Showing 51001 words to 54000 words out of 121992 words
Chapter 18 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*
📖📖29-30📖📖
Fadila tana gyara ɗaurin ɗan kwalin ta Abdul ya turo ƙofar ya shigo, koda ta kalle shi sai da numfashin ta ya kusa ɗaukewa ganin irin kyawun da yayi.
Sumayya dake ƙoƙarin ɗaure gashin ta, ta juyo tace; "wow Ya Abdul ka haɗu kamar yau ne ɗaurin auren ka", ya gyara links ɗin shi sannan yace; "ku fito fa, dan bana so First love tayi zaman jiran mu".
Fadila ta ɗaga kai alamun to, tana ƙara kallon ɗan uwan nata, cikin shigar manyan kaya wato shadda kalar sararin samaniya wacce taji aikin hannu.
Kanshi babu hula sai dai kwantacciyar sumar shi wacce ke ƙara mishi kyau, ya juya cikin ƙasaita ya fice daga ɗakin.
Fadila ta saki wata irin ajiyar zuciya har sai da Sumayya ta kalle ta, cikin sauri Fadilar ta basar tana me zama gefen gadon Sumayya.
Yana tsaye ya juya baya yana amsa waya suka fito dukan su, ganin waya yake yi yasa duka suka tsaya Surayya ita ma ta fito sanye da riga da skirt na atamfa.
Abdul tace; " ka bari later kawai yanzu zamu je ɗauko Mummy ne a airport", yana faɗar haka ya katse wayar.
Ya juyo ya kalle su, Surayya ita kanta sai da taga kyawun Yayan nata don haka cikin sauri ta kauda kai, ita fa abinda ke hanata tafiya tare dashi kenan sai tayi wanka na ƙasaita yana yin nashi sai ya shafe nata.
Suna gaba yana baya haka suka fito harabar gidan, anan suka tarar da Tameer da Sameer, kowannen su cikin shirin ɗauko iyayen nasu.
Abdul yayi murmushi yace; "to muje", yana ƙoƙarin buɗe mota, Tameer yace; "amma dai ya kamata ace mun hau motar da Daddy ya siya mana ko?".
Sai da Abdul yayi ɗan jimm sannan yace; "to shikenan", Tameer yace; "idan ma baka son jar ne, ga makullin tawa", Abdul ya kalli yayan nashi da mamaki sai kuma ya kauda kai cikin sauri yace; "nop bari naje a tawa kawai".
Tameer ɗin ya taɓe baki yana me nufar tashi motar, shima Abdul ya nufi tashi, Abdul da Sumayya sai Adnan a baya, sai Sameer da Fadila dan tace ba zata shiga jar mota ba kamar ta ƴan shan jini, Surayya kuwa ta Tameer ta shiga domin tafiyar su zata fi dai-dai.
Haka suka fice daga gidan cikin farin ciki domin zuwa ɗauko iyayen nasu babu ma kamar Abdus-samad wanda yake jin kamar ya shekara ne bega mahaifiyar tashi ba.
********* **********
Nusreen ta kalli Nusram wacce ta zuba ubam tagumi, itama cikin damuwa ta ajiye zanin gadon dake hannun ta, ta zubawa ƴar uwar tata idanu.
Ummi da Auntyn Tudu suka shigo tare wanda hakan shiya dawo da Nusram daga duniyar tunanin data tafi, cikin sauri ita da Nusreen suka amshi kayan dake hannun su.
Sai da suka zauna Aunty tace; "Wash wallahi na gaji, Allah yasa ma wancan yaron ya amso ragowar", Ummi tace; "tunda har kin faɗa mishi zai amso ne kada ki damu".
Kaya ne na kitchen sai kuma sauran kayan da zasu yi amfani dashi na bikin, nan aka baje ana gani, ita dai Nusram nata idanu ne babu abinda take tunani sai auren da zata yi.
Nusreen ta juyo ta kalli ƴar uwar tata sannan tace; "Ram koba haka ba?", Nusram ba tare da ta san me Nusreen ɗin ke magana akai ba ta ɗaga mata kai kawai tana miƙewa ta bar wajen.
Duka suka bita da kallo, Aunty tace; "Allah sarki ni dama na san Nusram ba zata taɓa farin ciki da wannan auren ba kawai dai zata yi shi ne".
Ummi tace; "nima na lura da bata wani farin ciki da bikin amma ko meye addu'a zamu taya ta dashi sai dai har yanzu ina kan baka ta matuƙar tace bata son shi to kuwa sai dai a fasa auren".
Nusram kuwa kan katifar su ta faɗa hawaye na zubo mata, ita ta san ba zata ce ga wani zaɓi da take dashi na wanda zata aura ba amma tabbas bata son auren me yara irin wa'innan yaƴa ashirin da ɗaya!".
Haka ta dinga zubar da hawaye cikin baƙin ciki da zafin abinda ke faruwa a kanta, cikin ƙarfin hali ta miƙe a zuciyar ta tana maimaita addu'ar da mutum keyi idan musiba ta same shi tana kuma me neman zaɓin Allah.
Haka ranar Auntyn wuni tayi a gidan suna ta shirye-shirye domin kuwa gobe ake saka ran dawowar mahaifiyar Shureim ɗin.
Kuma tabbas Baba ba zai ɗaga auren ba dan yace tana dawowa da sati biyu ko sati uku, Shureim kam dole ya amsa a hakan har yaje ya sanar da dangin mahaifin shi.
Su kansu sai da suka ce; "wannan wane kalar aure ne kamar an gaji dasu ai a bari mu muyi bincike idan su ba zasu yi ba ko", shi dai Shureim beda abin cewa nan suka gama maganganun su kafin wan baban nashi ya saka ƴaƴan shi guda biyu akan su zo suyi bincike.
Alhamdulillahi koda suka zo suka yi bincike basu sami wata tangarɗa ba domin kuwa an basu amsoshi me kyau sosai, dan an sheda musu ma ko ƙawa basu da ita mahaifiyar su ma basu taɓa ganin tana yawon gidan maƙwabta ba.
Sun komawa da mahaifin su da sakamako me kyau inda ya kira Shureim ya sheda mishi, aikuwa Shureim yayi murna sosai da sosai wannan shine abinda ya kira Abdus-samad ɗin yana faɗa mishi.
Sai dare sannan Yaya Sulaiman yazo ɗaukar Aunty, duka suka fito domin rakata Auntyn tace; yanzu sai ku fara zuwa gyaran jiki ko?", Nusreen ta amsa da to shikenan.
Yaya Sulaiman yace; "ke kuma meye ya ramar dake haka?, ko duk fargabar auren ne?", Nusram tayi yaƙe kawai.
Auntyn tace; "to ni dai kunji abinda na faɗa muku dan haka zanyi zaman jiran ku idan har kun dawo daga makaranta sai ku dinga wucewa can.
Yaya Sulaiman ya kalli Nusram bayan sun matsa gefe yace; "ƴar ƙanwata faɗa mini matsalarki mana", Nusram ta sauke ajiyar zuciya sannan tace; "babu komai, yauwa kayi bincike akan Shureim ɗin".
Yayi murmushi yace; "bashi da wata matsala, hakama mahaifiyar shi da mahaifin shi kan ya rasu, gidan su gidan mutunci ne, yanzu abinda ya rage shine wannan alhajin naki Baballe".
Nusram tayi saurin girgiza kai tace; "a'a kada kayi Yaya domin koda kayi ko baka yi aurena dashi babu fashi", Yaya Sulaiman cikin tsokana yace; "duk soyayyar ce haka?", Nusram ta saukar da kai ƙasa.
Haka suka yi sallama cike da ƙaunar juna kamar ƴan uwa na jini sosai, suna ƙoƙarin shiga Isa ya ƙaraso, Nusram taja hannun Nusreen dan su shige ya tare hanyar.
Ta gefe ta koma nan ma ya sake tarewa, ita dai Nusreen kallon ikon Allah take yi, Nusram ganin hakan yasa tace; "Rim shiga ciki gani nan zuwa", Nusreen ta taɓe baki sannan ta wuce.
Isa ya matso kusa da Nusram ɗin ta ja baya, ya kuma matsawa ta kuma jan baya, har sai da ta kai jikin bango, hannu ya kai kan saman fuskar ta, Nusram ta runtse idanu tana faɗin; wai Isa meye haka ne an faɗa maka ni ƴar iskace ko me?".
Yace; "ok nine ɗan iskan kenan? To ki ajiye a cikin ranki kema sai na maida ke ƴar iskar, sannan ki sani wallahi matuƙar baki janye auren da kike so kiyi ba nima ba zan janye ba nayi miki alƙawarin sai kinzo kina roƙo na akan na aure ki", yana gama faɗar haka ya fice ya barta a wajen.
Nusram taja dogon numfashi sannan ta shige cikin gida, Mama Jummai ta kalle ta tayi tsaki tace; "ayi dai mu gani".
Ita dai Nusram bata wani kula ta ba, koda ta shiga ɗaki ta samu an kawar da kayan nasu hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba domin bata ƙaunar ganin kayan daya danganci bikin kwata-kwata.
Da yamma zasu tafi makaranta Nusreen tace; "baki faɗa mini meye tsakanin ki da Isa ba", Nusram ta kwashe komai ta faɗawa Nusreen ɗin nan fa Nusreen ta hau masifa.
Ita dai Nusram ɗin sai toshe kunne tayi dan yanzu hayaniya damunta yake yi, haka har suka isa makarantar Nusreen bata bar mita ba.
Ƙarshe dai Nusram ɗin ta bar mata bencin, koda aka tashi haka ta dasa daga inda ta tsaya faɗi take; "wallahi ke kika bashi dama idan banda haka taya zai iya buɗe baki ya faɗa miki cewa wai yana son ki ko an gaya mishi bamu san asalin shi bane?, yaushe zai haɗa ɗan sunnah da ɗan zina".
Nusram cikin takaici tace; "wai ke Nusreen kin manta a kan titi muke ne", Nusreen ta dalla mata harara tace; "ina ruwa na ko filin arfa muke", jin hakan yasa Nusram ɗin ƙyale ta.
********** *************
Cikin farin ciki take saukowa daga matattakalar jirgin babu abinda idanun ta ke son gani kamar ɗan nata.
Dr Abubakar ya riƙo hannun ta ganin tana ƙoƙarin barin shi, cikin kunnen ta yace; "haba mana rabin raina ya zaki tafi ki barni", Brr Farida ta saki murmushi.
Abdul dake tsaye a can wajen da ake jiran ƴan tafiyar ya saki murmushi ganin yadda iyayen nashi suka yi, sai da ya ɗauke su hoto.
Dole Brr Farida ta jira mijin nata suka jero tare, Abdul ya saki hannun Adnan ɗin ya nufi wajen Mummyn tashi, ta buɗe hannayen ta ya shige ciki suka rungume juna cike da ƙauna da so.
Daddy kuwa wajen ƴaƴan nashi ya ƙarasa inda ya bisu ɗai-ɗai yana rungume su, suma cikin farin ciki suke.
Brr Farida ta shafa kan Abdus-samad tace;"nayi kewar ka sosai", shima cikin shagwaɓa yace; "nima ai kika tafi ki barni", taja kumatun shi tana faɗin; "kai ai ka fara tafiya ka barni", suka yi dariya duka.
Hannun su sarke dana juna suka ƙaraso inda sauran suke, Abdus-samad ya saki hannun Brr Faridar ya ƙarasa wajen mahaifin nashi suka rungume juna.
Dr Abubakar ya shafa kan Abdul ɗin yace; "Allah yayi maka albarka", Abdus-samad ya amsa da ameen, itama Brr Farida haka tabi yaran nata duka ta rungume su har da Fadila har tana tsokanar ta, Fadila kam murmushi kawai tayi.
Abdus-samad ya haɗa rai ganin sun nufi motar Tameer, Brr Farida tayi dariya tace; "sarkin kishi to muje na shiga taka", Dr Abubakar ya riƙo hannun ta yace; "gaskiya ban yarda ba, nifa kin ga kishi nake yi dashi", duka akayi dariya.
Abdus-samad ya shafa sumar kanshi yace; "shikenan kuje a tashi kawai", Brr Farida tace; "Surayya kije motar Abdus-samad ɗin".
Surayya ta zunɓuro baki tace; "ni wallahi ba zan shiga jar mota ba kamar wata ƴar shan jini", Brr Farida zata kuma magana Fadila tace; "Mummy ki ƙyale ta zo ki shiga ta Yaya Sameer ni bari naje ta Abdul ɗin".
Surayya ta shiga ta Sameer ɗin, Adnan kuwa yana wajen Mummyn shi, dan haka Sumayya da Fadila sune suka shiga motar Abdul ɗin.
Motar Sameer ɗin ke gaba sai motar Tameer sai ta Abdul, suna cikin tafiya Fadila ta kalli Abdul ɗin tace; "gaskiya yau kun birge ni".
Ya saki murmushi yace; "meya birge ki", ta ɗan kaɗa idanu tace; "yadda kuke son junan ku mana", Sumayya dake baya tace; "ai dama muna son iyayen mu sosai", Fadila ta jinjina kai tana faɗin; "na tabbatar da hakan".
Sumayya ta buɗe baki zata yi magana Babbar mota ta nufo inda suke, kan Abdul yayi wani yunƙurin kaucewa motar ta buge su.
Dr Abubakar ya kalli matar tashi, hannun ta ya riƙe yace; "na lura gangar jikin ki ke nan amma zuciyar ki na wajen Abdul".
Brr Farida ta ƙara kai kallon ta jikin madubin a karo na babu adadi tayi murmushi tace; "ka dena haɗa kanka da ɗana fa", kan ta rufe baki ta hangi abinda ya faru, cikin sauri tace; "innalillahi wa'inna ilaihir-rajiiuun.
Cikin sauri suka tsayar da motocin nasu, sai ga Brr Farida na gudu zuwa wajen motar tasu yau babu ƙasaita ba mulki ba gayu.
Duka su Daddy suma suka nufi wajen, can gefen titi motar ta faɗa kusa da wata bishiya, gashi wajen babu mutane kasancewar bayan gari ne basu riga sun shiga cikin gari ba suna kallo me motar ya gudu.
Da ƙyar aka iya zaro Fadila da Sumayya daga ciki, Abdus-samad kuwa sai da aka juya motar duk ta komatse, haka aka zaro shi kamar gawa.
Brr Farida ta faɗi a wajen sumammiya, Tameer ya kira abokin shi wanda ya kasance likita ne aka turo musu da ambulance, Sumayya kuwa dama ɗan kujewa tayi, Fadila kuwa hankalin ta na nan amma kuma gefen fuskar ta da hannun ta na dama duka jini ne, Abdul ne ko numfashi babu tare dashi.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*
📖📖29-30📖📖
Babu wanda hankalin shi ke jikin shi, koda suka isa asibitin cikin sauri aka wuce dasu *A&E* aka fara basu taimakon gaggawa. Daddy kuwa duk da kasancewar shi likita ya kasa taimakawa da komai.
Sumayya da Fadila aka yiwa dressing ɗin inda suka ji ciwo, har ita Fadilan aka ce ta ɗan kwanta domin ta huta.
Likitan ya fito yana cire handgloves ɗin hannun shi, da sauri suka bishi suna tambayar lafiya??.
Likitan yace; "Dr ka biyo ni Office", haka Daddy ya bishi, sauran kuwa ji suke kamar suyi tsuntsuwa su ji abinda ke faruwa.
Tameer ya zauna yana dafe kanshi, Sameer ya dafa shi yace; "ka dena damuwa Allah zai basu lafiya", Tameer yayi ajiyar zuciya yace; "yanzu wani sai yayi tunanin nina turo a kashe shi alhalin ba ni bane", Sameer ya girgiza mishi kai yace; "ka dena faɗin haka".
Cikin tashin hankali Tameer yace; "Sameer ko ma meye Abdul ɗan uwana ne kuma ba zan iya cutar dashi ba", ganin yadda hankalin Tameer ɗin ya tashi Sameer ɗin ya fara kwantar mishi da hankali.
"haba Tameer ai kowa ya san ba zaka taɓa iya aikata hakan a gare shi ba, domin kuwa ɗan uwa ya wuce wasa", Tameer dai babu abinda yake fata da buri banda Allah ya basu lafiya musamman ma Abdul ɗin wanda yake gani kamar shike da alhakin ciwon nashi.
Likitan yayi gyaran murya yace; "Dr ku kwantar da hankalin ku be wani ji mugun rauni ba, ya tafi doguwar suma ne saboda tsoratar da yayi, mun duba babu internal injuries a jikin shi, sai matar ka ita kam munyi mata allura domin ta samu ta huta kuma shima ɗin muna saka ran nan bada jimawa zai farka, Allah ya kiyaye gaba", Daddy ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha yace; "ameen yana me fita daga ɗakin".
Koda ya shiga ɗakin, suna kwance zaka iya tunanin barci ma suke, sai dai shi Abdus-samad ɗin hannun shi ɗaure da drip.
Sameer da Adnan suna jikin gadon mahaifiyar su, Tameer kuwa yana can zaune a gefe ne jikin window ɗin ɗakin tana kallon waje yanzu ya gama waya da Surayya yana faɗa mata abinda ya faru.
Daddy ya koma jikin gadon Abdus-samad ɗin ya tsaya, yana me tausayawa yaron wannan wane irin abu ne rayuwar yaron tana cike da hatsarrurruka gashi be san komai daga rayuwar shi balle ya dinga ƙoƙarin kare kanshi daga hatsarin.
Surayya ta buɗe ƙofa ta shigo hankalin ta a tashe, ta faɗa jikin mahaifiyarta tana sakin kuka sosai. Tameer da Sameer suke rarrshin ta dan Adnan ganin Auntyn shi tana kuka shima kukan ya fara Daddy kuwa ya kasa ce musu komai.