Showing 54001 words to 57000 words out of 112373 words

Chapter 19 - AGE MATE'S Complete Document book by Momy Fareesa .txt

23 Dec 2024

12831

fad'in mamy broth be shigo bane?"ya shigo ya fita Amarya"nama bashi nasa kason yayi murna ya tafi"sai tayi d'an murmushi bata ce komai ba"Ahaka kiran Abdallah Mashi ya shigo cikin wayarta"ta harari wayar tak'i d'auka "ki d'auka mana Ahyaan" ko Ammah ce?"ah ah"ba wannan Abdallah d'in bane kullum zafin waya baya gajiya shi"Ammah kuma Ai tuni ta hak'urah mamy ta dena fushi dani"musammun data san waye Abdallah da family nasa"shiru mamy tayi Aranta tace" Anya koda Nura yace" yanama son yarinyar nan kakarta zata Amince kuwa?"ta Ayyah Aranta sbd tasan halin Ammah burinta Ahyaan ta Auri me hali"dukda tasan babu wanda zai kushe nurah Amma gani takeyi da kamar wuya Ammah ta Amince.....kallonta ta maida Akan Ahyaan fuska Ad'aure tace meye haka Ahyaan?"ki d'auka mana yanata kira ba dad'i "kamar zatayi kuka ta d'auka ta wuce bed room d'insu.....
washe gari misalin k'arfe 12:11 pm Dr darma ne zaune a office nasa yana d'an hutawa be jima da gama ganin patient's ba"yadi ne coffee brown Ajikinsa,rigar me gajeran hannu "kansa babu hula"idanunsa na b'oye cikin eye glass bak'i sbd Jan da sukayi "har yanzun beci Abinci ba"ko yau da Asuba yaje ya gaida mamy be koma komawa gidan ba sbd beson ganin Ahyaan "ji yakeyi yadda zuciyarsa tayi rauni har rungumeta zai iyayi kodan ya sami sauk'in rad'ad'in daya keji Azuciyarsa"dukda idanunsa nason ganinta,kunnuwansa nason jin sautin zazzak'ar muryarta. Amma Aganinsa yin baya da ita shine Mafi Alkhairi Agaresa "tun ruwan Lipton daya sha da safe be koma cin wani Abu ba"duk yayi zuru zuru..laptop yake dannawa Amma hankalinsa ba'a kanta yake ba"har mu'az ya shigo yayi sallama sau biyu bejiba"saida ya daki k'ofar shigowa cikin office d'in "sannan Dr darma ya Ankara dashi"ya sauke wani zazzafan huci daga bakinsa yana lumshe sexy eyes nasa yana koma bud'ewa.Abokina lafiyarka dai ko?"yafad'a yana zama kan kujera"Alhamdulillah! kawai Dr darma yafad'a Atak'aice "mu'az yace"bakada kirki tun bayan kunzo cin girkin Amarya shikenan baka koma lek'o muba?"na d'auka ma ko Ahyaan zaka kawo mana ta mana wuni " yayi shiru yak'i mgn"hakan ya k'ara tabbatar masa ba y'an k'yaliyar kawai bane Akwai damuwa Atare dashi"dama yazo yamasa k'orafi wai An sakama Ahyaan ranah itada Abdallah Mashi Amma be sani ba sai yau da safe yaga Ana fad'in saka ranar tasu Agidan TV d'in da suke Aiki"A lokacin da yaji sai yake ganin hasashen sa Akan Dr darma nason Ahyaan yakeyi ba gaskiya bane"tunda gashi zatayi Aure"saidai kuma damuwar daya zo ya samesa Aciki yanzun ya tabbatar da cewa Abinda yake zato ba haka bane....Nurah! Nurah!! ya zare eye glass d'in ya kallesa bece komai ba "wai dan Allah bazaka mun mgn ba, ka sanar mun da damuwarka ba darma?"shin ko ban Isa nasan damuwarka bane?"Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kansa Ahankali yace"damuwata *Ahyaan ce*! Ita kad'ai ce damuwata Abokinah" sai yanzun na tabbatar da zuciyata tayi shishshigi,ta kuma saka nayi kuskuren Abari ya huce"gashi Allah ya kawo rabon wani"tun bayan nadawo daga London nafara jin sauye sauyen daban tab'a jiba game da ita"sai na dinga k'aryata zuciyata musammun idan Ina jin kishinta"ban Amince yes Ina son Ahyaan ba saida nafara ganin Abubakar Ibrahim mahuta yafara sonta har yasaka Aka saceni sbd ita"(ya labarta masa komai)"kafin yaci gaba da cewa" daga nan kuma sai muka dinga yawan samun matsala da ita tana neman ta rainani"Ahaka har wannan mutumin ya bayyanah Aka saka musu rana jiya dashi"ban tabbatar da nayi sake ba saida na samu labarin hakan"kuma Ashe mahutan ma yarinyar nan bilkisu dake bibiyata Ashe k'anwarsa ce sai jiya daya kawota nan babu lafiya na fahimci hakan"yaya zanyi da Raina mu'az? Ina ganin zan Amshi tayin zuwa k'asar India da Akamun last week "naje nayi course d'in wata shidda Acan"kafin na dawo nasan sunyi Aurensu"yak'are maganar cikin wani yanayi yana cije baki....Ajiyar zuciya mu'az ya saki yace"ko yanzun bazaka fidda rai ba sai An d'aura tukum"Ina maka jaje Abokinah"sbd najima da fahimtar ka mace a soyayya Ahyaan "ta kishinta da kake nunawa da kuma k'wayar idonka ta nan nagane"Amma duk idan na maka zancenta saika basar ka canza topic d'in "na jima Ina hasaso ku Amatsayin couples sbd kunyi masifar dacewa da juna"na kuma tabbatar da cewa Ahyaan kawai ce zata iya da fitinarka....dogon tsaki Dr darma yaja yana wurgo masa harara"saidai kayi hak'uri my man gaskiya na fad'a maka"Amma jin kanka yasaka ka b'oye mun"da tuni kasanar mun kana sonta da wlh munsan yadda zamuyi koda bata sonka har ka cusa soyayyar ka Azuciyarta"to san girmanka ya hanaka"saidai Ayanzun Addu'ar zab'in Alkhairi da dangana zakayi tayi"idan har Ahyaan rabonkace in sha Allah zaka sameta duk rintsi "haka idanma ba rabonka bace kome zakayi bazaka same taba "dama tunda naga suna yawan shirye shirye da Abdallah Mashi Raina yabani sonta yakeyi....pls mu'az kaje kawai "taya zaka k'aramun da wani zafin?"ya katse sa cikin zafin rai....kayi hak'uri Abokinah"Amma ka kwantar da hankalinka"yanda nasanka da jure Abu to haka zakayi karka bari Ahyaan ta fahimci ka damu ko kuma baka son tayi Aure"tunda dai ita bata san sonta kakeyi ba, zata d'auka da wani Abu"kansa kawai ya gyad'a masa bece komai ba.duk yadda mu'az yaso ya sake masa suyi y'ar fira k'iyawa yayi"hakan yasa ya barsa yatafi kawai cike da tausayinsa.....


*************
Hahahahahahahahaha!!sautin wata iriyar murya marar dad'i ke tashi cikin jejin"yayinda suke zaune su biyu gaban wani shed'anin boka Acikin wani bak'in daji"wanda kafin su iso saida suka hau kwalo kwalo"kafin suzo inda bokan yake kowace tayi sartse sama da guda goma ga hannu da kuma k'afa"tunma kafin suyi masa bayani yasanar musu yasan komai. bayan ya gama dariyar tasa kafin yace "zamu karya sihirin da likitah yasaka Amayar kanki"baki washe ummah tace"yauwa boka"sannan ka taimaka ka hana faruwar Auren nan da shegiyar yarinyar nan zatayi"kuma inaso Akoreta daga wajen Aiki "idan buk'atata ta biya zan dawo kan uwar tata...hahahahaha! kin cika marar Imani "to ki sani mu Aikinmu yasha banban dana wasu"kuma Ahankali muke Abinmu ba farar d'aya ba"koke sai kin kai kusan sati d'aya ko kwana biyar kafin ki dena warin jab'a"Aure kuma zamu lalatashi"Eh boka Asa mata tsanarsa da k'insa Azuciyarta ita yarinyar...bazai yuyuba! ta zaro Ido "ya kece da dariya kafin yaci gaba da cewa"yanzun yarinyar jikinta Ashirye yake da Addu'oin tsari"kuma tana Azkhar "saidai zamuyi Aikin Akan shi yaron dazai Aureta"batun Aiki shima zamuyi Abinda za'a koreta"saidai komai daki daki zaizo. Amma boka...ku Ajiye sadaka ku tafi , Akwai masu son isowa nan suma suna hanya"ya fad'a yana gimtse fuska"hannunta na kirma ta Ajiye masa kud'i kusan dubu 50" K! kud'inki nera dubu d'ari ne"kuma kinzo dasu"haka zaki Ajiye ki wuce"Aiki ukku za'a maki"sbd haka idan baki shirya ba tafi ki bani waje"uwale tace haba luba ki Ajiye muje mana"ummah hannu na kirma ta zaro cikon ta Ajiye"Atake hayak'i yacika wajen,suka kama tari"ku rintse Ido sannan ku bud'e"da sauri suka rintse,suka kuma koma bud'ewa ,sai gasu gaban kwalo kwalo "ba k'aramin tsorata ummah tayiba"yayinda uwale ta kama dariya sbd batayi mamaki ba"zuwanta Anan na ukku ne Ayau"na farko zuwan kanta ne,na biyu wata ta rako,yanzun ma ta koma rakowar Akaro na ukku.sai zuzuta Aikin malamin uwale keyi har suka shiga cikin kwalo kwalo ya tsallake ruwan dasu"yayinda luba kejinta cikin farin ciki"dama burunta shine rayuwar Ahyaan ta k'untata"so takeyi Ab'ata komai Akanta sannan tadawo kan mama"sbd itama ba k'yaleta zata yiba.....
misalin k'arfe 10:11 am na safiyar yau Asabar "garin yayi lullumi sbd hadarin dake A sararin samaniya"ga iska me dad'i na ratsa jiki"Ahyaan ta fito rik'e da wata k'aramar leda fara ta shopping Ahannunta"tana sanye da doguwar riga ta Atamfa red& white,sai mini hijab red colour"wacce tayi masifar yi mata kyau"ta k'awata kyakykyawar Choco face nata"yayinda plate shoes ne sanye Ak'afarta.sai sauri takeyi da k'yar mamy ta barta zataje gun saloon.....tana k'ok'arin fitowa daga k'ofar shiga shashen nasu shi kuma yana k'ok'arin shigowa! kusan fad'a masa Ajiki tayi"cikin hanzari tayi baya kamar zata fad'i "Dr darma yayi saurin rok'o hannayenta"Atake idanuwansu suka sark'e "Ahyaan dake jin wani iri Ajikinta sbd hannayenta daya rik'e"saita janye idanuwanta daga cikin nasa ta fara k'ok'arin zare hannayenta daya rik'e....ya kafeta da Ido tamkar yau ne ya fara ganinta"yana sanye da wondo 3 quarter da t shirt me gajeran hannu wacce ta fidda shape d'in body building d'insa"ya k'ara haske da frash saidai fuskarsa da rama har yanzun "ga k'asumba ta cika masa fuska"be jima ba da tashi daga bacci ba ya watso ruwa ya shigo cikin gidan sbd yayi break fast"yana kuma fatan Allah yasa karya ganta"gashi Addu'ar tasa bata karb'uba.....pls ka cika ni naje broth "ta fad'a tana b'ata fuska"cikata d'in yayi sbd shima wani irin Abu yaji yana fusgarsa daya rik'e hannuwan nata"zuciyarsa na ingizashi daya rungumeta koya sami sassauci, Amma saiya dake....Ina zakije?"ya fad'a tamkar bayaso"kallonsa ta komayi saita turo baki tace"wai broth tamkar baka duniyar"kamar ya?"hmm ! rabon dana ganka harna manta ni"ta k'are maganar cikin mamaki tana d'auke Idanunta daga kansa"sbd ganin kusan 2 weeks rabonta dashi"wanda yayi daidai da wata biyu cif kenan da saka ranar su itada Abdallah Mashi "yawanci duk sadda zai shigo gidan da Asuba"ko bacci takeyi ko tana sallah"be kuma sake shigowa sai k'arfe 2:30 pm "lokacin kuma tadawo daga office tana bacci"sbd data dawo tayi sallah kwanciya takeyi sai la'asar take tashi"shiyasa sai tayi har sati biyu ko d'aya bata gansaba....uhmmm !idan kin damu da son ganin nawa Ai kinsan inda nake kwana ko?"sai tayi shiru,tarama rab'a gefensa ta wuce"ya d'age kafad'a irin ko Ajikinsa d'in nan "yama d'auka koda motarta zata fita"da wannan tunanin yayi gaba Abinsa"saidai hoton fuskarta na'a cikin zuciyarsa "gaba d'aya yau ta masa wani irin kyau"ga wata k'uruciya daya gani Atare da ita "sai ta masa kamar y'ar 20yrs.... Ahyaan na fitowa ta wuce bakin titi ta tari nafef"kai tsaye zainab beauty saloon Aka Ajiyeta "suna isowa ta sallami me nafef d'in ta wuce ciki.saida ta d'auki kusan Awa guda Aciki sannan ta fito sbd ta samu layi"daga gaban shagon taga me nafef ya kara gefe"har zata wuce taji yace Hjy tafiya zakiyi?"Eh "Ina zakije?"*baya jidda road*"to shikenan shigo muje kud'inki 500 ne"okay ta fad'a tana shigowa"basufi mintina 5 suna tafiya ba wata mace ta tsaidasu"tana sanye da face mask da eye glass bak'i"haka nan Ahyaan taji fad'uwar gaba da suka tsaya "saita dake kawai tana kallon matar da sauraren inda tace za'a kaita"wansa kusa da Anguwar sune"bayan sun gama mgn dame nafef saita shigo"da sauri Ahyaan ta kalleta sbd k'amshin turarenta yamata kama da wani k'amshi data tab'a ji"sai kawai ta basar taci gaba da kallon waje suna tafiya....can kawai taji an dafa kafad'arta "ta waigo da sauri"Ikkhee dake zaune gefenta ta watso mata wata powder fara"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! ta furta tana tari"kasancewar jininta me k'arfi ne sai hodar batayi saurin gusar mata da numfashi ba"tana jin dariyar Ikkhee da ganinta bibbiyu"saita lumshe lulu eyes d'inta, Adaidai lokacin kuma Ikkhee ta kira Mr mahuta yana d'auka tace"yaya Abubakar gata nan mun kamota muna hanya ne...iya nan Ahyaan taji daga haka bata koma sanin inda kanta yake ba.......��


🫣🤫🤔 Sharhi kawai🤓

wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba


#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: � *AGE MATES* ��♀�


*41&42*










*Littafin kud'i ne!*


.......tafiya suka cigaba dayi me Nisa, wacce Ak'allah sun kwashe kusan mintina 30 suna yinta"daga bisani har suka iso wani gidan gona da Aka zagaye da get"daga can ciki Akwai gida d'an flat"wanda Acan Mr mahuta ke watsewarsa da matan banza"Dan ba kowa yasan yana bariki ba"yana yin Abinsa Ab'oye"kasancewar me gadi yasan da zuwansu saiya bud'e musu get suka shigo"Adaidai bakin k'ofar shiga parlourn suka tsaya"Ikkhee ta d'auki Ahyaan ta shiga da ita ciki ta kwantar da ita saman kujerah 3seeter tana sakin wani shu'umin murmushi"yayinda me nafef yayi gaba...bayan ta zauna ta d'auki wayarta ta fara kiran Mr mahuta"bugu ukku ya d'auka yana fad'in ya Ake ciki ne?"saida ta yamutsa fuska kafin tace" gata nan kwance bata san inda kanta yake ba"okay idan ta farka ki kirani zan k'araso "bayan na k'araso sai ke ki tafi gida"da komai ya kammala zan saka Amayar da ita titin Anguwar su"okay tace tana yanke wayar"kafin ta zuge hand bag nata ta zaro wasu kwalabe k'anana ta fara shaye shayenta.daga nan bacci ya d'auketa "sai wajen k'arfe 1:15 pm ta farka Afurgice sbd ganin bacci ya d'auketa....wata nauyayyar Ajiyar zuciya ta saki sbd ganin har lokacin Ahyaan na kwance kamar marar rai"ta yamutsa fuska had'e da tab'e baki "Adaidai lokacin wayarta tayi ringing"ta d'auka tana fad'in yaya Abubakar bata farkaba"nafiso kazo yanzun d'in"bazan ma tafi ba sai naga komai ya kammala"idan harba gani nayi ba kasaka Anyi raping nata hankalina bazai kwantaba....shiru tayi sbd ganin Ahyaan na motsi"wacce tun sadda wayar Ikhkheen ta fara ringing ta farka"tayi dai tsit sbd taji meye zatace idan ta d'auka?"saidai jin ta Ambaci raping ya saka k'irjinta bugawa "ba shiri tafara motsi"da sauri Ikkhee ta gyara face mask d'inta tana fad'in ta farka ma"daga haka ta yanke wayar..... *innalillahi wa inna ilaihir raju'un! La'ilaha illallah Antassubaha naka inni kuttu Minal zalimin*" cewar Ahyaan tana tashi zaune ta kalli Ikkhee"ta kalli kanta da cikin parlourn "kafin tace"bewar Allah lafiya?"meye ma'anar ganina Anan da nayi??uhmmm ! Ayanzun bada jumawa ba kuwa zakiga ma'anar hakan"saidai karki damu muba masu garkuwa da mutane ko kuma kashe mutum bane"shiru Ahyaan tayi k'irjinta nata fat fat fat!! sai kuma ta sauke Ajiyar zuciya Ab'oye data d'an lalibi gefen Aljihun rigar jikinta taji nokia d'inta"kallon Ikkhee dake zaune tana girgiza k'afafuwanta tayi kafin tace "Ina toilet zan kama ruwa nayi Alwallah?"banza ta mata tak'i kallonta"sai Ahyaan ta tab'e baki tare da cewa"inaso ki sani! ganina Anan tare dake bashike nufin kinci nassara Akan koma wane irin k'uduri kike dashi Akaina ba."sannan dakin bud'e fuskar taki na ganki ta haka zan tabbatar ke d'in tantiriya ce kum.....shiru tayi sbd shigowar wasu katti su ukku da makamai Ahannunsu "saida taji k'irjinta ya buga"saidai ta dake tana koma maimaita kalmar Ina toilet?"da hannu kawai Ikkhee ta nuna mata tana tabe baki....Ina jakarta?"cewar k'ato guda"babu jaka Atare da ita,gadai ledar da muka gani wajenta"ta fad'a Ahyaan na k'ok'arin shiga toilet d'in....kin tabbata babu waya Atare da ita?"da sauri Ahyaan ta shige toilet d'in ta rufe da key d'in dake jiki bataji wace Amsa Ikkhee tabama y'an daban ba....hannunta na kirma ta zaro wayar ta fara rubuta ma Dr darma sak'o kamar haka.....*broth! ka ceci rayuwata" Ina cikin tashin hankali, wasune suka saceni a hanyata ta dawowa gida"naji suna fad'in zasu saka Ayi raping d'ina. Pls kayi wani Abu Akai karna rasa martabata"naji suna kiran sunan wani Abubakar ta waya "kaceci rayuwata dan Allah,sannan karka kirani sbd karsu gane*......tana gama rubutawa ta tura masa hannunta na kirma"saida taga sak'on ya shiga sannan ta sauke numfashi"shima AA Mashi ta fara tura masa sak'o makamancin irin wanda ta turama Dr darma "saidai nashi gajere ne bamai tsayi ba.tun kafin ta gama sending d'in takejin suna mata wani mahaukacin knocking"tana gama sending ta maida wayar cikin rigar mama dake jikinta"sbd bata so ta kashe wayar ko kuma su san wayar na hannunta "sbd jikinta yabata daga Dr darma har Abdallah Mashi zasuyi treaking su gano inda take... tana gama tura wayar cikin bra ta wanke fuska da hannu da k'afa"sbd tace Alwallah tayi"bacin fad'uwa bbu Abinda gabanta keyi ga zulumi had'e da tsoro duk mak'ale Aranta"saidai tana so tasan meye ta tsare musu Arayuwa da suka zab'i su kawota Anan su cutar da ita?"tana wannan tunanin ta bud'e k'ofar Aranta tana Addu'ar da duk tazo mata Abaki....wani irin mugun kallo Ikkhee ta watso mata irin na tuhuma"saidai da yake Ahyaan tafita esperions bata bari tayi mgn ba, saita kauda kanta tana fad'in "mena muku kuma ku suwaye,me kuke nema wajena??? bamuda Amsar wannan tambayar"sallah kuma baza kiyi ba sbd banma yarda da shigarki a toilet ba"kamar ya?"ta fad'a cikin fad'uwar gaba"Ikkhee batayi mgn ba ta fisgo hannunta zata zare mata hijab nata"Ahyaan ta hankad'ata,tayi k'asa ta fad'i "K! wani k'ato yadako mata tsawa"batayi mgn ba tayi tsaye tana huci tana k'ara gyara hijab nata"ki tsaya ta dubaki ko kuma kiyi nadama"tashi ki dubata"Ikkhee taja tsaki tana tashi zaune ta matso gabanta"da kanta ta zare hijab nata duk suka bita da kallo"sai lokacin Ikkhee ta lura da rigar jikinta me Aljihu ce saita fara dubawa Amma bataga komai ba"yayinda Ahyaan zuciyarta keta bugawa tana Addu'ar da duk tazo mata....babu waya Ajikinta "Ahyaan ta tab'e baki tana maida hijab nata"k'ato guda yace ke karkiyi mana taurin kai yanzun na sareki na sari banza"sallah ki bari idan kin koma inda kika fito kyayi Abinki"Anan yamiki kama da inda zakiyi sallah?"shiru tayi musu sbd dama ita ba Alwallah tayi ba"hasalima batada nutsuwar da zatayi sallah tana Acikin wannan tsaka me wuyar datake"k'asa saman carpet ta zauna ta rak'ub'e tana Am batom sunan Allah"batayi zaman mintina 5 ba saiga wani namiji ya shigo da wata roba ta swan suka mik'a ma Ikkhee"ki bata tasha"sannan yace"idan tasha ki fito yana bakin get ki samesa"wata iriyar zabura Ahyaan tayi k'irjinta na tsananta bugawa Atake ta fad'i sumamma sbd furgitan da kalaman d'an Aiken sukayi Azuciyarta.....
Afannin su mamy kuwa tayi mamakin ganin Dr darma ya shigo da walwala Adaidai lokacin "sai kuma ranta yabata tabbas ya had'e da Ahyaan da zata fita.tunda kafin ya shigo yanzun ta fita"saidai batace masa komai ba"shi kuma ya zauna yamata barka da gida sannan ya wuce wajen dining table yaja kujerah ya zauna "d'an tak'aitaccen murmushi yasaki sbd ransa yabashi Ahyaan ce ta had'a break fast d'in"sosai yazuba Abinda yakeda buk'ata yaci ya k'oshi "koda ya gama be fitaba saima zama yayi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login