Showing 27001 words to 30000 words out of 121992 words
Chapter 10 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
sosa kai yace; "lafiya lau, har kin shirya".
Sai da ta juya idanu sannan tace; "eh har na fito na jira kazo breakfast baka zo ba shine na biyo ka dashi".
"am ok na riga naci abinci anan", sai da murmushin dake fuskar ta ya ɗauke cikin damuwa tace; "nifa da kaina na shiga kitchen na haɗa maka amma babu komai nasan maybe dan baka san zan maka bane".
Wani irin murmushi yayi wanda ya tafiyar da imanin su gaba ɗaya, shi kanshi yana jinjinawa haƙurin Auntyn tashi wannan kuma ke janyowa take matuƙar birge shi yana son mace me sanyin hali.
Saleema da take ji kamar ana ƙarawa zuciyar ta wutar son shi ta juya tace; "bari na wuce wajen aiki", tana faɗin haka ta fara tafiya.
Cikin sauri ya miƙe ya biyo bayan ta yana faɗin; "bari na raka ki", ya ƙarasa yana amsar jakar hannun ta.
Sosai Saleema taji daɗin hakan kuma ta san cewa yayi ne dan ya sanyaya mata rai na rashin cin abincin ta da beyi ba.
Husna kuwa kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu haka take ji yayin dasu Fadil suka kasa riƙe dariyar su sai da suka dara sosai.
Husna kuwa abin ya ƙara baƙanta ranta dan haka ta nufi ɗakin Hajja tana kuka, su kuwa suka cigaba da dariyar su.
Suna fita harabar gidan motar Abban su Fadil na shigowa, da sauri Saleema ta buɗe motar ta shiga yayin da shi kuma Abdul ɗin ya mika maya jakar tata.
Abba daya fito daga cikin tashi motar yabi motar ta da kallo yana girgiza kai, Abdul ya shafa kai sannan ya gaishe da Abban.
Cikin fara'a Abban ya amsa, hakan ba karamin daɗi Abdul ɗin yaji ba ganin yadda ɗan uwan mahaifin nashi ya sakar mishi fuska.
Haka ya riƙo hannun Abdul ɗin har cikin gidan, da gudu Fadil da Fadila suka yi wajen mahaifin su nan suka gaishe dashi ya amsa yana tambayar su ina wajen aikin ba, nan suka bashi amsa da yanzu zasu tafi.
"to ayi sauri a tafi bana son wasa da aiki", dole suka ƙarasa shiryawa da wuri suka fice, hannun shi cikin na Abdul suka shiga ɗakin Hajja.
Hajja tace" na rasa me dangin Malama suka baka da kake naniƙe muku kabi duk ka wani manne dasu, to ka sani su ɗin rabin ƴan uwan mahaifin ka ne".
Abdul ya saukar da kai ƙasa cike da kunya ga Abban su Fadil amma bata ji kunyar faɗin haka ba.
Abban Fadil kuwa yayi murmushi kawai idan da sabo yaci su saba da halin Hajjar; "ina kwana Hajja".
"mun tashi lafiya?", amsar data bashi kenan, beyi fushi ba yace; "lafiya lau", daga haka bata kuma cewa komai ba.
"bari na ƙarasa na gaishe da Malama, ga wannan a sa mana albarka", ya ciro ƴan dubu-duɓu ɗauri biyu ya ajiye a gaban ta.
Da ƙyar ta iya cewa; "an gode Allah yayi albarka", Abban Fadil ya amsa da Ameen yana me jinjina mulki irin na Hajja.
Yana miƙewa Abdul shima ya miƙe, Hajja tace; "to ɗan annace ina kuma zaka je?", kamar ba zai amsa ba sai kuma yace; "gidan Abba".
"wane Abban?", ta ƙara jefa mishi tambaya shifa ya fara gajiya dan haka a ɗan ƙarage yace; "Abban Kabeer", wani ɗan murmushi tayi sannan tace; "a dawo lafiya".
Har ya juya sai kuma ta kira shi, ba dan yaso ba ya juyo ya dawo, " yauwa ɗazu meya haɗa ka da ƴar uwar ka Husna".
Sai da yayi jim sannan yace; "meta ce miki?", Hajja cikin hasala tace; "ina tambayar ka kana tambaya ta?".
Yayi shiru be tanka ba, sanin cewa ba zai faɗa mata bane yasa itama bata kuma magana ba haka suka zauna tsayin minti goma sha biyar kowa yana ji da nashi miskilancin, dan kanshi ya miƙe ya fice, ita ma kuma bata ko kalli inda yake ba.
Yana fita ma ya fasa zuwa can ɗin dan haka ya nufi ɗakin Malama, har Abban Fadil ɗin ya fita.
Da kyar ya iya yin sallama ya shiga, ganin hakan itama Malamar tunda ta amsa mishi bata kuma cewa komai ba sai ma sallah data tayar.
Kan gadon ta kawai ya faɗa wanda yake tsaf-tsaf ya san aikin Fadila ne domin tare suke kwana da Malamar yana kwanciya babu jimawa barci yayi awon gaba dashi.
Malama tana idar da Sallah ta juyo tana kallon shi, cikin idanun ta babu abinda kake gani sai Ƙauna, tausayi da kuma bege, a hankali ta ƙarasa gaban shi tana kallon shi.
Hannu ta kai wanda har rawa yake yi ta shafa fuskar shi hawayen da ban san kona meye ba ya zubo daga idanun ta.
Baki take motsawa alamar addu'a take yi, sai da ta gama sannan ta shafa mishi tana cigaba da zubar da hawayen ta, tana gamawa ta tashi ta koma kan sallayar ta tana me ɗaga hannu sama tana addu'o'i hawaye na kuma zubowa wanda hakan zai nunar maka da tana cikin baƙin ciki.
Sai bayan azahar sannan ya farka, babu kowa a ɗakin hakan ya nuna mishi kenan Malama ta fita.
Ya sauko daga saman gadon ya shiga bayin ta yayi Alwala sannan ya fito, yana fitowa daga ɗakin Hajja na fitowa daga nata ɗakin.
Ta kalle shi cikin masifa tace; "ina raba ka da Malama da abinda ta haifa kana ƙara maƙale mata ko?, kana sane da cewa ba ita ta haifi Uban ka ba amma kabi duk ka shige mata, so kake yadda ta cinye ƴar ta kaima ta cinye ka?".
Ya juya cike da jin kunya domin kuwa Malama dake tsaye a wajen ya kuma san taji abinda Hajjar ta faɗa.
Malama cikin rawar murya tace; "Hajja me yasa kike faɗin haka ne taya uwa zata lashe kuruwar ƴar ta?, meyasa kike so ki raba ƴan uwan taka ne ki sani da Fiddausi da Baban Abdul Uban su ɗaya fa".
Hajja tace; "ai Uba kika ce ba Uwa da Uba ba sannan Baban Abdul ɗana ne Fiddausi kuwa ƴar ki ce wacce tsabar maita kike lashe kuwar ta dan haka ki tattara ki ƙyale mun jika dan yafi karfin ki".
Malama kasa cewa komai tayi dan haka ta shige ɗakin ta yayinda Abdul ya juya ya bar wajen da sauri.
*Fiddausi* shi kuwa ya jima yana jin wannan sunan, domin kuwa sunan Muhibba kenan, sannan Nihal ma sunan ta kenan sunan wata ne suka ci?.
Shi tunda yake be taɓa jin wannan sunan a wajen Mummyn shi ba, amma ya kan ɗan ji shi cikin Estate idan ya shigo wanda alama ya nuna ƴace ga Malama kuma ta rasu ne shekaru masu yawa.
Sai yamma sannan su Fadil suka dawo nan ya manta duk sauran damuwar shi ya dawo dai-dai.
Suna fitowa sanye da riga baƙa yayin da Abdul yasa wando fari, shi kuma Fadil ya saka baƙi sunyi kyau sosai idan ka gansu.
Sai dai duk da haka Abdul ya ɗara Fadil ɗin kyau, Saleema tayi sallama ta shigo jikin ta sanye da abaya baƙa tayi rolling da farin gyale.
Murmushi ɗauke a fuskar ta, Fadila da Husna da suka fito, suka kalli juna Fadila ta kwashe da dariya yayin da Husna ta ja tsaki.
"Yaya Abdul dan Allah mu tafi kawai", faɗar husna kenan cike da kishin ƴar uwar tata kuma yayar ta.
Saleema ta dubi Abdul tace; "fita zaku yi ne?", gira kawai ya ɗaga mata tayi murmushi tace; "da naga babu abinda zan yi ne shine nace bari nazo muyi fira amma tunda fita zaku yi shikenan bazan dakatar daku ba Allah ya kikaye hanya".
Abdul ya ɗan yi jim sannan yace; "ko dai zakije ne kinga sai muyi having fun tare?", Saleema ta ɗan yi dariya tace; "anya kuwa naga tafiyar ta yara ce amma tunda anyi mini tayi bana ƙi ba", da fadil da fadila suka kwashe da dariya saleemar na taya su.
Abdul kuwa kallon shi ya kai kan Husna yana sakin wani murmushi na rainin wayo, Husna kamar tayi kuka ta juya.
Fadil yace; "ya haka Husna kizo muje mana", cike da jin haushi tace; "ba zani ba na fasa", kan su ce wani abu ta shiga ɗakin Hajja.
Basu ƙara bi ta kanta ba suka yi waje, Abdul ke tuƙi a motar Saleemar yayin da Saleema ke gefen shi sai Fadil da Fadila a baya.
Ba wani fira suke ba dan Abdul ya maida hankalin shi kan tuƙi ne, ita kuma Saleema kacokan ta maida hankalin ta kan kallon shi, tana jin wani irin wuta ta ƙaunar shi kuma tane me fatan zamowa mata agare shi duk da tarin kunya da matsalar data hangowa a game da hakan.
Sun ɗan taɓa tafiya sannan ya juyo ya kalle ta yace; "Gamji get ko Peach palace?, wani irin abu taji daga kanta har zuwa ƙafafunta wanda yasa ta koma ta jingina da kujerar tana me lumshe idanu.
Tsinkayar muryar Fadila suka yi tana faɗin; "Abdul B mall Pls", ya juyo ya kalle ta sannan yace; "shikenan muje can ɗin kawai".
Yana tada motar ita kuma tana tsallako titin zata shiga unguwar su hakan yasa ya ɗan bangaje ta, da yake bangazar mota ne da mutum dan haka sai da ta faɗi kayan hannun ta suka zube.
Cikin sauri ya fito yana jan Innalillahi, suma su Fadil duk suka fito, kusa da ita ya ƙarasa yana taimaka mata wajen miƙewa.
Sai da ta miƙe tsaye sannan ya tsuguna yana tattaro mata kayan da suka zube sai dai abin ban haushi duk wasu sun fashe don taje kasuwa ne ta siyo, Flask, glass cup dinner set sai kuma plates na roba wanda Ummi ta bata kuɗi akan ta siyo mata.
Anyi sa'a dai dinner set ɗin da kayan robobin basu fashe ba amma flask da glass cup duk sun fashe.
Ya ɗauko dinner set ɗin da robobin ya zuba mata a ledar, ta ɗan ƙuje saman goshin ta sai kuma gwiwar hannun ta.
Sai da ya fara miƙa mata kayan sannan ya ga fuskar ta, gaban shi ya faɗi ganin yarinyar rannan wacce ya buge har ta nemi ta zage shi.
Itama Nusram gaban ta sai da ya faɗi sannan jikin ta ya ɗau rawa, ita kuwa bata son idanun wannan mutumin a kanta, ta kauda kai.
Abdul ya taɓe baki sannan yace; "kiyi haƙuri kuskure ne, ga wa'innan sauran kuma sun fashe".
"babu komai ai tsautsayi ne, na gode", ta faɗa in cool voice tana amsar kayan, mutanen dake wajen dai cece kuce suke yi.
Ya juya wajen Fadil yace; "akwai kuɗi a hannun ka?",Fadil ya girgiza kai yace; "babu wallahi Atm ne kawai".
Saleema da tausayin yarinyar ya kamata tayi saurin zaro kuɗi cikin jakarta dubu goma sha biyar ta miƙa ma Abdul akan ya bata.
Yayi murmushi yace; "thanks", sannan ya amsa ya miƙawa Nusram.
Nusram ta girgiza kai tace; "ba sai kun biyani ba tunda Allah yayi saiya fashe koba ta sanadiyar ku ba zai fashe ɗin".
Abdul ya damƙo hannun ta, wani yar suka ji gaba ɗaya hakan yasa ya kuma riƙe hannun, ita kuma da sauri ta ɗago ta kalle shi, kuɗin ya saka mata a tafin hannu sannan yace; "ba wai biyanki muka yi ba kya rage asara kiyi hakuri", daga haka ya saki hannun ta ya juya ya bar wajen.
Har suka tada motar suka tafi tana tsaye a wajen kamar statue sai da taga ɓacewar su sannan taja numfashi ta damƙe kuɗin ta juya ta fara tafiya itama jiki a sanyaye, mutanen wajen suna ta faɗin Allah ya kyauta amma ko samun damar amsa musu bata yi ba.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#FOLLOW @ WATTPAD 13DEEJA
#VOTE
*ga tambaya yau dai ku amsa mini naga masu bibiyar buk ɗin nan*.
-waye yafi birge ki a cikin su kuma ki kawo dalilin da yasa yafi birge ki?.
-wacece a cikin ukun nan kike tunanin itace jarumar littafin *Saleema,Nusreen ko Nusram* sannan ki kawo dalilin ki?.
-shin ko zaki iya cankar meke saka Malama kuka? Kuma menene dalilin da yasa Brr Farida tafi son Abdul kan sauran yaranta?.
-wai meke tsakanin Brr Farida da Brr Hauwa da yasa basa zama waje ɗaya, kuma meke tsakanin Brr Farida da surukanta wanda yasa bata son yayan ta suje gidan musamman ma Abdul?.
-Wai waye a tunanin ki su Tuge suke son kaiwa gaban matsafin su domin su bada jinin shi?.
-zuwa yanzu wane darasi kika koya daga wannan littafin? Idan babu ko ɗaya shin kina ganin a nan gaba zaki dauki wani darasi a ciki?.
-ya kika ɗauki littafin a ranki?
*bari muga wa'inda ke bibiyar littafin, idan kun amsa mini a dadinku ya kai na cigaba da idan baku bani amsa ba na dakata da littafin*
*Babyn Abdul, Maman Elham, Farouk da Meenal*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
*Zulaihat isma'il kamar yadda na alƙawaranta ga page ɗin ki ke ɗaya na gode sosai*
*Aunty oum deedat ina godiya sosai keda Aunty Ummee*.
*My Aunty Fatima mazadu barka da dawowa Allah ya kawo twins next time ya kuma raya mana baby*.
*ibnatu Baballe kinfi kowa son littafin nan kema na gode da kulawa*
📖📖17-18📖📖
Abin ya haɗe mata biyu ga yanayin da take ciki ga kuma dama sanyin da take dashi dan haka sai taga kamar an ƙarawa gidan nasu tsawo.
Tana shan kwanar lungun gidan su ta haɗu da Isa zai fito hannun shi riƙe da jaka, yana ganin ta ya washe baki, ita kuwa ta saukar da kanta ƙasa tana ƙoƙarin wucewa.
Ganin bata tanka ba ya gane Nusram ce dan haka ya ƙara washe baki sosai yana faɗin; "ƴar ƙanwa ta har an dawo", sosai mamaki ya kashe Nusram ganin ba haka suka saba ba a duk lokacin da suka haɗu hantara ce da tsana ke biyo baya.
"dama ina so muyi magana dake anjima fatan zaki tsaya ki saurare ni", ya katse mata tunani.
Kai kawai ta ɗaga mishi domin har yanzu tana jin hannun wannan mutumin a jikin ta ga yanayin daya saukar mata a jiki.
"yauwa ki same ni anjima bayan isha'i anan waje", nan ma dai ɗaga kai kawai tayi, daga haka ya wuce itama kuwa ta wuce.
Tana shiga ta tarar da Aziza da Ameera suna wanke-wanken kwanukan da suka yi talla yau gefe kuma sahura keta rizgar kuka.
Nusram ta matsa kusa da ita tace; "Sahura lafiya kuwa?", Sahura cikin zubar da hawaye tace; "Nusram har yanzu Idris be zo ba biko ni kuma na gaji da zaman gidan nan wallahi ina so na koma ɗaki na".
Sai da Nusram ta waiga taga babu kowa sannan taja Sahurar suka yi wajen famfo, ƙasa-ƙasa gudun kada a jiyo su tace; "Sahura ki faɗa mini ainihin abinda ya haɗaki da mijin ki".
Sahura ta ɗanyi shiru sannan tace; "Wallahi Nusram komai yana kawo mini ya ajiye to wani lokacin bana da kuɗin adashi shine sai na ɗauka na siyar ko kuma idan ina so na canza wani abin kamar shinkafa ko taliya tofa shine mamar shi ta faɗa mishi wai satar abinci nake mishi shine ya mini faɗa ni kuma naja tsaki shine ya tsinka mini mari ya koro ni gida".
Nusram ta ɗan yi jim sannan tace; "kinga Sahura ki yiwa kanki karatun ta natsu ki tsaya ki gyara gidan auren ki, ki san yadda rayuwar gidan nan take idan kuma ba tallan kike so ki sake komawa cikin shi ba to shikenan, kina ganin yadda har yanzu muke fama da rayuwa gashi nan Allah be kawo mana masoya ba da wuri dan haka ki tsaya ki yiwa mijin ki biyayya, ki bani number ɗin Idris ɗin zan neme shi gobe duk yadda muka yi zaki ji".
Sahura ta washe baki tana faɗin; "wallahi kinfi Nusreen hankali ke har Baba kinfi shi hankali, gashi nan ina so na koma ina tsoron na tunkare shi".
Nusram tayi murmushi har dimple ɗinta ya lotsa tace; "kai Sahura kece ai tun farko baki fada mishi gaskiya ba, ki bani zuwa gobe sai na neme shi kawai".
Sahura tace; "yanzu kuwa ƴar uwa Allah ya baki miji wanda yafi ɗan gote kuɗi muzo mu kwashi arziƙi", Nusram ta kwashe da dariya tace; "kada kiyi mini wannan fatan ai kuma sai abin ya shafe ku, kuna son gani na abu ya gagara ke dai bani kawai kada wani yazo ya gan mu tare, idan zakiyi mini addu'a kice ne Allah ya bani nagari".
Sahura ta janyo wayar ta Techno