Showing 66001 words to 69000 words out of 121992 words
Chapter 23 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
ko? Kema auren kike so kenan?", da sauri ta girgiza kai, cikin daka tsawa yace; "fita ki bani waje shashasha", har tana harɗewa wajen fita.
Sai da ta ganta a waje sannan tayi ajiyar zuciya kafin ta bawa bujen ta iska, Fadila dake kallo a falo ganin yadda Sumayyar ta shigo yasa itama ta ruɗe.
Nan ta hau tambayar ta abinda ya faru ba tare da ta bata amsa ba ta wuce ɗakin su, Surayya tayi murmushi tana girgiza kai.
"kada ki damu da wannan mashirmanciyar wata ƙila laifi ta yiwa Ya Abdul shi yasa ya tsoratata haka", Fadila banda ɗaga kai babu abinda take yi.
Koda aka yi kiran sallar la'asar ta ƙofar baya ya fice inda yaje yayi sallar shi sannan ya shigo ta ƙofar gaba.
Tun daga nesa ya hango su a tsaye da alama akwai abinda suke tattaunawa, ya ƙaraso wajen su da sallama, ya miƙawa Sameer hannu suka yi musabaha sannan ya kalli Fadila yace; "kinyi sallah ne?".
Ta girgiza kai da sauri, ya mata wani kallo babu shiri har tana harɗewa wajen barin wajen, Sameer na ƙwala mata kira amma ko juyowa bata yi ba, dan bata manta yadda Sumayya ta shigo ba ɗazu.
Sameer ya ɓalla mishi harara yace; "ka kore ta ko?", Abdul ya shafa gashin kanshi kan ya kalli Sameer ya taɓe fuska yace; "dan Allah yanzu me kuma nace ni", Sameer yayi dariya yana dukan kafaɗar Abdul ɗin.
Tameer daya shigo ya kalle su yace; "me kuke yi kuma anan?", Abdul yace; "firar auren ka muke yi Yaya", Tameer ya harare shi yace; "ina wasa da kai kenan?", Abdul ya shagwaɓe fuska.
Tameer yace; "maganar gaskiya na kasa tarar Mumny da maganar, wallahi", Abdul yace; "shikenan sai ka zauna a matsayin gauron ka", Tameer ya riƙo shi yace; "dan Allah mana, ka faɗa mata", yace; "me zance".
Tameer ya sosa kai yace; "ka gane yarinyar da nake so ne na tabbatar Mummy ba zata amince ba, ƴar wani ma'aikaci ne a company ɗin mu, kuma kasan halin Mummy tafi son ƴar me kuɗi".
Abdul ya ɗaga kafaɗa yace; "taɓ ai ra'ayi ne me sunan shi da sunan ta?", Tameer ya kuma washe baki yace; "Sunan ta Bilkisu ƴar Malam Sunusi Ladan", Abdul yace; "shikenan zan gwada sa'a ta".
Tameer yace; "nama san zata amince dan inda kaine magana ta ƙare", Abdul yace; "to idan ta amince meye tukuici na?", Tameer yace; "baƙar motar ka", Abdul ya shafa kai yana murmushi.
Sameer kuwa dariya yayi ganin yadda ɗan uwan nashi ya sallama haka da wuri, Abdul na barin wajen Sameer ya janyo Tameer yace; "anya kuwa soyayyar da kake nunawa Abdus-samad yanzu ta gaske ce?".
Tameer yace; "har cikin raina da gaske nake a da ɗin ma ina tunanin shine matsalar rayuwata ne sai da naga na kusa rasa shi sannan na tabbatar da ina son shi sai dai maganar gaskiya har yanzu ina kishin shi", Sameer yayi murmushi.
"bari naje nayi sallah", daga nan Sameer ɗin ya fice shi kuma Tameer ɗin ya shige cikin gida domin kuwa shi yayi sallar shi dama.
Fadila tana zuwa ta tarar da Sumayya ta idar da sallah, cikin sauri ta shige bayi ta hau alwala, Sumayya ta kwashe da dariya domin ta san kome ya faru.
Ta san cewa Abdus-samad babu abinda ya tsana irin mutum me wasa da Sallah duk shirin da kuke yi idan har kana wasa da Sallah to lallai zai ci ƙaniyar ka ne.
Fadila ta fito daga bayi, ganin Sumayya na dariya yasa ta kwaɗa mata harara sannan ta tada kabbarar sallah sai da ta idar sannan ta bata labarin abinda ya faru.
Nan itama Sumayya ta bata nata labarin, lokacin Surayya ta shigo haka suka haɗu suka dinga yiwa juna dariya.
Surayya tace; "haba Aunty Fadila ina shekarun ku kusan ɗaya me yasa kike tsoron shi", Fadila ta galla mata harara sannan tace; "ke baki san wannan bane wani lokacin fuskar yara gare shi wani lokacin kuma babu wasa wallahi ban san lokacin dana bar wajen ba", suka kuma kwashewa da dariya.
A falo ya same su zaune Bayan Sallar isha'i, ya kalle su yace; "kun yi sallah ko?", duka suka amsa da eh, yace; "First love fa?", Surayya tace; "tana sama", be kuma magana ba ya nufi saman.
Da sallama ya shiga ɗakin, Dr Abubakar na zaune saman carpet inda Brr Farida ke gefen shi tana mishi fira, Abdus-samad yayi murmushi soyayyar dake tsakanin iyayen shi abin yana bashi mamaki kuma yana birge shi.
Brr Farida ta tashi ta riƙo hannun shi har suka zo suka zauna, Dr Abubakar cikin zolaya yace; "gaskiya na kusa fara kishi da kai, waye ma ya kawo ka a wannan lokacin da nake buƙatar kulawar mata ta".
Abdus-samad yasa hannu biyu ya rufe fuskar shi, a dole nan yaji kunya, Brr Farida ta kwantar da Abdus-samad saman ƙafar ta sannan ta harari Dr Abubakar ɗin cikin wasa tace; "ai shi koda yaushe nake kulawa dashi kaine ma kake da ƙaiyadajjen lokaci".
Dr Abubakar ya ciza yatsa yace; "wayyo Allah na zasu haɗe mini kai", su kam banda dariya babu abinda suke yi.
Abdus-samad ya gyara zaman shi sannan yace; "Daddy dama magana nazo muyi", Dr Abubakar yace; "akan me fa?".
"dama magana ce akan Yaya Sameer da Yaya Tameer sune suka samu wa'inda zasu aura shine suka ce a sanar maka".
Ya ɗan saci kallon Brr Farida idanu kawai ta zuba mishi ya kauda kai ya maida kan Dr Abubakar sannan yace;
"To shine nace bari a sanar da kai", Dr Abubakar yayi murmushi sannan yace; "ka kira mini su yanzu", Abdus-samad ya ɗauki wayar shi ya kira su duka wanda babu ɓata lokaci suka zo.
Dr Abubakar ya kalle su yace; "naji saƙon ku a wajen Abdus-samad kuma insha Allahu zan bibiya na kuma yi bincike akan gidajen nasu yanzu sai ku mini bayanin su waye?".
Sameer ya shafa kai sannan yace; "ni dai yarinyar da nake so ita ce Fadila", Dr Abubakar yace; "wace Fadilar?", Sameer yace; "Fadilar nan gidan".
Brr Farida ta zaro idanu cikin sauri tace; "ba zai taɓa yiwuwa ba da raina ba zaka janyo mini abin ɓacin rai ba wallahi tun wuri ka canza ba zan taɓa amincewa ba".
"me yasa kike hakane Farida?", da sauri Brr Farida ta miƙe tace; "dangin ka Dr dangin ka fa ba zai taɓa yiwuwa ba kaima ka sani ba zan taɓa amimcewa ba".
Dr Abubakar yace; "Farida ki tsaya ki duba wannan lamarin mana", ba dan ranta yaso ba ta koma ta zauna ta wurgawa Sameer harara.
Dr Abubakar yace; "naji naka saura kai kuma", Tameer yace; "Bilkisu ce ƴar gidan Sunusi Ladan".
Brr Farida ta miƙe cikin sauri tace; "wane Sunusin ba dai wannan talakan ba?", Tameer ya ɗaga kai cike da tsoron kada taƙi amincewa.
Ta girgiza kai sannan tace; "ni Farida Alƙali zaka ɗaukowa ƴar talaka wanda beda cin yau balle na gobe, ni talaka wallahi ba zai yiwu ba".
Duka suka bita da kallo cike da mamakin abinda take faɗa, duk tabi ta birkice lokaci kaɗan.
Dr Abubakar yace; "ku tashi ku tafi Allah yayi muku albarka", suka amsa da ameen jikin su duk a sanyaye.
Dr Abubakar ya kalli Abdus-samad yace; "kaima jeka mana", Abdus-samad cike da damuwa ya fice daga ɗakin.
Bayan fitar shi sannan Dr Abubakar ya miƙe ya riƙo hannun ta, kusa dashi ya zaunar da ita sannan ya cika kofi da ruwa ya miƙo mata, ta amsa ta shaye tass.
Ya matse hannun ta sannan yace; " haba My Brr ki dena irin wannan shifa komai a rayuwa yana zuwa ne dai-dai yadda ka ɗauka, ki daure ki rage ƙiyayyar da kike yiwa ƴan uwa na da kuma talaka".
Brr Farida ta zame hannun ta sannan tace; "Dr har kana tunanin zan manta ƙiyayyar da ƴan uwan ka suka nuna mini?, ko kuwa na manta abinda talaka yayi mini ya rabani da abar ƙauna ta ƙawata aminiya ta wacce nake matuƙar ƙaunar ta".
Dr Abubakar yace; "Assha! Be kamata ace kin riƙe abinda ya faru a baya ba a cikin ranki, ki sani su ɗin yan uwa na ne kuma ba zan taɓa canza su ba shin ke ba zaki ɗauke su a matsayin ƴan uwa ba, haba Farida ki dinga haƙuri mana babu fa abinda yake tabbata a rayuwa komai da kika gani wucewa yake yi kada ki riƙe abinda ya faru cikin ranki, sannan maganar talaka ina so ki fahimci wani abu a ciki talaka akwai mutumin kirki akwai wanda yake akasin haka, haka acikin masu kuɗi akwai mutumin kirki akwai akasin haka, sannan baki san me Allah ya shirya musu ba a rayuwa, ki saka musu Albarka a matsayin ki na mahaifiyar su sai suga haske a rayuwar auren nasu amma fushin da zaki yi dasu shine zai bawa maƙiyin su da kuma wanda yake ƙoƙaerin cutar dasu dama wajen aiwatar da nufin su".
Lallai magan-ganun na Dr Abubakar ya shige ta, cikin sanyin jiki tace; "shikenan Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi", Dr Abubakar yayi murmushi yace" yauwa ko ke fa".
Zata yi magana ya dakatar da ita yayinda yace; "tashi muje muci abinci", Brr Farida ta miƙe haka suka jero cikin farin ciki.
Akan dinning suka same su, duka uku babu wanda ya iya cin abinci, fatan Sameer da Tameer shine Mummyn tasu ta amince da zaɓin nasu yayin da Abdus-samad kuma tunanin halin da ya baro Mahaifiyar tashi shine yasa.
Yana ganin su yayi saurin miƙewa ya ƙara inda take ya rungume ta, Brr Farida tayi dariya tace; "My Baby kenan?", shi ya ja mata kujera ta zauna.
Ganin yadda yaran nata suke cikin damuwa yasa ta fara jan su da fira har suka sake da ita, nan suka ci abincin su cikin annashuwa.
Bayan sun gama suka koma saman kujeru suka zauna, Abdul ya ɗora kanshi saman ƙafar ta yace; "First love na tambaye ki?".
Tace; "eh Baby na", ya yi murmushi sannan yace; "Waye Mustapha Abubakar Tuge", Brr Farida taji saukar sunan kamar saukar aradu.
Cikin sauri ta ture kan nashi daga jikin ta sannan tace; "a ina kaji wannan sunan kuma waye yace ka tambaye ni?".
"shi da kanshi ne ya faɗa mini, kuma muna kama sosai dashi, kin san na sanshi tun a london domin kuwa yana yawan zuwa ɗaya daga cikin attajiran dake Africa".
Brr Farida tace; "to wannan shine amsar tambayar ka, shi ɗin me kuɗi ne wanda ake ji dashi a Africa, sai kuma me kake son sani?".
Abdus-samad ya girgiza kai domin yadda Brr Faridar tayi magana ya nuna a hasale take.
"yauwa First love ya kira ni da Murad", ya faɗa yana me kallon mahaifiyar tashi, Brr Farida ta miƙe tsaye cikin hasala tace; "na faɗa maka Murad baya nufin komai a wajen ka, kada kuma ka sake tara ta da wannan maganar idan ba haka ba ranka zai ɓace", tana gama faɗar haka ta bar falon.
Abdus-samad ya kalli Dr Abubakar, cikin sauri kafin Abdus-samad ɗin yace wani abu, ya kalli Sameer yace; "ka shirya gobe zamu je Hayin rigasa daga nan zamu wuce Abuja", yana gama faɗar haka ya wuce ya bar falon.
Abdus-samad ya kalli Sameer, Sameer ya ɗaga mishi kafaɗa alamun i don't care, shima Abdul ɗin ya taɓe baki kafin ya miƙe ya fice.
Kida ya shiga part ɗin shi bayi kawai ya wuce yayi wanka, a gaban mirror ya tsaya yana ƙara kallon kanshi, so yake ya gano meye suke da bambamci da wannan mutumin na ɗazu wato Alhaji Mustapha.
Komai nasu kala ɗaya ne gaba ɗaya kamar tasu har ta ɓace, bambamcin su kaɗan ne wato bakin shi ƙarami ne ba kamar na wancan ba, banda wannan kuwa babu abinda suke da bambamci da juna sai tsufa kawai.
Ya lumshe idanu, ganin fuskar ta yasa yayi saurin buɗe idanu, babu abinda yake tunawa sai lokacin da gashin ta ya bayyana.
Cikin sauri ya ɗauko kayan daya cire ɗazu ya hau binciken ribbom ɗin nata, babu jimawa ya ganshi a aljihun shi, ya riƙe a hannun shi yana kallo.
Tuno yadda fuskar ta ke nuna tsantsar tsoro a duk lokacin da suka haɗu yasa yayi murmushi a hankali ya furta; "Nusraaaaaam!".
Yasin yana Abdul yana ruwa 🙄🙄🙄.
******** ***********
*MAƘARFI ROAD, KADUNA (GIDAN AMARYA)*.
Nusram ta miƙe cikin yanayi na rashin lafiya ta nufi bakin ƙofa ta fice daga ɗakin, bata taɓa tunanin Alhajin zai kai zuwa yanzu be shigo ba.
Ta tsaya tana kallon falon nata, bata san lokacin data ja tsaki ba inama ace wannan kuɗin da maman nata da Auntyn ta suka kashe gidan wanda take so ne.
Kanta da yake sara mata ta dafe sannan ta nufi wata ƙofa data gani, ganin ta a inda take zato wato Kitchen yasa taji daɗi sosai.
Buɗe-buɗe ta fara tana neman abinda zata ci, babu komai wanda zata iya ci dan haka dole ta fito, hango fridge yasa ta nufi can.
Allah ya bata sa'a domin ta sami ruwa pure water a ciki me sanyi dan haka ta ɗauko ɗaya daga ciki ta wuce ɗakin nata.
Bincike ta fara yi har Allah yasa taga kayan dubulan ɗin ta nan kuwa ta ɗiba ta hau ci hannu baka hannu ƙwarya, sai da ta ƙoshi sannan ta kora da ruwa.
Ta kai kallon ta kan agogon ɗakin ƙarfe sha biyu da rabi duk inda ango yake ya kamata ace zuwa yanzu yana cikin gidan shi.
Mema zai saka ta damu bayan ba wani son shi take yi ba, ita kanta tayi mamakin rashin tsoron data nuna, Allah sarki Nusreen ko yaya take yanzu oho, ko ta dena kuka zuwa yanzu bata sani ba.
Nan taji hawaye yana zubo mata, Allah yasa ma Shureim yana tare da ita ta san cewa yanzu zai rarrashe ta, ita fa bata da kowa, ta share hawayen daya zubo mata sannan ta nufi bayi.
Alwala ta ɗoro domin tazo tayi nafila, ta ɗauki hijab ta saka, Sallama taji a falo kafin tayi wani yunƙuri taji an nufo ɗakin ta wanda yayi dai-dai da fitowar mutum daga cikin wardrobe ɗin ta.
Kallon shi take bakin ta ɗauke da addu'a don a tunanin ta Aljani ne, ya matso kusa da ita yace; "yauwa masoyiyata kiyi sauri mu tafi kafin wancan ƙaton ragon ya shigo".
Alhaji Baballe da yayi niyar shigowa jin abinda ke gudana a cikin ɗakin yasa ya turo ƙofar cikin fushi, ya bisu da kallo yadda fuskar Nusram ya nuna tsoro da kuma hijab ɗin dake sanye a jikin ta ya gasgata abinda yaji.
Ya nuna ta da hannu "wato sai da kike nuna ban isa ba haka Uban daya haife ki ma be isa ba wallahi, dan haka sai na sauya miki kamanni ta yadda gobe wani namiji ba zai ga wannan kyawun naki ba har ya janyo hankalin shi gare ki", yana gama faɗar haka ya kulle ƙofar inda ya tafi neman abin duka.
Ganin haka yasa Bangis ɗaga window ya dira yayinda ya bar Nusram kamar statue, bata dawo hayyacin ta ba sai da taji ana buɗe ƙofar.
Alhaji Baballe ta gani hannun shi riƙe da zabgegiyar bulala irin ta wayar wuta, nan jikin Nusram ya fara rawa; "ka dakata kaji wallahi ba abinda kake tunani ban.......", bata samu damar ƙarasawa ba sabida saukar bulalar da taji.
Sosai ta daku a hannun Alhaji Baballe wanda dama kamar ƴa take a wajen shi, dan dai kawai aure ya ratsa tsakanin su ne, dama fatar Nusram fashewa take idan taji duka dan haka dan danan ya fasa mata jiki.
Tana bashi haƙuri tana zagaye ɗakin haka yake binta yana duka, har ta faɗi a ƙasa amma haka yasa ƙafa ya dinga takata yana huci.
Sai da ya gaji dan kanshi ya ƙyale ta, a lokacin gaba ɗaya kukan ma ya dena fita sai dai hawaye kawai da take yi na tsabar azabar da ta sha.
Ta dafe cikin ta wanda ke mata wani irin tsananin ciwo, tana ji tana kallo ya kira police akan suzo gidan shi, amma bata da damar yin magana.
Ya tashi ya shiga bayi ya taro ruwa ya fita be jima ba ya dawo hannun shi riƙe da bokitin ya nufi inda take ya shara mata ruwan.
Nusram ta runtse idanu tana jujjuya kai cikin wahala da tsananin raɗaɗin da take ji a inda ya zuba mata ruwan.
Ya kamo wuyan ta ya shaƙe yana faɗin; "ina ɗan iskan saurayin naki yake?", Nusram babu baki wuya kam ta sha ta, idanun ta yayi ja babu abinda take jira banda mutuwa tazo ta tafi da ita.
Ƙarar isowar motar ƴan sandan ya ƙwace ta daga hannun Alhaji Baballe, hijab ɗin ta ya kama ya jata har zuwa waje inda ƴan sandan suke tsaye sannan ya cilla musu ita yace;