nawa Allah na tuba? wlh idan naga dama sai nace yasakar mun y'a wata tsiyace"talakan banza da wofi"mamah dai ranta yab'aci sosai tayi dai shiru sbd gudun kar tayi wani Abu cikin fushi tazo tayi dana sani...dana san haka zakiyi daban biye miki nazo ba"kuma wlh Alh (mahaifinsu) yasan kinyi hakan kinsan yadda zaku kwashe"sbd haka tashi muje gida nasan zuwa 7pm mun iso gida"Anty zainab kiyi hak'uri dan Allah "kuma hakan bazai koma maimaita kansa ba"wanda Ahyaan ta kawo in sha Allah shine za'a bata"karki damu zan kirashi ta waya"Ammah ta mik'e tsaye tana gyara mayafinta tace"idan kin gama fushin juye mun snacks d'in aleda babba na wuce da Abina"ke y'ar dad'i miji sbd shi kike wannan fushin ko?"sai kace wata uwa ya miki Arayuwa...dan Allah Hjy kiyi shiru"ta tab'e baki batace komai"mamah ta juye mata ta mik'a mata ledar ta Amsa tana musu Allah ya tsare hanya"har bakin get ta rakosu ,tana gani Ammah ta hana uncle mustapha zuwa yakira Ahyaan suyi mata sallama"saidai batace komai ba ta wuce cikin gidan"su kuma suka fita wajen get inda motarsu take..... Misalin k'arfe 4:13 pm"Ahyaan na zaune d'aki ta gama sallar la'asar kenan" fuskarta bbu walwala sbd uncle mustapha yabata haushi"hamza ya shigo d'akin da yunifoam Ajikinsa yace Anty Ahyaan yaya yace kizo yana can zaune k'ofar d'akinsa"dato kawai ta Amsa ta tashi ta maida kayanta na d'azun"ta gyara d'aurin d'an kwali ta fito"ta kalli mamy suka had'a Ido"mamy zanje wajen broth"saikin dawo Ahyaan"naji Ai sadda yaturo hamza"Amma ki dena wannan fushin tunda dai kin nuna bakyaso shikenan"fatanmu Allah yabaki nagari"duk zagaye zagaye da guje gujen masoyanki da kikeyi da lokacin Auren yayi za'a yi"d'an murmushi tayi tace ba Amma bace duk keso"uhmm kawai mamy ta furta"ita kuma ta wuce kitchen ta d'auki basket d'in data shirya warmer d'in farfesun ciki"ga plate da service spoon ta saka"ledar bread sabo guda da ba'a tab'a ba ta d'auka ta saka masa"sannan ta d'akko goron ruwa da lemo fanta na gwangwani duk ta saka ta fito"mamy dai na zaune tana kallon ta Aranta tace" sun shirya kafin su koma b'atawa kuma"Allah dai ya shiryamun yaran nan......��




wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba


#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: *Littafin kud'i ne!*


.......Cike da nutsuwa had'e da sanyin jiki take tafiyar tana tunanin yadda zasu kwashe da Ammah idan taji labarin ta nuna zahiri bata son Alh Ahmed.tasan dole sai tayi dogon fushi da ita"hakan kuma be dameta ba, sbd ba zata cutar da kantaba ta zab'i namijin da bata ra'ayi ba"iya Abinda ta sani bata ra'ayin cewa dole sai mai kud'i zata Aura "indai namiji nada halayen kirki kuma yamata tana sonsa,taji ta yadda zata Auresa kud'insa ba damuwar ta bace"haka ka zalika in har yamata ko yanada kud'i zata iya Aurensa.....tunda ta doso inda yake,gaba d'aya ya maida hankalinsa gareta sbd ya fahimci tunanin zuci takeyi"shi kansa waya yakeyi da Ikkhee "wacce tafi wata 2 rabonda ta kirashi sai yau data kasa jurewa ta kirashi suna gaisawa"saidai yana ganin Ahyaan yama manta da wata waya"sai furta hellow! Hellow!!takeyi Amma Anyi shiru"hakan yasa tak'i yanke kiran tana dai son jin meyasa yayi shiru? sbd ranta ya bata ba matsalar net work bace.....Dr darma kuwa janye idanuwansa yayi sbd ganin tana gab da isowa gabansa"saiya basar yana d'an shafa lallausan gemunsa yana furta"*Amun dago*! numfashi ta sauke ta Ajiye basket d'in saman center table d'in data gani gabansa ,saita zauna gefen sa tad'an dubesa suka had'a Ido"shine Ammah ta tafi koki sanar mun nazo muyi sallama da ita?"wai da gaske kakeyi broth ta tagk?"nifa bansan tama tafinba sai yanzun daka fad'a"shine ta tafi babu sallama sbd tana fushi dani ko?"ta kare maganar cikin shagwab'a kamar zatayi kuka "shi kuwa uban gayyar ya zuba Ido yanata Aikin kallonta"Atake ya fahimci tayi kuka "kukan meye kikayi keda baki gajiya da saurin kuka??"ya furta Afili ,wanda Azuci yaso yayi maganar"ita kanta Ahyaan saida taji k'irjinta ya buga"ga muryar tasa ta saka mata jin kasala"saita kasa mgn ta sunkuyar dakai"tambayarki nakeyi fa?"ya fad'a yana dannah waya"Abin mamaki yaga Ikkhee bata yanke wayar ba"sai yaja tsaki ya kashe wayar"okay tunda tsaki kake mun bara naje na baka wane, zuwan nawa beda Amfani "ta fad'a ranta Ab'ace zata Mike tsaye"bece komai ba sai wayar tasa daya Aza mata saman cinyarta ya nuna mata da hannu"saita tab'e baki ta kalli fuskar wayar taga number d'in Ikkhee da baiyi seving ba"ga just now ! Alamar yanzun suka gama waya"saita tab'e baki ta fara k'ok'arin ture wayar"nifa da wata nake bada keba ko *bestie*? Ai fushi ba naki bane keda kike da patient"dukda kin tafi kin barni har saida na Aiko kizo kuma"yanzun haka Ake jinya?kasa mgn tayi sbd mamakin sa"ga sabon suna daya saka mata "ganin tak'i yin mgn ya saka shi cewa laifin meye kika yiwa Ammah d'in?"saida ta kwab'e fuska kafin tace"Allah kasan broth bata kyautawa haka kawai saina yadda naso wani k'aton tuzuru daya gand'ame Agida ya tuzurance "bayan haka kuma nifa bemun ba"wai yana sona bayan yana sa'an uncle mustapha"kusan 45yrs"never wlh! d'an jim yayi sbd yanzun ya fahimci shiyasa sukazo tare da uncle mustapha"kuma Abba yazo d'azun sbd suyi zancen kenan?"dariya taci k'arfinsa ya dinga b'abb'akawa harda rik'e ciki"kamar ba d'azun shine kwance magashiyan ba"Broth ka gani ka dena mun dariya ko?
Uhmmmm! *Aminatu* kenan! kece da abun dariya Ai"Amma tunda bakyaso na dena"dama shawarah zamu yi"saida ta hararesa tace"yanzun zaka nemi shawaran tawa bayan bakada mak'iyiyar data wuce ni?"nine yaka mata nace miki haka "Amma mu barshi bisaga Abinda ya wuce"kinga gobe sunday tunda ba office zanjeba zamuje ki rakani wajen friends d'in Fatima muyi mgn naji meye za'a basu na hidimar biki?"tab'e baki tayi tare da cewa Allah ya kaimu"Amma ni meye nawa na Aje dani?"kika san ko na samu budurwa idan ta miki saiki had'amu ko?"banza ta masa tana dannah waya, shi kuma yana kallon lips nata data tsuke.....wai yanzun bazaka ce Allah yasa Alkhairi da Aikin dana samu ba balle ka bani shawara me kyau?' "Inada niyar yin hakan sai kika yi maganar"tun last 2 days su Abba suka sanar mun nayi murna da Addu'a da fatan Alkhairi "batun shawara koda baki nema ba zan baki sbd wasu dalilai. Amma yanzun ki zubamin roman nasha inata jin k'amshi kin Ajiye "ba tace komai ba ta zaro kular ta bud'e k'amshin ya daki hancinsu"cikin wani plate me d'an zurfi ta zuba masa cinya da k'ugu(kwatar kaza) "gashi shine rabonka"ta fad'a tana wani shan mur"ya kalleta ya kalli plate d'in fuskarsa da d'an murmushi yace"haba bestie! koda rabon gaskiya zakiyi saiki zubamin k'irji da fiffike ko?"ya fad'a yana saka spoon ya d'ebi roman yakai bakinsa"lumshe Ido yayi sbd yamasa dad'i sosai"gashi yajin beyi yawa ba,beyi kuma kad'an ba"nidai shine rabonka gaskiya"to shifa wannan bread d'infa?"nazo maka dashi ne ka dinga dangwalawa da roman sbd nasan bakayi lunch ba, ka Isa jin yunwa yanxun"kamar kin sani"Ina jin yunwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login