Showing 99001 words to 102000 words out of 121992 words
Chapter 34 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
Nusreen ta ajiye mata takalmi me tudu ta saka, Nusreen ta ɗaukar mata duk wani abu da ta san zata buƙata ta saka cikin ƙatuwar Trolley bag ta ɗauka.
Suna fitowa tsakar gida Nusreen ta rangaɗa buɗa, Mama Jummai taja dogon tsaki, Nusreen kuwa ƙara sakin wata buɗar tayi ta ciri turare tana kuma fesa mata.
Har zasu fice Baba yace; "to sarakan zumuɗi an kwana biyu ba'a sami namijin da za'a ɓata ba shine yanzu har sauri kuke yi ko to ai sai ki dawo".
Nusreen ta juya tana zumɓurar baki, Nusram kuwa wajen Baban ta nufa, yace; "wajen Mamanki zaki je gata can a tsaye".
Nusreen data kusa ficewa daga gidan ta juyo tace; "a'a Baba ba sai taje wajen ta ba, ai na riga nayi mata faɗan da Uwa ke yiwa ƴarta".
Baɓa ya ɗauki takalmin dake kusa dashi ya jefa mata, da sauri tayi waje tana janye da jakar Nusram ɗin.
Koda ta fita sai da gaban Abdus-samad ya faɗi, Shureim yayi saurin taro ta ya amshi jakar.
ta juyo sannan tace; "ina angon yazo ya buɗe mana booth", Fadil dake tsaye yayi saurin zuwa ya buɗe mata Booth ɗin ta saka.
"yanzu ina zaki je?", Shureim ya faɗa ganin zata koma gida, ta kalle shi tace; "Hubby zan shiga ne ciki zan fito babu jimawa", daga haka ta shige.
"to kina dai gani da ƙyar kika samu wanda ya aure ki, shima ana bashi yana ƙin amsa da ƙyar aka shawo kanshi dan haka kada naji kada na gani, idan kika sake kika kashe wannan auren sai dai ki nemi wani uban ba dai ni ba", abinda Baba ya faɗa kenan kafin ya miƙe.
Nusram kuwa hawaye kawai take yi, wai shima ana bashi yana ƙin amsa, ita kuma haka take da baƙin jini🙆.
"tashi mana muje suna jiran ki", jin hakan yasa ta miƙe, suna zuwa zasu fita Nusreen na shigowa, ta riƙo hannun ƴar uwar tata kafin suka fice, Mama Jummai da Ameera da Isa suna bin su a baya.
Fadil na cikin mota a zaune, Shureim kuma yana jingine da motar yayinda nesa kaɗan Abdus-samad ke tsaye tare da Liman suna magana.
Suna fitowa waje, Nusreen ta rangaɗa buɗa Mama Jummai ta wulla mata harara, ta turo baki tace; "tunda ke ba zaki yi mana kara ba ai sai.muyi da kanmu", ta sake rangaɗa wata guɗar, hakan shine ya janyo hankalin Maƙwabtan nasu.
Fadil kam ji yake kamar wasa wai Abdul da mata, gashi har yanzu basu samu damar yin magana ba balle yaji taya akayi hakan ta kasance.
shi ya buɗe motar Nusreen ta riƙe hannun ƴar uwarta, sai lokacin Nusram ta samu hawaye suka zubo mata, rungume ƴar uwarta tayi suka fashe da kuka.
Baba dake tsaye bayan su ya ja tsaki yace; "wannan kuma wane sabon iskanci ne, dallah saketa su tafi kuna ta faman ɓata musu lokaci".
Nusreen ta saki Nusram tayi murmushi tace; "kada ki damu ƴar uwata ina ji a jikina ƙarshen wahalarki kenan?", Nusram ta jinjina kai.
Abdus-samad ya dafe kai, wannan wane irin ƙaddara ce, ya kuma kallon su ya ɗan taɓe baki sai faman ƙanƙame juna suke yi.
Baba yazo ya fincike hannun Nusram sannan ya sakata a mota, Nusreen ta zumɓuro baki, Baba ya harare ta yace; "kema wuce ki tafi gidan mijin ki".
Daga haka Baba ya kaɗa kai yayi gida, Liman ne ma ya ɗan ƙara yiwa Abdus-samad ɗin nasiha kafin su tafi.
Nan suka yi sallama da Shureim inda shima ya ɗauki matar shi suka wuce gida, sun fara tafiya Fadil yace; "Abdul me kenan?".
Bece komai ba, shima ganin hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru, har suka shiga Estate ɗin babu wanda yace komai.
"dakata anan", cikin sauri Fadil ɗin yayi parking, Abdus-samad yayi ajiyar zuciya yace; "fito sai muyi magana", Fadil ya amsa da to yana fita.
Kan wasu kujeru suka ƙarasa suka zauna, wajen dama daga gani irin na hutawa ne, Abdus-samad ya dafe da kanshi.
Fadil yace; "ka kira ni kuma ba kace komai ba", Abdus samad yaja ajiyar zuciya sannan yace; "Fadil banda abinda zance maka ne yanzu, shawarar ka nake nema kaina gaba ɗaya ya kulle, kaga tun ɗazu First Love ke kirana amma na kasa ɗagawa saboda tension ɗin dana shiga", ya ƙarasa yana ɗago mishi wayar shi.
Fadil ya tsaya yana kallon shi, Abdus-samad ya cigaba da cewa; "ka dai ga duk abinda ya faru yanzu wace shawara zaka bani?".
Fadil yace; "to ni dai ban san me zance maka ba a halin yanzu, dan na san ko giyar wake ka sha ba zaka doshi su Abba kace wai an ɗaura maka aure ba, haka ma Mahaifiyar ka, wannan kam ba me yiwuwa bane idan kayi la'akari da tsarin gidan nan".
Abdus-samad yayi shiru yana nazari tabbas abinda ɗan uwan shi ya faɗa gaskiya ne, yanzu me zai yi kenan, ya dafe kanshi.
Shi ji yake ina ma ace Baba wuƙa ya samu ya caka mishi ko kuma marin shi ya dinga yi, wannan wane irin abu ne?🙄.
Haka dama ake auren ko kuwa nashi ne yazo a haka, yanzu waye zai tunkara da wannan auren?, Abban Nihal ko Abban Fadil?, taɓ babu ko ɗaya, First Love ya san abinda ba zai yiwu ba kenan, me zai ce mata yaja bawa Uba haƙauri akan kada ya aurar da ƴar shi, shi kuma ya aura mishi ko me?".
Fadil yace; "ina jin ina da shawara", da sauri Abdus-samad ya buɗe idanu, Fadil yace; "me zai hana ka faɗawa Malama, idan yaso sai ta riƙe yarinyar a matsayin ƴar aiki?".
Ya jima yana kallon Fadil ɗin kafin ya girgiza kai, "wannan ba zai yiwu ba, taya kake ganin Malama zata iya ɓoye baban al'amari kamar wannan?".
Fadil yace; "hakane kuma gaskiya, sannan Hajja zata iya matsawa abin da bincike, to ka kai ta wani gidan mana sai ka ɓoye ta".
"wannan ma bana ji hakan me yiwuwa ne, ka duba ka ga yanayin yarinyar tana buƙatar me ɗebe mata kewa wanda zasu ɗan dinga fira, idan na kaita gida na ajiye ita kaɗai ban yi mata adalci ba".
Fadil yace; "kai sai ka dinga zuwa", wani kallo Abdus-samad yayi mishi kafin ya ɗauke kai, "kaima ka san Firzt Love ba zata yarda da fita ta any how ba, dole ta dinga bincikar ina naje, ina jin tsoron ranar da zata gane cewa mace na ajiye a gida nake kula da ita, ka nemo wata shawarar".
Fadil ya miƙe yace; "to ni gaskiya banda wata shawarar, ko kuma zaka kaita wajen Fadila ne sai ta kasance a matsayin ƙawarta?".
Abdul yayi jim kafin yace; "Fadila da zata yi aure babu jimawa, dole idan tayi aure na samu wajen ajiye ta", Fadil yace; "hakane kuma ka san bikin Familyn nan ba wani jan shi suke yi ba".
Shiru ya biyo bayan haka, kowa tunanin da yake yi daban, sun jima a haka kafin Fadil yace; "to ka kaita wajen Aunty Saleema mana".
Sai da ya tsaya yayi nazari kafin yace; "kana ganin hakan zai yiwu kuwa", Fadil cikin ƙwarin gwiwa yace; "tabbas kuwa zai yiwu, Aunty Saleema nada sauƙin kai kaga kenan zaka sami sauƙin kula da ita, na san soyayyar da take yi maka zai sa ta kula da ita sosai kuma kaga bata da wata damuwa sosai", Abdul ya jinjina kai.
Wayar shi ya zaro ya kira Saleemar akan ta same shi Garden yana jiran ta, cikin ɗoki da murna ta amsa da gata nan zuwa, shi kanshi sai da yayi murmushi saboda yadda ta nuna murnarta a fili.
Anya ba kasada zai yi ba, idan kuma kishi yasa ta ƙi amsarta fa ko kuma ta tona mishi asiri fa?, wannan kam anya ba ganganci bane zai aikata🙄.
#LIKE
#SHARE
#COMMENTS.
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
📖📖53-54📖📖
Tunda ya hangota gaban shi ya yanke ya faɗi, kada fa garin neman mafita ya jefa kanshi a matsala idan kuma bata amince bafa ta faɗawa Abban ta.
Ƙarasowar ta shine abinda ya katse mishi tunani, cikin natsuwa tayi sallama suka amsa mata, da murmushi taja kujera ta zauna sannan ta kalle shi tace; "lafiya kuwa?".
Abdus-samad ya juya ya kalli Fadil wanda dama shi yake kallo, Fadil yayi saurin girgiza mishi kai, Abdus-samad ya maida kanshi ya lumshe idanu.
Shiru ya biyo baya, ganin ba zasu yi magana bane yasa Saleema riƙo hannun shi tace; "Abdus-samad ka faɗa mini meke faruwa mana, damuwarka ai tamu ce, kada ka manta bakada wanda zai yaye maka damuwarka bayan Ubangijin daya halicceka sama da mu, idan har akwai shi to bayan mu yake kada kaji komai ka faɗa mini abinda ke faruwa nayi maka alkwari zan taimakeka kuma zan rufa maka asiri".
Ya buɗe idanu ya kalleta, gaban shi babu abinda yake yi banda dukan uku-uku ga wasi-wasin ya faɗa mata ko kada ya faɗa mata, can ya girgiza kai baya jin wannan mafitar zata ɓulle mishi.
Fadil yayi gyaran murya, ta juya ɓangaren shi nan ya bata labarin iya abinda ya sani akan yadda aka ɗaura auren ɗan uwan nashi da yarinyar da haƙuri yaje bawa Babanta.
Saleema tayi murmushi bayan ta gama jin abinda ya faru ta maida kallonta kan Abdul wanda ita ya zubawa idanu yana so yaga yanayin yadda fuskarta zata yi.
"taɓ, yanzu me kuke so ayi?", ta tambaya, Fadil ya sosa kai yace; "dama wai cewa muka yi ko zaki kaita appartment ɗinku, sai kice ƙawarki ce kafin komai ya dai-daita".
Saleema taja ajiyar zuciya tace; "Abban Nihal ya dawo jiya, Abban mu kuma nan da kwana biyar zai dawo amma zan yi ƙoƙari naga ba'a sami matsala ba, yanzu tana ina?".
"tana mota", amsar da Fadil ya bata kenan, bata kuma cewa komai ba sai wajen motar data nufa ta ɗan ƙwanƙwasa, Nusram da har lokaci banda kuka babu abinda take yi ta saka hannu ta buɗe ƙofar.
Saleema ta sakar mata murmushi sannan tace; "fito ko?", babu musu ta fito a ranta tace; "gidan yankan kai harda mace?", bata samu amsar tambayar ta ba, Saleema ta riƙo hannun ta suka nufi inda su Abdul ke zaune.
Tunda suka taho Abdus-samad ya zuba mata idanu, gaban shi sai faɗuwa yake yi, suna zama Nusram ta ɗago ta kalle shi yayi saurin kauda kai yana zaro wayar dake aljihun shi wacce keta faman tsuwwa tun ɗazu, kamar yadda ya zata Brr Farida ke kiran shi.
"Hello First Love", bata amsa ba sai cewa da tayi; "haba Baby ina ka shiga ne?, me kake aikatawa haka ka san dai ban fiye son yawo ba jiya ma Surayya tace mini da wuri ka bar Company amma baka taho gida ba yauma haka".
Abdul yaja numfashi yace; "First Love bafa wani waje naje ba, ina........", tayi saurin dakatar dashi; "kaga niba wannan ba duk inda kake ka tabbatar ka iso gida nan da minti talatin", tana faɗin haka ta katse wayar, ya bi wayar da kallo yana sakin ajiyar zuciya.
Saleema tace; "abinda za'ayi shine ka tafi gida kawai insha Allahu babu me sani har zuwa lokacin da zaka faɗa musu, zan yi iya ƙoƙari na mu bar wajen nan kada wani yazo ya gan mu", duka suka miƙe itama hannun Nusram ta kama suka miƙe tare.
Ta ɗan saki hannun ta sannan ta juya ta sauka, Fadil ma fita yayi daga rumfar, ya kalle ta ya kauda kai me kenan? Wai su nan sun bar su suyi sallama, yayi wani miskilin murmushi.
Nusram kuwa gabanta ke faɗuwa kawai, Abdus-samad yace; "kinga zaki zauna da wannan da tazo na san zata yi miki bayanin komai ki kwantar da hankalin ki insha Allahu komai zai dai-daita, yanzu ba zan iya fitowa nace an ɗaura mini aure dake ba duk abinda kike buƙata ki mata magana", be jira me zata ce ba ya fara tafiya.
Nusram ta saka hannu ta share hawayen dake zubo mata daga idanu kafin ta fito itama daga wajen, a bakin mota ta same su, Fadil na fito mata da kayanta.
Saleema tace; "ya sunanta ne?", Abdus-samad ya ɗan kalle ta ya basar, maida hankalin shi yayi kan Fadil yace; "zan tafi sai da safe", Fadil yace; "baka ji abinda Aunty Saleema tace bane?".
Ya ɗan lumshe idanu shifa wannan auren har ya fara zama takura a gare shi,cike da ƙagara yace; "Nusram", yana faɗin haka ya buɗe mota ya shiga.
Saleema na riƙe da hannun Nusram tana murmushi har suka dena hango shi, Saleema tayi murmushi kafin ta kalli Fadil tace; "shigar mana da kayan", suna gaba yana bin su a baya.
Da sallama suka shiga Mommy dake karatun jarida ta ɗago ta kalle su, Dr Saleema taja Nusram suka zauna a kujera.
"wannan fa daga ina?" ta jefo mata tambaya, Dr Saleema tace; "ƙawata ce dake karatu a KASU bata sami Hostel ba shine ta roƙe ni akan tana so ta zauna anan na ɗan wani lokaci", Mommy ta jinjina kai tana ƙara bin Nusram da kallo.
Nusram sai sake saukar da kai ƙasa take yi, cikin dashashshiyar muryar ta gaishe da Mommyn, ta amsa babu yabo ba fallasa.
Dr Saleema tace; "muje ciki ki ɗan huta tukunna", daga haka ta miƙe itama Nusram ta bita a baya, kayan da Fadil ya shigar mata dashi Dr Saleema ta gyara musu wajen zama sannan ta kalli Nusram tace; "ga bayi nan ki shiga kiyi wanka sai kizo muyi magana", ta amsa da to.
Hijab ta cire, Dr Saleema gabanta ya faɗi ganin irin yadda Nusram take da kyau na halitta, lallai kwanan nan Abdus-samad zai fara sonta, towel ta miƙa mata cike da kunya Nusram ta cire kayan ta ta saka towel ɗin, ita dai Dr Saleema babu abinda take sai binta da idanu, "fatabarakallahu Ahsanal khaliƙeen", abinda Dr Saleema ke maimaitawa cikin ranta kenan.
Nusram ta jima a bayin tana kuka ganin yadda rayuwa take wulagegeduwa da ita, daga nan sai nan, sai da Dr Saleema taji shirun yayi yawa sannan ta ƙwanƙwasa bayin, cikin sauri Nusram ta fara wankan.
Koda ta fito wajen madubi ta nufa, mayuka da turarruka da kayan kwalliya duka ta gansu masu tsada da kyau duk da kasancewar ta me yin kwalliya kuma tana yawan binciken kayan kwalliya ta network amma sai da taga abinda bata sani ba.
Mai ta shafa da powder sai ɗan man baki, ko kwalli bata saka ba, wajen jakarta ta nufa ta zage ta ciro riga half gown da wando blue and pink ta saka, ba tare da ta ɗaura ɗankwalin ba ta ɗora shi saman kai kawai.
Kusa da Dr Saleema tazo ta zauna kafin tace; "na gama Aunty", Dr Saleema tayi murmushi tace; "kinga nan shine gidan mu ni da Babana da Mama na da kishiyar ta da kuma ƴan uwana, gidan da kike ciki gida ne me mutane da yawa saboda haka sai kinyi taka tsantsan, kasancewar kinga mun kusa Family meeting duk wani wanda yake da jinin gidan nan zai halarta dan haka ki ƙara kulawa, kamar yadda nace ke ƙawata ce to zaki zauna a matsayin ƙawata, kullum idan zan tafi wajen aiki zan tafi da ke idan na dawo ma zamu dawo tare kin fahimta".
Nusram ta ɗaga kai, Dr Saleema tayi murmushi tace; " na san zaki ce me yasa Abdus-samad be kaiki gidan su ba ya kawo ki nan, dalili kuwa shine kinga gidan nan gidane na ƴan boko duk wanda kika gani a ciki mace da namiji ko ɗalibi ko ma'aikaci, sannan namiji aƙalla yakan kai shekara talatin kafin a bar shi yayi aure mace kuma ashirin da bakwai zuwa da takwas har ma sama da haka dan haka wannan shine dalili, ina so ki ɗauke ni ƴar uwar ki duk wani abu da kike buƙata kizo ki tambaye ni insha Allahu zan yi ƙoƙari ganin baki