Showing 3001 words to 6000 words out of 121992 words

Chapter 2 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt

28 Dec 2024

16079

mana bauta", Nusram ta saukar da kanta ƙasa kawai tana me jin zafin magan-ganun na Mama Jummai.


Nan ta zube su ta juya tana mita; "to dama meye amfanin ku a gidan yara tun nonowa suna kirji har sun faɗi amma kun ƙi ku fitar da mazaje,ai wallahi dani daku ne a gidan ga uwar can tsohuwar munafika kullum tana ɗaki a kile kamar kayan wanki Musa a baki Fir'auna a zuci", Nusram ta ƙara kallon hanyar bayin inda ta tabbatar da cewa Nusreen na jiyowa fatan ta dai ace bata jiyo duka ba,sai dai ta makaro domin kuwa duka magan-ganun Mama Jumman a kunnen ta suke kuma Allah-Allah take ta gama ta fito domin bata amsa.


Tana fitowa Nusram tayi sauri ta miƙe, idanun ta cike da hawaye tace; "Pls Rim kada kice mata komai dan Allah", Nusreen ta galla ma ƙofar ɗakin Mama Jumman harara sannan tayi ƙwafa ta wuce, Nusram kuwa ganin hakan yasa tayi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da wanke-wanken ta, Kan wani lokaci ta gama sannan ta kwashe nasu ta kai ɗaki ta ɗauki na Mama Jumman ta kai mata itama ƙofar ɗaki sannan ta juye nata ruwan ta shiga wanka.


Bata jima ba ta fito inda ta shiga ɗaki ta tarar da Ummi na zaune tanawa Kubra tsifa yayin da Nusreen ke faman sheƙa kwalliyya, Nusram ta kalle ta tayi murmushi kawai sannan itama ta hau shiryawa.


Atamfa ta saka me kalar pink da ash sai ratsin fari da baƙi kalar ta jikin Nusreen ɗin sai dai banbancin shine ɗinkin domin kuwa Nusreen tata fitted gown ne ita kuma Nusram tata me buɗewa ce daga ƙasa, bata tsaya kwalliyya ba kamar ƴar uwar ta mai da hoda kawai ta shafa sai kwalli data zizara ta ɗauki hijab ta saka kalar ash wanda ya kasance kalar uniform ɗin makarantar kenan ta tada sallah, haka itama Nusreen ɗin sai da ta gama tata ƙyale-ƙyalen sannan tayi sallah suka fice cikin sauri suna yiwa Ummi sallama akan sun tafi islamiyyar.


Ummi tayi musu addu'a da fatan nasara sannan ta ɗaga Kubra domin ta gama yi mata tsifar saura wanke kan.


Suna fitowa suka iske yaran Mama Jumman Atika da Ameera sun dawo daga tallan shinkafa da waken data ɗora musu, Nusreen ta kalle su tayi tsaki tace; "mutum bashi da aiki sai yawon tallace-tallace wata rana garin jarabar son kuɗi a kwasowa mutum abinda zai jefa shi a masifa", Mama Jumman ta fara balbalin masifa ita dai Nusram taja hannun ta kawai suka fice.


Kan hanya ma sai faman masifa take ita dai Nusram bata kula ta ba har suka iso bakin makarantar, ana ta taron latti amma da yake Nusreen ɗin akwai rigima haka ta wuce cike da taƙama tana taku ɗai-ɗai.


Nusram kuwa da sauran ɗaliban suka tsaya suna kallon ta, Malam Abbas shima ya bita da idanu da sauran malaman dake bakin wajen, ganin da gaske take yasa shi daka mata tsawa yace; "Nusreen Abdullahi Dabai ki dawo nan", ta juyo cike da ƙasaita tace; "sunan haka yake malamin addini babu kuskure", duka wa'inda ke wajen sai da suka kwashe da dariya wanda hakan ya kuma tunzura Malam Abbas ɗin yayo kanta da bulala.


Tsayawa tayi ƙyam tana kallon shi harya kawo kusa da ita kafin yaja dan kan shi ya tsaya, tana ganin ya tsaya ta saki murmushin ƙasaita tace; "ya ka fasa ai da ka zuba mini a jiki kawai", ta ƙarasa tana mishi wani kallo.


Duk abinda yake faruwa akan idanun shi kuma yana kallon meke faruwa ganin idan beje ba za'a yi abinda be kamata ba yasa ya taho wajen da sauri.


"meke faruwa ne?", ya tambaya, Malam Abbas yace; "latti tayi amma tazo ta wuce kamar zata shiga ɗakin su", Malam Saleem yayi murmushi sannan yace; "Malam Abbas ai kun riga da kun san halin wannan domin samun maslaha ka ƙyaleta kawai ta wuce", haka dole yasa Malam Abbas ya barta ta wuce ya koma kan sauran yana jibgar su, koda yazo kan Nusram sai da ya sauke haushin Nusreen akan ta tsaf sannan ya ƙyaleta gaba ɗaya ya farfasa mata hannu, haka ta tafi aji tana kuka.




🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸


Ta ɗagawa ƴar matashiyar data kawo mata Coffee ɗin hannu tana me cigaba da amsa wayar ta hankali kwance.


"Baby ban san wannan ƙorafe-ƙorafe,dole fa ka dawo gida gobe na ƙara jadadda maka, shiru tayi alamun magana yake har zuwa lokaci me tsayi kafin tayi murmushi tace; "yauwa ko kaifa", ra ƙara sakin murmushi tana fadin; "Mummy loves you more, bye", daga haka ta ƙatse wayar.


Cikin isa da ƙasaita ta hau kiran; "Aziza! Aziza!!", kan tayi kira na uku ta iso gare ta, cikin isa da bada umarni tace; "kije ki faɗawa sauran ma'aikatan gidan kan cewa Baby yana kan hanya gobe sannan ki tura Salma ta buɗe ɓangaren shi gani nan zuwa na gyara mishi", jiki yana rawa Aziza ta amsa da"to", haka ta tafi cikin murna da farin ciki domin kuwa sun san cewa hanyar ƙofar samun su ta kusa dan akwaishi da kyauta sannan ko ita kanta uwargidan tasu bataso yin abu ba indai kayi kamun ƙafa dashi tofa aikin ya gama cika,koda ta sanar da ma'aikatan gidan nan suka hau murna suna sam barka da dawowar tashi.


Babu jimawa ta miƙe ƙafafunta sanye da slippers ta fice daga ɗakin nata zuwa part ɗin shi, a falon ƙasa ta tarar dasu kamar koda yaushe, Surayya ta danna waya, Sumayya kuma littafi ke hannun ta da alamu karatu take, Sameer kuma yana operating system ne yayin da Tameer ke kwance idanun shi a lumshe kamar me barci, duka suka yi mata sannu da fitowa ta ɗaga musu hannu sannan ta kalli Surayya tace; "kije kan drower a ɗaki na zaki ga box saƙon sarƙar ki ne da kika ce".


Cikin farinciki ta hau godiya, kallonta ta mayar kan Tameer kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta kalli Sumayya tace; "ina Auta na?", tayi murmushi tace; "Mummy Auta yayi barci", ta nufi hanyar fita kan tace; "kije ki tashe shi yamma tayi", ta amsa da to sannan tace; "Mummy ina zaki je?", sai da ta juyo ta kalle ta sannan tace; "Baby zai dawo gobe zanje na gyara mishi part ɗin shi ne".


Sumayya tayi tsallen murna sannan tace; "Mummy nazo na raka ki", tayi gaba tana faɗin; "ki fara tashin Fahad daga barci tukunna", Sumayya cikin murna tayi hanyar ɗaki domin tashin Fahad ɗin.


Tameer ya buɗe idanu sannan yaja tsaki yana faɗin; "aikin banza kawai", Sameer ya kalle shi ya girgiza kai kan ya cigaba da abinda yake yi.


Babu jimawa Sumayya ta tashi Fahad, sai da tasa Salma tayi mishi wanka sannan ta fito cikin gaggawa, tana zuwa falon Tameer yace; "banza mara tausayin kanta", ko kallon shi bata yi ba ta wuce.


A buɗe ta tarar da part ɗin da kuma alamu Mummy ta riga da ta fara aikin ta, aikuwa kamar yadda ta zata tana shiga ta tarar falon ƙyal-ƙyal ko'ina tsaf-tsaf, tayi hanyar bedroom ɗin, Mummy na tsaye tana gyara kan madubi ta ɗago ta kalle ta, Sumayya tayi murmushi tace; "Mummy na gama", ta ɗaga mata kai tana me cigaba da abinda take yi.

Sumayya na tsaye tana kallo har ta gama gyaran bedroom ɗin ta canza bedsheet saman gadon sannan ta shiga bathroom ta wanke tass, Sumayya tayi murmushi tana me jinjina soyayyar dake tsakanin ɗa da uwar, ta san cewa idan zata kwana tana tambayar ta akan ta bari ta taya ta ba zata bari ba shiyasa taja baki tayi gum.


Tana gama wankewa ta ɗauko turare ta zuba a burner ta kunna sannan ta hau fesa Room freshner sai da ta tabbatar da ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan ta fito daga bedroom ɗin Sumayya tana bin bayan ta.


Ɗakin dake kallon wannan ta shiga, shima bedroom ne sai dai a maimakon gado sai aka saka ƙatuwar katifa babu wasu tarkace a nan, wardrobe ne sai dressing mirror shikenan, sai dai jikin bangon dake ɗauke da manya-manyan hotunan ƴan ƙwallo.


Shima ta gyara shi tsaf ta saka mishi turare ta wanke bayin sannan ta rufo ɗakin ta fito Sumayya ma na bayan ta, haka ta rufe part ɗin ta fice.


Suna isowa parking space ta ɗaga kai ta kalli motocin dake wajen, "Bala! Bala!!", cikin sauri ya ƙaraso, ta dube shi tace; "banga ka gyara motocin da za'a ɗauko Baby bane".


Ya shafa kanshi yace; "Hajiya walllahi Tameer ne yace na wanke tashi na bar wa'inn..", kan ya ƙarasa ta dakatar dashi ta hanyar cewa; "dakata mini, Bala ban san cewa Tameer ka fara yiwa aiki ba sai yau", jiki na rawa ya fara bata haƙuri, bata kalle shi ba tace; "kasan bana iya haƙuri da abinda ya shafi Baby a gidan nan amma kake neman ka maidani abokiyar wasan ka".


"Hajiya dan Allah kiyi haƙuri", ta girgiza kai tace; "magana ta ƙare kaje wajen Aziza ta baka dubu hamsin ka kama gaban ka bana buƙatar ƙara ganin ka", jiki na rawa ya tsuguna yana bata haƙuri haka tayi wucewar ta.


Nan sauran ƴan aikin suka fara bashi haƙuri shi kuma yana kuka, yaje ya tattara kayan shi sannan yaje wajen Aziza ya amshi kuɗin.


Aziza tace; "ka bari gobe idan ƙaramin oga ya dawo sai ka dawo ka roƙe shi", ya yarda da shawarar ta sannan yayi godiya ya tafi.


"waye nake magana yake canza mini ita a gidan nan", ta tambaya bayan ta shigo ta sami Tameer da Surayya a zaune, ganin yadda fuskar ta ke ɗaure yasa duka suka sauke kan su ƙasa.


"ina tambayar ku, wane ishashshe ne wannan?", ta faɗa cikin daka tsawa, a sanyaye duka suka hau bata haƙuri, ta ɗaga hannu ta nuna su tace; "har yanzu dai nice Brr Farida suna na be canza ba, kuma nima ban canza ba", tana faɗin haka ta kalli Tameer tace; "kaje ka cewa Ali ya mayi aikin Bala a fito da motocin da za'a je ɗauko Baby a wanke su", tana faɗin haka ta wuce sama ta barsu cike da baƙin ciki.


Tameer na ganin ta wuce ya buga tsaki cikin ƙuluwa yace; "wallahi idan na cigaba da zama a gidan nan wata rana mutuwa zan yi", Surayya tace; "to Yaya ka fito da mata mana kayi aure", yace; "ai dole ma idan ba haka ba baƙin ciki sai ya kashe ni", haka dole ya tafi inda ta aike shi cike da jin haushin wannan so da Mummy ke yiwa ƙanin shi.


Haka ya basu umarni daga nan ya wuce part ɗin su dan haushin halin Mummy yake ji, gashi basu da yadda zata yi, ita komai Baby.


🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸


Koda aka taso su daga makarantar a hanya Nusram keta bata baki akan abinda take yi, "haba Rim kinga fa rashin jin magana da kuma yiwa babba rashin kunya baya haifar da komai face ci baya, dan Allah ki dena".


Nusreen tace; "Allah ko! Yau kuma wa'azi kika koma, to bari kiji ni ba zan iya rayuwa kalar taki ba ina kallo ana cuta ta nayi shiru ko kuma na koma ina kuka wannan ba zai taɓa yiwuwa ba".


Nusram tace; "ai na sani amma dan Allah ki rage tsiwar nan ko zamu sami wanda zai kalle mu, muma mu wuce gori", Nusreen ta kwashe da dariya tace; "kice ga inda maganar ki ta dosa ta ki sani wannan kuma daga Allah ne ba daga ni bane kuma ki faɗa mini shekarar mu nawa ne just 24yrs da ƙuruciyar mu fa".


Nusram tace; "Nusreen ki duba fa kiga ƙannen mu nawa aka yiwa aure, uku fa sannan ki duba ƴaƴan Auntyn Tudu, itama ta aurar da yara biyu Safeena da Halima kuma duka mun girme su, dan Allah ki maida hankali".


Nusreen ta kalli ƴar uwar ta na wani lokaci sannan tace; "Ram ba zan taɓa yin aure na barki ba kema kin sani kuma alƙwari ne na ɗauka kan cewa sai kin sami naki mijin sannan nima zan tsayar beside ma duk wa'inda ke zuwa waje na babu wanda yayi mini".


"Rim ki manta da ni kiyi auren ki wataƙila tawa ƙaddarar kenan, bazan taɓa samin miji ba ke kuwa fa ko jiya fa wani yazo kan yana son ki kika ƙi fita".


Nusreen ta taɓe baki tace; "ai sai kiyi tayi wallahi ba zan yi aure na barki a wajen wannan matar mara tausayi ba ta dinga muzguna miki a hakan ma wai duk da tana tsoro na ya aka cika ina ga na tafi na barki, kuma maganar wai ke taki ƙaddarar kenan ashe kema zaki iya yanke ƙauna daga rahamar Ubangiji?, to bari kiji Allah yana sane dake kuma na san addu'ar da mahaifiyar mu take mana ba zata taɓa faɗuwa ƙasa banz.....", bata ƙarasa ba saboda ruwa da wata mota ta shiga ya fallatso mata duk ya ɓata mata jiki.


Nusram na ganin yadda ta haɗe rai yasa tayi saurin riƙo ta tace; "dan Allah Rim mu tafi kada kice komai", Nusreen ta ɓalla mata harara tana kallon motar da ta rage gudu a hankali kuma motar ta fara dawowa baya.


Nusreen na ganin motar tayi parking ta fincike hannun ta daga na ƴar uwar ta tayi kan motar cikin sauri kuma ɗauke da fushi.


Tana zuwa yana fitowa ta galla mishi harara kafin tace; "kai ɗin waye da har zaka zubawa mutum ruwa kuma ka cigaba da tafiya, kodan kana taƙama da cewa mahaifin ka nada kuɗi shikenan dama haka halin ku yake kallon talaka kuke a banza a wofi to wallahi ni ba irin sauran bace banda haƙuri mutum nayi mini zan yi mishi, mutum ya hayo titi kamar na ubanshi to kaji ka sani ba ɗauka zanyi", ya tsaya yana kallon ta cike da mamaki.


Ta ɗaga hannu ta nuna kanta tace; "kalle ni da kyau na wuce raini kuma idan taƙamar ka kuɗi ni kuma ina da Allah domin shiya tsaya mini......", kafin ta ƙarasa abinda zata faɗa aka buɗe ɗayar ƙofar aka fito.


Wata dattijuwar mata ce fara sosai, tana ɗingisa ƙafa ta ƙaraso gaban ta, tayi murmushi sannan tace; "Ƴan mata kiyi haƙuri bada sani bane, sauri yake ya kaini airport domin zan tafi syria inda za'a mini aikin ƙafa da take damuna".


Nusreen ta kalle shi, shima dai itan yake kallo yana murmushi ta galla mishi harara tace; "Allah ya taimake ka da wallahi saina ɗauke ka da mari", tana gama faɗin haka ta juya ta bar wajen.


Nusram ta saukar da kai ƙasa tace; "dan Allah kuyi haƙuri kuna sauri mun tsayar daku", ta maida kallon ta kan shi wanda shima ita yake kallo cike da mamakin kamar ta da waccen har muryar su sai dai ita wannan muryar ta sanyi-sanyi take; "kayi haƙuri ba haka take ba ranta ne ya ɓaci, Mama Allah ya baki lafiya yasa ayi aikin a sa'a", tana gama faɗin haka ta juya tabi bayan ƴar uwar ta.


Duka suka bita da kallo wanda kowa da irin nashi ma'anar, shi yana mata kallon girmamawa yayin da mahaifiyar shi ke mata kallon sha'awa da birgewa tana fatan inama ƴar ta ce.


Ta maida kallon ta kan ɗan nata sannan tace; "Shureim muje ko", yayi ajiyar zuciya sannan ya shiga motar ya jata suka tafi.


Nusram duk iya saurin data yi bata tarar da ƴar uwar tata ba har ta isa gida, tun kan ta shiga gidan ta jiyo muryar ta tana faɗin; "wallahi mutum yayi mini na mishi dukan mutuwa".


Tana ƙarasa shiga, Mama Jummai na fitowa tana faɗin; "to shegiya fitsararriya sai kizo ki dake tan a gaba na, anƙi aure anzo an ishi ƴaƴan masu gida", Nusreen tace; "to mu ai sai a sheganta mu, yadda yake gidan uban su haka yake gidan uban mu, maganar aure kuma naga wata ma tsabar daɗewa sai da ta shekara talatin da biyar sannan tayi auren fari, aka kuma tafi da me daka gidan mijin gwara mu ma muna da kyan jiki, mtsew abu kamar guzuma", saukar mari taji wanda ya hanata ƙarasawa ta juyo ta kalli Ummi, Ummi kuwa cikin ɓacin rai tace; "wuce ɗaki", babu musu ta wuce tana faɗin; "wallahi sai na dake ta sai dai ta dena fita".


Mama jummai kuwa sanin da ita Nusreen take yasa tana huci tana faɗin; "bari uban naki ya dawo sai na tambaye shi idan shi ya zauna ya kitsa miki, shegiyar ƴar tasha".


Nusram ta fara zubar da hawaye tana me baƙin ciki da halin da gidan nasu yake, Allah yayi ta da rauni shiyasa hayaniya koya take bata iya jure ta.


Ummi ta kallo ta cikin tausayawa kasancewar ta mahaifiya gare su ta san halin su ya bambamta duk da kamar da suke, tace; "Nusram jeki cire hijab ɗin mana kizo ki share gidan", ta amsa da to sannan ta wuce.


Tana shiga ɗakin ta tarar da Nusreen har ta fara gyara ɗakin, ta wuce ta ta ajiye hijab ɗin sannan ta fito ta ɗauki tsintsiya ta share gidan tas.


Ummi kuwa kan lokacin ta gama girki dan haka ta tattara kayan da Ummin tayi amfani dashi ta wanke sannan ta wuce tayi alwala ta shiga ɗakin nasu domin yin sallah.


Koda suka idar nan suka zauna kowa yana nashi karatun har aka yi kiran isha'i sannan suka tashi suka yi sallar.


Sun fara cin abinci kenan suka jiyo Mama Jummai na kasawa yaranta tallan kunun aya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login