Showing 6001 words to 9000 words out of 112373 words

Chapter 3 - AGE MATE'S Complete Document book by Momy Fareesa .txt

23 Dec 2024

12851

kara wayar sa gefen kunne ya fito daga cikin motar da Alama Fatima yake kira"Ahyaan kuwa tsaki taja tana fad'in wlh mu zuba nida mutum....waye kike ma tsaki? ya fad'a murya Adake"ya juyo yana binta da wani razanan nan kallo, sbd ya tsani Amasa tsaki"cike da rashin kunya ta d'ago kanta suka had'a Ido! Duk sai taji ta daburce saboda mugun kwarijinin daya mata da cika waje... Amma dukda haka saita zabga masa harara tana janye Idanunta tace da wanda ya tsargu nake"Azuciye ya fito daga cikin motar har huci yakeyi ya nufi back sit d'in Azafafe"Adaidai lokacin kuma Fatima ta fito daga cikin get d'in gidan su"mu'az nata k'ok'arin dakatar dashi Amma yamasa banza ya bud'e k'ofar"Ahyaan kuwa ta gudan gefen damarta ta bud'e tayi wuf ta fito sbd tsoron Abinda zai mata musammun da taga ta fusatashi"saidai zuciyarta fes da fushinsa tayi tsaye daga gefen motar "be hak'ura ba sai nufarta ya komayi"ta wani tsuke fuska murya can ciki tace"wlh kana cin zalin nawa ba k'yaleka zanyiba saina rama na kuma baka kunya gaban yarinyar "ta kare maganar tana tab'e baki ta wani ci face "d'an dakatawa yayi domin zancen gaskiya beson mutuncinsa ya zube a idon Fatima, musanmun da yau ne zai fara had'uwa da ita"saidai da yake kaifi d'aya ne saiya nuna kamar zancenta be shige saba ya koma had'e rai yana tunkaro gefenta"itama saita dake ta tsaya tana satar kallon mu'az da Fatima da suke kashe juna da murmushi"ta tab'e baki Aranta tana fad'in" *jikinki yakeso* "sbd Aganinta duk idan namiji yace yana son mace tofa jikinta yakeso....wuce muje! sautin sanyayyar muryarsa me cike da dattako ta katse mata tunani "k'in kallonsa tayi"shi kuma be damuba ya matso ya finciko hannunta "kaga bansan wulak'anci Akanme zaka wani dinga tab'amun hannuna?"ko dama London d'in dakaje tab'ara ka koye ne?"idanma Akwai Abinda yafi tab'ara duk na koyo kuma Akanki zan sauke Abinda na koyo d'in"saidai da Alama har yanzun naga kanki na rawa"Amma fa Ashirye nake dana saita miki shi"ya fad'a normal tamkar maganar Arzik'i sukeyi"ita kanta Fatima ta d'auka masoya ne wuf d'aya data kallesu.....zaki wuce muje ko kuwa saina jaki ta k'arfi ne?"d'an murmushi ta saki me sanyi da yayi mata wani irin kyau kamar me rad'a tace "kaima kasan dama idan bata k'arfin ba Ai baka Isa ka tur sasani da kurin kaba har naje "mezai hana ka dena nuna k'arfin "*many Ansha tatala*" ?ta kare maganar tana kecewa da dariya domin tasan ta k'ulesa data fad'i hakan daga k'arshen maganarta ...."tun yana yaro haka yake cewa idan zasuje siyan k'ank'arar kwarbebe"sau d'aya ya kalleta ya maida idanunsa k'asa bece komai ba, saidai yata naji Abinda zai mata da saiya sata kuka"duk yadda taso taga ya fusatu k'in nuna ya fusatun yayi, be kuma cika hannun nata ba yajata da d'an k'arfi suka nufi wajen su mu'az dake tsaye gefen get d'in gidan su Fatima suna mgn.....kaga bansan iskanci ka cika mun hannuna mana"ta fad'a tana son turjewa"tamkar da bango take mgn haka yamata banza"kasan Allah cizonka zanyi! duk ya share yanama kallon wani wajen"saida suka iso gefensu yad'an saki fuska yana musu sallama"Fatima ta Amsa tana murmushi tace"na d'auka Ai bazaku iso da wuri ba sai Angama firan soyayya?"ya mutsa fuska Ahyaan tayi tace"Allah ya kiyaye nayi soyayya da k'a.....nayi soyayya da d'an uwana"ta furta ba shiri sbd wani Arnen mintsini da darma yasakar mata gefen hannunta"gurin har saida yayi ja"kasancewar ta chacoolate colour ce itama fatar jikin ta.... mu'az kuwa dariya ya kamayi sbd jikinsa ya bashi wata muguntar Darma yamata shiyasa tak'i furta Abinda tayi niyar fad'a tun farko"saita canza "Amma sbd kafiya irin tata sai ta kasa cewa yayanta ta juya zancen zuwa d'an uwanta....Masha Allah! Ashe yayanki ne? na d'auka Ai masoya ne ku"Ina wuni ya gida??"ta fad'a tana yaba tsarin had'uwar Abokin mijin nata dashi da sister nasa"Anutse darma ya Amsa mata da tambayarta y'an gida kafin yasaka hannunsa ya d'alli lips d'in Ahyaan yana fad'in baki iya gaisuwa ba?"bata kallesaba Amma taci burin saita rama"saita d'an yi murmushi tare da cewa na bari ku gama gaisawa ne"hakane Ahyaan "my princess ga Ahyaan nan Ina fatan zaku zama friends da ita"cewar mu'az"in sha Allah "ya gida yasu mama?"cewar Ahyaan "Fatima ta Amsa cike da kulawa tana fad'in zo muje ciki ku kuma kuje kuyi sallah"dukda Ahyaan bata so shiga ciki ba kodan sbd karta bi umarnin wannan d'an iyayin Amma saita nuna zata bita da nufin idan sun tafi ta fito ta hau Adaidaita ta koma gida"sai ta koma had'a masa bom wajen Mamy"duk Darma na hankalce da yanayin ta,kuma jikinsa na bashi Akwai Abinda zatayi idan sun tafi yasanta da shegiyar kaffiya kan ra'ayinta"kallonsa tayi ta zabga masa harara tana fad'in bazaka cikamun hannun ba?"be cikaba sai matsowa yayi da fuskarsa dab da tata murya can k'asa yace"kinsan Allah idan muka tafi na dawo na samu kin gudu zane miki jiki zanyi muka koma gida"karkiga kin koma wata y'ar lukuta kiyi zaton bazan iya hukuntaki ba......tsabar yadda ya kasheta da takaici kasa mgn tayi sai Ido kawai"ga k'irjinta nata fat fat fat!! sbd kusancinsu da yayi yawa"ga fad'uwar gaba datake ji"itadai Fatima na tsaye tana satar kallonsu zuciyarta na mata kokonton bata yadda shida ita yaya ne da k'anwa ba saidai ko cousin d'inta neshi"mu'az kuma yasha Alwashin yimata baya nin dangan takarsu daga baya.... Ajiyar zuciya Ahyaan ta sauke sbd cika mata hannunta da yayi"Fatima ta matso tana murmushi taja hannunta suka wuce cikin gidan"tana lura da darma na Aiko ma Ahyaan da harara......sosai Ahyaan ta yaba da kirkin y'an gidansu Fatima"badan tasoba tabi fatima d'akinta sukayi sallah"kafin su gama mamanta ta shiryama Ahyaan Abinci da lemo da ruwa"kasancewar yunwa takeji ga gajiyar mota saita daure ta fara cin Abincin suna fira da Fatima"Ahaka kiran Mamy ya shigo cikin wayarta k'irar IPhone 11 11"d'an murmushi tayi ta d'auka tana fad'in Mamy nah?"daga d'ayan bangaren Mamy ta sauke Ajiyar zuciya tace"Ahyaan duk na damu da naji shiru saida na kira Nura yanzun yace mun wai kun biya ta gidan su yarinyar mu'az zaku gaisa da ita?"Eh hakane Mamy"Ina fatan sababben me miki wani abu ba?"be yimun komai ba Mamy yanzun ma zamu taho gida sun tafine suyi sallah shida yaya mu'az"Amma ga Fatima ku gaisa"ta k'are maganar tana mik'a ma Fatima wayar"ta Amsa suka gaisa da mamy Amutunce kafin suyi sallama"ba'a fi mintina ukku ba da gama wayar tasu ba mu'az yakira yace su fito zasu tafi"Ahyaan ta wani tsuke fuska tana fad'in wlh saina b'ata masa lokaci "saida Fatima ta kashe wayar ta kalleta da murmushi sbd ta fahimci Ahyaan zata girme mata"wai dan Allah keda darma da gaske y'an uwa ne?"uhmm! Amma causin d'ina ne"daga haka tayi shiru taci gaba dacin Abincinta.....sau biyu mu'az na koma kiran su fito Amma Ahyaan tak'i fitowa"ba k'aramin hassala gogan naku yayi ba"sbd yana so yakoma gida yanada uzurin da zaiyi"ya lura saiya biyoma yarinyar ta bayan gida tukum zasu daidaita"Ayanzun beso ya tafi yabarta sbd yasan saiya sani Awajen Mamy"musammun data kirashi yanzun taji lafiya basu isoba sai fad'a take masa"wannan dalilin kawai zai saka ya jirata Amma zata gane kuranta..... gaskiya *Darma* baka kyautawa ko kad'an!ya wuce Ace har yanzun kaida Ahyaan kuna irin y'ar haka tsakanin ku.....kaga mu'az ka rabu dani "sanin kankane bazan d'auki rainiba"Agabanka fa yarinyar nan kemun Abinda ta gadama kana wani bata hak'uri"d'azun harda kama yimun dariya ko?"mu'az na k'ok'arin mgn Ahyaan da Fatima suka fito daga cikin gidan.....kicin kicin darma yayi da fuska beko kalli gefen da take ba, cike da shan k'amshi yace"princess d'in Abokinah zamu wuce"to shikenan ustazah muna godiya da ziyara"d'an murmushin gefen baki yasaki tare da cewa abakin Abokinah kikaji wannan sunan ko?"Eh mana"duk sukayi murmushi Fatima ta rakosu gefen motar ta musu godiya bayan ta Amshi contact d'in Ahyaan sannan ta wuce ciki"wannan karon mu'az ne yashiga driver sit sbd yasan halin mutumin nasa yadda ya shak'a d'in nan zai iya zubar dasu kan titi "saidai ganin Ahyaan taja tayi tsaye tana danna waya yasaka shi fad'in tsayuwar me kikeyi da bazaki shiga mu wuce ba?"ya mutsa fuska tayi tak'i mgn tana cigaba da Abinda takeyi"Afusace ya matso ya bud'e k'ofar back sit d'in "yana k'ok'arin kama hannunta da nufin yaturata ciki sai tayi wuf ta shige ta zauna tana yatsina tace" thanks my k'ani ,dama na tsaya saika bud'e mun k'ofar saina shigo"ta k'are maganar murmushi na sub'uce mata ",duk yadda mu'az yaso danne dariyarsa kasawa yayi saida ya fara"saidai DARMA bece musu uffan ba daga shi har ita"ya zagaya ya shige gefen me zaman banza zuciyarsa na k'una tare dashan Alwashin yanzun suka fara wasan zai barta tayi iya nata idan Aka fara nashi tofa ta shiga ukku"har suka doso cikin layin Anguwar tasu babu me mgn Acikinsu"tun kafin ya gama parking Darma ya bud'e k'ofar ya fito ya wuce cikin gida ko sallama be masaba sbd ba k'aramin haushi yabashi ba"yayinda Ahyaan zuciyarta fari k'ar ta fito tana fad'in dan Allah yaya mu'az bara na turo Ad'auki troley d'in kayan nan"dato ya Amsa ta masa godiya ta fito cikin takunta na Isa tamkar wata tarwad'a haka ta nufi bakin get d'in gidan nasu very slowly "mu'az ya bita da kallo ya girgiza kansa yana mamakin ko tsinin takalmin k'afarta basu takurata wajen tafiya, kamar bada takalmi me tsini take tafiyar ba"may be ta riga ta saba saka irin su"ya fad'a Azuciyarsa...... Akan idon babban yaron Mr mahuta dake bibiyarsu tun d'azun ta shige cikin gidan nasu"hakan ya tabbar masa da cewa Anan ne gidan su"sai kawai yaja nafef d'in ya wuce da nufin zuwa yamma sai ya dawo yayi binciken wacece ita,miye Alak'arta da darma??wanda Mr mahuta ne yabasa yin wannan Aikin.....kai tsaye sashen mamy ta fara nufa cike da kewarta"batama fara nufar sashensu mama ba"mamyn na zaune a parlourn tana lazimi da Alama sallar Azahar ta idar"Darma na zaune gefen kujerah yacire p.cap nasa ya aza k'afa d'aya kan d'aya goran ruwa me sanyi Ahannunsa yana sha"sai tambayarsa Ina Ahyaan d'in mamy keyi ?sau d'aya yace gata nan zata shigo.....Mamy najin sallamarta ta mik'e tsaye cike da murnan ganin y'ar tata tana fad'in ga Ahyaan d'in Mamy da daddy"da gudu Ahyaan d'in ta rungumeta tana fad'in I miss you so much my mamy! ta k'are maganar suna cika juna suka zauna kan kujerah"Ahyaan na d'an murmushi ta wani baje kan kujerah tana kallon parlourn sbd yadda ya canza mata"Ahankali tace"Ayyah broth troley d'in nacan Amota yamun nauyi bazan iya d'auka ba pls"ta k'are maganar cikin marairaice murya"Aranta dama Tasha Alwashin shine zai koma ya d'akko mata shi "d'ago kansa Darma yayi yabita da kallo saidai tak'i yadda ta kallesa"jin yayi shiru yasaka Mamy cewa katashi mana ka shigo mata da troley d'in "beyi mgn ba yanata cin magani ya mik'e tsaye Ahyaan ta kallesa suka had'a Ido"gwalo ta masa ta d'auke kai tana fad'in Mamy su khaleel fa?"sun tafi skul harma Autah"dukda yanata murnan dawowar ki"Allah sarki baby hamza"Amma mamy parlourn nan yayi kyau wlh "Eh Nura ne yamasa wannan gyaran"gaskiya broth ya kyauta daya k'ara gyara mana parlourn mu"ta fad'a cikin jin dad'i"Adaidai nan
ya shigo cikin parlourn rik'e da troley d'in kayanta yana turowa"Amamakinta fuskarsa bbu irin d'aurewar nan"sai kuma taji gabanta yafad'i! kodai ya shirmun wani abun ne?"ta tambayi kanta"sai kuma ta basar dashi cikin jin k'warin gwiwar ganin daidai take dashi"har d'akin baccin mamy ya shigar mata da troley d'in kafin ya dawo inda ya zauna ya d'auki p cap d'insa"itadai tana satar kallonsa tana mamakin yadda ya koma yakuma canza.... Ahyaan tashi kiyi wanka kici Abinci?"to mamy Amma Ak'oshe nake sai Anjima zanci"to shikenan me kikeso na k'walama sai Asiyo miki?"kauda kansa Darma yayi ya mik'e tsaye da nufin yanufi dining area yaci Abinci"karma Mamy ta sara masa Aiki game da Ahyaan "
. Ahyaan kuwa na lura dashi sai tayi murmushi tace "Ai mamy yanzun nadena irin wannan yawan ciye ciyen musammun Abu me sanyi sosai"ko ice cream yanzun bana sha"Amma dai bara na fito sai naga meye nake so?"to shikenan kinje can cikin gida wajensu mama?"ah ah banjeba"to tashi kije ku gaisa saiki dawo kiyi wankan"dato ta Amsa ta d'auki mayafinta daya zame ta aza saman gashin kanta dake d'aure yaji gyara"kan idon mamy ta kalli darma ta masa gwalo ,shi kuma ya wurgo mata harara "d'auke kanta tayi tamkar bata gansuba"Ahyaan ta fita shi kuma ya zuba Abincinsa ya fara ci Anutse yana lumshe Ido sbd mamy ba bayaba wajen iya girki.....
Da murnah da farin ciki mamah ta tarbi Ahyaan da Asma'u Autah da bata jima da dawowa daga skul ba tana js3 yanzun"yayinda ummah gaisuwa kawai ta had'asu da Ahyaan"ba k'aramin haushi tajiba da irin yadda ko yaushe Ahyaan d'in canzawa takeyi"saidai Aranta tace Abanza kyau ba miji"ko Aikinma bazaki samesa ba indai Ina numfashi ta fad'a Aranta"Khadija kuwa da k'yar tace mata Ahyaan Ina wuni?"ko Amsawarta bata jiraba ta saki labulen parlourn mama tayi gaba"Ahyaan taci face tana jan tsaki tace"mama ni yarinyar nan zata kira sunana tsagaga?"ko khaleel da Abdul Aziz Anty suke kirana sai ita?....bance ki damuba balle harki tada kanki ki kallah "ita rayuwa kome kayi me kyau ko marar kyau sai Ammaka"iya sanina kin bata shekara goma sha biyu da haihuwa"Amma bance kice komai ba"kima tashi kije ki watsa ruwa"in kuma Anan zakiyi shikenan "ni can zanyi wankana wajen Mamy nah"mama na murmushi tace to shikenan Ammah ta kirani tace kin sauka? nace mata Eh kawai"Amma ki kirata ko?"Eh dama zan kirata"Abba be dawo ba?"sai yamma keda ganinsa gaskiya"Abdul kuma exams yakeyi shida Affan duk sai yamma zaki gansu"okay kawai ta fad'a ta mik'e tsaye ta nufi wajen fridge ta bud'e taga ruwa swan da lemo na roba jere"ahhh su mama kun zama y'an gayu keda mamy nah ko Ina yak'ara kyau"ta fad'a tana d'aukar lemo guda d'aya ta rufe fridge d'in ta zauna tanata y'an kalle kalle cikin parlourn"kedai bari Ahyaan duk Aikin Nura ne daya dawo ya canza mana kujeru Akayi soma ,yamana fanti"drinks kuma khaleel da Abdul ne suke kamana wai musha muba bak'i "gaskiya ne inaga broth yayi kud'i"murmushi mama tayi tace"Ai yanzun dai chemist yake zuwa zaidai fara Aikin dai koda safe munyi mgn da Alh"yacemun kema yake jira ki dawo Akwai Abokinsa da sukayi mgn game dake yace akawo takardun naki za'a samar miki Aikin in sha Allah "ihun murna Ahyaan tayi ta rungume mama"bazaki girmaba ko Ahyaan? "ta fad'a tana murmushi "itama tana murmushi tace burinah dana gama karatu na sami Aiki mama kodan sbd nadinga kyautata muku keda mamy nah Ina saku farin ciki....mamah na k'ok'arin mgn inna Asabe yayar Abba ta yaye labulen d'akin ta shigo fuska Ad'aure tanata y'an Harare Harare"sau d'aya Ahyaan tace mata Ina wuni?"daga haka ta mik'e tsaye "Adak'ile ta Amsa tana kallon mamah dake gaisheta tace"yauwa zainab bani 300 zan bama me nafef na jirana waje"d'an murmushi mama tayi sbd tuni tasan matar nayi mata hassada"koda take makka bata fasa kiranta da zainab kai tsaye ba"sai tace Aiko banida changi"to ki bani Asamo mana"murmushi ta koma saki kai tsaye tace banyi niyar bayarwa ba"kije wajen y'ar uwarki luba ta baki mana"iyye! lallai zainab kin Isa"to ko iliyasu k'asa dani yake balle ke"in bacin nasan kud'in na dan uwanane kinma Isa nazo nace kiba nii?"banza mamah tayi mata ta d'auki remote ta kunnah tv"Ahyaan kuwa Azafafe ta fita ranta Ab'ace "wani irin tsanar dangin mahaifin nata na k'aruwa Aranta"bayan mama data haneta da k'in shiga sabgarsu da wlh ta gaya mata mgn"tana fitowa daga cikin parlourn Mubarak na shigowa tsakar gidan"yayi wani shegen aski irin na mararsa jin mgn da tarbiya"ga asdown yayi baki yayi bak'i k'irin sbd shaye shayen da yakeyi Ab'oye"saidai Abin mamaki yana ganin Ahyaan ya had'e rai ya d'auke kai beko kalli gefen da take ba"itama nunawa tayi tamkar batama tab'a sanin saba"dan idan jin kai da izza yakeji to ita tafishi iyawa fintin kau.....tana k'ok'arin shiga parlourn shi kuma yana k'ok'arin fitowa"da sauri tayi baya sbd takusan fad'a masa"yamutsa fuska yayi yatsaya yak'i matsawa yana binta da kallo"Atake ya fahimci ranta Ab'ace yake"dallah mlm ka gyara na wuce"ta fad'a cikin masifa"shi kuwa dayake jiranta yakeyi saiya fake bakin k'ofar parlourn yak'i matsawa"ta saki k'aramin kuka tana turashi da kiran sunan mamy"Adaidai nan taji sallamar inna Asabe "pls broth ko tace kabata 300 kace baka dashi"matsa na wuce"bece komai ba ya janye ta wuce ciki da sauri"shi kuma be bar wajen ba"jikinsa na bashi innah Asabe tayima Ahyaan wani rashin kyautawa"harga Allah shima dangin Abba basuyi masaba"in bacin sbd mamy da mama ko gaisuwa bazata had'asu dasu ba"Ina wuni?"ya fad'a da k'yar zai rab'ata ya wuce"lafiya qlau Nura"dan Allah ko Akwai 300 wajenka zan sallami me nafef, wlh babu chanji" *bani dasu* shine Abinda yafad'a yana yin gaba Abinsa"Aransa yana mata tur da Allah wadai"Akallah zatayi shekara sittin da wani Abu Amma ta tsaya tana rok'o"ada tayi niyar shiga wajen Mamy komai ta tuna oho saita fasa tayi gaba tana mai tsananin jin zafin nura.... Ahyaan duk tana lab'e ta window tana ganin komai"bayan ta tafi ta shiga yima mamy dake zaune tana kallonta bayanin komai...."Ai Ahyaan mutanan can basuda hali"bansan meye suke so su maida Abbanku ba?"daga ita har harira basu sati d'aya basu zoba"suci na dare nan suci na rana nan"abasu kud'in Abin hawa"yanzun da sukaci suka gyare sai in sunzo suce abasu kud'i subama me nafef"koda ta shigo wlh nima bazan bataba"basuda tausayi kansu kawai suka sani"sai yawan bani bani da suke matsama Abbanku dashi suna zubar da mutuncinsu"cikin takaici Ahyaan tabar parlourn ta wuce d'akinta......bayan sallar isha'i tana zaune a parlourn kan kujerah Tasha wankanta da k'ananun kaya jikinta tana kallon indian firm"yayinda Mamy tana sashen daddy"ada itada khaleel ne ke fira a parlourn saiya fita"sbd ya Aiki hamza be dawoba shine yabi bayansa"tana cikin kallon taji fad'uwar gaba "hakan kuma yayi daidai da aka turo k'ofar parlourn, k'amshin turarensa me ratsa zuciya ya kaima k'ofofin hancinta ziyara"cike da shan k'amshi ya shigo da sallama "yana sanye da jallabiya Ash me gajeran hannu kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login