Showing 45001 words to 48000 words out of 112373 words

Chapter 16 - AGE MATE'S Complete Document book by Momy Fareesa .txt

23 Dec 2024

12821

ta wuce kitchen "tana tafiya ya saki murmushin mugunta ya kwashe sauran tsoka biyun da suka rage"sannan ya d'auki Ayaba guda biyu ya fice da sauri....
sam Ahyaan bata kawoma ranta zai tsokaneta harya gudu ba"tana shigowa cikin parlourn taga wayam bbu me kama dashi"ta kalli plates d'in taga Abinda ya d'auka "me makon taji haushi saima d'an murmushi ta saki tare da cewa zamu had'u dakai Allah kuwa"zamanta ta gyara ta balle maltinah d'in ta shanye"kafin ta cinye sauran Ayabar taci gaba da kallonta hankali kwance"sai wajen goma saura ta kashe kayan kallon suka bar parlourn itada hamza.....
Afannin Ikkhee tun lokacin da taji sanyayyar muryarsa yana yiwa wata mgn ranta yabata gadararriyar yarinyar nan ce da suke zaune *Agida biyu* "saidai kuma bata gama wannan tunanin ba taji muryan Ahyaan d'in,sai kuma yakashe wayar "data kira daga baya Aka sanar mata yayi blocking nata"gaba d'aya sai taji har shi Ayanzun ta tsana"sbd in bacin wulak'anci ko yaya kaso me sonka koda bada soyayya ba"saidai taci burin daga shi har ita sai ta musu sanadin shiga k'unci kamar yadda sukayi sanadin sakata Adamuwa"Ayinin ranar taje club tayi shaye shaye son ranta"musammun da taga yayanta dake kulawa da duk wani Al'amarin yaran gidan nasu baya k'asar.....
washe gari misalin k'arfe 4:11 pm "Ahyaan na zaune kan kujerah a parlourn mamy tana chats da Khairiyyah sai murmushi take saki"tasha gayunta cikin sabuwar doguwar riga ta wani had'ad'd'en embroidery material "wanda ta fito lady in copy brown"ga wani sanyayyan k'amshi jikinta na fitarwa"ba make up saman fuskarta Amma tayi masifar kyau"mayafin na saman kafad'arta"yayinda take sanye da takalmi have cover masu ma d'auri,kuma masu tsini copy brown "sai y'an hannu da Agogo da zobba dake mak'ale a hannayenta"tunda ta zauna tana jiran shigowarsa su wuce wajen friends d'in Fatima mamy dake zaune take ta kallonta. har cikin zuciyarta da ranta tana yiwa Nura fatan mallakar Ahyaan Amatsayin matarsa in har ita dashi Alkhairi ne ga juna"to fad'an su yasaka ta dena wannan tunanin"Amma yanzun Al'amarin yaran tsoro yake bata"ta kuma kasa fassara meke tsakaninsu?"dukda dai k'asan zuciyarta na mata zargin Nura fa yafara kamuwa da soyayyar Ahyaan yadai b'oye ne.... Assalamu Alaikum! nutsatstsiyar muryansa ta katse ma mamy tunani"Atake ni'imtaccen k'amshin turarensa ya cika parlourn"Ahyaan ta d'ago kanta suka k'urama juna Ido"itace ta fara janye Idanunta"Azuciyarta tace kamar shine Angon" yana sanye da sky blue d'in shadda wacce taji Aikin hannu da navy blue d'in zare"hula, Agogo,takalmi sawu ciki,duk navy blue yasaka"fuskarsa kadaran kadahan be saketa ba be kuma daure taba "wanda yayi hakane sbd d'azun da safe ya shigo da nufin suyi break fast sai wani sharesa takeyi,ko mgn ma da k'yar tace masa ya jiki"kuma tak'i gaidashi"shiyasa har break fast d'in yak'iyi ya fita"sai kuma d'azun daya shigo ta kamasa Abinci daga nan take tambayarsa yaushe zasu fita ?yace 4:00pm"daga nan ta sharesa shima haka"ko yanzun d'in kin tankata yayi sai mamy kawai yayima sannu da gida"ga wani irin zafin kishinta daya taso masa "wanda yakasa fassara hakan da kishi ne kome?"to itama da yake y'an izzar sun motsa sai taci gaba da danna waya tunda suka had'a Ido bata koma kallon gefen dayake ba"mamy dai na lura dasu kowa ne na dannah waya"dan shi uban gayyar yana tsaye ne bakin k'ofar parlourn "yayi wani irin shegen kyau kamar bad'an k'asar Nigeria ba....wai ba fita kikace mun zakuyi ba?"cewar mamy tana kallonta"Eh Mamy"to zaman jiran meye kukeyi?"ita za'a tambaya" tunda tafi k'arfin tace muje ko?"ya fad'a yana fita"Ahyaan batace komai ba ta mik'e tsaye ta yafa mayafi ta rik'e hand bag d'in ta kalli mamy tace"sai mun dawo"Allah ya tsare ki kula da kanki"kar kuma ki bari kiyi magrib Awaje kina jina?"Eh Mamy"ta fad'a tana fita"lokacin data iso bakin get harma yafita da motar yanata danno mata horn"ta fito tana yamutsa fuska had'e da gallama motar harara sannan ta iso gefen me zaman banza ta bud'e ta shigo"sai lokacin ya d'auke idanunsa daga kanta yana cije baki had'e da tunanin wace irin zuciya ce da ita?"idan ta gadama Ayi raha idan ta gadama ta dinga shan k'amshi kenan"Aransa yace "hakanne y'a macen"very slowly yake jan motar Anutse wak'ar music na tashi"basufi mintina 5 saman titi ba mu'az harya girtse yakirashi"dama kuma sunyi Appointment dashi can zasu had'u "tab'e baki yayi yak'i d'aukar wayar"broth kanafa ji Ana kiranka?kamar yana jira yafara fad'a da cewa"na d'auka Ai jin kan naki bazai barki kiyi mgn ba"idan na koma cewa ki rakani wani wajen sai kimun yadda kika gadama"na lura Akwanan duniya in har baki b'atamun rai ba baki jin dad'i"Amma laifina ne da nake shiga sabgarki....tunda ya fara fad'an nasa bata ce masa komai ba har yayi shiru "sbd Aganinta ita bataga Abinda zaima kumfar baki ba"tasan kuma idan ta biye masa rayukan nasu b'aci zasuyi sai kawai tayi shiru"shi kuwa ba k'aramin shak'a da shirun nata yayi ba....har suka iso bakin get d'in gidansu Fatima babu me mgn cikinsu"bayan yayi parking ya hango mu'az zaune saman mota "Fatima na tsaye gefensa suna mgn" kusan Atare suka fito daga cikin motar shida ita suka nufosu "mu'az ya saki murmushi sbd yana ganin matuk'ar dacewar Dr darma da Ahyaan"saidai da yake yasan halinsu Atake ya fahimci sunyi halin nasu a mota. sbd yadda yaga fuskar Abokin nasa ya d'aure sosai"y'an uwan juna barkanku da zuwa! cewar Fatima tana d'an murmushi"itama Ahyaan murmushin tayi tare da cewa Amarya kinsha k'amshi"kema haka"Ina yininku?"mu'az ya Amsa yana dirowa daga saman motar ya kalli.dr darma ya kama dariya"shi kuma ya tab'e baki yana Amsa gaisuwar Fatima kafin yace"kin mun laifi Amarya "ta d'an zaro Ido tace kaina bisa wuya babban Amininmu"sai yasaki wani Miskilin murmushi har fararen hakoransa suka bayyanah"yana d'an jingina Ajikin motar mu'az "ya saci kallon Ahyaan yaga shima take kallo"saiya d'auke kai yana fad'in yanxun kin kyauta nazo naka miki invitation card Amma baki je har gida kin kaima bestie nah ba?"Ada tacema bazata zo bikin da ba'a gayyaceta ba"Amma yanzun dai gata nan saiki kare kanki....daga Ahyaan har Fatima sunyi mamakin kalamansa"saidai mu'az beyiba sbd sarai yasan halin Dr darma "idan yaga dama zai iya yarfa mutum duk shirin sa dashi.haka idan yaso kuma zai iya nuna duk duniya kunfi kowa yin shiri dashi"fatima dai hak'uri ta bama Ahyaan"tare da cewa jibi zasu zoma har gida ta kawo"okay ba damuwa Ina k'awayen naki?"su ukku ne suna ciki"okay muje ko?"baza mu jira Jameel ba?"(Abokinsu ne shima) "yamutsa fuska yayi tare da fad'in kasan a tsarina ba African time "so idan yazo bamu Ida mgn ba zai iya shigowa dg baya"to shikenan babban likitah yadda kace haka za'a yi"cewar mu'az yana murmushi"Dr darma ya wurgo masa harara yana kallon fatima yace kiyi masa fad'a"kema Ahyaan ki dinga yima bestie d'in ki fad'a"murmushi kawai tayi batace komai "Dr darma ya matso gefenta yace"wuce muje"k'in mgn tayi....sai gaba d'aya suka nufi cikin gidan.....��


wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba
#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: *Littafin kud'i ne!*


.........kai tsaye Asit room d'in gidan Fatima ta musu jagora"ita dai Ahyaan na biye dasu har suka iso cikin sit room d'in"Fatima ce daga gaba sai Ahyaan,sannan Dr darma sai Abokinsa Ango dake bayansa"cike da Aji had'e da shan k'amshi ya zauna gefen Ahyaan da itama ta wani d'auke kai sbd taga y'an matan gaba d'aya ta girme musu bama sa'an ninta bane"tana lura da guda cikinsu ta cika iyayi sai faman cusa kai takeyi"Atake taji yarinyar bata mataba"sbd ta tsani mace marar Aji me cusa kai gun maza"tana lura da mutumin nata yadda yaketa wani basarwa ko gaisuwar y'an matan be Amsa ba"ta saki murmushi duk yana Ankare da ita.....shidai mu'az kallon fatima yayi ya mik'e tsaye sai ta bishi suka fita"haleesa tabi Ahyaan da kallo dashi kansa Dr darma d'in"sai ranta ya bata su masoya ne ,sbd basu santa Acikin friends d'insu ba Anutse Ahyaan ta musu sallama da gabatar da Dr darma Amatsayin babban Aminin Ango"wanda tayi hakanne sbd ganin yak'i yin mgn"yayinda su kuma matan ke zaton sbd yaga Ahyaan d'inne sai kowace ta kama kanta"saidai haleesa uwar iyayi ce tace"to Masha Allah! dama Amarya ta sanar mana da zuwan nasu dukda shi kad'ai ne muka gani bayan tace su biyu ne"Ahyaan tayi murmushi ta d'an matso da kanta gefen kunnansa tace"broth !yaya wannan tayi maka?"ta fad'a k'asa k'asa tana murmushi"shima d'an murmushin ya saki ya juyo ya rad'a mata"da Ace lips nata k'anana ne kuma ba gajerah bace dana taya"gaba d'aya suka saki murmushi Atare .sosai haleesa ta tsargu"Dr darma ya wani ci face Anutse yace" Agurguje Ina son jin nawa kuke buk'ata?me suna hafsat tace" duk Abinda kuke da hali zaku iya bayarwa"sai lokacin ya d'ago ya kalleta yace" good! haleesa ta yatsina fuska tace"ah ah gaskiya hafsat Akan me zakice haka?"Hafsat ki saka acc details naki Asa muku! suka ji sautin sanyayyar muryarsa me cike da haiba da dad'in Amo "haleesa ta yamutsa fuska tana tunanin kodan sbd yaga shida budurwar sa suna da kyau shiyasa yake wani d'aukar kai da hura hanci?"shidai besan tana yiba"saima mik'a ma hafsat wayar yayi"ta matso ta Amsa ta saka masa acc n"cikin second 35 ya musu transfer d'in 500k ya mik'e tsaye yana kallon Ahyaan yace" tashi muje *Aminene*! Amamakin sa sai yaga tayi d'an murmushi batayi mgn ba "wai meye kike b'oyewa cikin hand bag d'in ne? ya k'are maganar yana matsowa ya karb'e jakar"gaba d'aya suka bisu da kallo"be bud'e ba saima fitowa da yayi,ta biyosa Abaya tana tunanin ya sakko daga fushin kenan?"yanzun fa ya gama sauke mata tujararsa Amma gashi yanzun kamar ba'a yiba.....da wannan tunanin ta fito haraban gidan"samun su tsaye tayi shida mu'az da Fatima suna mgn yana kuma yimata bincike cikin jaka"nidai Allah kadena mun bincike cikin jaka"uhmm! hajjaju kenan kud'i nefa da ita Abokinah "ya fad'a yana zaro kud'i y'an 1k besan ko nawa bane ya saka cikin Aljihu tare da fad'in na Amshi zakkatah."yama d'auka ko zata masa daru tace saiya biyata"sai yaga Akasin hakan ,saima matsowa tayi ta Amshe jakar mu'az da Fatima na musu dariya"itadai tana tsaye tana murmushi Ahaka kira ya shigo cikin wayarta"saidai tana dubawa taga bak'uwar number ce"dakewa tayi ta d'auka tayi sallama cikin zazzak'ar muryarta "daga d'ayan bangaren ya wani lumshe Ido yana Amsawa kafin yace" kina mgn da *Abdallah Aliyu mashi* dam! k'irjinta ya buga" tana tambayar kanta Ina yasamu contact nata?"hellow! kina jina?uhmm "Ina wuni?"lfy qlau"nasan zakiyi mamakin kiran nawa ko?"ah ah "meyasa? babu"malama Ahyaan kenan"ni kuma?"Eh mana"yanzun kina Ina?"banafa gida "Anguwa kika jene?"Eh"keda waye?"nida broth mana"wai yayanki da ranar dana fara ganinki naganku tare?"uhmm ta fad'a tana d'ago kanta taga Dr darma na yiwa mu'az sallama "fuskarsa babu yabo bbu fallasa"Amamakin ta kallo bata isheshiba yayi gaba Abinsa "tana ji AA mashi na mata mgn Amma ta kasa cewa komai sbd mamaki....saima kashe wayar tayi ,shidai mu'az da Fatima suna kallonta basuce komai ba "saida ta kallesu tace" mun wuce sai Anjiman ku"godiya suka mata ta fito daga cikin d'in gidan"lokacin harma Dr darma ya shige mota ya bata wuta"zai jata kenan ya hangota ta fito"sai kawai ya tsaya harta shigo"ta kallesa tace broth shine zaka tafi ka barni?"Arzik'in ya kalleta koya tankata bata samu ba"ta bishi da kallo taga idanunsa sunyi d'an ja"ba k'aramin mamaki tayi ba"saima ta fara zaton kodai yanada Aljannu ne?yanzun fa yake tsokanarta Amma gashi ya burkice ya had'e rai......zaman mintina 15 sukayi cikin motar kafin su iso gida"saidai har suka iso kanzil Dr darma bece mata ba"jikinta Asanyaye ta fito ta wuce cikin gida"Adaren ranar ko shigowa cikin gidan beyiba"washe gari da Asuba tana ji ya shigo cikin parlourn suka gaisa da mamy"Amma be neme taba"haka nan taji zafin abun Aranta.....tun wajen k'arfe 7:00am ta gama gyara bed room & parlourn tayi wanka ta shirya cikin jallabiya bak'a irinta larabawa .ba k'aramin kyau tayi ba"Amma yau takalmi plate ta saka"turarema bata saka da yawa ba"saita yane kanta da mayafin"gashin kanta dake d'aure sai yayi kamar ta saka Acuci....mamy ta shigo cikin d'akin ta kalleta tana tsaye gaban mirror tace Ahyaan kizo kiyi break fast saiki tafi ko?"to mamy bana so na makara wlh"hakane Allah yabada sa'a "ki tabbatar kinyi Addu'a sannan ki shiga mota"canma in zaki shiga kiyi Addu'a,ki Kuma shiga da k'afar dama"sai Abu na k'arshe dan Allah ki kasance me tarbiya da kamun kan dana sanki dashi Ahyaan "in sha Allah Mamy"ta fad'a suna fitowa gaba d'aya daga cikin bed room d'in "Agaggauce tayi break fast d'in ta fito ta shiga parlourn daddy ta gaidashi"shima dai Atak'aice ya mata nasiha "sannan ta shiga wajen su mama Agurguje suka gaisa sannan ta fito zata wuce wajen motarta"sai ta lura da motar Dr darma na fake gefe"haka nan ranta ya bata yana cikin motar"halan kuwa hasashen ta gaskiya ne yana ciki zaune yana kallonta"yak'i kuma tafiya ne sbd yana son ganin da wace shiga zata fita wajen Aikin"har tsayawar datayi tana kallon motar duk yana gani"sai kuma yaga ta iso tana masa knocking"zuge glass d'in motar yayi kyakykyawar fuskarsa ta bayyana,suka had'a Ido"gabanta ya fad'i tad'an yamutsa fuska tana fad'in dama kana ciki kenan?"ga Alama kin gani"yafad'a cike da shan k'amshi "Ina kwana?"ki rik'e Gaisuwar bana buk'ata"ko jiya kin gaidani ne?"Agabana kika gaida su khaleel "Akan me zan Amsa gaisuwar daba kullum Ake mun itaba"sai bata ce masa komai ba ta wuce ta shiga mota"Anutse ta jata ta fice daga cikin get d'in gidan kasancewar Abud'e yake"sai tunani takeyi da hasashen zuci"saidai ta gama yanke hukuncin ta fita harkanta "su koma kamar da saiya kama sannan su kula juna"Aganinta kamar hakan zai fi tunda shiryawar tasu beda Amfani da An shirya sai An koma samun matsala.taji zafin Abin matuk'a tadai dake bata nuna masa ba.....tana isowa cikin get d'in wajen tayi parking ta zaro eye glass nata bak'i faskeke ta rufe Idanunta"cikin nutsuwa tamkar hawainiya haka take takun nata dake d'aukar hankalin duk wanda ya Aza idanunsa saman nata.....barka da zuwa princess! taji sautin muryar sa Abayan ta"cike da shan k'amshi ta tsaya saidai k'ememe tak'i juyowa"ganin ya d'auki kusan second 5 be iso inda takeba kawai saita cigaba da tafiya Abinta"ya saki murmushi yana binta da kallo harta tura k'ofar glass d'in shiga ciki ta wuce"ya sauke Ajiyar zuciya yana jin ta k'ara shiga ransa"sbd yana son mace me kamun kai da Aji wacce babu ruwanta da kowa harkan gabanta kawai takeyi.....duk Abinda ya dace data shiga tayi"Aka bata takardan da zata karanta news na k'arfe 9 am"sannan ta wuce office d'in da aka bata tana dubawa "kafin lokacin yayi ta shiga tafara Ana d'aukarta "saidai ta fahimci Anjima da k'arfe 12 na rana zuwa k'arfe 1 zasu jagorancin shirin y'an siyasarmu itada AA mashi"wanda sam bata so hakan ba"taso Ace itada wata mace ce ko kuma wani da bata sani ba.....misalin k'arfe 1:7 pm ta fito Ahankali cike da gajiya zata shiga mota, yayi saurin shan gabanta yana tsareta da Ido yace"madam babu ban kwana sai tafiya?"uhmm kawai ta furta"wai meyasa baki tab'a cewa Abdallah ba?"bayan ni nasan sunanki kuma?"ya k'are maganar tamkar wani d'an yaro"sai murmushi yasub'uce mata tace"shikenan zan dinga fad'a "to meyasa jiya kika kashemun waya "kuma da dare na miki mgn ta what's app Amma kikak'i yimun reply??" kanta Ak'asa tace" banma ganiba gaskiya dan bancika chats sosai ba"jiya kuma inata sauri yamma tayi kar mamy nah tamun fad'a shiyasa na kashe nabiyo broth muka tafo gida"wai shi broth d'in namu beda suna?"tad'an kallesa suka had'a Ido"ya wani marairaice fuska tamkar d'an yaro"sai ta saki murmushi"Ahankali tace "sunansa *Dr Nura Darma* yana Aiki a FMC "kice yayan namu doctor ne?"Eh babban likitah ne"saidai bafa yaya na bane nida shi *Age mate ne*! wai da gaske?"uhmm Amma ba parents naku d'aya ba ko?"Eh cousin d'ina ne" shiru yayi na kusan second 5 kafin yace okay zan kiraki Anjima pls"sbd me bayan mun gaisa yanzun?"ta fad'a tana bud'e k'ofar motar"idan na kiraki zakiji dalili"sharesa tayi ta shige cikin motar tabar wajen........ Ab'angaren Dr darma kuwa yana office zaune yana duba patient "tun wajen 8:35 am ya kamo channel d'in tashar gidanTV d'in
*tauraruwa* " k'arfe 9:3 suka hasko kyakykyawar fuskarta da take mgn ba hayaniya da turancinta me fita cikin nutsuwa ta gabatar da kanta "kafin tabfara labaran "shidai yana kallo yana kuma saurare"daga nan data gama ba'a koma nunotaba sai wajen k'arfe 12 pm Aka haskosu itada *AA Mashi* ! har lokacin kuma TV d'in office d'in nasa na Aiki yana kallon su"tunda yaji muryan guy d'in ya d'ago ya kallesa Atake ya shaida fuskarsa . Dukda ganinsa dashi sau biyu ne Amma sarai yagane sa"kallonsu kawai yakeyi baya fahimtar meye suke cewa"daga k'arshe yaja dogon tsaki ya kashe TV d'in......


*bayan kwana 10*
Duk yadda Allah yaso da bawansa ya zama babu wani mahaluk'in d'aya Isa ya hana hakan"kuma d'aukaka ta Allah ce.hak'ika *Aminatu iliyasu lawal* ta shigo da farin jini Agidan TV d'in tauraruwa"gaba d'aya mutane na sonta musammun mata sbd wayar da kan data keyi Acikin shirin *mu kula da muhallinmu*! gefe guda kuma maza y'an siyasa nata son cusa kansu wajenta sbd ta wankesu Agun jama'a ta labarai"dukda bata jima da fara Aiki ba Amma cikin k'ank'anin lokaci ta zama tauraruwa tayi suna"harta Ikkhee tana ganinta ta ganeta ,kuma har gobe burinta A kanta na nan ,dama kawai take jira ta samu ta Aiwatar da k'udurinta Akanta....yayinda suke yawan shirye shirye itada AA Mashi "tun bata sakar masa fuska da d'an sakewa dashi suyi mgn har tafara "be yin wani k'asa Agwiwaba ya fara nuna mata sirrin dake cikin zuciyarsa"wanda mutane da yawa daga cikin Abokan Aikinsu zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login