Showing 117001 words to 120000 words out of 121992 words

Chapter 40 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt

28 Dec 2024

16096

Farida suka koma falo, kanshi ya kwantar saman ƙafar ta.

Ta saka hannu a saman kanshi tana shafawa, "baka ci komai ba fa?", ta faɗa fuskar ta ɗauke da damuwa, ya ɗan yi jim sannan yace; "bana jin yunwa ne".

Ta ɓalla mishi harara tace; "idan kana wani abin sai kace ƙaramin yaro amma kasan dai rabon ka da abinci tun a gida ko?", ya riƙo hannun ta yayi murmushi.

"First Love zan ci ne zuwa anjima kada ki damu", bata kuma cewa komai ba, kallon agogo yayi har takwas tayi.

Number ɗin Dr Saleema ya kuma kira, "wai har yanzu ba'a gama muku bane?", ya faɗa bayan ta ɗaga.

"eh idan an gama ai zamu taho ko, saura kaɗan a ƙarasa", ta faɗa a ɗan hasale domin ita a tunanin ta ya damu ne saboda matar shi.

Ya katse kiran kafin ya miƙe, Brr Farida tace; "ina zaka je ne?", be kalle ta ba yace; "zan je wajen Dr Saleema ne tun ɗazu ace wai ba'a gama ba, ko meye amfanin gyaran jikin ma oho".

Ita dai Brr Farida bata kuma cewa komai ba, juyawa yayi ya fice, a harabar gidan suka haɗu da Sumayya tace; "yaya wai ina Yaya Fadil ya shiga ne tun ɗazu nake neman shi?".

"nima ban ganshi ba", ya faɗa yana yin gaba, da sauri ta kuma biyo shi tace; "ina zaka je", be mata magana ba sai mota daya buɗe ya shiga, babu shiri Sumayya ta buɗe ɗayan gefen ta shiga, shi kuma yaja motar suka fice daga Estate ɗin.

Sai da suka yi nisa kafin ya kira Fadil, yana ɗagawa yace; "ka bani address ɗin inda kuke gani nan zuwa", Fadil yayi wani murmushi kafin yace; "ka gaza haƙuri ne mu dawo, kada ka damu yanzu zamu taho fa an kusa gama musu me kake ci na baka na zuba ai yanzu zata zo ka ganta".

Abdus-samad ya ja tsaki yace; "nifa ba wannan na tambaye ka ba, ka bani kawai idan zaka bani".

"kusa da Bio......graphics sabon Mall ɗin nan da aka buɗe to opposite ɗin shi", yana gama faɗar hakan Abdus-samad ya katse wayar.

Babu jimawa suka iso wajen, Fadil ya taso da sauri ganin ɗan uwan nashi, side hug suka yi da juna, Sumayya kuma ta gaishe dashi, Ya amsa yana tsokanar ta ita kuma tana dariya.

Ana haka suka buɗe ƙofar wajen suka fito, Muhibba da Fadila suna gaba sai Saleema da Nusram a baya, su Muhibba na ganin shi suka saki ihu sannan suka nufo wajen shi cike da murna.


Ya cire yatsun shi biyu daya saka ya danne kunnen shi yana hararar su, "kuna girma kuna cin ƙasa", Fadila ta kwashe da dariya tace; "aifa gyambo sarkin ƴan son girma ya zo".

Muhibba ta ɗago hannun ta tana nuna mishi lalle baƙi dake zane a hannun nata, "ga gayun da muka tsaya yi", ya kalla kana ya taɓe baki yace; "dama hutar da kanku kuka yi dan beyi kyau ba", Fadil ya kwashe da dariya yayin da Muhibba ta ɗaure fuska.

ya kai kallon shi wajen Dr Saleema wacce ta haɗe rai, gaban shi ya faɗi dan sam yama manta da ita, ita kanta Nusram din sai yanzu data ganshi ta tuna dashi kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannun ta.

muryar Fadil ta dawo dasu daga yanayin da suka shiga, "ni dai dan Allah kuzo mu tafi".

Duka suka nufi motar Fadil ɗin, dan dai ita Dr Saleema haushin shi take ji ganin kallon da yake bin Nusram dashi, ita kuma Nusram bin Dr Saleema kawai take yi.

Suna daf da shiga suka tsinkayi muryar shi yana faɗin; "Dr Saleema zo ku shiga nan", ita ba ƙaramar yarinya bace ta fahimci me yake nufi dan haka ta janyo hannun Nusram suka koma tashi motar.

Sumayya na gaba su kuma suna baya, Sumayya tace; "Aunty Saleema ina kika samo wannan kyakkyawar?".

Dr Saleema tayi yaƙe tace; "ƙawata ce karatu take a nan kaduna", Sumayya ta dinga santin Nusram.

Ita dai Nusram kanta yana ƙasa don duk ta takura kasancewar duk ɗagowar da zata yi zasu haɗa idanu ta madubi wanda yake saitin ta.

Haka har suka ƙarasa gida bata ce ko um ba, duka suka fito suka rankaya zuwa gidan, Abdus-samad ya saka hannu ya janyo Nusram ɗin ta dawo baya.

Hannun daya riƙe yake kallo, be taɓa ganin lallen daya birge shi kalar wannan ba, ja ne babu ɗigon baƙi ko kaɗan sai dai ya kama hannun nata sosai.

Dr Saleema dake baya ganin babu Nusram yasa ta juya, yayin da sai da tayi dana sanin juyar tata domin ganin abinda ke faruwa.

Cikin matuƙar damuwa ta sake juyar da kanta tana cigaba da tafiyar ta, wato Nusram ɗin ta san Abdul ya fi son lalle ja shiyasa taƙi yarda ayi mata baƙi don su dukkan su baƙi aka yi musu.

Hannun yake shafawa cike da birgewa, ya ɗago ya kalle ta kafin yace; "yayi kyau sosai", bata ce komai ba sai ƙoƙarin ƙwatar hannun ta da take yi.

Bata yi aune ba taga ya janyo ta jikin shi, hannu ya saka ya zame mayafin dake saman kanta, ya kuma zame ribbom ɗin dake kanta gashin ta ya sauka har gadon baya.

Cike da jin haushi Nusram ta fara ƙoƙarin ƙwacewa, doghnut ɗin da akayi shi da ƙyar saboda santsin gashin ta da kuma yawa shine ya kama ya wani kwance mata.

Bata dawo daga takaicin da take ciki ba taga ya buɗe motar shi ya shiga kana ya saka hannu ya janyo ta, kan jikin shi ta faɗa.

Hawayen takaici ya zubo mata, ita fa yanzu bata so ana takura mata, kanta ya ɗora saman ƙirjin shi ya saka hannun shi tsakiyar gashin ta yana shafawa a hankali.





#LIKE
#SHARE
#COMMENT




*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.






*ƳAR MUTAN ZAZZAU*








♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠



*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*






https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/






w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.




*_daga alƙalamin ✍_*



*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*


*sadaukarwa gare ku*



*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*


*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*


📖📖63-64📖📖


Shiru Nusram tayi domin yadda yake yi mata kamar tafiyar tsutsa, sai dai takaicin ta da kuma baƙin cikin ta yadda yake lalata mata adon da aka yiwa kan.


Abdus-samad kuwa wata irin natsuwa ke saukar mishi a duniya yana ƙaunar mace me gashi, ko dan wannan yake ji a ranshi zai iya zama da yarinyar.


Sun kai minti ashirin a haka, jin saukar numfashi a ƙirjin shi hakan ya tabbatar mishi da barci take yi, sannu a hankali ya ɗago da fuskar ta, fuskar ya zubawa idanu ba zai ce ga abinda yake ji akanta ba.


Idanun shi ya kai saman leɓen ta, barci take amma ta cuno shi gaba, "akwai tsiwa wannan", abinda ya faɗa kenan.


Abdul idan da kuma Nusreen ce fa🙄.


Bakin shi ya kai kan nata ya sumbata, yana ɗagowa suka haɗa idanu, saurin haɗe fuska yayi ya kauda kai, itama Nusram ɗin ta fara ƙoƙarin ƙwacewa.


Be sake ta sannan bece mata komai ba, sai ma kara ƙwaƙume ta da yayi, ganin ta kasa ƙwatar kanta yasa ta kalle shi tace; "dan Allah ka sake ni, Aunty Saleema na can na jira na".


Be sake ta ba kuma bece komai ba, shiru wajen yayi na ƴan daƙiƙu kana yace; "dama ashe kina magana kenan amma shine kika ganni a matsayi na na mijin ki ko gaisuwa ko?".


Nusram ta kauda kai tana taɓe baki, wai miji!? Shi har wani kiran kanshi miji yake yi, hannu ya saka saman fuskar ta shine abinda ya dawo da ita daga tunanin data faɗa.

"me kike tunani haka?", tace; "babu komai", hannun ta ya ɗago ya kuma kallon kunshin dake kwance saman fatar tata, "waye yayi miki wannan?".

"nima ban san sunan wajen ba, amma inda muka je da Aunty Saleema, beyi kyau ba ko", ita kanta bata san ƙarashen maganar ta fito ba.

Ya kalli ƙwayar idanun ta wacce ta kafe shi dashi tana jira taji me zai ce, ya ɗan kauda kai yayi murmushi yace; "idan nace beyi kyau ba me zaki ji", bata ce komai ba sai cuno baki da tayi gaba.

Ƙarar wayar shi ya katse shirun da suka yi, ganin First Love a jiki ya sa shi ɗagawa, ajiyeta yayi saman pocket ɗin motar ya maida ta handsfree.


"Baby kana ina ne?", tun daga jin sunan Nusram ta miƙe zumbur, cikin ranta ta maimaita "baby, lallai ma wato budurwar shi ce kenan?", kallon shi tayi shima ita yake kallo suna haɗa idanu ta wurga mishi wata harara kafin ta fara ƙoƙarin fita daga motar.


Lumshe idanu yayi sannan ya saka hannu ya maida ta jikin shi ya ƙara matsewa yadda tayi ba ƙaramin birge shi abin yayi ba ga wata dariya da tazo mishi, wai ita kishi take ko me?.


Nace; "oho muku munasirai😏😏 Kuna so kuna kaiwa kasuwa".


"hello Baby kana jina kuwa?", Brr Farida ta ƙara maimaitawa, cikin kasala yace; "First Love ina jin ki".


"kana ina?", tambayar data jefo mishi kenan, kai tsaye yace; "naje taɗi ne", cikin tsananin mamaki da tashin hankali tace; "tadi kuma?", bece komai ba.


Ta kuma cewa; "kaga minti biyar na baka ina buƙatar ganin ka, bana ciki da shirmen ka, kana jina minti biyar idan ka wuce ranka sai ya ɓace kana jina", bata jira me zai ce ba ta katse wayar.


Kallon shi ya maida kan Nusram data runtse idanu babu abinda take ji banda wani haushin shi wato sai ya nuna mata bata da amfani kenan.


Gefen fuskarta ya shafa, sannu a hankali ta buɗe idanun, kallo ɗaya tayi mishi ta kauda kai sakin ta yayi suka fito daga motar, kafin yace wani abu harta nufi ciki da sauri.

Cikin sauri ya biyo ta, hannu ya saka ya riƙota ya dawo da ita baya, wani kallo ya aika mata kana yace; "baki da hankali ne a haka zaki shiga gidan?".

Wannan yayi dai-dai da fitowar Dr Saleema wacce ta kasa haƙurin jure barin nasu tare, tunda ta shiga hankalin ta ke kansu idan tayi kamar ta kauda kai sai ta kasa.

Ƙarshe ma dai ɗaki ta shige tana zubar da hawaye, sosai hakan ke taɓa ranta ta rasa ina zata saka kanta a wannan lokacin ji take da ace tana da yadda zata yi ta cire soyayyar Abdus-samad ɗin a ranta da tayi kodan ta huta da wannan takaicin da tashin hankalin.

Fitowa tayi ta nufi waje domin dai haƙurin ta gaza yin shi, sai kuma tayi rashin sa'a da mugun gani domin wannan maganar tashi a kunnen ta ta sauka ga kuma yadda taga Nusram ɗin, mayafi da ribbom a hannu ga gashi a warwatse.

Runtse idanu tayi zuciyar ta na bugawa da sauri, shikenan aikin gama ya gama, ko ba'a faɗa mata ba yanayin yadda ta gansu kawai zuciyar ta bata me afkuwa ta afku.


kasancewar Nusram ta juya baya yasa bata ga Dr Saleemar ba, shi kuma Abdus-samad ɗin hankalin shi na kan Nusram ɗin bema lura da bayan ta ba.


Cikin kishin da bata san tana dashi ba tace; "a'a ba First Love ba saura Last Love", ta ƙarasa tana ajiyar zuciya.


Hannu ya saka a ƙugunta ya janyo ta jikin shi, fuskar su ya haɗe kafin yace; "ai zan samu Last Love ɗin kwanan nan", kan tace komai ya sumbaci goshinta da saman hancin ta.


Yana ƙoƙarin kaiwa bakin ta Dr Saleema da ta kasa haƙuri ta kira sunan ta, "Nusram!".


Da sauri suka waiwayo, Dr Saleema ta ɗan ja numfashi kafin tace; "dare nayi bana so Abba yazo ya same ki a nan ki shiga matsala nima ki jefa ni ya kamata ki dinga kiyayewa".


Hannun ta tazo ta kama, Abdul yayi saurin sakin ta, daga Dr Saleemar har Nusram ɗin babu wanda ya kalle shi suka wuce.


Ya bisu da kallo yana murmushi, a hankali ya shafa gashin kanshi yace; "na shiga uku na ni Abdus-samad", kowacce kishi take yi, ita Nusram tana kishi da First Love😁, ita kuma Dr Saleema da Nusram dan yadda fuskar ta tayi ya tabbatar mishi da ranta a ɓace yake.


Juyawa yayi ya shiga motar shi ya bar gidan, koda ya ƙarasa Appartment ɗin su Hajja da sauri ya shiga ciki.

Kafin ya ƙarasa falo ya sami Husna a tsaye kallon shi tayi idanun ta jajir alamar kuka tasha.

Cikin ɓacin rai tace; "Yaya na me nayi maka da baka so na?, me waccen yarinyar ta fini dashi, ka san irin son da nake yi maka amma baka taɓa kallo na a matsayin masoyiyar ka ba, sai dai kullum nayi ta wahala da son ka a cikin raina, ba zan hanaka zuwa taɗi ba amma zan ji zafi duk lokacin daka tafi, sai dai duk da haka ina roko da fatan Allah yasa nima wata rana ka soni kamar yadda kake son waccen", tana gama faɗar haka ta shige ciki tana cigaba da kukan ta.

ya sa hannu ya dafe kanshi, shi kam yau yaga ta kanshi kowacce tana fushi dashi da kuma nuna kishin ta ƙarara abin dariyar kuma kowacce akan abu mabambamta, ita kuma wannan me ta jiyo ne?.

Lokacin da yake faɗawa Brr Farida yana wajen budurwar shi ne ai tana wajen a lokacin, wannan shine abinda ya 9 hankalin ta.


Ya saki wani murmushi, shi abin nasu dariya ma yake bashi, lallai me mata uku yana ƙoƙari to ina shi ina wannan aikin ai ko biyu da wuya ya iya haɗawa kodan gudun irin wannan.


Da sallama ya shiga, mutane da yawa ke zaune a falon amma babu Brr Farida, gaishe dasu yayi wasu daga cikin su har suna jan shi da wasa shi dai sai dai kawai yayi murmushi.


Ɗakin Hajja ya nufa a tunanin shi Brr Farida na can, bata ciki don haka ya fito ya nufi ɗakin Malama anan kuwa ya same ta, zaune tare da Ummin Fadila suna fira.


Su kaɗai ne a ɗakin dan haka ya shiga da sallama suka amsa mishi, Brr Farida ta bishi da kallo har ya ƙaraso kusa da ita.


Ganin kallon yaƙi ƙarewa ya saka shi taɓe fuska yace; "First Love wannan kallon fa?", hannu ta saka ta kama kunnen shi tace; "wannan kunnen baya jin magana ko?", ya ɗan saki ƙara yana turo baki.


Malama ta shigo da sallama itama, ganin shi yasa tace; "ashe har ɗan naki ya shigo kenan?", Brr Farida ta saki kunnen shi ta maida kallon ta kan Malama tace; "eh gashi nan ya shigo yanzu".

Gefe ya koma ya zauna yana turo baki gaba, Brr Farida kuwa ta juya suka cigaba da firar su da Ummin Fadila, ganin tayi banza dashi yasa ya matso kusa da ita.

Bata juyo inda yake ba, gaban ta ya dawo ya zauna harda tankwashe ƙafa, Brr Farida ta balla mishi harara tace; "matsa ka bani waje", ya shafa gashin kanshi yace; "First Love yunwa fa nake ji".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login