Showing 111001 words to 114000 words out of 121992 words
Chapter 38 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
sanar dasu zuwan nashi.
Ɗaya daga cikin masu tsaron gidan shine yayi mishi jagora har cikin falon baƙin, Abdus-samad yabi falon da kallo sosai tsarin falon ya birge shi.
Gida ne wanda ya amsa sunan shi ya ƙayatu sannan kana gani ka san cewa mamallakin gidan me kuɗin gaske ne bana wasa ba.
Wata ƴar matashiyar budurwa ta tura ƙofar ta shiga, tana zaune saman kujerar kwalliya tana fuskantar madubi, budurwar ta ɗan taɓe baki.
Tun da aka gama kwalliyar take zaman kallon kwalliyar wacce aka kashe maƙudan kuɗi domin yin ta, gaba ɗaya jiya zuwa yau ta hanasu sukuni da zuwan baƙon nata.
"Aunty baƙon ki ya iso yana falon ƙasa Hassan yace a sanar dake", jin abinda aka faɗa yasa tayi wuf ta miƙe, turare ta ɗauka ta kuma fesawa a jikin ta a karo na babu adadi ta kuma kai kallon ta jikin madubin.
Ta kalli matashiyar nan tace; "dan Allah nayi kyau kuwa Siddiƙa kina ganin zan iya birge shi".
Siddiƙa tace; "wallahi kin yi kyau sosai kuma koshi dutse ne sai yaji kin birge shi", jin abinda Siddiƙar ta faɗa yasa tayi ihu ta runguma Siddiƙar.
Sai kuma ta sake ta kafin ta ƙara gyara kanta sannan ta fice, cikin yauƙi da yanga ta nufi falon baƙin.
Hajiya Salma dake hangota ta taɓe baki tana jan dogon tsaki, yaushe zata yarda shirin ta ya ruguje, tuno abinda suka shirya yasa ta saki dariya.
Cikin sauri ta nufi kitchen ɗin kulolin dake saman cabinet ɗin ta buɗe lafiyayyen girki ne wanda Khausar ɗin ta saka akayi domin tarba Abdus-samad.
Sai da ta leƙa ta tabbatar babu wanda ya taho sannan ta ciro wani ƙullin magani ta buɗe ta zuba a ciki, cikin sauri ta rufe ta fice daga kitchen ɗin.
Khausar ta shiga da sallama a bakin ta, Abdus-samad ya amsa mata, ta ƙaraso da sauri kamar zata shige jikin shi.
ya ɗan janye daga jikin ta, "finally yau gashi kazo gidan mu", yayi murmushi kawai.
Jameel ya kira Brr Fairda ya faɗa mata cewa Abdus-samad gidan Alhaji Mustapha Tuge ya shiga, sosai hankalin ta ya tashi jin abinda aka faɗa.
Meye alaƙar shi da Alhaji Mustapha ne da har yaje gidan, lallai dole ta ɗauki mataki idan ba haka ba asirinta yana daf da tonowa.
"oh! mustapha na tsane ka a rayuwata", abinda ta faɗa kenan.
Khausar ta ƙwalawa Siddiƙa kira, cikin sauri tazo, "muje mu kawowa baƙona abin motsa baki", hakan ta faɗa sannan suka fice daga ɗakin.
Babu jimawa suka dawo ɗauke da wa'innan kololin, Hajiya Salma dake laɓe ta saki murmushi a ranta tace; "taka ta ƙare Abdus-samad".
ta kalle shi tana me tura mishi plate ɗin tace; "dan Allah kaci mana, tun safe nake wahala akan wannan girkin dan Allah kaci".
Abdus-samad yayi murmushi sannan yaja plate ɗin gaban shi, cokali ya saka ya ɗebo haɗaɗɗiyar fried rice ya kai bakin shi......
*ban san haka littafin nan haka yake da masoya ba sai jiya, gaskiya naji daɗi sosai Allah ya saka da alkhairi nagode sosai*.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouƙ*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
*Fatima Janyau (Teeymer) Shadown mu, keda Fatima Umar Modibbo (Bloody na), ku sani nima ina sonku sosai kamar yadda kuke sona*
📖📖59-60📖📖
Ƙarar wayar shi shine yayi sanadiyar da ya fasa kai abincin bakin shi, ya zaro wayar daga aljihun shi ganin Brr Farida yasa gaban shi faɗuwa.
Miƙewa yayi cikin sauri sannan ya ɗaga, Brr Farida najin an ɗaga cikin tashin hankali tace; "Abdus-samad meye ya kaika gidan Alhaji Mustapha?? Me kake nema wanda banyi maka shi ba?? Me yasa baka gudun ɓacin rai na duk irin son da na nuna maka shine kake ƙoƙarin juya mini bay............", bata sami damar ƙarasawa ba saboda kukan daya kufce mata, cikin sauri ta katse kiran.
Idan hankalin Abdus-samad ya kai dubu to sai da ya tashi, sakato ya tsaya riƙe da waya a hannun shi, what! A dalilin shi First Love ke zubar da hawaye🙄 Lallai ya aikata laifi mafi girma a rayuwar shi.
Khausar dake tsaye bayan shi tayi saurin ƙarasowa kusa dashi, hannu ta kai ta riƙo nashi tace; "Abdul meya faru?".
"Dan Allah ki ƙyale ni", abinda ya sami damar faɗa kenan yana kuma ƙoƙarin zare hannun shi dake cikin nata.
Khausar ta kuma riƙe hannun gam tace; "Abdul dan Allah kada ka rabu dani, ka tsaya dan Allah.....", wata tsawa ya daka mata wacce ta saka da sauri ta janye daga inda yake.
Ya jefe ta da wani kallo kafin ya juya ya fice daga falon, dai-dai zai shiga motar shi Alhaji Mustapha ya shigo, kallo ɗaya Abdus-samad yayi mishi ya ɗauke kai.
A halin yanzu duk sai yaji ya tsani Alhaji Mustaphan da duk wani abu daya shafe shi, ba zai iya jure ganin abinda zai zama sanadiyar zubar hawayen Mahaifiyar shi ba.
Cikin sauri ya buɗe motar shi ya shige kana ya fice daga gidan cikin matuƙar tashin hankali.
Alhaji Mustapha ya bishi da kallo hankali tashe, meya same shi?, ko dai wani abu ne ya faru dashi?", menene silar shi zuwa gidan?".
Cikin sauri ya nufi hanyar da zata sada shi da cikin gidan shi amma hakan ya gagara, dan haka ya juyo ɗaya daga cikin securities ɗin shi ya kira.
"Muhsin ka tabbatar da cewa yaron da ya fita ya isa inda yake son zuwa cikin ƙoshin lafiya", abinda ya faɗa kenan kana ya juya ya shige gida.
Ɓangaren Khausar kuwa tana ganin fitar Abdul ɗin ta saki wani irin kuka me ban tausayi, ita kuwa ya zata yi da rayuwar ta kenan?", kamar wacce aka tsikara ta miƙe da gudu ta bar ɗakin.
Hajiya Salma dake zaune tana huci, duk abinda ya faru akan idanun ta ya faru, kwata-kwata sun kasa ida nufin su kan wannan yaron gaba ɗaya so yake ya zamar musu *RAINA KAMA*.
Duk wani buri nasu da suke dashi ba zai taɓa cika ba matuƙar wannan yaron yana raye a duniya lallai dole su san yadda zasu yi ya bar duniya.
Faɗowar Khausar jikin ta shine ya dawo da ita daga kogin tunanin da ta faɗa, Khausar cikin kuka tace; "Mummy soyayyar Abdul zata kashe ni".
Wannan maganar karaf a kunnen Alhaji Mustapha, saukar ta kuma dai-dai da saukar aradu ya jita, cikin sanyin jiki ya ƙaraso falon inda Hajiya Salma ke aikawa da Khausar ɗin harara.
"yauwa Alhaji gwara daka dawo, yarinyar nan kan wannan yaron so take ta kashe kanta", abinda Hajiya Salma ta faɗa kenan cikin jin haushi.
Alhaji Mustapha dake zare idanu kamar wanda yayiwa Sarki ƙarya cikin inda-inda yace; "ki barni da ita Hajiya sai na ɗauki mataki akan ta tukunna zata ƙyale yaron nan, Khausar wannan yaron ba sa'an auren ki bane, ki manta dashi da wata banzar soyayyar da kike yi mishi kinji".
Khausar ta cuno baki kana ta miƙe ta bar wajen, ita bata san me yasa iyayen nata suke ƙinta da Abdul ba, ita kuma tayi alƙawari akan soyayyar Abdus-samad babu gudu babu ja da baya.
Hajiya Salma ta miƙe ta bar falon cikin sauri, ita wallahi da be ci ba ji take kamar ta ɗora hannu a kai ta saki ihu ko zata sami sauƙin abinda taƙe ji a ranta.
Ta zaro wayar ta sannan ta kira Alhaji Sa'eed, yana ɗagawa tace; "Alhaji kaga wacan ɗan iskan yaron beci wannan abincin ba?".
Alhaji Sa'eed yayi wani ihu kana ya zunduma ashar yace; "Salma wasa kike yi mini ko?, kin san kuɗin dana kashe wajen samo wannan maganin ko kin san irin wahalar dana sha kan na samo wannan maganin?".
Jin shiru ya kuma hasala shi, cikin ɗaga murya yace; "sai da naje har ƙasar India, a Kashmir na sami bokan daya bani wannan maganin, da ƙafa na hau saman dutse me ƙanƙara, ya bani tabbacin mutuwar Abdus-samad wanda ba zata bar alamar komai ba, zai yi hauka kafin nan ya mutu mutuwar wulaƙanci, na yarda dake na ɗauki maganin na baki ga dama ta samu amma kika bari har ya tafi be ci wannan maganin ba?".
Salma tayi huci tace; "wallahi komai ya tafi dai-dai bansan ɗan iskan yaron nan meya tuna ba wanda ya hana shi kai abincin nan bakin shi".
Alhaji Sa'eed yace; "duk yadda za'a yi ki tabbatar da cewa yaci wannan abincin idan ba haka sharrin da zai biyo baya ban san nima wane kala ba ne", daga haka ya katse wayar.
Hajiya Salma ta zuba uban tagumi yanzu ita yaya zata yi ta janyo Abdus-samad ɗin har yaci wannan abincin?, tunawa da bata kwashe abincin ba a wajen yasa ta miƙe zumbur.
Ɓangaren Alhaji Mustapha kuwa jiki a sanyaye ya wuce nashi ɗakin, zarya ya fara yi tsakanin falo zuwa bedroom ɗin shi, lallai dole ya ɗauki mataki idan ba haka ba kwaɓar shi zata yi ruwa.
Hannu ya ɗaga sama yace; "ya Allah duk da na san cewa ni me laifi ne amma ina roƙon ka daka kawo mini mafita da gaggawa".
Wayar shi ya ciro ya fara kiran Brr Jabeer, bata jima tana ringing ba Brr Jabeer ya ɗaga.
"Alhaji dama ina so mu haɗu domin magana akan takardun wannan companyn naka na garin jos".
Alhaji Mustapha ya tare shi; "dakata Brr ba wannan yasa na kira ba, Brr asirina yana daf da tonowa, Khausar da gaske son Abdus-samad take yi, na rasa ina zan saka kaina".
Brr Jabeer ya ɗan yi jim kana yace; "Alhaji Mustapha lokaci yayi daya kamata ka fito ka shaidawa duniya cewa Abdus-samad ɗan ka ne koda Brr Farida taso ko bata so ba".
Alhaji Mustapha yace; "wannan ba zai taɓa yiwuwa ba, Brr nafi so wannan maganar ta cigaba da kasancewa sirri sama da bayyanar ta domin idan ta bayyana tofa tawa ta ƙare".
Brr Jabeer yace; "Alhaji Babu fa abinda yake kasancewa sirri har abada dole watan wata rana Abdus-samad ya san gaskiyar abinda ya faru".
"bayan mutuwa ta ko?, da wane idanu kake so na kalli yaron nan idan gaskiyar lamari ya fito wallahi bana da wannan ƙarfin halin, dan haka ka canza shawara kawai".
"to shikenan Alhaji duk yadda kayi ma ai dai dai ne domin kuwa banda shawarar data wuce wacce na baka, sai anjima zan shigo insha Allahu".
Daga haka ya katse wayar, Alhaji Mustapha dai shiru yayi yana nazari kan wannan lamarin dake neman dagula mishi lissafi.
******* ********
*HAYIN RIGASA, KADUNA*
Yau saura kwana biyu a gudanar da meeting ɗin iyalin na wannan gidan wanda yayi dai-dai da kwanan Nusram takwas a gidan.
Zuwa wannan lokacin Nusram ta saba da ƴan gidan sosai musamman ma Dr Saleema wacce bata barin ta cikin kaɗaici sannan ga Muhibba da kuma Fadila wa'inda suka bi suka liƙe mata.
Duk yadda Nusram taso kaucewa Kabeer da Kamal abin ya faskara domin da zarar sun zauna ita da Muhibba a falo tofa suma zasu zo su zauna ga kallo da suke binta dashi.
Ɓangaren Nusram hankalinta ya kwanta sosai da sosai, sai dai har lokacin tunanin ta da zuciyar ta yana kan ƴan uwanta da mahaifiyar ta, sauƙin ta ma da yake yau suka je suka yi registration, wannan abu shine ya ƙara sauƙaƙa mata abinda yake damun ta domin ta san cewa idan har ta shiga makaranta zata samu damar ganin ƴar uwarta.
Abdus-samad kuwa rabon data ganshi tun ranar da yazo ya murɗe mata hannu, bata damu da rashin ganin shi ba domin Dr Saleema ta tsaya mata akan komai.
Gidan sosai ya kacame domin duk wani na nesa ya iso, na kusa kuma washe gari ake saka ran na kusa su iso suma, wannan dalilin yasa Nusram ja baya don tunda suka dawo daga asibiti bata leƙo falo ba domin komai taga na ƴan boko ne.
Dole Muhibba da Fadila suka biyo ta har ɗaki suna tambayar ta lafiya nan dai ta sanar dasu ita lafiyar ta lau, ita kuwa Dr Saleema bata ce mata komai ba dan itama ba hayaniyar ta cika so ba.
Ɓangaren Abdus-samad kuwa a gigice ya isa gida, ko gyara parking beyi ba ya afka cikin gidan.
A falo ya sami Brr Farida ƴaƴan ta kuma duka sun zagaye ta fuskar su ɗauke da damuwa.
Cikin sauri ya nufo inda take amma tsawar data daka mishi shine silar da ta saka ya dakata.
Ta ɗago fuskarta tayi ja alamun tasha kuka ta ƙoshi da hannu take nuna mishi hanyar waje.
Wannan karon kam har su Sameer sun tsorata da yanayin mahaifiyar tasu, "ba magana nake maka ba ka fita nace!!!!", ta sake faɗa da ƙarfi
Abdus-samad gaba ɗaya ruɗewa yayi ya rasa ina zai saka kanshi, shin fitar zai yi ko kuwa tsayawa zai yi.
Brr Farida ta miƙe a fusace tace; "tunda kai ba zaka fita ba ni bari na fita", jin hakan yasa da sauri Abdus-samad ya juya ya fice daga gidan.
Kan sitiyarin motar shi ya ɗora kanshi yana sakin ajiyar zuciya, idanun shi jajir saboda tashin hankali, be taɓa zaton ƙiyayyar da Mahaifiyar shi take yiwa Alhaji Mustapha ta kai haka ba.
Yanzu ina zai saka ranshi kenan?", wata zuciyar tace; "ka wuce Hayin Rigasa kawai", ya girgiza kai a fili yace; "babu inda zan je".
Shigowar motar Dr Abubakar itace ta saka shi sauke ajiyar zuciiya, cikin sauri ya fito, Dr Abubakar ɗin yayi saurin taro shi zuwa jikin shi ganin halin da yake ciki.
"Meya same ka?, baka da lafiya ne?", tambayar da Mahaifin nashi ya cillo mishi kenan.
Abdus-samad ya girgiza kai, cikin dasashshiyar murya yace; "Daddy First Love ce".
jin sunan da ya ambata ya saka hankalin Dr Abubakar tashi sosai a gigice yace; "meya same ta ne?".
Abdus-samad ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar dashi, sai lokacin hankalin Dr Abubakar ya ɗan kwanta.
Ya riƙo hannun Abdus-samad yace; "Abdul Mahaifiyar ku tana ƙoƙari wajen inganta rayuwar ku ya kamata ace duk abinda ta nuna bata so to ku guje shi", ya ɗan yi mishi nasiha sannan yace su shiga ciki.
Babu kowa a falon don haka sama suka wuce ɗakin ta, Brr Farida dake jikin window tana kallon komai ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna saman gadon ta.
Ita da kanta tace ya bar gidan amma kuma zuciyar ta taƙi bata haɗin kai, ta gode Allah da mijin nata ya dawo dashi, bata so ta nunawa maƙiyanta ta gaza.
Sallamar da suka yi itace ta dawo da ota daga tunanin da take yi, kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai.
Ta miƙe zata bar ɗakin Dr Abuɓakar yayi saurin riƙota, "Haba Brr kada ki kwashe ladan aikin da kika yi tsayin shekaru ashirin da bakwai mana".
"dan Allah First Love kiyi haƙuri, banyi tunani zuwana gidan Alhaji Mustapha zai ɓata miki rai har haka ba" , Brr Farida tayi shiru kamar bata ji shi ba.
Kusa da ita ya matsa ya ɗora kanshi saman kafar ta, bata kalle shi ba balle ya saka ran zata saurare shi, zuwa yanzu ya fara gazawa.
Cikin murya me rauni