Showing 90001 words to 93000 words out of 121992 words

Chapter 31 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt

28 Dec 2024

16105

ma ba wani sona kike yi ba ta wannan me kan gwandar kike".


Brr Farida ta riƙo hannun shi tace; "idan banda abinka, ai kai ne na gaban goshi, ita kuma a ƙeya take", wannan yasa suka kuma dariya.


Sameer yace; "mu dai ka wuce ka kaita zamu jira ka a office idan kayi latti kuma zaka amsa query", Abdus-samad ya murguɗa mishi baki.


Sameer zai kuma magana Brr Farida ta dakatar dashi tace; "dan Allah ka bari su tafi kawai".


Dr Abubakar da ya fito cikin shirin tafiya wajen aiki yace; "au har yanzu baku tafi ba kun tsaya wasa ko".

Brr Farida ta ƙarasa wajen mijinta tace; "nima abinda nake faɗa musu kenan, su tafi kawai Baby kuje Allah ya kiyaye hanya idan Ka kaita ka wuce company zaka sami Daddyn ku yana zaman jiran ka", Abdus-samad ya amsa da to.


Suna tsaye suna ɗaga musu hannu har suka fice daga gidan, kafin kowa kuma ya shiga tashi motar ya bar gidan, domin tafiya wajen aiki.


Kamar yadda Mahaifiyar tashi ta umarce shi a hankali yake tuƙin, Fadila ta kalle shi tayi murmushi.


Shima murmushin yayi sannan yace; "kin san umarnin uwa dole na cika shi", Fadila tace; "ni ina tsoro sai nake gani kamar Hajja ba zata amince da wannan auren ba".


Abdul cikin halin ko in kula yace; "to kada ta amince mana, ai ba ita keda iko da ke ba", Fadila kai tsaye tace; "amma ai tana da iko da iyayen mu ko".


Bece komai ba banda hankalin shi daya mayar kan tuƙin shi, dai-dai kwanar layin nasu yabi da kallo, tuno yadda suka yi kwanaki yasa yayi murmushi kawai.


Har ƙofar appartment ɗin su Hajjan ya kaita, Fadila ta buɗe ƙofa sannan ta waigo tace; "na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ga wannan dan Allah kada ka manta ka taho mini dashi".


Ya amshi ƴar paper ɗin, rubutu ne wanda shi ba zai tantance meye a jiki ba, ya kalle ta yace; "meye wannan", ta ɗan kauda kai tace; "abin amfani ne kai dai kawai ka siyo mini", ya balla mata harara yace; "wato har kin fara aike na kenan".


Tayi dariya tana ficewa daga cikin motar, shi kuma ya girgiza kai kan ya ja motar ya tafi, ya san ko yace zai shiga su gaisa ran shi ne kawai zai ɓace, gashi zuwa yanzu ya san Fadil baya gida yana wajen aiki.


Hanyar Companyn kawai ya ɗauke, gudu yake shararawa sosai domin kuwa ya san yayi latti gashi zuwa yanzu ya san Mahaifin nashi yana can yana zaman jiran shi.


*FARIDA AND SONS NIG LMTD*, sunan companyn nasu kenan, wanda kusan yayyin shi ke jan ragamar companyn, yana parking ma'aikatan suka fara gaishe dashi, ya tsaya suka gaisa cikin mutunci da girmama juna.


Kai tsaye ya wuce office ɗin CEO ɗin, inda a can ya sami Dr Abubakar na zaman jiran shi, koda ya shiga basu wani jima ba.


Dr Abubakar ya kalli Sameer wanda ya kasance shine CEO a wajen yace; "ga ɗan uwan ka nan zamu je yanzu mu dawo sai ka nuna mishi nashi office ɗin".


Sameer yace; "to", daga haka ya juya ya fice Abdus-samad ɗin na bin shi a baya, motar Dr Abubakar ɗin suka shiga dukan su.


Suna tafiya ya juyo ya kalli Abdus-samad yace; "abinda yasa zaka yi aiki a wancan companyn shine dan ka matsa kana so ka fara aiki amma yanzu zamu je inda nake company ɗin yake ana ta aikin shine amma insha Allahu nan bada jimawa ba za'a gama sai ka koma can", Abdul ya amsa da to.


Da ɗan tazara tsakanin wancan Companyn da wanda suka.je yanzu, a girma da faɗi wanda suka baro yafi wannan sai dai yadda tsarin wannan yake ya bambamta da wancan.


Dr Abubakar yace; "wannan shine Compnyn ka shiga kaga yadda tsarin shi yake ni zan wuce wajen aiki ne, idan naje zan saka driver ya kawo maka mota sai ka koma wajen naka aikin", Abdus-samad yace; "to".


Dr Abubakar ya tafi yayin da Abdus-samad ahi kuma ya shiga ciki domin ganin yadda tsarin companyn yake da duk yadda masu ginin ke aikin nasu.


********* ************


Nusram ke tsaye bakin titin da zai sadaka da Unguwar tasu, fuskarta tayi ja tsabar kukan da taci, yau shine cikar kwanakin da aka ɗibar mata gashi har zuwa lokacin bata sami wani wanda ya amsa zai aure ta ba.


akai-akai takan saka hannu ta share hawayen da yake zubo mata, kasancewar hanyace babba wacce mutane kan gifta suna hada-hadar su kowa yazo wucewa sai ya bita da kallo.


Ita kuwa duk ta ruɗe duk yadda ta dauki abin ya wuce haka, ta kalli samarin dake tahowa, baya ta koma kaɗan ta jingina da ginin dake kusa da ita.

Koda suka ƙaraso gare ta, tayi musu sallama, duk suka kalle ta, cikin rawar murya tace; "dan Allah mijin aure nake nema", wannan maganar ta basu dariya suka kuwa dara.

Nusram ta share hawayen daya zubo mata tace; "auren mahaifiyata Babana ya ɗora akan nawa yace idan ban fito da miji nayi aure ba a bakin auren ta, dan Allah ku taimake ni".

Suka yi shiru suna kallon ta, dan kyau akwai kyau, hijab pink ta saka dogo har ƙasa hakan ya hana ni ganin wane kalar kaya ne a jikin ta, ta janyo hijab ɗin ya rufe rabin fuskar ta wanda sai ka natsu sosai zaka iya fahimtar wacece.

Ɗaya ya kalli ɗaya yace; "Bello ko zaka shiga daga ciki ne, ni dai ka san yanzu ba zai yiwu na ɗaɗɗako aure ba ko?".

Wanda aka kira da Bello yace; "kai Aminu rabani da kyawawan matan nan, nifa gwara na nemi dai-dai ni na aure, kaga kalar wa'innan kayi shiru kawai, waye ya san me take aikatawa da mahaifin nata ya koro ta, ni dai kam ba zan iya ba kai dai idan zaka aure ta to bismillah sai muje a toshe ƙofar naka ɗakin a maida shi ta cikin gida".

Aminu yace; "bakada hankali ne yanzu ina naga kuɗin aure, sadaki akwati, waye yace maka mace kamar wannan zata iya zama a irin gidan mu, ɗaki ciki ɗaya".

Jikin Nusram har rawa yake yi wajen durƙusawa ƙasa tace; "wallahi zan zauna, ni dai dan Allah ku taimaka mini", suka kalli juna kafin Bellon yace; "kai anya kuwa wannan mutum ce Aminu yau munyi gamo", da sauri suka fara tafiya.

Nusram ta bisu kamar sabuwar mahaukaciya tana kuka tana roƙon su, ganin hakan yasa suka zuba a guje kowa na ƙoƙarin ceton ranshi.

Nusram kuwa ganin sun gudu yasa ta tsaya tana share hawayen da ya zubo mata, bata taɓa ɗauka matsalarta zata girma ta kai hakan ba.

Duk masallatai da kuma ƴan layin su kowa gudun ta yake yi, yanzu gashi tazo inda ba'a santa ba nan ma kallon aljana suke mata.

Tun safe take garari a hanya tana neman me auren ta amma ta rasa kowa ya kalleta sai yace tafi ƙarfin shi, ko kuma be san me take aikatawa wasu ma kallon zararriya suke yi mata.

Jin an fara kiran sallar Magrib yasa ta matsa can jikin wani masallaci ta zauna dole ta sake tunani, ta jima zaune tana kuka tare da tunanin halin da zata shiga ta kuma jefa auren mahaifiyar ta a ciki, kafin ta miƙe ta fara tafiya cikin galabaita.

Har ta ƙaraso gida babu wanda ya yarda da buƙatar ta, tana shigowa zaure Isa na fitowa ganin yadda tayi.wujiga-wujiga yasa ya kwashe da dariya yace; "lallai na ciri tuta ai dama na faɗa miki baki da miji sai ni", bata kula shi ba shi kuma be fasa faɗan abinda ya ke son faɗa ba.

"ki shiga ciki Baba na zaman jiran ki ai", jin hakan yasa gaban Nusram faɗuwa, cikin sanɗa ta leƙa tsakar gidan, Baba ne kuwa zaune saman tabarma yana faman masifa.

Ta jima tsaye tana tararrabin ta shiga ko kada ta shiga, a ƙarshe dai haka ta yanke shawarar shiga cikin gidan.

"eh da yake ni an raina ni.wato ke kaɗai zaki je Saudiar to naga wanda zai barki kije ɗin" maganar da Baban keyi kenan wacce ta daki kunnuwan Nusram ɗin.

Nusram tayi sallama ta shiga, Baba yace; "yauwa an dawo daga yawon barikin, zo nan", jikin Nusram ya kama rawa.

Ta tsuguna tace; "Baba gani", Baba yace; "ke wato dai sai kin kashe ni sannan hankalin ki zai kwanto ko", Nusram ta girgiza kai.

"to wallahi baƙin cikinki ba zai kashe ni ba, kinfi ƙarfin kowa yanzu sai dai mu zuba miki idanu ko?, ina ita me ɗaure miki gindin?".

Ummi dake zaune ƙofar ɗakin ta tace; "ina jinka ai faɗi abinda kake so ka faɗa", Baba yayi ƙwafa yace; "yauwa ai ina so kiji da kunnen ki ne".

Ya kalli.Isa da Mama Jummai yace; "kuma ina so kuji abinda zan faɗa domin ina so ku zama sheda".

Ya dawo da kallon shi kan Nusram sannan yace; "kin sami mijin auren", Nusram ta girgiza kai tace; "dan Allah Baba kayi haƙuri".

Baba ya ɗaga mata hannu yace; "sati me zuwa ɗaurin auren ki da Isa", Ummi tace; "wannan ne ba zai taɓa yiwuwa ba wallahi matuƙar ina da rai".

Baba ya miƙe yace; "shikenan sai ki fara shirya kayan ki na tafiya Dabai", babu tsoro ko shakka Ummi tace; "to shikenan".


Nusram ta fashe da kuka ta riƙo ƙafar mahaifin nata tana faɗin; "dan Allah Baba kayi haƙuri", ya zare ƙafar shi yace; "wallahi matuƙar wanda zaki aura be zo gobe ba to sai Uwar ki ta bar gidan nan sannan kuma auren ki da Isa babu fashi", be jira me zata ce ba yayi ficewar shi.


Nusram ta cigaba da kukanta cikin baƙin ciki, yanzu shikenan tayi sanadiyar rabuwar iyayen nata kenan, Ummi tazo ta miƙar da ita tsaye tace; "kada ki damu muje ɗaki".

Mama Jummai tayi shewa tace; "ahayye! Zamu gani dai idan tusa zata hura wuta ai duk wanda yaja dani sai naga bayan shi".

Ummi ta juyo tace; "ta Allah ba taki ba, duk sharrinki akan ki zai ƙare", daga haka taja Nusram suka shige ɗaki.

Mama Jummai tace; "ni yanzu ba zan ce miki komai ba amma ki sani ƴar ki zata shigo hannun mu ne nan da lokaci kaɗan zaki gane ruwa shayi ne".

Nusram ta zuba tagumi tana kallon Ummi na haɗa musu kaya, Nusram tace; "Ummi dan Allah kiyi hakuri ki bari na auri Isan kawai, in dai hakan zai saka ku cigaba da zaman aure da Baba".

Ummi tace; "ki bar wannan maganar Nusram, ki haɗa naki kayan domin kuwa tare zamu tafi dan wallahi ba zan taɓa bari ki auri Isa ba".

Nusram ta saka kuka tace; "ni kuma Ummi ba zan iya bari auren ku ya rabu ta dalilina ba, Ummi me zan ce da Nusreen da kuma Kubra", Ummi tace; "ba wannan na tambaye ki ba, ki tashi ki.haɗa kayan ki kawai".

Dole.haka Nusram ta fara haɗa kayan ta, tana yi tana kuka, Ummi kuwa ta miƙe ta fice don ɗauro alwala tazo ta tada sallah.

Ganin.fitar Ummi yasa Nusram miƙewa, jakar ta ƙarama ta ɗauko, kuɗin da Aunty ta bata ranar da taje gidan ta ɗauko ragowar ta saka a ciki ta ɗauki wayar wannan da bata san ko waye ba ta saka a ciki sannan ta saka hijab ta fice.

Akan ta dai ake faɗa ko to gwara ta bar gidan, dan ita ganin ta hakan shine maslaha kawai ba zata iya zama taga wannan ranar ba wacce zata kasance itace ta zama silar rabuwar iyayen nata.

Sai yanzu take data sani ta amsa auren Yaya Sulaiman ɗin wata ƙila ta sami mafita akan wannan bala'in da yake tinkaro ta, ta juya ta kalli gidan Allah sarki! Ummi ko yaya zata ji idan ta gane cewa guduwa Nusram ɗin tayi?.

Wane hali Ƴar uwar haihuwar nata zata ji a yayin da labari ya iske mata akan abinda Nusram ɗin tayi, yanzu ƴan layi dasu Mama Jummai zasu sami damar gorantawa Ummin, anya kuwa abinda kike so ki aikata Nusram ba kuskure bane?"abinda zuciyar ta ke faɗa mata kenan.

Ta girgiza kai tace; "wannan itace kawai mafita akan abinda ke damuna, dama ace Ummi zata yarda ne na auri Isan da rabuwar auren su ai gwara auren Isan", ta ƙara sauri a ƙoƙarin ta na ganin ta bar inda aka santa.

Haka ta iso bakin titi, lokacin ma yawanci mutane sun shiga sallar Isha'i, ta ƙara damƙe jakar dake hannun ta, kuɗin ciki tana tabbacin zai ishe ta ta sauka wani garin idan yaso sai ta siyar da wayar nan ta sami wajen zama da kuma jarin da zata riƙe kanta.







#LIKE
#SHARE
#COMMENTS




*babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.




*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


📖📖47-48📖📖


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*








*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



Addu'a A Kan Abokan Gaba


اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ.


Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar'a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum.
Ya Allah! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya
Allah! Ka karya su, ka girgiza su.




*_daga alƙalamin ✍_*



*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*


*sadaukarwa gare ku*



*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*


*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*

📖📖47-48📖📖



Abdus-samad yayi miƙa tare da yin hamma, agogon hannun shi ya duba ƙarfe shida harda rabi, gaskiya ya gaji daga fara aikin shi yau.


Cikin sauri ya fara tattara kayan shi domin tafiya, Tameer ya turo ƙofar ya shigo, ganin yadda yake haɗa kaya yasa yayi dariya yace; " duk ɗokin aikin kuma har ka gaji".


"amma dai ka san lokacin tashi ya wuce ko, a ƙa'ida 4 ya kamata ace na bar nan", Tameer ya buɗe baki cikeda mamaki yace; "a matsayinka na Co-ordinator".


Ya.lumshe ido yace; "as normal staff bari ka gani na gudu wajen First Love", be jira me zai kuma cewa ba ya fice.


A harabar Companyn ya haɗu da Surayya, "yauwa wuce mini da wannan gida, ki cewa First Love zan je Rigasa", ta amsa da to.

Ya shiga motar shi ya tafi, a hanya a ka fara kiraye-kirayen sallah wannan dalilin yasa ya sami masallaci yayi parking sai da ya idar da sallah sannan ya tafi.


Wani ƙaramin Mall yayi parking, ya ɗauko takardar ya juya ta a hannun shi, shi dai gaskiya babu abinda ya fahimta game da takardar.


Ya duba cikin Mall ɗin mutane ɗai-ɗaiku ne a ciki, wata matashiyar budurwa ya hango da sauri ya nufi inda take.


"amm dan Allah taimaka mini da wannan takardar", Yarinyar ta juyo, a tare suka zaro idanu.


Cikin mamaki Khausar tace; "Abdus-samad", yayi murmushi yace; "dama kecce", ta jinjina kai tana dariya.


"me kazo yi, mu ga takardar", ta faɗa tana miƙo hannu, ya saka mata takardar, ta ɗan jima tana dubawa sannan ta ɗago tace; "na san dai ba ƙanwarka ta aiko ka ba haka ba Mama bace, faɗa mini gaskiya budurwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login