Showing 111001 words to 112373 words out of 112373 words
Chapter 38 - AGE MATE'S Complete Document book by Momy Fareesa .txt
 tausayinsa Aranta"ta jawo yaran nata ta nuna musu shi sbd shine kawai ke basu sani ba"tace"kunga wannan ?shima uncle d'in kune kamar su uncle khaleel Kuna jina?"duk tana maganar ne da indian ci"su Asma'u nata dariya wai suma zata koya musu.....daga bisani gaba d'aya su Ahyaan sukayi shashen mamy da nufin suci Abinci su huta sannan su tafi nasu gidan Aci gaba da hidimar murnar cika shekara goma da Aure da sukayi....misalin k'arfe 4:30 pm gaba d'aya haraban gidan Dr nurah darma ya k'awatu da decorations na Alfarma, ga tables &chairs da mutane zasu zauna"daga nesa kuma wata kujerah ce 2 seeter Ajiye wacce zasu zauna shida Ahyaan"ga cake babba Ajiye saman wani table"dangi da y'an uwa da Abokan Arzik'i na zazzaune wasu ma'aikata nata raba Abinciccika da drinks da namomi"gaba d'aya gidan Ankara canza masa fasali"yayi kyau k'arshen kyau"Abin sai godiya"Anutse wata mota ta shigo tayi parking "kafin wata mace da yara 3 suka fito daga ciki"saida na duba sosai naga Ashe Khairiyyah ce"yara biyu mace da namiji na biye da ita"sai wata baby girl da zatayi 8 month rik'e A hannunta"kai tsaye katafaren babban parlourn gidan ta nufa.....Dr darma da Ahyaan na zaune tare da yaran nasu me photo nata musu"suna sanye da riguna iri d'aya"wanda daga bayan rigar An saka *happy Anniversary Mr &Mrs nurah darma*! gaba d'aya duk riga da wondo ne suka saka"Ahyaan ce kawai ta saka siket na jeans navy blue irin kalar t shirt d'in jikinta ta yane kanta da veil navy blue....tana daga gefen Dr darma zaune ya dafa gefen kafad'arta suna murmushi,yayinda yaran ke tsaye su biyu"sai Ahyaan ta rik'e babyn"yayinda Ahmed ke zaune saman cinyar Dr darma "ba k'aramin kyau sukayi ba"Ahaka me photo ya d'auka "Ahyaan ta kalli Khairiyyah ta wurgo mata harara tare da cewa ki koma mana. haba k'awata! tunfa jiya mukazo garin nan muka kwana Agida sbd jiran dawowarku"gobe kuma nakeso na juya kar both yadamu ko?"wlh nayi missing naki sosai k'awata "yarana kuzo mu gaisa"ba musu suka.nufeta sbd sun santa itama ta waya.dr darma ya matsa suka gaisa"kafin su had'e kai itada Ahyaan suna k'us k'us "yana murmushi yace"gulmarmu Akeyi idan kun gama ki taso muje daga waje"dato ta Amsa gaba d'aya suka fita"sai sautin kid'an music ke tashi"MC na hangosu yafara mgn da Asaurara"hakan yasa kowa yayi shiru"sai kallonsu Akeyi har suka iso suka zauna"Aka bud'e taro da Addu'a Dr darma yayiwa kowa barka da zuwa kafin suje su yanka cake"aka dinga yi musu tafi"sai gab da magrib taro ya watse saidai muce Masha Allah.....bayan sallar magrib suna zaune a parlourn Ahyaan na mgn da sabbin masu yimata Aiki yayinda Asma'u ke kwance saman 3 seeter "sai kallonta Ahyaan keyi tana d'an murmushi had'e da girgiza kanta"sbd tasan komai Allah keyi"yanzun Asma'u duka shekarunta 25 Aduniya gashi zatayi haihuwa ta ukku"ita kuwa saida tayi 28 yrs sannan tayi Aure "tanada 29 yrs tayi haihuwar fari"ta tabbatar tsaikon Aurenta nada Alak'a da Dr darma ne mijinta da kuma sanadin zuwan AA rayuwarta har haka yafaru ya Auri k'anwarta.... Assalamu Alaikum! muryar AA ta katse mata tunani "ta d'ago kanta ta kallesu shida Dr darma daya shigo dashi ciki"rabonta data gansa tun ranar dayazo neman gafaranta kwana 2 da Aurenta da Dr darma "garama takan ga pic nasu shida Asma'u. Amma ko mgn ta waya basu tab'a yiba.....fuska Asake ta Amsa tana murmushi tace"Abban khalifah! kaine Agidan namu?"yo Ai bestie da bance ya shigo ba wai daga bakin get zai tsaya sai kace wani bak'o?"cewar Dr darma suna zama kan kujera "AA ya kalli Asma'u ta sakar masa murmushi,shima yamaida mata duk Ahyaan na lura dasu"cikin barkwanci suka gaisa yana tsokanar Ahyaan wai matarsa dai batayi Aikin wahalaba kar Abarsa dayin tausa da dare"duk sukayi dariya "ita Asma'u nauyinsu ma takeji"ta tashi ta wuce d'aki Ahyaan ta biyota"kusan Akwati guda ta bata tsaraba dake cike da kayan baby"sannan suka fito tare ,harma AA yafita shida yaran.bayan sun fita Dr darma ya zauna gefenta zai kwanta saman cinyarta tayi saurin cewa"bestie karfa yaran nan su shigo?"Ina ruwana ni"kinsan me?"saika fad'a "wlh duk idan na tuna AA yasoki sai naji zafi Araina"sadeeq kuwa har yanzun iyakata dashi gaisuwa"tunda yasan na Aureki ya k'ullaceni"Hjy kafin ta rasu sau kusan biyu muna waya tana cewa karna yi gaba da sadeeq "to ai gashi ita ta mutu ko bestie?"ya kamata ka manta da komai tunda shima yayi Aure ko?hakane bestie "wlh munyi Abubuwa ba kad'an ba"kinga idan nakiraki sadda muna gida naji wayarki busy ko bacci bana iyawa"nayi kishinki kamar hauka"duk masu cewa suna sonki nafi kishin sadeeq da Mahuta "naga Alama Ai"ta fad'a tana dariya had'e da murd'e masa kunne "ya rungumeta yana fad'in yaka mata bestie ki k'ara bani yara biyu kinga 6 kenan"daga nan in sha Allah saimu rufe haihuwa sun ishemu rayuwa"yanzun da munkai 45 yrs haihuwa zata miki wahala sbd kin d'auki hanyar girma ko?"nidai broth haihuwar da wahala"in bacin Allah yasa kana likitah da wahalar da zanci saita fi haka" daurewa zakiyi ki k'ara banaso har mu Aurar da Amnah kina haihuwa"wlh kuwa bestie da kunya siriki yaji wai sarkuwarsa ta haihu, bazan iya wannan kayan kunyarba"hmm! saidai idan be kamaba Amma ko Ajikinah"miye Aciki dan sirikinmu yasan mun haihu?"Alamar baban nasa nada ishashshiyar lafiya kenan ko?"yafad'a k'asa k'asa yana d'age gira "nidai daddy ba ruwana ka tashi kaje masallaci kabi jam'in sallar isha'i"to shikenan habibty"idan nadawo Anjiman pls ki dubani"2 days fa yaka mata ki tausayamun "ta sunkuyyar dakai tak'i mgn"kinji bestie?"nidai baby kaje kayi sallah mana"ta fad'a cikin shagwab'a "ya lakkace mata hanci yatashi yafita....washe garin ranar misalin karfe 9:18 am suna tsaye gaban mirror a master bedroom d'insu "dataji kayan k'awa tamkar suna k'asar turai...lolx"suit ne golden brown Ajikinsu"sam fuskarta bbu walwala "tana gyara masa suit d'insa ta feshesa da turare"habibty wai wannan fushin duk na meye?"yafad'a yana rik'e hannayen ta"ni kuma?"murmushi ya saki ya rungumeta Ajikinsa tayi lamo"murya can ciki yace"nasan kishi ne ke damunki "nifa nakine kin sani?to meye na damuwa?"so nakeyi daga nan mu wuce gidan mu'az ku gaisa da Fatima sai mu wuce tare dashi"Ayi komai gabanki is okay?"to wai ma'aikatan da zaku d'auka ba duk y'an mata bane?"koma sune me ruwana dasu?"kinga dake nurse ce shikenan muna tare har Asibintin ko?"tayi shiru tak'i yin mgn"bestie kenan bazaki girma ba ko?"dama Ana girma ne wajen miji?"ah ah jinki nakeyi kamar y'ar 2yrs "tana k'ok'arin mgn sukaji knocking"ta yamutsa fuska tana fad'in nasan yarinyar nan ce Nanny d'inta ta maidota"ta fad'a tana zare jikinta daga nasa taje ta bud'e k'ofar....Hjy gata ta farka Angama shiryata dama"batayi mgn ba ta Amsheta ta wuce da ita ciki"gefensa ta zauna ta gyara rigarta ta fara shayar da ita"ya bisu da kallo yana murmushi yace"saifa kinyi sauri bestie time na tafiya "gashi inaso naje skul d'in da Akayima yaran nan transfer muyi mgn"to kodai kaje tunda sauri kakeyi?"bestie yau na lura kina so muyi fad'a dake ko?"haba bestie! saidai idan Allah yaso hakan Amma bana son Ina maka laifi sai bisa kuskure"hakane mace ta gari"kadena fasamun kai mutumin kirki"duk sukayi murmushi Atare yanata kallonta da breath d'in nata yana jin tsikar jikinsa na tashi"ya lura har yanzun mamanta basu fad'i ba.... bestie rik'eta na d'auki hand bag nawa"ni idan mun dawo gida zaka rakani nataho da yaran nan"to sarauniya Angama"kai ko broth?"ta fad'a tana murmushi ta matsa ta d'auki hand bag nata yana sab'e da babyn suka fice daga cikin k'ayataccen bed d'in nasu cikin farin ciki......!!
tamat bi hamdilillahi �
Anan nakawo k'arshen wannan littafi me taken Age mate's! kuskuran da nayi daku baki d'aya yah Allah ka yafe mun�
*Godiya* ta musammun ga Allah S W T daya bani ikon farawa lafiya har zuwa kammalawa"tsira da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitta manzon Allah S A W 
Ina mik'a sak'on d'inbin godiyata gareku jama'ar da kuka zuba kud'inku kuka biya wannan littafi Allah yasaka muku da Alkhairi yak'ara bud'i da lafiya me Amfani Ina yinku totally guys Love all😻🥰
sai mun had'e a sabon book d'ina me taken NAYI SAKE! 🔥💔
Wannan book d'in na kud'i ne duk wacce ta karanta bata biyani hakiinaba kota fitar mun Allah ya Isa ban yafe ba  har Abada karma la'ananniyar data mun mgn wai takaranta na yafe mata 
Sadaukarwa ne gareki Hjy Amina saudiyya mmn noor ina Alfahari dake 🥰









