Showing 6001 words to 9000 words out of 121992 words
Chapter 3 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
da kuma ƙwai, Nusram cike da baƙin cikin halin Mama Jumman ta kauda kai kawai.
Nusreen kuwa bata ce komai ba banda zama data gyarawa Kubra suna cigaba da cin abincin su, babu jimawa Baban nasu yayi sallama ya shiga, gaban Nusram ya yanke ya faɗi.
Suna gama cin abincin Nusreen ta kwashe kwanukan ta gyara wajen sannan ta koma kusa da ƴar uwar ta suka yi zaman fira.
Babu zato babu tsammani ya banko ɗakin ya shigo, yana hango su yayi kan su ya hau dukan su, yana faɗin; "marasa mutunci kawai".
Nusreen ta miƙe domin guduwa yasa ƙafa ya taɗiyo ta ta faɗi a wajen yayi kanta yana duka, daman ita yake so ya daka rashin gane wacece a ciki yasa ya haɗa su duka amma da ƙoƙarin gudun da tayi ya gano itace wacce yake nema dan haka ya rabu da Nusram yayi kanta.
Nusram kuwa tana kuka tana bashi haƙuri amma yaƙi haƙura, Ummi kuwa tunda ta saukar da kanta ƙasa bata kuma ɗagowa ta kalle shi ba, ganin hakan yasa Nusram faɗawa jikin ƴar uwar tata tana tare mata dukan.
Haka ya haɗa yayi musu duka sannan ya ƙyale su ya fice, ganin fitar shi yasa Nusram janye jikin ta cikin wahala domin ita fatar ta bata jure duka ko yaya yake, ita koda wanki ne ya cika yawa sai ya fasa mata hannu balle duka gashi kuma dama ɗazu tasha na Malam Abbas yanzu kuma tasha na Yayan su Isa.
Da ƙyar itama Nusreen ɗin ta miƙe ta zauna tana dafe da gefen cikin ta inda tasha ƙasa ɗazu, sai dai abin baƙin ciki kan su gama jimamin wannan duka suka jiyo hargagin mahaifin nasu ya nufo ɗakin nasu.
Nusreen haka taja jiki ta gudu ɗaki yayin da baƙin ciki ya hana Nusram tashi daga wajen, yana shigowa ya fara zuba mata wayar wutan dake hannun shi, tun tana zaune har sai da ta kwanta a wajen haka ya bita ya cigaba da duka sai da ya tabbatar da ko yatsa ba zata iya ɗagawa sannan ya ƙyale ta.
"kuma wallahi ko ku fito da mijin aure ko nayi ta azabtar daku a cikin gidan nan shegu masu baƙin jini irin na mahaifiyar su", ya cillar da ragowar wayar yayi waje yana bambami.
Sai da suka dena jiyo hargagin shi sannan Nusreen ta fito da sauri tazo ta kama ƴar uwar ta, Ummi kuwa tsabar ɓacin rai numfashin ta har sarkewa yake yi.
Duk yaji mata ciwo a fuska da jikin ta, Nusreen tace; "Ram ki dinga guduwar wa dukan Baba dana Yaya Isa", yadda tayi da fuska ya tabbatarwa da Nusreen cewa ranta ya ɓace.
Ummi ta miƙe ta juye mata ruwan data ɗora saman murhu bayan ta sauke abinci, kaɗan ta sirka mata sannan tace; "Nusreen kai mata bayi, ke kuma ki tashi ki cire kayan kije ki gaggasa jikin ki", babu musu duka suka miƙe suka hau aikata abinda Ummi ta umarce su.
Mama Jummai tayi shewa tace; "ai dama ni na wuce tunanin mutum gobe ma ki kuma turo su suyi mini rashin kunya ni kuma na kuma sa su gashi ahayye sai ni Jummala ƴa ga Habu sarkin wanzamai", babu wanda ya kula ta har tayi ta gama.
Nusram kuwa taji daɗin jikin ta data gasa tana fitowa Nusreen ta shiga tayi nata wankan.
Koda Nusram ta shigo ɗaki Ummi ta miƙo mata mansileta tace; "amshi wannan ki shafa", ta amsa ta shafa inda hannun ta ba zai kai ba Ummi ta taya ta ta shafa sannan ta miƙo mata wata doguwar riga mara nauyi hannun vest gare ta tace ta saka ta ansa ta saka sannan ta kwanta.
Nusreen ma koda tayi wanka kayan barci kawai ta saka riga da wando,rigar iya gwiwa sai wando dogo tana gama shiryawa ta haye bayan ƴar uwar ta ta kwanta.
Ummi ta kalle su cike da tausayawa tana me tausayin su, gasu duka mata Allah ya basu sai dai Allah ya bata ɗaya wacce ita ke ɗan ƙwato musu ƴancin, ta share hawayen ta tace; "Allah kana kallon wannan zalunci".
*WACECE NUSRAM DA NUSREEN*.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
📖📖5-6📖📖
Malam Abdullahi haifaffen ƙauyen dabai ne, mahaifin shi tun yana ƙarami Allah yayi mishi rasuwa sai mahaifiyar shi ta auri me garin Dabai.
Me garin Dabai kamar yadda yake tura ƴaƴan shi suyi karatu haka ya tura Abdullahi shima Zaria domin yin karatun, da yake me ƙwazo ne ya samu ya gama secondry yana dawowa me gari ya haɗa shi aure da Maimuna ƴar wazirin shi.
Sun zauna a garin dabai tsayin shekara ɗaya cikin so da kulawa daga nan sai ya sami aikin messenger na wani company a kaduna hakan shine silar dawowar su Kaduna, Tudun Nufawa
Anan Allah ya azurta su da yara guda biyu duka mata, shine aka saka musu Nusram da Nusreen, Malam Abdullahi ƴaƴa maza yaso amma Allah be bashi ba haka dole ya haƙura ya barwa Allah.
Anan inda suke suka haɗu da Hajiya Kaltume wacce ke zaune tare da mijin ta itama sai dai su suna da rufin asiri babu laifi.
Kamar ƴan uwan juna haka suke ita da Maimuna, ita ta raini Nusram kasancewar tafi Nusreen haƙuri tun suna ƙanana, babu ƙyashi ba komai duk abinda ta samu zata basu.
Har su Nusram suka kai shekaru bakwai amma Maimuna bata kuma samin ciki ba wannan fa ya soma kawo matsala a tsakanin zaman Abdullahi da kuma Maimuna.
Ita dai sai dai idan abin ya ishe ta tayi kukan ta godewa Allah, haka suke zaune cikin rufin asiri.
Nusram yarinya ce data biyo halin mahaifiyar ta na haƙuri da rashin son tashin hankali, yayin da Nusreen ta kasance me tsiwa da faɗa ga saurin fushi, sha yanzu magana yanzu.
Haka rayuwar su take gangarawa har lokacin da Abdullahi ya samu aikin zama a plaza wanda shine silar tashin su suka koma Hayin Rigasa domin can zai fi mishi sauƙi.
Maimuna da Kaltume sun ji zafin rabuwa da juna sai dai basu da yadda zasu yi, ita Kaltumen a lokacin tana da yara guda shida, Sulaiman shine babba sai Halima,mai bi mata Safeena sai Sadiya, Musa sai ƙaramin su Adam.
Shi kanshi Sulaiman ɗin shekara ɗaya kacal ya bawa su Nusram yayin da sauran ƙannen nashi duka su Nusram sun girme su da shekara biyu saboda shekara uku ke tsakanin ƴaƴan Kaltumen.
Anan wajen aiki anan Abdullahi ya haɗu da Jamila wacce ake kira da Jummai, ta kan kawo abinci ɗan gaban wajen kaɗan inda su kuma ƙananan ma'aikata su kan fita su siya.
Nan soyayya ta ƙullu a tsakanin su, har ta kaisu ga yin aure, Jummai macece da take ganin ta kai ta isa wacce taƙi aure da wuri tana ganin ai yawancin masu jinkirin nan sun fi samun mazaje masu kuɗi, sai da ta shekara ashirin da takwas sannan ta fara neman ya zata yi ta auru, nan fa mazaje suka ce basu san wannan ba.
Ana haka wani yaro wanda ba zai wuce shekara ashirin da biyar ba ya fito a kan yana son ta, nan fa ta hau tsalle tana murna ita da mahaifiyar ta Iya Nafi, ganin su zaman alkhairi ne.
Yayan ta Adamu ya kira ta yayi mata faɗa ya kuma yiwa yaron tatas domin ya san yaron zai yi wuya ya aure ta, aikuwa ta miƙe ta ci mishi mutunci ita da mahaifiyar ta ganin haka sai kowa ya saka musu idanu.
Aikuwa ta kira yaro suka cigaba da soyewa kan ta ankara ya ɗirka mata ciki ya gudu, koda suka farga sun ji takaici da haushi yayin da sauran ƴan uba suka shiga farin ciki da murna.
Babu abinda ba'a ɗurawa cikin ba amma da yake Allah ya raya kayan shi babu abinda ya sami cikin wannan ya ƙara ɗaga hankalin su, suna ji suna gani ta haifi yaron nata aka saka mishi suna Isa.
Daga nan mahaifiyar ta ta cigaba da rainon yaron inda ita kuma ta cigaba da ɗaukar tallar duk da ranta baya so tana ganin ta wuce talla haka mahaifiyarta ta lallaɓa ta domin kuwa idan tayi a gida babu me zuwa ya siya sai dai a barta dashi.
Lokacin da Abdullahi ya nuna yana son ta, sunyi matuƙar farin ciki da hakan, jin tsoron kada ya fasa idan yaji tana ɗa a waje yasa suka je aka rufe bakin shi ruf.
Lokacin da labarin auren yaje kunnen Maimuna bata wani tada hankalin ta ba domin kuwa babu rashin ci ko rashin sha, ƴaƴan ta suna zuwa makaranta dan suna primary five islamiyya ma sukan je kuma yana biya dai-dai gwargwado.
Ana auro Jummai komai ya fara taɓarɓarewa, amma duk da haka Maimuna ta cigaba da zaman haƙuri da Abdullahi.
Haka ta ɗauko ɗan shegen ta tazo dashi kuma Mal Abdullahi ya nuna yafi son shi sama da ƴaƴan daya haifa, tun yana ƙarami dan ya girmi su Nusram da shekara huɗu suka taso da ƙiyayyar juna, haka Jummai zata saka yayi musu dukan tsiya amma duk da hakan sai Nusreen ta san yadda tayi itama ta rama.
Sai da Jummai ta shekara guda sannan ta sami ciki, murna wajen Mal Abdullahi ba'a magana inda yake ganin zai sami ɗa namiji ta ɓangaren ta wannan ya bata lasisin shuka rashin mutuncin ta yadda take so.
Bayan wata tara sai gashi ta santalo ƴar ta mace aka saka mata Habiba, wannan shine abinda yaso ya kawo matsala tsakanin su sai dai da yake da asiri hakan be wani tasiri ba.
Kafin Habiba ta cika shekara ɗaya Jummai ta sake samun wani cikin nan fa sabuwar murna ta tashi, a lokacin kuma Nusram suka gama primary suka shiga aji ɗaya a secondry yayin da Isa ke aji uku a secondry.
Nan ma ta sake haifo mace inda murnar Malam Abdullahi ta koma ciki, ranar suna aka saka mata suna Sahura, sai da Sahura ta shekara Uku sannan ta sami wani cikin ta haifi mace aka saka mata Sakeena, to daga nan fa sai haihuwar ta ɗan tsaya mata.
Bata kuma samun ciki ba sai da su Nusram suka shiga aji huɗu a secondry shi kuma Isa yana aji shida a secondry sannan ta kuma samun ciki ta haifi ƴar ta mace aka saka mata suna Atika bata kuma cika shekara ba ta sami wata ƴar inda taci sunan mahaifiyar shi Kareema ake ce mata Ameera daga nan bata kuma samin wani cikin ba.
Nusram kuwa suna aji na shida a Secondry sannan maman su ta sami ciki, babu kunya ba tsoron Allah Malam Abdullahi ya fara murna akan zai sami ɗa namiji, nan kuma bakin Jummai ya mutu.
Su dai suka zubawa ikon Allah idanu, babu inda Jummai bata je ba don asiri amma kuma ciki yaƙi zubewa hakan ne ya ƙara tada hankalin ta.
Ciki na shiga watan haihuwa ta haifi ƴar ta mace, ranar Jummai har party sai da ta haɗa a gidan, su Habiba suna gama jss 3 ta cire su daga makaranta ta fara ɗora musu talla.
Haka Malam Abdullahi na kallo amma bashi da yadda zai yi da ita dole ya ƙyale ta, Kubra nada shekara ɗaya aka fara gane cewa aljanu sun taɓa ta wannan dalilin yasa Malam Abdullahi ya dena kwana a ɗakin Maimunar wai tsoron ta yake ji.
Ummi kuwa magani ta shiga nemawa ƴar ta, ta manta dashi, Nusreen kuwa ta buga tsalle tace Mama Jummai ce tayi mata asiri, sai da Ummi ta tsawatar mata sannan ta bari.
Tun daga lokacin da faɗa ya taɓa haɗa su da Nusreen ta kama ta zata dake ta Nusram taji haushi ta shiga.
Dama ance faɗan me haƙuri be iya ba, haka ta jibgi Mama Jummai da itace a kai dalilin kuwa Habiba ta fara tsayawa da saurayi sai takewa Nusreen ɗin habaici shine ita kuma ta gaza haƙuri har ta tsinkawa Habibar mari a lokacin Mama Jumman bata ce komai ba.
Sai da ta bari Nusreen ta saka guga a rijiya taje ta rufe ta da duka, Ummi tana zaune tana kallo bata ce komai ba, Nusram kuma na riƙe da Kubra tana shafa mata maganin da Auntyn Tudu (Hajiya Kaltume) ta amso ta kawo mata.
Wani haushi da zuciya ya taso mata, dama Maman ta ɗora abincin siyarwa tana dafawa ta saki ta tafi duka, wajen murhun ta nufa tana zuwa ta ɗauki itace ɗaya tayi kan Maman.
Tasa hannu ta janyo ta ta haɗa da bango, ta sa itacen ta dinga rafka mata a kai tun tana faɗin ta sake ta har ta gaji ta fara ihu, da kan ta Nusram ɗin ta sake ta Ummi bata ce komai ba.
Tunda ta sake ta, Maman tayi ɗaki bata fito ba a ranar girkin ma Habiba da Sahura suka ƙarasa suma a tsorace suke da Nusram ɗin domin sun san ba halin ta bane.
Baban na dawo ta faɗa mishi aikuwa har ɗaki ya bisu yayi musu shegen duka, wanda har ya jiwa Nusram ɗin ciwo a goshi wannan tabon shike bambace Nusram ɗin da Nusreen ɗin dan be ɓace ba sai dai ya disashe yadda sai ka ƙura idanu zaka ganshi.
Haka da Isa ya dawo ta sake faɗa mishi, shima ya kuma yi musu duka amma tun daga wannan lokacin ta tsorata bata kuma kai hannu ta daki Nusreen ɗin ba duk iya abinda zata yi mata in dai ta san Nusram ɗin tana nan sai dai suyi ta fatar baki, sai dai cewa da tayi tunda haka ne su da aure sai dai suga anayi.
Wannan be dame su ba domin sun san ta Allah ba tata ba, sun gama karatun su na secondry amma babu wanda ya taɓa zuwa sallama dasu.
Nan fa Baban ya kuma takura su da masifa ga Maman tana nata habaicin, Ana haka Habiba da Atika suka sami nasu tsayayyun nan fa gori da masifa ya sake tashi.
Babu me tanka musu sai Nusreen, haka abu yayi ta tafiya har aka zo aka yi biki ƴan dabai sun zo nan suka dinga shan surutu dan ma Nusreen ɗin tana mai da musu.
Bayan biki ne Auntyn Tudu ta bawa Ummi shawara maimakon zaman da zasu yi haka me zai hana su cigaba da karatu wannan dalilin yasa suka fara fafutukar shiga jami'a.
Lokacin da labari ya isa kunnen Baba cewa yayi ba saka hannun shi haka Ummin kan yi wankau da sana'ar ƙulle-ƙulle domin samun na rufin asiri.
Daga haka ma wata rana yace; "shifa ya gaji da ciyar da ƙatti dan haka zai dena bata kuɗin cefane", bata ce komai ba haka taje Dabai tasa aka siyar da shanun da take kiwo guda biyu.
Wanda wannan ne ya saka ta sami kuɗin dasu Nusram suka yi registration sauran kuma ta siyo shinkafa da taliya,macaronic,siga,gishiri,magi wake da sauransu ta fara siyarwa a gida.
Ita kuma dama Nusram ta iya kitso da lalle dashi suke samun rufin asiri, da taimakon Abba( mijin Kaltume) suka sami addmission a nan KASU inda Nusram ke karantar Business administration Nusreen kuma ke karantar Mass com.
Isa kuwa dama diploma yayi akan inter sci ya sami koyarwa a wata makaranta dake kusa dasu nan yake gangara rayuwar shi.
Duk da makaranta hakan besa su Nusram ɗin zama haka ba sukan je wajen Auntyn Tudu su amshi kayan ƙamshi, wato turaren tsinke dana wuta,humra,kwalakca, detol da air freshner su shiga dashi makaranta su siyar.
Abban ya buɗewa Sulaiman plaza inda yake siyar da takalma kayan sawa da sauran su wannan yasa har Takalma da sarƙoƙi sukan amsa su shiga dashi makaranta su siyar.
Suna aji ɗaya a jami'a Sakeena ta sami miji itama aka yi mata aure, wannan karon har duka sai da Baban yayi musu dan haushi.
Rufin asiri dai-dai gwargwado suna samu, Nusram kuwa idan ta sami lokaci har amarya ta kan shirya kwaliyya da komai-komai tana yi sai dai ita ɗin ba ma'abociyar yin kwalliyar bace a fuska sai dai takan yiwa wasu.
Nusreen dai ita tafi son karatun sama da sana'ar hannu wannan dalilin yasa bata cika maida hankali akan komai ba sai dai ta kan taya Nusram ɗin wajen kwalliya.
Wannan shine taƙaitaccen labarin su inda yanzu suke da shekara Ashirin da huɗu a duniya kuma har lokacin basu da tsayayyen saurayi gwara ma Nusreen ta kan samu sai dai tace bata