Showing 96001 words to 99000 words out of 112373 words

Chapter 33 - AGE MATE'S Complete Document book by Momy Fareesa .txt

23 Dec 2024

12840

dole ki hak'ura na miki Allura habibty kinjiko?"yafad'a cikin tsananin tausayi yana matsowa ya d'agota ya d'aura mata towel d'in "sai cije baki da rintse Ido takeyi sbd Azaba"saidai yadda ta lura da yadamu saita daure "ya d'auketa yanata faman jera mata sannu ya kaita cikin bath room d'in...
. k'ara ta saki daya sakata cikin ruwan d'umin ta rirrik'esa "sannu ! broth kaje zanyi da kaina"bece komai ba yafito kamar yadda ta buk'ata.bayan ya fito ya canza bed sheet d'in sannan yaje d'akinta ya d'akko mata doguwar riga ta shadda light green me Aiki,ya had'o da duk Abinda yasan zata buk'ata "saida ya Ajiye mata sannan ya d'auki kayansa irin nata yafita daga cikin d'akin.....cikin mintinah 25 Ahyaan ta kammala wanka da shiryawar ta"sosai shaddar tayi mata matuk'ar kyau da haskata"ta kuma sake sosai wajen shiryawar sbd baya cikin d'akin"Ahankali ta matsa gaban mirror d'in ta shafa lipstick red data gani ya Ajiye mata, ranta yabata yana son ta shafa ne"bayan ta gama tayi d'aurin d'an kwali ture kaga tsiya ta fito da gashinta dake d'aure daga baya"tana fesa turare Dr darma yaturo k'ofar d'akin ya shigo"k'irjinta ya buga!ta cikin mirror ta hangosa sanye da irin shaddar jikinta"ta saki murmushi tana Ajiye turaren ta rintse Ido sbd ganin yana tunkarota....wata kyakykyawar runguma yamata ta baya yana fad'in oya bud'e idon "ba musu ta bud'e suka kalli juna ta cikin mirror d'in suka saki murmushi Atare "kafin yace kinyi kyau habibty ki dinga make up Ina so pls"juyowa tayi ta rungumesa ta kwantar da kanta saman faffad'an k'irjinsa "yamata zobe da hannayensa yana fad'in Allah yayi miki Albarka Aminatu"jiya da yau kin bani farin ciki "nima yaka mata ki samun Albarka Dana kawo miki samartaka na ko?"ba k'aramin kunya yabata ba ta b'oye fuskarta Ajikinsa tana dariya "Allah da gaske nakeyi"nidai Adena zancen "nak'i ya"inma zaki doje ki Ajiye y'ar kunya garama ki Ajiye "ni kece komai nawa sbd haka baki daga cikin mutanan da zanjima kunya"tayi shiru"kinji Amarya?"nidai muje parlourn"saina miki Allura na shafa miki cream"idan munyi break fast saiki sha magani ko?"inaso idan kinyi bacci zan d'an fita kafin ki farka zan dawo"Ina zakaje?"cikin gida na gaidasu"kuma zanje office nayi signing na d'aukar hutu"sati nawa zakayi ?"2 ne habibty"gaskiya bestie yayi kad'an "hak'uri zamuyi bestie dukda nan gaba kad'an k'asar zamu bari"muje Ina?"India! zanyi wani course na 6 month Acan"k'ilan ma ki haihu Acan ko?"haihuwa kuma?"Eh mana "Ai jiya na zuba Ajiyata Anan?"yafad'a yana shafa cikinta"shiru tayi sai son janye jikinta daga nasa da takeyi"ya kama murmushi ya matseta"ta kama yimasa chakulkuli"ya dinga k'yalky'ala dariya yaci kata ta juya zata fita ya cafkota suka fad'a saman bed d'in ya haye samanta"ta rintse Ido"habibty Ina jin tausayin ki ki gane mana"to nidai ka d'aga ni wlh nauyine dakai"banma sake miki ko rabi ba"kina so na d'aga ki?uhmm"to ki tsaya zan shafa miki magani"tayi shiru"kinji?"ko kunya kike jine?"nifa mijinki ne miye zaki b'oye mun ,bayan kinsan ni likitah ne kuma?"batace komai ba"saiya d'agata Ahankali ya ware mata k'afafuwanta yafara janye pant d'in yaduba wajen"saida yaji tsikar jikinsa ta tashi"ya dake ya shafa mata cream d'in ya maida mata pant d'in"ya kalleta yaga Idanunta Arufe "sauran Alluran tana can cikin waccan ward rope d'in "to"shine Abinda ta fad'a "gabanta nata fad'uwa sbd tana masifar tsoron Allura"tana kallonsa ya wuce ya d'akko ya had'a,tun kafin yayi mgn ta kwanta zuwa ruf da ciki"yayi sama da rigar "Atake manyan cinyoyinta zuwa jibgegen k'ugunta suka bayyanah"saida yaji tsikar jikinsa ta tashi"ya shafi cinyoyin nata yana lumshe Ido "broth kamun mana"beyi mgn ya zauna ya maidota saman cinyoyinsa d'in ya matseta sosai yana jin yadda jikinta ke kirma"Ahankali yafara tsira mata Alluran bayan yayi k'asa da pant d'in nata....ahhhhhh! washhhhhh! ta furta tana sakin k'aramin kukan da bbu hawaye tana rirrik'esa"bayan ya zare yafara lailaya mata wajen yanata fama jera mata sannu "ita kuma tanata kuka irin na tab'ara"yayinda mutumin naku harya fara jin wani iri daurewa kawai yayi"Ahankali ya d'ago kanta ta lumshe Ido"habibty sannu kiyi shiru"yanzun muje na miki tausa ko?"ta nok'e kafad'arta "to fad'amun meye kikeso Ayi?"tayi shiru tana shigewa jikinsa "saiya matsa ya jingina bayansa a fuskar gadon ya d'auki wayarsa yana y'an danne danne ita kuma tana sauke numfashi"yaushe rabon da Amiki Allura?"nifa har na manta"ki daure ki rage rakin Allura bestie karki b'atamun yara da tsoron Allura bayan mahaifinsu likitah ne kuma?"ni Ina ruwana dasu"kaima bbu ruwana dakai"yakama dariya yace"nid'in kuma?"Eh mana "beyi mgn ba sbd wayarsa data hau ruri.....
Ab'angaren cikin gidan kuwa "da safe da yake ummah ce keda girki mamah bata jira daga gare taba ta shiga kitchen nata sbd had'a Abin break fast nasu"batama yi k'ok'arin had'awa dasu Ahyaan ba sbd tasan mamy zatayi dasu.tun jiya da Khadija ta sanarwa ummah taga Abdallah Mashi da Asma'u suna mgn suna murmushi"kuma wajen dinner Atare suka yima Ahyaan da Dr darma lik'i ranta yabata Akwai wata ak'asa "sai kuma yau da safe Mubarak ke sanar mata yaji labarin wai AA Mashi yanzun Asma'u yakeso"ba k'aramin b'aci da haushi ranta yayi ba"itada Ayau take da niyar cika Aikinta da boka yabata Agidan"Wanda Dr darma zai koro Ahyaan da takardan sakinta"sannan daga baya ta samu ta saka boka Ahada' soyayyar Abdallah Mashi da Khadija sai taji wani zance daban"duk yadda taso ta hak'ura kasawa tayi Mubarak na fita daga cikin parlournta itama ta fito zata wuce d'akin Abba"Adaidai lokacin Asma'u ta shigo tsakar gidan tana fad'in" mamah! mamah!! lafiya sarkin hankali?"cewar mama tana fitowa daga cikin kitchen nata.dama mamy data kirani tace nazo muje nida yaya khaleel yakaini gidan Anty Ahyaan nakai musu Abin kari"to shikenan Allah yatsare ki gaidasu"dato ta Amsa ta wuce d'aki"mamah kuma ta koma kitchen "yayinda ummah taja tsaki ta nufi cikin parlourn Abba....yana zaune kan kujerah yana karatun jarida"yana sanye da jallabiya fara "da mamaki ya d'ago kansa ya kalleta sbd ganin babu ko sallama ta shigo"yana yinta kawai ya kallah yasan ranta Ab'ace yake "shidai yasan yabada duk Abinda za'a buk'ata na kari to kuma miye ya b'ata mata rai?sai bai tan kataba yaci gaba da Abinda yakeyi"banyi mamaki ba sbd kaga ba zainab bace ta shigo y'ar masu kud'i shiyasa ka maida kanka cikin ko in kula"to inda na godema Allah mahaifiyarta batada mak'iyi kamar ka Aduniya"yayi murmushi bece komai ba "na rasa wace irin tsana kayi mun dani da yarana Agidan nan?? kamar ba jinin kaba"yaron nan Abdallah daya fasa Auren Ahyaan "maimakon ka bashi khadijah shine ka tura masa Asma'u"yarinyar dako shekara 16 batayi ba"ga khadijah dake cikakkiyar budurwa....dama wannan zancen banzan yaka ki?shine zaki zo kimun tsaye saman kai kina mun mgn cikin rashin ladabi sbd ga sa'anki?"to bari kiji! bana neman kaida kai da y'ay'a nah"idan ita yace yana so zan Amsa masa"to ba ita yace yana soba ki yarda ko karki yadda damuwar kice"Abu d'aya nakeso na sanar miki shine"zainab d'in nan dai data tsare miki komai Arayuwa itace nakeso! sbd kyawawan halayenta"bana zaton zanso wata mace bayanta ko kamar irin son danake mata"bazan gaji da sanar miki sbd mahaifiyata nake zaune dake ba"muddin kika kaini mak'ura wlh zakiyi nadama"yana fad'in hakan yaja tsaki ya d'auki jaridarsa ya wuce cikin bed room d'in yabar mata parlourn gaba d'aya..
Bayan Dr darma ya gama Amsa wayar mu'az ya shafi fuskarta yace"parlourn zamu koma sbd kar wani yazo idan Anyi knocking ba zamu jiba bestie"to nidai ka d'aukeni mana"Angama sarauniya Aminatu"ko kuma nace Queen minart?ta saki murmushi ya mik'ar da ita tsaye ya jera fuskokinsu ya zaro wayarsa yafara yi musu selfie suna murmushi "sun shagala sosai da yin pics kiran khaleel ya shigo cikin wayarsa"yad'an tab'e baki tare da cewa"kiran me kuma yaron nan kemun?"ka d'auka kaji mana yaya babbah"ya dungure mata kai yana d'aukar wayar "sallama khaleel yayi yace"yaya gamu nan bakin k'ofa munata knocking "ko muba me gadi ne?"ah ah nidai su shigo"cewar Ahyaan dake sauraren su"ku jirah gani nan"yana fad'in hakan ya yanke wayar ya kalleta"bestie wayace miki Ana yima Amare sammakon zuwa?"su kawo su juya"in kuma so kike nayi kissing naki gabansu niba ruwana"ya k'are maganar yana kama hannunta suka fito tana girgiza kanta batayi mgn ba.yana rik'e da hannunta suka sakko down stairs d'in ya bud'e k'ofar Ahankali....."khaleel na tsaye yana waya da Alama da budurwansa yake wayar"yayinda Asma'u ke tsaye daga gefe rik'e da basket d'in "Autan mama k'araso mana"yafad'a yana d'an murmushi suka matsa"Ahyaan ta sakar masa mintsini tare dajan gefen sajensa da k'arfi yasaki k'ara"Khadija da khaleel suka kallesu"Ahyaan ta kama b'abb'aka dariya"yayi saurin matsowa zai cafkota ta ruga gudan bed room d'in Aguje"Atake uban gayyar ya rufa mata baya.... khaleel ya kama murmushi yana fad'in Asma'u Ajiye musu break fast nasu muyi tafiyar mu tunda bata tamu suke ba"itama tana murmushi ta Ajiye musu basket d'in saman center table"suka juya suka fita.
Ahyaan kuwa turo k'ofar taso tayi ta rufe, sai gashi ya sako kansa cikin d'akin "ta saki ihu tana fad'awa saman bed tace pls bestie kayi hak'uri kaga banda lafiya fa.lallaima habibty kinsan Aida baki lafiyar kika Jani bayan kinsan Ina tausaya miki ko? yak'are maganar yana haurowa saman bed d'in "da sauri tayi k'ok'arin sauka"ya fisgota ya haye samanta ya sake mata duka nauyinsa gaba d'aya"ta zaro Ido tana sakin nishi da k'yar tace"pls yayanah I'm sorry kanada nauyi ka d'agama mamy y'a tam"nak'i wayon"tunda kin jamun gemuna ni kuma Anan zan rama"ya fad'a yana Aza hannuwansa saman tudun nashanunta"pls broth yunwa fa nakeji"wayyo Allah mamy! ya kama dariya yana d'agata ya d'akkota suka fito daga cikin d'akin"k'asa kan carpet suka zauna kanta na saman kafad'arsa sai shagwab'a take zubawa son ranta shi kuma yana biye mata "sai d'an murmushi yakeyi yana duba komai da mamy ta shiryo musu"Aransa yana jin k'aunar mahaifiyar tasa na nunkuwa Aransa "ya lura k'aunarta da Ahyaan daga Allah ne"yakuma fahimci tasan tabbas sai wani Abu yafaru sbd irin Abincin data dafo sak.irin Abinda yaka mata mace ta cine idan ta tsintsi kanta cikin wannan matakin.shi kansa ruwan shayin yaji kayan yaji da k'amshi"ga naman rago ga shashshe me ruwa ruwa da yaji"wanda Ahyaan na gani taji ya burgeta"shi kansa chips d'in harda soup d'in k'oda aka zuba samansa"Abindai shar "bayan ya had'a musu tea d'in yadinga bata shibai shaba"dataga haka saita dena Amsa tama fara cin naman da tun d'azun k'amshinsa ke dukan hancinta"bestie pls kaci Nima Ai zanci komai ko?in kuma baraka ciba Nima haka"zanci habibty naso dai ke kifara k'oshi kisha magan...be rufe bakiba ta d'auki cup d'in ta nufi bakinsa dashi"beyi musuba suka cigaba da break fast d'in Atare"bayan sun idar yabata magunguna "da yake Akwai na bacci cikinsu danda nan ta kama bacci"ya sunbaceta ya tashi ya fita ya rufe ta da key....sai wajen k'arfe 12 na rana Ahyaan ta farka sbd shima knocking d'in dataji ne Anayi"ta tashi rik'e da d'an kwalinta ga hannu taje bakin k'ofar tana fad'in waye ne?"nice k'awata kona koma ne?"da sauri ta bud'e k'ofar "Khairiyyah da Asma'u suka shigo rik'e da botikan su,dubulan,cincin,Alkaki,nak'iya, dambun naman kaji da sauransu"Ahyaan ta tarbesu da murna suka shigo suka zauna"Asma'u ta kwashe komai takai kitchen "Khairiyyah tace Amarya baki laifi"kona kashe d'an masu gida"duk sukayi dariya gaba d'aya"na d'auka bazaki zoba?"ah ah dama nace bara na biya nayiwa su mamy ya gajiyar biki idan da
sak'o na wuce dashi"shine na samu Asma'u zata zonan sai muka taho tare"kafin Ahyaan tayi mgn khaleel da Isma'il sun shigo da kaya na cefane da drinks A hannuwansu"Amsa sallamarsu Ahyaan tayi tare da cewa sbd bestie ya Aiko ku shine kuka zo ko?"ba haka bane Anty Ahyaan "suka fad'a suna Ajiyewa suka fita"Ahyaan ta kira Asma'u ta fito ta dinga shiga da kayan cikin kitchen tana jerasu inda yadace "bayan sun kawo sauran suka sanar mata Anjima zasu dawo cin girkin Amarya "Ahyaan na murmushi ta d'auki wayarta tana fad'in ni baby tunda yafita bema kirani ba"Ayyah Ashe bawan Allah yaturo mun text ma "ta fad'a tana murmushi tana karantawa"Khairiyyah tace soyayya dad'i k'awata "kedai bari"yanzun ki tashi muyi sallah saimu Aza lunch"sbd nacema baby yasanar ma mamy kar Akoma kawo mana Abinci.gaskiya ne me baby "irin wannan soyewa haka"shareta Ahyaan tayi ta kira Asma'u "ta fito daga cikin kitchen d'in rik'e da waya baby Nokia da Alama waya takeyi da Abdallah mashi"ki zauna Anan Auta muyi sallah"idan mun fito sai kije kiyi.kanta ta gyad'a musu ta zauna gefen kujera....
Bayan sallar la'asar...��
wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba
7/21/24, 11:01 - Buhainat: � *AGE MATES* �


*71&72*






*Littafin kud'i ne!*




........bayan sallar la'asar Ahyaan na tsaye gaban mirror tana d'aura d'an kwalin red d'in lace me zanen golden dake jikinta"d'inkin fited gownt wacce ta bayyanah Asalin shape d'in jikin nata"fuskarta ta d'auki make up "sai wani irin k'amshi ke tashi Ajikinta"ko yaya tayi motsi sai mazaunanta sun juya.Khairiyyah ta bita da kallo tana ninke prayer mate d'in data idar da sallah Akansa tace"k'awata nifa wucewa zanyi dama munyi da Hjy karna wuce 4 ban dawo ba"na kuma lura babynki na hanya ko?"harara ta ballah mata tana fad'in kina nufin sbd shi zakice zaki tafi?"Khairiyyah na k'ok'arin mgn Dr darma yaturo k'ofar d'akin yana fad'in habibty ! Habibty!! kina Ina??ya fad'a yana rufe k'ofar fuskarsa d'auke da murmushi "lips nasa sun bushe"yana rik'e da hularsa ga hannunsa saiya musu sallama yana fad'in sarauniyata tare da k'awarta "Khairiyyah na murmushi ta gaidashi "ya Amsa cike da kulawa da tambayarta y'an gidan?yana kuma kallon Ahyaan data wani d'aure fuska tace"sannu da zuwa! yauwa habibty kinyi kyau sosai"ni kuma inata yawo cikin rana ga zafi ko?...K'awata Ina parlourn ki fito muyi sallama"ta k'are maganar tana fita"Dr darma ya matso yayi hugging nata ta baya"suka sauke Ajiyar zuciya Atare"ya jata suka zauna gefen bed d'in yasata saman cinyoyinsa yana sinsinar jikinta yana lumshe Ido....shine bestie kayi tafiyarka ka barni sai wani kirana zakayi ko?"naso ki d'auka dana kira"Amun Afuwa kinji?"wlh duk nayi busy Amma Alhamdulillah"bayan na fita Asibiti na fara zuwa"daga nan naje gida na gaishesu "sai kuma mukaje cefane "bayan nayi sallah muka tafi wajen zana'idar Abokin su daddy harma da Abba shiyasa kikaji shiru Ayi hak'uri bestie kinji?"nifa dama ba fushi nayi ba"toba kinyi wanka ba ni bandani"tayi murmushi sbd ya bata dariya daya kwaikwayi muryarta"ga jin nauyin ta masa zaune Ale Ale saman cinya tana ji"yaka mata ki had'a Ido dani sai kije wajen k'awar taki kuyi sallama "inaso ki dawo zanyi wanka"zuwa k'arfe 5 su mu'az zasu xo gulma da k'wak'wa "kai bestie baka ji ko?"ta fad'a tana murd'e masa kunne "ya d'ago kansa ya kalleta suka had'a Ido"Atare suka saki murmushi saita rufe Idanunta "kin san Allah ki bud'e idon"ya fad'a yana matso da fuskarsa saitin tata har tana jin hucin numfashinsa "da sauri ta bud'e idon"yayi saurin had'e bakinsa da nata yana tsotsa kamar zai cinye bakin....duk yadda taso ta janye Dr darma kin bata damar hakan yayi"saima janta saman bed d'in yayi suka kwanta yafara lalubarta"gaba d'aya ya shanye jam bakin dake saman lips nata tas"ganin zai zuge mata zif d'in riga ya saka ta rik'e masa hannuwa tana girgiza kanta murya Amarairaice tace"Khairiyyah fa nanan dan Allah,hakama Asma'u,kuma su khaleel zasu zo...Ina ruwana da suna nan habibty?"chakulkuli ta kama yimasa,ya cikata ta sauka da sauri tana dariya ta fice"ya lumshe Ido yana yin matashin kai da hannayensa"gaba d'aya kasala da mutuwar jiki sun dirar masa"ya kalli gefensa yaga duk saman bed d'in ya yamutse"gaskiya habibty dole ki daure ki zama jaruma"ya fad'a yana tashi yanufi gaban ward rope nata ya bud'e ya d'auki towel d'inta dake ninke Ajiye"Anutse yafara rage kayan jikinsa ,sannan ya d'aura towel d'in yashiga bath room....da murmushi A saman fuskarta ta sakko k'asan,Khairiyyah ta bita da kallo ta kama y'ar dariya sbd ganin babu jam bakin saman lips nata ya goge"Anty Ahyaan Ina wuni?"cewar su khaleel da Isma'il da suke zaune a tsakkiyar carpet suna cin Abinci ga snacks da drinks da Asma'u ta kamasu"zama tayi suka gaisa sannan ta wuce kitchen ta had'o ma Khairiyyah kaya masu yawa na dangin su dubulan,cincin,nak'iya da Alkaki da snacks.bayan ta fito ta sameta tsaye gefen k'ofar fita tana waya da hajiyarsu"k'awata gashi ki kaima hajiyarmu sai munyi waya ko?saida ta kashe wayar kafin tace"to shikenan godiya muke"nidai keda ganina sai bayan wata 3 "harara ta ballah mata"Allah kuwa sbd ba'a zarya gidan sabbin Aure "kedai kika sani idan yaran can suka jiki ba ruwana"tana dariya ta bud'e k'ofar ta fita"Ahyaan kuwa upstairs d'in ta wuce "kai tsaye bed room d'inta ta nufa ta samu yana wanka
...shine broth zaka mun wanka Adak'i bayan ga naka d'akin ni bana gayya"ta fad'a tana murmushi ta fita.bata jumaba ta dawo rik'e da wani gogaggyan yadi navy blue da farar vest da boxer data feshe da turaruka ta Ajiye masa gefen bed "ta nufi gaban mirror kenan shi kuma ya fito"ta juyo suka had'a Ido "da sauri ta sunkuyar dakai k'asa"ya girgiza kansa tare da cewa har yanzun kunyar?"nidai baga d'akin kaba?"to Anan nakeso in kuma zaki koreni zo mugani"zan iya mana"to shikenan zoki fiddani ni kuma na miki Alk'awarin har goyaki zanyi"Ahyaan ta saki murmushi me sauti har hakoranta na bayyanah tace"to Ai k'arfi zaka nuna min ko?"ai dama bakida wani k'arfi "shiru tayi tajawo stool tace"zoka zauna na maka shafa"ba musu yazo ya zauna ta d'auki body cream nata da Ayauma ta fara using dashi"Anutse ta fara shafa masa daga bayansa zuwa k'irji da wuya"ya lumshe Ido sbd shine kawai yasan me yakeji Ajikinsa "ganin idan ya bari tana masa wannan shafar komai zai iya faruwa sai ya mik'e tsaye yace"bara na zare towel d'in Ashafa ko Ina"nidai Allah bazan iyaba ka shafa nan mana da kanka"kinma Isa yarinya kece zaki shafamun"yafad'a yana sakin towel d'in k'asa "da gudu Ahyaan ta fad'a saman bed

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login