Showing 75001 words to 78000 words out of 121992 words

Chapter 26 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt

28 Dec 2024

16083

"ta mutu mana waye ya damu yarinya taje ta gama iskancin ta, ta nuna mini ban isa ba ta kwaso abin kunyar ta shine zaki zo ki tasa ni a gaba wai sai na kaita asibiti, to wallahi babu inda zanje, ai inda Allah ya taimake ni ba ita kaɗai na haifa ba da sai dai a ɗauki gawata a gidan baƙin cikin ta ya kashe ni".


Ummi cikin kuka tace; "dan Allah ka taimaka kazo a kaita asibiti duk wannan idan ta sami lafiya ayi maganar", Baba yace; "wallahi Maimuna babu inda zanje ina saurayin da yayi cikin yazo ya kaita mana", be bari ta kuma cewa komai ba ya maida ƙofar ya rufe.


Nusram zuwa yanzu jikin ta har rawa yake yi, ga zafin ciwo ga kuma baƙin ciki na magan-ganun da Mahaifinta yake faɗa akanta.


Ummi ta jima a tsaye a wajen tana share hawaye kafin ta koma wajen Nusram ɗin ta taimaka ta ɗago ta suka fara tafiya a hankali har suka fice daga gidan.


Garin yayi tsit ga duhu, haka dai suke tafiya a hankali idan cikin ya murɗa sai dai ta tsugunna a wajen idan yayi sauƙi sai su cigaba da tafiya.


A haka har suka ƙaraso bakin titi, babu mutane sosai sai jefi-jefi kuma yawanci sai dai su kallesu kawai su wuce wasu ma basa ko kallon inda suke.


Duk motar da Ummi tayi ƙoƙarin tarewa bata tsayawa, ita dai Nusram na tsugunne tana riƙe da cikinta duk addu'ar da tazo bakin ta ita take yi.


Zasu kusa rabin awa a wajen sannan wata mota da har ta wuce ta kuma dawo da baya ta tsaya, mutumin ya leƙo da fuskar shi yace; "ina zuwa Hajiya da daddare haka".


Ummi tace; "kaga yarinya tace bata da lafiya shine nace ko zaka taimaka mana ka kaimu asibiti, wand ake kusa duk idan dare yayi rufewa suke yi".


Ba tare da ɓata lokaci ba ya buɗe musu ƙofa suka shiga, sannan yaja suka tafi, sun yi tafiya me ɗan nisa sannan suka iso asibitin.


Sai da ya taimaka ma Ummi suka shiga har cikin asibitin, aka bata gado har aka shiga duba ta domin babban mutum ne, ya duba agogon hannun shi ya kalli Ummi kafin ya ciro kuɗi a aljihun shi ya miƙo mata yace; "gashi ko zaku buƙaci wani abin, yanzu idan zan fita zan muku clearing bill ɗin ku", Ummi tsabar murna kamar ta tsuguna a ƙasa ta mishi godiya.


Yace; "kada ki damu ɗa na kowa ne Allah ya bata lafiya", Ummi ta amsa da ameen, haka ta bishi da kallo har ya fice daga asibitin, ga dai shi babban mutum amma kuma yana da sauƙin kai sosai.


Ta jima zaune a wajen kafin likitan ya fito sannan Nurses suka fito janye da gadon da Nusram ɗin ke kai a kwance, likitan yace; "ki bisu zasu kaita ɗakin da zata huta Alhaji Mustapha ya riga ya biya duk wani kuɗi da za'a yi muku aiki a nan, dan haka zuwa safe zaki je Pharmacy ki amso mata magun-gunan ta, inda ta buge ne ko kuma takata akayi dai ban sani ba to wajen ne ke mata zafi yaso ma ya taɓa mahaifarta amma Allah ya kiyaye be taɓa ba ɗin yanzu munyi mata allura insha Allahu nan da safiya zata sami sauƙi", Ummi tace; "to an gode sosai", tabi Nurses ɗin don kai Nusram ɗin ɗakin hutu.


Ɗaki na musamman aka kai su, su kaɗai ne a ciki ga couch nan sai gado har da tv wato plasma ga sanyi babu wani hayaniya, sai da suka jona mata drip sannan suka fice daga ɗakin.


Ummi ta shiga bayi ta ɗauro alwala sannan tazo ta shinfiɗa ɗan kwalin ta, dan bata ɗauko komai ba ta hau kai ta tada sallah.


Ta jima tana sallah kafin barci kuma ya kwashe ta wanda bata farka ba sai asuba, tana idar da sallah Nusram itama ta farka, zuwa lokacin ruwan ya kusa ƙarewa Ummi ta ɗauko mata roba me faɗi ta taimaka mata tayi alwala sannan tayi sallar a saman gadon.



***********⬇️⬇️⬇️******


*MAƘARFI ROAD, KADUNA*.


Hajiya Salma ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da kofi, ya juyo ya kalle ta, da sauri ta ja ɗan ƙaramin table ta ajiye a kai sannan ta nufi inda yake.


Ta taimaka mishi ya ƙarasa shirin shi, sannan ta riƙo hannun shi ta zaunar dashi, ta ɗauki cup ɗin data ajiye ta fara bashi a baki da kanta.


Tana gama bashi ya miƙe ta bishi da kallo yace; "meya faru ne Hajiyata?", tayi fari da idanu sannan tace; "account ɗina yayi low", yace; "zan miki transfer yanzu, baki da matsala sai ta kuɗi", ta ɗaga kai tana murmushi.

Ya matso kusa da ita yace; "har ni ba zaki yi kewa ba?", ta riƙo hannun shi cikin kissa tace; "shine ma kan gaba da zanyi, muje na raka ka, kada kayi missing flight", yana gaba tana bayan shi hannun ta riƙe da jakar shi don tafiya.

Suna saukowa akan steps yace; "ki kula da Khausar kin san yanayin rawar kanta and dan Allah ga amanar gidana nan da kuma yarana da dukiya dake kanki na damƙata a hannun ki, ki kula kinji".


Tace; "kada ka damu yadda ka tafi ka barmu haka zaka dawo ka same mu, zan kula da duk wata amana taka har kaje ka dawo".


Har bakin mota ta raka shi, masu tsaron lafiya suka buɗe mishi mota ya shiga, tana ɗaga mishi hannu har ya fice.


Taja tsaki tace; "taya zan so ɗanka bayan ni baka son nawa ƴaƴan", ta juya cikin sauri ta nufi cikin gida.


Tana shiga falon ta tarar da Khausar ta fito sanye da wando ɗan ƙarami zuwa cinya sai kuwa riga iya cibiya.


"kin tashi Baby?", Hajiya Salma ta faɗa, Khausar ta ɗaga kai sannan ta nufi dinning table domin karyawa yayin da Hajiya Salma kuma ta nufi ɗakin ta.


babu Jimawa Hajiya Salmar ta fito jikin ta sanye da Riga pink da ratsin fari sai wando pink, ta ɗora after dress a sama pink me shara-shara, sai ƙaramar jaka data rataya itama pink sai kuma makulli, ta yiwa Khausar peck a kumatu tana faɗin; "Baby na tafi sai na dawo", Khausar tace; "to Mummy".


Tana fita masu tsaron lafiya suka taho tayi saurin ɗaga musu hannu hakan yasa suka koma, motarta ta shiga ta tayar ta fice daga gidan cikin sauri.


Khausar na ganin fitar Mahaifiyar tata, ta ɗauki waya ta fara kira, bayan an ɗaga tace; "Baby dan Allah kiyi sauri ina jiran ki".


Ba'a ɗau lokaci ba sai ga ƙwanƙwasa ƙofa, cikin sauri Khausar ta buɗe mata ƙofa, suka kalli juna fuska ɗauke da murmushi kafin Khausar ta rungumo yarinyar suka yi cikin falon.


Hajiya Salma tana fita bata zarce ko'ina ba sai guest house ɗin Alhaji Sa'eed, kamar koda yaushe a can ta same shi sai dai wannan karon shi kaɗai ta samu babu Brr Hauwa.


"Kamar yadda muka tsara Alhaji Mustafa ya bar ƙasar nan", cewar Hajiya Salma kenan lokacin da take ƙoƙarin cire After Dress ɗin dake jikin ta.


Alhaji Sa'eed yayi murmushin mugun ta daga kwancen da yake yace; "kamar yadda muka tsara komai yana tafiya dai-dai, saƙon mutuwar ɗan shi zata riske shi a can", Hajiya Salma tayi murmushi tana kwanciya a jikin Alhaji Sa'eed.


******* ***********


*HAYIN RIGASA, KADUNA*.


sai da gari yayi haske sannan Ummi ta miƙe tace da Nusram; "bari na fita na ɗan zagaya na san ba za'a rasa abin siyarwa nan kusa ba da zaki karya dashi", Nusram tace; "to", dan har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba.


Ummi kuwa ficewa tayi daga asibitin domin neman abinda zasu karya ɗin hannun ta riƙe da wasu daga cikin kuɗin da bawan Allan da taji an kira da Alhaji Mustafa.


Bata daɗe da fita ba Nusram taji anyi sallama an turo ƙofar, ta ɗago tana me amsa sallamar, tsayawa tayi tana kallon mutumin, tabbas fuskar shi ce, wannan dai wanda takewa laƙabi da ɗan yankan kai sai dai wannan ya ɗan manyanta.


Duk ta ruɗe jikinta har rawa yake yi mata, tunanin ta shine kada dai canza kama yayi yazo domin cin galaba akanta wato ya tafi da ita.

Alhaji Mustafa ya zauna saman kujerar yana satar kallon yarinyar, a ranshi yana mamakin meye dalilin birkicewar ta lokaci ɗaya.

Sun jima a haka ɗakin shiru babu wanda yayi magana a tsakanin su, Ummi ta shigo da sallama hannun ta ɗauke da baƙar leda me ɗan girma.


Tana ganin Alhaji Mustafan ta washe baki tana faɗin; "sannu da zuwa Alhaji", ya shafa kanshi tare da yin murmushi har kumatun shi ya lotsa yace; "sannu da ƙoƙari ya me jikin".

Kaɗan ya rage Nusram ta suma, lallai ma wannan wato canza kama yayi dan yazo ya yaudare su kenan?, "tabbas shine wannan", Kallon da suke mata yasa ta gane a fili tayi maganar.

Ummi tace; "waye kenan?", Nusram kuwa duk yadda gabanta ke faɗuwa be hana tace; "wato kazo ka yaudare mu ne ko?, shine har da yin shigar dattijai to Allah ya tona maka asiri", bin ta kawai suke da idanu.


Ganin hakan yasa ta cigaba da cewa; "to ai na gane ka, dan fuskarka bata canza ba sannan ɗabi'ar ka ma haka", Ummi tazo kusa da ita ta riƙe ta.


"Nusram ki dawo hayyacin ki, wannan fa shine mutumin daya taimake mu jiya ya kawo mu nan asibitin", Nusram ta kalli Ummi tace; "na sani mana Ummi ai ba yau ya saba ɗauko ni ba kwanaki ma haka ya kawo ni.har ƙofar gida sai dai ba mutumin arziƙi bane kamar yadda kike faɗa, wannan da kike gani mugu ne ɗan yankan kai ne".

Tofa! Nan zufa ta fara karyowa Alhaji Mustafa, cikin inda-inda yace; "karya take yi ni ban taɓa ganin ta ba sai jiya daga taimako", Ummi tace; "ina jin dai bata hayyacin ta ne bari na kira likita", ta ƙarasa tana ficewa da sauri.


Alhaji Mustafa ya kuma kallon yarinyar, Nusram ta balla mishi harara tace; "wallahi idan ma wayar ka kake so ka amsa ba zan taɓa baka ba har sai ka bani ribbom ɗina, me fuska biyu kawai, a wajen bikin da akayi kwana huɗu daya wuce kayi shigar yarinta amma anan kayi shigar tsofaffi".


Kafin Alhaji Mustafa yace wani abu likita da Ummi sun shigo dan haka yaja bakin shi yayi shiru, banda zare idanu babu abinda yake yi, likita ya dubata babu abinda yake damunta amma gudun kada Alhaji Mustafa yace be san aikin shi ba gashi ya san cewa babban mutum ne yasa yayi mata allurar barci.

"kada ki damu stress ne yayi mata yawa insha Allahu zata dawo dai-dai zuwa anjima", Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace; "to likita angode sosai".

Bayan fitar likitan Alhaji Mustafa yace; "ni zan wuce dama na biyo na duba yadda jikinta yake ne, ga wasu kuɗin ko zaku nemi wani abin, yanzu zan bar ƙasar ne gabaki ɗaya Allah ya ƙara mata lafiya", Ummi ta amsa da "ameen", tana kuma me amsar kuɗin da ya miƙo mata.

"Alhaji a ƙara haƙuri dai, shirme ne irin na mara lafiya", Alhaji Mustafa yace; "babu komai Allah ya bata lafiya", daga haka ya fice daga ɗakin.

bayan fitar Alhaji Mustafan Ummi ta kira Aunty a waya ta faɗa mata cewa suna asibiti, Aunty tayi salati tana me faɗin gata nan zuwa yanzu Sulaiman zai kawo ta.

Ummi ta zubawa Nusram idanu lallai Allah kaɗai ya san wahalar da yarinyar nan tasha, abu kuma harda taɓin ƙwaƙwalwa.


Koda Aunty tazo kamar ta zubar da hawaye dan tausayi bayan Ummi ta gama bata labarin abinda ya faru, shi kanshi Sulaiman ɗin ya kai matuƙa wajen ɓacin rai.

"ki zauna dai Maman Nusreen wata rana sai kin kashe kanki da kuma yaranki, kada ki miƙe ki ƙwaci ƴancin ki", faɗar Aunty kenan.

Ummi ta miƙe tace; "ba haka ba Maman Adam haƙuri shine kan gaba kuma shine gimshiƙin zaman aure, bari naje gida na bar Kubra ita kaɗai babu kowa na san ba wanda zai kula da ita a gidan", Sulaiman ya miƙe yace; "muje tare Mama sai na rage miki hanya", tare suka fice yayinda suka bar Aunty a wajen Nusram ɗin.


Alhaji Mustafa kuwa koda ya dangana da motar shi, babu abinda yake sai sauke ajiyar zuciya, kada dai ace yarinyar nan ta san ainihin abinda yake aikatawa.


Magan-ganun ta babu abinda ya tsinta a ciki sai shirme wai ribbom da waya? Yaushe kuma akayi hakan?, ya kasa fahimtar inda ta dosa.

Can naga ya saki murmushi har kumatun shi ya lotsa, ya lumshe idanu yana ƙarara gasgata abinda zuciyar shi ke raya mishi🙄.

Ya girgiza kai yana me yin dariya, a fili yace; "lallai ta haɗu da Murad ne wajen ɗaurin auren su Alhaji Baballe".


Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace; " *ABDUS-SAMAD ƊANA GUDA ƊAYA TILO, YAUSHE ZAKA DAWO GARE NI NE?*.







#LIKE
#SHARE
#COMMENT



*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*





*ƳAR MUTAN ZAZZAU*





♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*








*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*












*_daga alƙalamin ✍_*



*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*


*sadaukarwa gare ku*



*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*


*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*

📖📖41-42📖📖


Kwanan Nusram biyu a asibiti sannan aka sallameta, zuwa lokacin kuwa ta sami sauƙi sosai sai dai har lokacin gefen cikin ya kan mata ciwo lokaci zuwa lokaci, likitan kuwa yace kada ta damu zai dena a hankali.


Babu wanda yazo daga gida dan ya dubata, dama kuma bata saka rai ba, Aunty ce dama ita kullum sai tazo.


Babu yadda Ummi bata yi ba akan Nusram din ta bari Yaya Sulaiman yazo sai ya kaisu gida taƙi yarda, domin ita asibitin ya ishe ta dole hakan nan Ummi ta tattara musu kayan su, suka taho.


Me Keke Napep suka ɗauka shata har ƙofar gida, abin ban haushi suna dawowa maƙwabta suka fara leƙe, ita dama Nusram Kubra ta ɗauka suka shige gida.


Tana jiyo yadda mutane ke ƙananan magan-ganu suna dariya, wasu harda yiwa Ummi ya mai jiki, ta ɗauka da zuciya ɗaya ne ko kuwa ta sani ita dai Nusram taji ta amsa daga nan kuma ta shige bata ƙara jiyo su ba.


Ameera na zaune tayi sallama amma ko ɗago kai bata yi ta kalle ta ba, Mama Jummai dake bayi tayi wuf ta fito, ta kalli Nusram ta riƙe haɓa tace; "eh lallai Abdullahi yayi gaskiya ciki ne fa aka zubar gashi nan tayi haske kamar me jego".

Nusram ta bita da kallo kawai, Ummi na zuwa ta ja hannunta, ta kaita ƙofar ɗaki sannan ta buɗe mata ƙofar tace; "shiga ciki", Nusram tabi umarnin Mahaifiyar ta.

Kubra ta ajiye saman kujera sannan ta fara kakkabe ɗakin kafin ta ɗauko tsintsiya ta hau shara, Ummi kuwa ruwa ta ɗora saman murhu don suyi wanka.

Yana yi zafi Nusram ta juye ta fara yi ta sawa Ummi wani, ta fito daga wankan kenan Isa ya shigo, bata ko kalli inda yake ba.

Ya matso kusa da ita yace; "ya jiki?", ba tare da ta kalle shi ba tace; "da sauƙi", yace; "Allah ya ƙara lafiya ya kawo me amfani", bata amsa ba sai dai cigaba da tayi da abinda take yi wato shanya Soson wankanta a sama.

Ya kuma cewa; "Nusram ni duk abinda kika yi a hakan ina sonki, kada ki damu tunda dai an zubar da cikin kawai ki amince muyi auren mu", ta ɗan juyo ta kalle shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login