Showing 78001 words to 81000 words out of 121992 words
Chapter 27 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
kan ta juya tayi tafiyar ta.
Isa cikin takaici ya bita da kallo, wato abinda ya faru da ita har shine take da damar jan aji ko?, ya yi murmushi mugunta yace; "zan riƙe ki ne a hannu na", shima ya juya ya fice.
A hankali komai ke tafiya haka ranaku ke kwaranyewa kamar ƙiftawar idanu, yau dai bikin Nusreen keda wata ɗaya yayin da bikin Atika yake da wata ɗaya babu kwana ɗaya.
Idan kaga Nusram a lokacin ta dawo yadda take babu wani abu dake damun ta, bata dai fita ko'ina saboda Baba ya hanata kai koda ace ma be hanata ba zata iya fita ba saboda tsegumin ƴan unguwa.
Bayan sunci abincin dare Nusram ta shafe Kubra da ruwan Addu'a sannan ta kwantar da ita, daga waje ta fara jiyo muryar Baba yana faman ƙwala mata kira.
Cikin hanzari ta ɗauki hijab ta saka sannan ta fito, yana tsaye a ƙofar ɗakin shi ya kalle ta sannan yace; "kira mini uwarki", sai da ta ɗan yi jim tukunna ta juya zuwa ɗakin nasu.
A zaune ta tarar da Ummi da alamu taji abinda Baba ya faɗa dan tana zuwa ta miƙe tace; "muje", Nusram ta juya kawai suka kuma ficewa.
Da sallama suka shiga ɗakin, Baba na zaune gefen shi kuma Isa ne sai Mama Jummai itama tana zaune a wajen.
Baba yace; "kin dai san kowa ya san meke faruwa a rayuwar ku ko, kuma tarbiya daidai gwargwado na baku amma da yake ance duk wanda ya hau motar kwaɗayi zai sauka a tashar wulaƙanci, gashi dai abinda kika gani ko ince kike kan gani".
"babu irin abinda bana yi muku a gidan nan babu rashin ci🙄 Babu rashin sha, amma kuka zama karuwan cikin gida kuma a gida na wannan ya ɗauka wannan ya ajiye na yanke shawara ta ƙarshe shine aurar daku, Alhaji Baballe yazo da Allah na haɗa shi ya amince zai aure ki ya rufa mana asiri, kowa ya sani babban mutum ne a Nigeria gabaki ɗaya, amma kika ɗebi ƙasa kika watsa mini a idanu abin ban haushi a daren da aka kaiki gidan mijin ki Nusram kwarto aka kamaki dashi, ya ɗirka miki ciki kuka je zubarwa yazo da matsala shine kuka kwana biyu a asibiti, ina faɗa miki wa'innan magan-ganun ne dan ki san cewa na san duk abinda kike aikatawa, Nusram Allah yayi miki baƙin jini ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yana son ki ba, ga Ameera nan ƙanwarki ce amma ta fiki yawan samari, na kuma ƙoƙarta domin sauke nauyin da Allah ya ɗora mini naku amma kika aikata yadda kike so saboda ban isaba, Nusram ba zan yi miki baki ba amma kije yadda kika baƙanta mini kema zaki gani".
Izuwa yanzu kukan Nusram ya fara tsananta, jin abinda Mahaifin nata yace yasa ta ɗagowa tana girgiza kai, cikin kuka tace; "Baba kayi haƙuri kada kayi mini baki wallahi bana da masaniya akan duk abinda kake magana akai".
Baba yace; "ayya Nusram rayuwace fa gaki ga tanan, ni dai Allah ya gani nayi iya ƙoƙarina a kanki na ganin na sauke haƙƙin dake kanku, sannan magana ta biyu shine ɗazu ɗan uwanki Isa yazo mini da wani batu, yace shi ya yadda a duk yadda kike zai aure ki dan haka na saka ranar bikin ku nan da wata biyu".
Ummi ta miƙe tace; "a matsayina na Mahaifiyar Nusram ban amince ba, maganar da kake yi duka naji kuma bazan amince ba, kana magana akan haƙƙin yara daka sauke kai bakaji kunyar kanka ba, wanne haƙƙi nasu ka sauke ci ko shayarwa ko kuwa tufatarwa? Wallahi matuƙar ina numfashi ba zan taɓa bari ƴata ta auri wanda beda asali ba".
Duka ɗakin tsit yayi, abin mamaki yau Ummi da kanta take maida martani akan abinda ake mata a gidan, Mama Jummai ta kalli Baba ganin ba zai yi magana ba yasa tace; "au Abdullahi kana ji dan za'a rufawa ƴarta asiri shine take cewa bata amince ba wai har karuwa tana da damar da zata zaɓi miji".
Ummi ta kalli Mama Jummai tace; "me zai hana kuwa tunda har ɗan shege ma ya sami damar zaɓar mata ai ina ganin ba laifi bane dan karuwa ta zaɓi nata, da kike wannan maganar naga ke har sheda kike dashi gashi nan a gabanki, kuma kike tare mishi faɗa to wallahi babu wanda ya isa ya kuma takani ko ƴata a gidan nan".
Mama Jummai tace; "haka kika ce? To shima ya fasa auren nata", Ummi tace; "wannan kuma matsalarku ce", ta kama hannun Nusram zasu fice Baba ya dakatar dasu.
"dawo ki zauna kun gama naku nima yanzu zanyi nawa", Ummi ta dawo kamar yadda ya umarta ta xauna.
"na riga na gama magana aure tsakanin Isa da Nusram babu fashi, tunda ita bata da wanda zai aure ta", Nusram ta girgiza kai tace; "Baba kayi haƙuri ni bana son Isa dan Allah ka nemo wani amma ba Isa ba".
Baba yace; "to shikenan tunda baki son Isa sai ki kawo wanda kike so na baki nan da sati biyu idan baki kawo wanda kike so ba zan aura miki Isa nan da sati uku".
Ummi tace; "ko bata kawo wanda take so ba, ba zan bari ta auri Isa ba", Baba yace; "to idan kuwa har sati biyu ya cika bata kawo wanda take so ki tattara kayanki ki tafi Dabai".
Cikin dakewa Ummi tace; "na yarda zan tafi amma ka sani ko bayan bana nan ka aurar da Nusram wa Isa ba zan yafe ba", Baba ya juya ya kalli Nusram yace; "to auren Mahaifiyar ki a hannun ki yake idan kin so kada ki kawo wanda kike so", ya miƙe ya fice.
Isa cikin takaici ya miƙe yace; "ni na tabbata baki da wanda kike so, nine kika tsana kuma ki sani aure na dake babu fashi, ƙarin gargaɗi shine matuƙar kika shigo hannu na to wallahi sai na illata ki, ki sani sai ka fanshe duk wani wulaƙancin da kika yi mini".
Ummi ta riƙo hannun Nusram tace; "ta Allah ba taka ba", daga haka taja hannun Nusram suka fice.
Mama Jummai tana huci tace; "wallahi sai na wulaƙanta Maimuna da zuri'ar ta, gobe dole mu koma wajen Malam", Isa ya ciza yatsa sannan ya fice.
Baba ya tsaya a waje yana mamakin yau yadda Maimuna ta iya maida mishi da martani kuma a yadda ya sani tsaf zata iya rabuwa dashi, gashi suɓutar baki yasa shi yin katoɓara.
Shi kuwa ya zaiyi da rayuwar shi🙆 Allah yasa dai Nusram ta sami miji kan lokacin, idan ba haka ba to be san ya zai yi ba dan be shirya rabuwa da matar shi wacce itace rufin asirin shi ba.
Ummi kuwa koda suka koma ɗaki bata nuna wata damuwa ba, sai ma sakayau da take jin ranta da zuciyar ta tayi ashe haka mutum yake ji idan har ya maida martani na wani abu da ake mishi lallai ƴanci yana da daɗi.
Ta kalli Nusram wacce ta zuba mata idanu cike da fargaba, tayi mata murmushi tace; "ki kwanta mana kada wani abu ya dame ki", Nusram jiki har rawa yake yi wajen cika umarnin Mahaifiyar ta.
Ummi ma sallah tayi sannan ta kwanta, babu ko ɗar a cikin zuciyar ta, tabbatar ko yanzu ta koma Dabai bata da wata matsala domin kuwa tana da gatanta.
Nusram tayi shiru dama gashi dare ya tsala sosai, tunani ta faɗa na neman mafitar abinda ya tinkaro ta, yanzu ita a ina zata sami mijin aure🙆.
Ba zata taɓa yadda ta zama sanadin rabuwar iyayen ta ba, kai bama ita ba ta san Nusreen da Kubra ba zasu yafe mata ba idan ta zama silar gutsirewar auren nasu musamman Kubra wacce take halin buƙatar iyayen nata, gata dai a kwance shekara shida tana kwance babu ƙafa sai dai zama.
Ta tashi ta zauna tare da zuba uban tagumi yanzu ina zata saka ranta?, bata da mataimaki sai Allah kullum da abinda ke tinkarota.
"ina da ɓuƙatar ganin Nusreen dole, muyi magana da ita", to wacce waya kike dashi? Wayar ta tun ranar da aka kaita gidan Alhaji Baballe bata kuma sanin inda take ba.
Zumbur naga ta miƙe, wata jaka dake rataye ta fara zazzagewa cikin sa'a kuwa ta gano wayar data ajiye tun ranar bikin nasu.
Kamar wacce ke tsoron taɓawa ta ɗauko, addu'arta ɗaya Allah yasa babu password, tana dannawa hoton shi ya bayyana.
Kyakkyawan saurayi, me zubin fulani, jersey a jikin shi blue da ratsin fari, gashin kanshi a kwance ya jingina da kujerar da yake zaune idanun shi ya ɗan ƙara ware su da alama wani abu ya gani ko kuma style ne na ɗaukar hoto bata sani ba, murmushi ke kwance saman fuskar shi har sai da ƙananan haƙoranshi farare tas suka bayyan.
Ta kai hannu daidai kumatunshi daya lotsa ta shafa, bata san ta shagala da kallon shi ba, itama dai murmushin take yi kawai, tama manta da wata matsala dake gaban ta.
*********⬇️⬇️⬇️********
*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.
Ya ƙara kallon agogon dake hannun shi sannan yayi tsaki, suna tsaye suna magana, ya kalli Sumayya sannan yace; "ba zaki wuce ki shiga ba", Sumayya ta zunɓuri baki kafin ta buɗe motar ta shiga.
Ya ƙara kai kallon shi gare su sannan ya taɓe fuska kamar yana gaban first love ɗin shi, ya shiga motar sannan ya danna musu horn.
Brr Farida ta kalli Fadila tayi murmushi tace; "kije idan ba haka ba wancan ɗan ujilar zai.iya tafiya ya barki, ku tabbatar kun zaɓo kayan daya dace ki kuma saki jiki ki zaɓi abinda kike so kinji, dalilin na san zaki fi sakewa yasa nace kuje tare da Baby dan na san sai kunfi jin daɗin siyayyar jeki ƴata Allah yayi muku albarka".
Fadila ta juya cike da kunya, Brr Farida ta bita da kallo tana murmushi a baya bata wani son auren amma yadda yarinyar ta natsu yasa taji auren ya kwanta mata a rai.
Koda ta shiga motar sai da Abdus-samad ya harare ta sannan yaja motar suka fice yayin da masu tsaron lafiya suka biyo bayan su.
Suna tafiya kowa ya natsu babu wanda yayi magana, Fadila tace; "wai yaushe zaka je wajen Malama ne?", yace; "kina son komawa gidane", ta ɗaga kai.
Suka kalli juna shida Sumayya sannan suka yi murmushi, yace; "yarinya ai kinzo kenan", Fadila ta ɓata fuska, su kuwa suka sami damar tsokanarta har suka ƙarasa Mall ɗin.
Yana gaba suna binshi a baya har ciki, kowacce taja kwando yace; "Sumayya an sami abinda ake so ko?", tace; "Yaya Abdul ai dai ba'a kuɗin ka bane".
"duk Daddy ne ya ja mini da ya barni na fara aiki na ai da babu yarinyar da zata raina ni", suka tafi suna mishi dariya.
Kiran wayar shi yasa ya ɗan matsa baya domin amsa kiran, "Aunty na barka da warhaka", ta ɗan ja numfashi kan tace; "idan kace mini Aunty sai naji wani iri".
Yayi murmushi yace; "dole na baki girmanki Saleema", ta ɗanyi jim kan tace; "kai baka iya kiran mutum ba sai dai a kira ka ko?", ya ɗan shafa gashin kanshi yace; "afuwan zan dage na koya yanzu lafiya kuwa".
"ina zaune naji ba zan iya haƙuri ba sai na kira ka, zuciya ta ke bani kamar wani abu ya same ka shine na kira naji ko lafiya?", Abdul yabi inda yake da kallo yace; "lafiya ta lau yanzu ma ina Kareem Shopping Mall na kawo Sumayya da Fadila siyayya".
Tayi murmushi tace; "hmm da ace ban gaji ba da nazo sai na taya ka fira, sannan ka faɗa musu kada su sake su wahalar mini da kai, ka kula da kanka".
"an gama ranki shi daɗe, na kuma gode da kulawar ki, kema ki kula", daga haka ya kashe wayar.
Idanun shi ya sauka a kan ribbom ɗin da suke jere a saman canter, yabi su ɗaya bayan ɗaya da kallo har yazo kan wani ya tsayar da idanun shi a kai, ya jima yana kallon shi sak kalar na Nusram wanda ya amsa a wajen ta kalar golden.
Hairat ta kalli Khausar tace; "kinga me na gani kuwa?", Khausar tace; "na gani mana", Hairat ta runtse idanu tace; "damn Sexy, gaskiya gayen ya haɗu dole na shawo kanshi" ta faɗa tana ƙoƙarin zuwa gare shi.
Khausar tayi saurin janyo ta baya tace; "wannan ai yafi ƙarfin ki Baby sai dai ni, amma abinda yake bani mamaki yana kama da Daddy na", Hiarat ta ƙaro zaro idanu tace; "tabbas hakane".
Khausar taja hannun Hairat tace; "zo muje dole na shawo kan wannan gayen", suna isa kusa dashi Khausar ta kai hannu ta kwaso Ribboms guda biyu ta ƙaraso gaban shi hannunta janye dana Hairat.
"amm pls dan Allah duba mana wanne kala yafi kyau", ya juyo ya kalle su, nan fa ƙafar Khausar ta fara rawa ji tayi kamar shi kaɗai ne a cikin Mall ɗin gaba ɗaya ya cika wajen.
Abdul ya kalle su sama da ƙasa, Khausar riga da wando ne a jikin ta daga ƙugunta belt ta saka ta ɗaure shi, sai Hairat data saka pencil skirt baki da kuma riga fara, babu ko mayafi a jikin su.
"kina da magana ne?", ya faɗa yana ƙara buɗe idanun shi a kansu, Khausar tace; "am dama......dama........dam......dama.......nac......nace......ko zaka duba.........ko zaka duba mana wanne yafi kyau".
Ya ɗan taɓe baki sannan yace; "banda sani akan kayan mata", da sauri Khausar taja hannun Hairat tace; "shikenan muje na gode", sai lokacin Hairat ta sami damar haɗiye miyau ɗin dake bakin ta.
Har suna harɗewa wajen fita, basu ɗauki komai ba dan haka basu tsaya wajen cashier ba.
Abdul ya bisu da harara, kamar ance ya kalli ƙasa yaga ƴar ƙaramar purse ɗin Khausar a ƙasa wato tsabar ruɗewa harta yarda abinda ke hannun ta.
Yana tsugunawa ya ɗauka Fadila da Sumayya suka ƙaraso, dan haka hanyar waje kawai ya nufa, babu bata lokaci aka lissafa kayan ya miƙa Atm ɗin shi aka cira sannan suka fice inda kuma za'a saka a kai musu kayan su mota.
Koda suka fito ya bi wajen da kallo, can ya hango su, da alamu jakar suke nema dan buɗe motar su, ya kalli Sumayya yace; "amshi makullin nan, ki buɗe ku shiga ku zauna ina zuwa" ya ƙarasa yana juyawa ya tafi.
Hajiya Salma ta kalli Alhaji Sa'eed suka yi murmushi, wato tun zuwan Abdul suke wajen kuma duk suna kallon shigar shi da fitosar shi.
"yanzu ne lokacin daya kamata mu aiwatar da nufin mu", faɗar Alhaji Sa'eed kenan yayin da yake danna wayar shi, motar yaran shi dake gaba.
Yana ɗagawa yace; "Scorpion ka aikashi lahira kawai", Scorpion yace; "an gama ranka shi daɗe yanzu lahira zata yi baƙo", ya ajiye wayar sannan ya zaro pistol daka aljihun motar shi ya saita ƙirjin Abdul wande ke nufar motar su Khausar ɗin dan bata jakar ta, kasancewar motar su Khausar ɗin tana gaban ta scorpion ɗin, babu ɓata lokaci ya harbi Abdus-samad ɗin.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
*brr zahra Allah ya ji kanshi yasa Aljanna ce makoma ubangiji ya yafe mishi kurakuren shi*.
Godiya ga ƙungiya ta guda ɗaya tamkar da dubu ko ince miliyan, *GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION*, musamman jajurtattun cikin ta *UMAR ƊALHAT da kuma *SHAMSIYYA IBRAHEEM ƊAN MUSA*.
*JINJINA GARE KU*
*Auntyna Amina Alhassan (Oum deedat)*
*Auntyna Ummee Yusuf(oum yusuf)*
*Sumayya Abdullahi Babayo(Sumiee B)*.
*Faridaty(Ƙafar yawo)*
*Harira Aliyu(ƴar fillo)*
*Ummeeteey Yusuf*
*Fatima Batula(Bloody)*
*Maryam Shahada*
*Maryam ankudi*
*Shatu*
Da duk sauran da ban ambata ba, Allah ya ƙara haɗa kanmu ya tsare mu daga sharrin mahassada.
📖📖43-44📖📖
Cikin tashin hankali da kiɗima Sumayya da Fadila